← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 198

Sashe 4

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

D’ago idanu Zulfah tayi tana dubanta, Aunty B taci gaba da fad’in “ki kwantar da hankalinki komai zai wuce ya zamto labari kinji koh, zuciyarki mai kyaune nayi imani bazaki dawwama cikin k’unci ba da yardar Allah....”

Jinjina kai Zulfah tayi a hankali kana tace “Na gode Aunty....”

Aunty B ta kuma murmusawa kana tace “Always remember that we’re here for you kinji koh....”

A hankali ta jinjina kai had’ida k’ak’aro murmushi kana suka kuma yin sallama sannan Zulfah ta wuce gida....

***

*Kaduna*

Yauma kaman kullum shiryawa sukayi cikin pajamas d’insu mai launi guda, saman gadon ta hauro yanda yake zaune yana aiki bisa computer d’insa...

Kiss ta manna masa a chick kana ta mak’ale cikin jikinsa bowl d’in crackers rungume a hannunta tana ci, ganin ya bada hankalinsa sosai ga aikin da yake ya sanyata sakin murmushi kafin ta d’au cracker guda ta shiga tura masa a baki tana fad’in “C’mon Partner open up, have som.... eat....”

Kaucewa yake yana fad’in “Oh no no Partner I don’t wan to, stop... I said stop...!”

Ina kaman cewa yake ta k’ara sai tsalle take akansa tana tura masa bakinsa....

Mirgino da ita yayi ya shiga mata cakulkuli ta ko ina su duka biyu suna dariya cikeda so da k’aunar juna....

Saida sukayi laushi gaba d’aya kafin ya janyota jikinsa suka kishingid’a, yatsunsu cikin na juna Sameer ke fad’in “You know Partner, I think Khalid was right.... Bai kamata idan mun samu matsala kad’an ki tafi gida ba, if we have problems kamata yayi mu solving matsololinmu just the 2 of us ba sai an samu third party ba ballantana yajega iyayenmu kinji koh, I want this to be first and last... Can you promise me Partner...”

Cikin sanyin jiki ta jinjina kai kana tace “I promise Partner, insha Allah hakan bazai sake faruwa ba... I’m sorry...”

Murmushi yayi kana ya manna mata light kiss a labb’anta kafin ya janyo laptop d’insa yana mai ci gaba da aikinsa...

Hannunsa ta kuma janyowa kana ta kishingid’a a jikinsa, idanu a lumshe take furta “Hey Partner, guess how much I love you...?”

Murmushi yayi had’ida kuma kwantar da kanta cikin k’irjinsa yana mai shafa kwantattun sumarta had’ida lumshe idanu...

“Must I guess...?” Ya tambaya still idanunsa a rufe...

Murmushi take tana duban kyakkyawar fuskarsa kana ta shiga janyo hannunsa tana fad’in “No no no don’t guess, come I wanna show you something...”

Sauk’owa sukayi daga saman gadon Siyama tayi d’igyalgyal ta rufe masa idanunsa da tafukan hannayenta, saida suka iso bakin window kana ta bud’e tapka tapkan labulaye da aka k’awata manyan windows d’in dasu, sliding glass d’in tayi fresh air ya bugi fuskokinsu duk da cewa akwai sanyin Air-conditioner a d’akin....

Kallon taurari dake baje iya ganinka a sararin samaniya tayi kana ta saki murmushi ta cire hannayenta daga fuskarsa, tsayuwa tayi gefensa suna fuskantar window su duka biyu kana ta sakalo hannunsa cikin nata...

Saitin kunnensa cikin sigan rad’a take fad’in “Open your eyes Partner...” Ta fad’i murmushi bai gushe saman kyakkyawar fuskarta ba...

A hankali ya bud’e idanunsa had’ida sauk’esu ga sararin samaniya yana mai shak’an dadd’an iska, Muryar Siyama ya katse masa wasu tunani da sukazo zuciyarsa lokaci guda...

Ta bayansa ta zagayo had’ida rungumarsa bata daina duban taurarin ba take fad’in “Ina sonka Partner iyaka yawan taurarin dake sararin samaniya....”

