← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 158 OF 198

Sashe 158

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tinda ya ida wayar taji yai shiru baice komai ba saima k’urama fuskar wayarsa idanu da yai, tanaso ta tambayesa meke damunsa amma bazata iya ba, ta d’an saci dubansa a hankali har lokacin fuskar wayarsa yake duba, toh kodai ta tambayesa ne...? Tai tambayar ma zuciyarta... Kaman wanda yaji zancen zucin nata ya soma fad’in “Seriously, I’m exhausted... I’m tired of all this...” Ya d’an karkato sosai yana dubanta had’ida d’aura d’aya hannun nasa saman nata, yai crossing hannayen nasu cikin na juna kana yaci gaba da fad’in “Iyakacin abinda nake buk’ata a halin yanzu shine na kasance taredake, na k’yale dik wannan damuwa behind, and to be with you... In somewhere far away from here... Yanda babu stress d’in komai... Just....the two of us” Ya k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarsa had’ida k’ura mata idanunsa masu rikitar da ita.... Gaba d’aya sai jinta take wane iri haka nan, tai k’ok’arin k’ak’aro murmushi ta d’ago had’ida d’an dubansa kad’an... Saida ta d’an muskuta kana tace “Har yanzu babu wani labari gameda Akram...?”
Ya d’an fuzar da iska kana ya girgiza kai kad’an “Wayar da na gamayi kenan... Har yanzu babu wani tak’aimemmen bayani gameda case d’in nasa... Amma dai jam’an tsaro zasu tsananta bincike...” Shiru ne ya d’an ratsa tsakani kana yaci gaba da fad’in “Idan wani mugun abu ya sami Akram bazan tab’a yafewa kaina ba.... Na sani Akram bai kyauta ba ta wani fuskar... But dikda haka ya zab’i ya sanar damu gaskiya a ranar d’aurin auren koda ace bai fuskancemu ba, ya zab’i ya sanar damu ta wata hanyar, nida Akram are practically brothers, ina sonshi tamkar yanda nake son k’anina.... Idan wani mugun abu ya sameshi zanji a raina na kasa tsareshi ne... Shin kina ganin zan iya jagorancin Al’umma if I couldn’t protect my own family....? Why am I having this feeling now.... I feel like stepping down... Inaji kaman bazan iya...!” Ya k’arashe cikin murya mai cikeda nuna damuwa da kulawa....
Zulfa’u tai masa k’uri tana dubansa cikeda tausayawa... Lokaci guda ta d’an gyara zamanta kana ta soma fad’in “K’warai zaka iya, domin kaw kaid’in zab’in al’umma ne... Kai d’in su suka tsaida kai ba kai ka fito da kanka ba, hannunta ta d’aura saman nasa wanda ya sanyashi d’ago idanu yana dubanta, murmushi saman fuskarta taci gaba da fad’in “You are our choice... Kai ne zab’inmu a matsayina na number one fan d’inka...”
Murmushi saman fuskarsa yace “Did you say you are my number one fan...?”
Jinjina masa kai tai a hankali murmushi bai bar saman fuskarta ba.... Lokaci guda taci gaba da furta “Idan ka janye zaka breaking zuciyoyin d’inbin magoya bayanka ciki harda ni....”
Wannan karon murmushi mai bayyana hak’wara yai kana yace “Ban tab’a samun k’arfi gwiwa kan abinda nake nema ba irinta yau.... Thank you so much.. My number one...” Ya k’arashe yana mai k’ura mata idanu....
