← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 198

Sashe 59

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sawwama tai saurin tare gabansa cikin salo kana tace “Haba Hafizy ina zaka daga shigowa, Kausar dai bazata b’ace ba k’arewa gidanku take ba wani wajen ba, aidai ka tsaya kaci abinci ko Hafizy musamman na maka girki abinda kafi so...” Ta k’arashe tana shafar fuskarta cikin salo...

D’ago kai yai da niyyar magana Sawwama tai saurin d’aura d’an yatsarta saman labb’arsa tana mai furta “Shiiii karkace komai... Zo muje....” Ta k’arashe tana janyoshi har suka komo cikin parlorn... Lokaci guda ta zaunar dashi ta nufi kitchen ta had’o masa abincin da aka gama tsibbace shi da kayan tsibbace tsibbacenta na toshiyar baki...
Zaman dirshan tai tana basa abincin tana shafa kansa tamkar wani d’anta, cikin salo da mad’e taita cika ma Hafiz ciki da abincin da aka kawo mata daga can kantin Magajiya.... Aiko yana ida ci yaji kansa na juyawa kaman mai jin bacci bai wata wata ba dama ta samu tuni ta janyosa d’aki don dama a hannu take don da ace bai dawo ba da tuni ta tafi wajen Alhajinta wa’iyyazu billah.... Ya Allah kai mana tsari daga aikin danasani.... Da yawan matan aure sun halak’a sun fad’aga halak’a da tsananin fushi da tsinuwa ta Ubangiji, zinace zinacen matan aure ba zallan ‘yanmata ba ta yawaita a duniyarmu, mu sani irin wad’annan bala’u suna d’aya daga cikin abinda ke kawo annoba cikin Al’umma... Manzon tsira SAW ya fad’i mana zinace zinace bazatai yawa a doron k’asa ba har ya zamana ana bayyanata face Allah ya jarabci wannan al’umma da cutar da babu wanda ya tab’a sanin irinta... Muji tsoron Allah mu komaga Allah mu gyara tsakaninmu da Ubangijinmu sai Allah yaji k’anmu ya kawo mana d’auki, Allah Ka gafarta mana kaji k’anmu ka shiryamu da zuri’armu ta farkin addininka... Ameen ya Rabbi..!

***

Kan kace mai labarin mutuwar Kausar ya riski kowa idan ka d’auke mahaifinta, duk irin waya da Baba Alhaji mahaifinsa ke masa bai d’aga ba domin kaw tuni Hafiz ya b’ige da bacci, Sawwama na ganin wayar na shigowa saidaima tai tsuka ta katse kiran, k’arshe ma kashe ma kashe wayar tai gaba d’aya ta cilla gefe ta gyarawa Hafiz kwanciyarsa....
Iyakacin b’acin rai Baba Alhaji yakai, har shine Hafiz ke katse masa kira k’arshema ya kashe wayar gaba d’aya, lallai Hafiz ya cika d’ah maras tarbiya... K’wafa Baba Alhaji yai kana ya umarta liman da sauran jama’a dasu k’arasa da Kausar makwancinta domin kaw bazasu tsaya jiran tsammanin Hafiz ba....