Murmushi Sameer yayi kana ya kaikaito suna fuskantar juna, yatsa yasa yana gyara mata kitsonta guda da ya sauk’o fuskarta, lokaci guda yake furta “And I love you without a limit Partner, much more than all those stars shining in the Sky.... I love you more than love itself, I love you more than my own life Siyaam...”

Tinda ya soma magana Siyama ta kasa daina kallonsa, batasan wani irin so Sameer ke mata ba, take taji k’walla na neman ciko idanunta, lokaci guda ta rungumesa tsam cikin jikinta tamkar mai tsoron kada wani ya k’wace mata shi...

Murya na rawa take furta “Partner I don’t know what I do without you... I love you....”

Rungumeta shima yayi cikeda sonta da k’aunarta.... A haka har bacci yayi gaba dasu....

***

Wajajen k’arfe 11pm ya shigo gidan yana faman huci, cikin bacci ta sinkayo muryarsa na faman doka mata kira...

A firgice Zulfah ta mik’e zaune zuciyarta na faman yankewa....

“Zulfa’u..!!!”

Ya fad’i a karo na hud’u, tsaki ya buga kafin ya nufi uwar d’akin....

K’iris ya rage bai bangajeta ba yanda ya turo k’ofar, matsawa gefe tayi fuska a tamke...

“Wani rashin kunyar kikaje kikayi a gidan Hajiya, sannan abin naki har yakai ki dinga d’ebo k’annen mahaifiyarki suna zuwa suciwa Hajiyata mutunci... How dare you Zulfah...?”

Tak’aitaccen murmushi tayi wanda yafi kuka ciwo kana tayi saurin gimtsewa, dubansa da kyau tayi kafin taci gaba da fad’in “First of all, kar ka saka k’annen mahaifiyata ciki, sannan meyasa baka tambayi Hajiya da k’annenka mai yakai Aunty B gidan ba... Kai kanka sanin kanka ne hak’uri nake da mahaifiyarka da k’annenka don haka kada ka kaini bango....” Tana ida fad’in haka tasa kai zata shige...

Shaye da tsananin mamaki Hafiz ke kallonta, shine Zulfa’u ke gaya masa magana haka, bai bari ta shigeba ya fincikota ta dawo da baya.....

*SameenaAleeyou📚*
[25/11, 16:42] +234 703 745 3539: *INDA RAI*
_................DA RABO_

*04*

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*

*Dedicated to my Trio ♥*

Cikin karaji Hafiz ke ci gaba da fad’in “Ni kike cema kina hak’uri da mahaifiyata.... Ni nake aurenki ko ke kike aurena... Idan kin mance bari na tuna miki Zulfah... Duk duniyar nan idan akwai mai k’arshen hak’uri toh kuwa shakka babu nine tinda kowa gudunki yake yana k’inki amma ni nayi hak’uri na amince da aurenki, na maki sutura, na baki matsuguni sannan nake ciyar dake.... Idan baki baki mance ba you’re nothing but a Curse to our family..... Shin bayan gata da na miki har kinada bakin magana...?!”

Tunda ya soma magana take zuban hawaye zuciyarta naci gaba da k’una da tafarfasa.... Muryan Hafiz ya kuma dakan dodon kunnuwanta sanda yaci gaba da fad’in “Daga ranar da aka haifoki a zuri’armu farin ciki suka gushe, mahaifanmu suka rasa wani sashe na kasuwancinsu, al’umman gari kowa ya yarda kece silan komai, tsiyane ke bibiyarki duk yanda kika saka k’afa, gashi nan babban misali akaina tunda kika aureni na kasa mallakar kasuwancin kaina da kaina, har yanzu mahaifina ke d’awainiya dani dake...”

Baikai aya ba cikin zuban hawaye ta katsesa da fad’in “Hafiz idan ka gaji da zama dani ka sallameni gaba d’aya, ka daina k’untata min kana cemin jeki gida kawai, ka bani shaidar tafiya gida mai tushe wanda idan na tafi babu mai dawo dani.... Ka bud’e baki kace na sakeki Zulfa’u.....” Ta k’arashe muryarta har na sark’ewa sabida tsananin kuka.....