Murmushi kurum tai had’ida sadda kanta k’asa, nan ta sinkayo muryarsa yana fad’in “Sanda Akram yake zuwa wajenki, did you notice something about him...? Or maybe akwai wani wanda ya sanar dake suna samun sab’ani...? Na sani inada d’inbin masoya haka nan ina d’inbin ‘yan adawa masu son ganin bayana, so bazanyi mamaki dan sun tsare babban yaro na ba... Abinda ban gane ba a nan shine, idan har kidnappers ne suka sace Akram... Maiyasa har yanzu basu fara batun ransom ba... Wannan dalili yasa nake tinanin idan ba ‘yan adawanmu na siyasa bane suka sace Akram toh waye zai sacesa haka...? Ko kina tinanin tsohon mijinki zai iya aiwatar da hakan...?” Ya k’arashe in a serious tune....
Wannan karon saida k’irjin Zulfah yai wani irin bugawa... A fili ta furta “Ya Hafiz...!”
Ta d’ago tana duban Engr da shima ita yake duba.....
Lokaci guda ta shiga tino threats d’in da Hafiz ya dinga jifanta dasu hardai bata janye batun Auren Akram ba, cewa da ya dingayi idan har tana sonsa Toh fah saidai ta rabu dashi dan idan ba haka ba dik abinda ya masa ita ta janyo... Take taji zuciyarta na wane irin tsinkewa... Bata tab’a tsammanin Ya Hafiz zai iya cutar da mutum har haka ba dikda cewa tasan zuciya irin nasa amma baza tai tinanin he can go this far ba... Lokaci guda take girgiza kai tana mai furta “No... No Ya Hafiz bazai iya aikata haka ba.... Bazai iya sace mutum ba...!” Ta k’arashe fuska fal damuwa....
Kamo hannayenta Engr yai kana yace “Zulfa’u... D’ago ki kalleni....”
Zulfah ta d’ago idanunta masu rauni tana dubansa, lokaci guda yaci gaba da furta “If you know something zaifi kyau idan kika sanar dani ni kuma zan sanarda jami’an tsaro, yin hakan zai taimaka... Rayuwar Akram yana cikin had’ari.... Kuma idan har Hafiz zai iya aikata haka, now I understand maiyasa Akram zai nemawa kansa aurenki ba ni ba... Hakan yana nufin Akram ya min yak’in ne ba tareda sani na ba.... Now I understand... Shisa ya biyewa Muhibbah dan ya kaucar da hankalinta... Ya tari battle d’in shi kad’anshi.... Wannan shine irin soyayyar da Akram kemin....” Ya k’arashe yana duban Zulfah da tuni hawaye sun soma ciko idanunta... Engr ya kuma jinjina kai yana mai ci gaba da furta “Akram yanada reasons d’inshi da yasa yai abinda yayi... Yanzu na fahimta... Akram ba butulu bane kaman yanda kowa ya d’auka... Now more than ever bazan huta ba har sai na samo shi....” Ya k’arashe yana mai mik’ewa tsaye... Itama d’in tsaye ta mik’e hawaye na gangaro mata cikeda tsoro take furta “Ban tab’a zaton Ya Hafiz zai aikata mugun abu irin haka ba.... Ashe da d’an ta’adda nai rayuwan aure a baya... Ko da wasa ban zaci zai aikata mugun abu irin haka ba....” Ta k’arashe cikin tsananin kuka....
Kamota yayi had’ida mata masauk’i cikin jikinsa, lokaci guda yake shafa bayanta a hankali alamun lallashi yana mai kwantar mata da hankali... Saida ya tabbata tayi shiru kafin yai mata sallama ya nufi wajen Ammah da yaransa ma yai masu sallama kana ya fice yana kiran jami’an tsaro a waya.....
Yau d’in ya shirya sanar da Muhibbah cewa ita d’in tanada abokiyar zama a halin yanzu dikda baisan da wata fuska zata d’auka ba...
***