SameenaAleeyou 📚

*INDA RAI*
_...............DA RABO_

*48*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Tareda Sameer akai komai, daga nan bai wuce gida ba don ko Siyama batasan da dawowarsa ba, kai tsaye asibiti ya nufa wajen Abbah....
Ya jima yana tsaye k’ofar d’akin yana duban Abbah daga yanda yake kwance k’walla na neman ciko idanunsa.... Sam Abbah baisan da zuwan Sameer d’in ba domin kaw idanunsa a lumshe yake, Sameer ya rintse idanunsa da k’arfin gaske hawaye suka kwaranyo masa domin kaw baisan ta yanda zai soma ba saidai d’ago idanun da zaiyi sukai ido hud’u da Abbah wanda ya masa k’uri babu k’yafta idanu.... Cikin sauri Sameer ya shiga k’ok’arin saita kansa yana goge hawayen da suka wanke masa fuska.... Cikin sauri had’ida d’an sassarfa ya soma shigowa d’akin lokaci guda yake k’ok’arin d’aura murmushin k’arfin hali saman fuskarsa....
K’ok’arin bud’e baki yake da niyyan gaida Abbah saidai kuma Muryarsace yaji ta sark’afe lokaci guda... Daga shi har Abbah kasa daina kallon juna sukai saima sabon hawaye dake k’okarin ciko idanun Sameer.... Lokaci guda bakin Sameer ya shiga rawa... Bai iya furta ko kalma guda ba sai rungume Abbah da yayi cikin wani irin shauk’i yana mai fitar da kukansa gaba d’aya.... Tsananin sanyi jikin Abbah yayi dukda cewa ba k’oshin lafiya bane dashi ga wani irin damk’a da Sameer ya masa yana mai jin kukan Sameer d’in har cikin zuciyarsa da ruhinsa... Gaba d’aya Sameer ya mance da condition d’in Abban, lokaci guda cikin muryar kuka yake furta “Abbah why...? Why Abbah... Meyasa kuka rabu dani, meyasa baku nemeni ba...? Meyasa kuka barni na rayu ba taredaku ba... Why Abbah....?”
Hannayen Abbah suka shiga rawa sosai sanda yake k’ok’arin dafa bayan Sameer cikin tsananin bugun zuciya....
Dukda rawan da hannun Abbah keyi bai hanasa k’ok’arin kamo kafad’un Sameer dake tsanin kuka ya d’agosa ba... Shima Abban kwantattun hawayene saman fuskarsa....
Cikin rawar murya Abbah ke furta “Ma’aruf...! Ma’aruf...!! Ma’aruf d’ahnah....!!!!” Lokaci guda ya kuma rungume Sameer da k’arfin gaske sai bursting cikin kuka da yayi... Suka k’ank’ame juna su duka biyun ko wannensu kuka yake sosai da kuka zuciyarsa....
Cikin kuka Abbah ke furta “Ma’aruf ka dawo...! Ashe zaka dawo garemu... Ashe zan sake ganinka..? Ashe kana nan raye d’ahnah... Mahaifiyarka tayi gaskiya datak’i aminta cewa ka mutu tunda jimawa... Ma’aruf ashe zaka dawo gareni.... Alhamdulillahi Alhmadulillah..! Allah na gode maka daka nunamin rana irin wannan kafin ka karb’i rayuwata... Allah na gode maka na gode...” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya yana mai kuma k’ank’ame Sameer cikin jikinsa....
Mamy dake daskare bakin k’ofa tai masu k’uri hawaye naci gaba da gangaro mata, tamkar mutum mutumi take takowa cikin d’akin idanunta basu daina duban Sameer ba tana hango Ma’aruf d’inta tun yana yaro har izuwa lokacin da ya b’ace mata....
Tsananin rawa hannayenta keyi sanda ta shiga shafa bayansa a hankali tana mai ci gaba da dubansa tana tuno rayuwarta da d’anta Ma’aruf, cikin rawar murya take furta “Zuciyata ruhina da gangan jikina bazasumin k’arya ba.... Tin daga randa na soma saka a k’wayan idanuna suka fad’amin cewa kaine.... Kaine Ma’aruf.... D’ah nah.....!!” Ta k’arashe cikin tsananin kuka da rawar jiki tamkar zata zube k’asa.... Cikin sauri Sameer ya tallafota lokaci guda ya rungume mahaifiyarsa su duka biyun suna kuka sosai, babu mai iya cewa komai cikinsu sai kuka da suke sharkaf da hawaye, sun jima a hakan kafin Sameer ya k’arasada mahaifiyarsa saman kujera ya zaunarta had’ida duk’awa gabanta... Ya rik’o hannayenta duka biyu yana dubanta cikeda ai da k’auna murmushi had’ida hawaye saman fuskarsa, lokaci guda ya kifa kansa saman cinyoyinta hawaye suna ci gaba da d’igo masa, itama Mamyn dafa kansa tai da duka hannayenta biyu hawaye naci gaba da d’igo mata....
Cikin sanyin murya yake furta “Mamy nah..! Mamy maiyasa kika bari suka rabani dake...? Why Mamy.... Maiyasa baki nemo d’anki ba, maiyasa kika bari muka kwashe shekaru sama da talatin bama tare Mamy why...?” Ya k’arashe yana mai kuma aje kansa saman cinyarta....
Cikin muryar kuka tana mai girgiza kai alamun a’a take fad’in “Ko kad’an d’ahnah... Ko kad’an bamuso rabuwarmu dakai ba saidai babu yanda muka iya da hukuncin mahaliccinmu, Ma’aruf d’ahnah ban tab’a cire ran cewa bazan sake ganinka ba daidai da rana guda.... A koda yaushe dakai nake rayuwa cikin zuciyata tsawon shekarun nan, d’ah nah ka yafeni ka yafemin....” Kuka yaci k’arfinta...