Banda kallon banza baya watsa mata komai, saida ya d’auki wasu dak’ik’ai yana watsa mata kallon banza kafin ya buga tsaki ya shige yana fad’in “Aikin banza abinda kika iya kenan.....” Har yakai k’ofa ya dawo da baya yana mai nunata da ‘yar yatsa yake fad’in “And let me warn you for the last time... Wllhi wllhi kinji na rantse duk randa kika sake tattaran wata dangin mahaifiyarki kukaje kukaci mutuncin Hajiyata ranar ne zakiga kalana da baki tab’a gani ba....!”

Daga haka wucewa yayi ya shige uwar d’aki had’ida banko k’ofar da k’arfin gaske....

Zamewa tayi had’ida zama cikin kujera k’irjinta na mata zafin gaske.....”

Ita kuma kalan tata k’addarar kenan, wannan shine rayuwarta... A hankali ta zame cikin kujeran hawaye basu daina gangaro mata ba, a nan yanda take kwance bacci yayi gaba da ita....

Cikin dare take jiyo muryarsa a tsakar kanta yana doka mata kira, babu wani lank’wasa murya balle kalaman soyayya yake sanar da ita buk’atarsa, sannan da zai biya buk’atar nasa haka nan zai tsallaketa tamkar kuyanga aka ijiye masa... Wannan shine rayuwar gidan auren Zulfa’u, sam batasan akwai wata soyayya tsakanin miji da mata ba saidaima wani abu da yafi kama da k’iyayya....

***
Safiyar Washe gari...

Babu walwala a fuskarsa ya shigo parlorn, Marliya da Nabila zaune parlor Marliya na kallo yayinda Nabila ke karatu sabida jarabawarsu na k’arshen zangon karatu da suke fuskanta,...

A tare suka gaida mahaifin nasu saidai babu wani walwala ya amsa masu...

Da mamaki Abbah ke dubansu kana yace “Mai ya hanaku tafiya karatu....?”

Nabila tace “Abbah lecture free week muke sabida satin sama zamu fara exams....”

Jinjina kai yayi kana ya maido da dubansa ga Marliya yana jiran nata amsan...

“Abbah midterm break muke....”

Nan ma ya jinjina kai kafin ya k’arada “Ina Mamyn taku....?” A tak’aice....

A tare suka basa amsa da “Tana ciki Abbah....”

Gyad’a kai kurum yayi kafin yasa kai ya nufi uwar d’akin Mamy.....

Nabila da Marliya suka kalli juna don koda basu sani ba Mamani ce ta tinziro Abbah don ta had’asu fad’a da Mamy....

Nabila ta yab’e baki tace “Nifa wai sai naji mutane suna son Grannies d’insu suna wani jidasu ni kuwa wllhi Allah ya gani addu’a nake nawa ta mutu ko zamu samu peace cikin gidan nan....”

“Umm Mamani case....” Marliya tace sanda take kishingid’a cikin kujera had’ida rungume throw pillow....

Aiko daga yanda suke zaune suka soma jiyo muryar Abbah ta yanda yake shiga ba ta nan yake fita ba duk akan maganganun da Mamani ta kitsa masa gameda Mamy da Zulfah....

Nabila tayi jifa da handouts d’inta ta k’arasa jikin k’ofar sosai tana sauraren maganganun Abbah....

Marliya dai girgiza kai kurum tayi had’ida ficewa daga parlorn don batama fatan taji wani abinda zai d’aga mata hankali....

A bakin farandar Mamy Marliya suka kusan yin karo da Aunty Lami, ganin yanayin Marliyan ya tabbatar mata wani abin na faruwa...

“Lafiya Marliya ina zaki haka cikin fushi....?” Aunty ta tambaya....

“Abbah ke fad’awa Mamy nah kuma shirin gari ya waye nake kalla amma bazan iya ci gaba da kallo ina jiyo sautin fad’arsawa Mamy ba....” Ta fad’i kaman zatayi kuka...

Aunty ta janyota cikeda tausayawa kana tace “Kiyi hak’uri kinji Marliya kar kiyi kuka maza jeki parlor na kiyi kallonki, ki kalli tashan da kike so....”

Marliya ta jinjina kai kafin ta nufi parlorn Aunty....

Murmushi Aunty tayi kafin tayi saurin kimtsa kanta ta nufi parlorn Mamy....

Mamakine ya cikata ganin Nabila mak’ale jikin k’ofa ta manna kunnenta...
Chapter 4 · 0% Book details