KADUNA

Tin jiya take mafarkai marassa kyau gameda Daddy da kuma Khalid, gashi cikin su duka biyun ta gaza samun layukansu, baccin rana da ta tashi yanzu ma mafarkin ne ya d’agata... Yanzu kam hankalinta yakai k’ololuwa wajen tashi, Daddy bai tab’a kwanaki haka bai kira yaji daga gareta ba, kai ko fad’a sukai zai sauk’o da kansa ya kirata, amma kam wannan abu da mamaki da kuma tashin hankali yake, shima Khalid da bai yini ya kwana ba tareda sunyi waya ba yau d’in dik bata jisa ba, ko jiya ma da sukai waya sama sama ya amsata ya katse kiran yana mai ce mata yana zuwa aiki ya taresa... Sai faman kumbura take tana sauk’e huci... A haka Siyama da Laila suka shigo da ganin Siyamar hankalinta a matuk’ar tashe yake.... Ammi na ganinsu a haka ta mik’e itama babu shiri....
“Ke ke lafiya....? Meke faruwa...? Ya na ganku haka....?”
Basu kaiga bata amsa ba Siyama ta bud’e murya taceda Sultan ya shigo.....
Mamaki ya kuma cika Ammi, duban Sultan tai dan kaw tsaf ta ganesa abokin Sameer ne.... “Yaya dai.... Lafiya dai koh....?” Ammi ta kuma fad’i tana dubansu su duka ukun.....
Sultan ya d’an duk’a yana gaidata....
Bata amsashi ba sai cewa da take “Wai lafiya na ganku haka nan....? Kaikuma uban wa ya baka izinin shigomin parlor...? Ke Siyama banson sakarcin banza tambayarki fah nake, uban me wannan abokin shashashan mijin naki ya shigo min har parlor.....?”
Siyama daketa k’ok’arin k’unshe kukan dake bakinta kama hannun Ammi tai ta zaunarta saman kujera lokaci guda take furta “Ammi kin sami Khalid d’in....?”
Ammi kanta ya kwance gaba d’ai.... Sororo take duban Siyama kana tace “Mai ya sami Khalid talk to me Siyama.... Wai meke faruwa ne...??”
Caraf ta sinkayo muryar Sultan yana fad’in “Hajiya babu abinda ya sami Khalid amma ya sami mijinki....!”

Da tsananin mamaki Ammi ke dubansa, kaucar da hannun Siyama dake rik’e da ita wacce hawaye ke bin k’uncinta tai kana ta mik’e sosai tana kuma dubansu musamman Siyama wacce hawaye ke kwaranyo mata....
Ammi ta isa gaban Sultan tamkar wacce zata shak’osa dan har saida tsoro ya d’an nuna a fuskar Sultan d’in....
Ammi tace “Maimaita abinda kace....”
Sultan da tuni ya d’an soma daburcewa yace “Mijinki ya sami had’arin mota a hanyarsa ta komawa Abuja daga Kano... Yana can babban asibitin birnin tarayya.....”
Bai kai aya ba Ammi ta shiga girgiza kai tana furta “A’a badai mijina ba.... Ina Khalid....? Khalid ya sani.....? Nasan bai sani ba shima, bai sani ba koh....?” Gaba d’aya ta daburce masu lokaci guda.... Siyama ta kuma rik’ota tana k’ok’arin calming d’inta saidai inaa Ammi fad’i take “Siyaaam Daddynki.... Daddynki Siyaaam kice min na cikin k’oshin Lafiya... Call Khalid right now... Just call him.... Bai sani ba shisa bai sanar damu ba koh....?” Ta k’arashe cikin murya mai matuk’ar nauyi... Lokaci guda kuma kaman wacce aka sinkara ta maidoda dubantaga Sultan tana kuma hura hanci take fad’in “Ta yaya zaka rigamu sani muna a matsayin family d’insa...? Ta yaya kaine zaka kawo mana wannan labarin...? Ta yaya zamu yarda ba k’arya ka guntula mana ba...??!”
Wannan karon Laila ce ta tari maganar.... “Ammi, ba accident d’in Daddy bane zai baku mamaki da tsoro daga ke har Siyama... Abinda zakuji yanzu shi zaifi komai baku mamaki da tsananin tsoro.....”
Daga Siyamar har Ammin juyowa sukai sosai suna duban Laila shaye da mamaki....
Siyama ta bud’e murya tace “Laila so kuke kuce mana Daddy bashi a raye...?”
Laila ta girgiza kai kad’an tace “K’warai Daddy yana nan a raye amma fah rai kwaikwai mutu kwaikwai sannan ba wannan ne nufi na ba da nace abinda zakuji gaba zai matuk’ar baku mamaki da tsoro....”
A harzik’e Ammi tai kanta tana fad’in “Ke banson salon iskanci da rashin kunya Ki bud’e baki Ki sanar damu abinda kika sani.... Meke faruwa...?”
Chapter 158 · 0% Book details