Sameer ya d’ago yana dubanta hawaye naci gaba da gangaro masa yake share mata hawayenta tsananin tausayi da k’aunar mahaifiyarsa naci gaba da mamaye illahirin zuciyarsa....
Abbah ne ya taso daga saman gadon da yake ya k’araso har gabansu yanai masu duba cikeda shauk’i, tinda yazo asibitin saidai a d’agasa amma sai gashi yau ya mik’e har ya tako da kansa... Haka nan yai tsaye had’ida masu k’uri yanajin yanayin da ya jima baiji irinsa ba a rayuwarsa, gaba d’aya ya had’esu ya rungume su duka ukun suna rungume da juna fuskokinsu d’aukeda hawayen annuri zukatansu cikeda tsan tsan farin ciki da annashuwa had’ida godiyawa Ubangijinsu maras misaltuwa da ya nuna masu rana irinta yau.....

***

“Daddy please zan bika...!” Tai maganar tana mai turo baki gaba had’ida rik’e hannun mutumin data ambato da Daddy....
K’uri ya mata fuskarsa cikeda taananin tausayi don yarinyar sosai ta saba dashi irin sabon da ya kamata tayida mahaifiyarta wacce sam bata samu hakan ba....
A hankali ya duk’a ya kamo hannayenta guda biyu yana mai share mata hawayen da suka kwaranyo mata...
Cikin muryarsa mai cikeda taushi yace “Baby kiyi hak’uri kinji wajenda zanje yara basa zuwa, kiyi hak’uri ki zauna da ‘yan uwanki da kuma Nanny kinji koh...”
Mak’e kafad’u tai sabbin hawaye suna zubo mata lokaci guda take furta “No Daddy I don’t wanna stay.... Please take me with you, I promise I’ll behave kaji please....”

D’an fuzar da iska yayi ba tareda ya kuma cewa komai ba a daidai sanda wani matashi mai kimanin shekaru 35 ya k’araso cikeda risinawa yana fad’in “Sir lokaci na gab da k’ure mana kasan sun maka shaidan mutum mai tsananin mutunta lokaci da cika alk’awari....”
A hankali ya jinjina kansa kana ya k’arada “Alright Akram... Zamu isa akan lokaci In sha Allah....”

Mutumin da ya ambata da Akram jinjina kai yayi kana ya fice, jim kad’an ya fito ya nufi taron motocinsa da ko wanne yana d’aukeda sunan MUTALLAB wajen da ake rubuta lambar mota....

Mutanen sai gaidashi suke kowa na k’ok’arin shigewa mota cikin sauri domin su d’au hanya, kai tsaye ya nufi mota guda wanda nake taammanin tasace, har ya iso jikin motar Akram bai sani ba, idanunsa a lumshe yana sauraren radio....
K’uri yayiwa Akram daga yanda yake tsaye yana duban yanda Akram ke sakin murmushi idanunsa a lumshe... Ya saki murmushi a hankali had’ida girgiza kai kana ya d’an k’wank’wasa gilashin motar da yatsun hannunsa guda biyu....
Cikin sauri Akram ya bud’e idanunsa had’ida d’an zabura kana ya bud’e lock d’in yana mai daidaita kujeran zaman nasa yake fad’in “Sorry Sir... Na d’an sha’afa ne....” Ya k’arashe yana mai sosa k’eya....

Murmushi ya saki a hankali kana yace “Akram kenan.... Mai kake sauraro haka....?”

Lokaci guda Akram ya bud’e sautin radio d’in da a baya ya rage kana yace “Shirin muryar ‘yanci nake saurare... Gaskiya gidan radio d’in suna k’ok’ari wajen sharhi da fashin bak’i kan abindake faruwa a gwabnatancen a k’asar nan.... Sir ya kamata ka fara sauraron shirye shiryen....”

Tak’aitaccen murmushi kurum yai kana yace “Toh banda abinka Akram idan ka saurara ai tamkar ni na saurara, besides kasan ban saba sauraren radio ba...”

Akram yace “Sir ya kamata ka fara sauraren irin wad’annan shirye shiryen domin ta haka ne zaka fahimci yanda siyasarka ta dosa tsakaninka da al’umma....”
Chapter 59 · 0% Book details