Sashe 131
Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un... Kalaman da Mamani da Abbah suke iya nanatawa kenan kurum..... Mamani ta had’iyi wani miyau da ya tokare mata mak’oshi da k’yar.... Ganin Mamani na k’ok’arin zubewa yasa Abbah saurin rik’ota Naja’atu na taimaka masa... Duban Naja’atu yai kana yace “Taimaka min mu k’arasa da ita can yanda babu mutane sai ki sanar dani komai...”
Naja’atu ta jinjina masa kai sukai yanda Abban yace, can gefe bayan sashen Mamani yanda babu kowa sai tabarmai yanda ‘yanmatan gidan sukai zaman yin k’unshi, nan suka samu suka kwantar da Mamani a wajen Naja’atu nai mata fifita suna binta da sannu itada Abbah...
Duban Mamani Abbah yanda take numfasawa da k’yar kana yace “Mamani zaifi kyau idan bakiji wannan labari ba, ki bari ni naji komai, hakan bazai kyau ma lafiyarki ba...”
Girgiza kai Mamani tai kana tace “Alk’ali zanji komai... Inaso naji komai, inaso naji wasu azzalumai ne suka jefamu cikin wannan uk’uba da k’unci tsawon rayuwarmu... Inaso naji komai Alk’ali...”
A hankali Abbah ya sauk’e ajiyan zuciya kana ya jinjina kai... Duban Naja’atu dake duk’e wajen tana kallon Mmani cikeda tausayawa Abbah yai kana yace “D’iyata muna saurarenki... Sanar damu mai kika sani... Daga ina kikaji kuma waye ya sanar dake....?”
Naja’atu tasa bayan hannunta ta goge hawayen da suka siraro mata, lokaci guda ta gyara zamanta kana ta shiga karanto iyaka abinda taji d’aga Hajiya Haule da mahaifinta Baba Alhaji da kuma Aunty Lami, ta kuma sanar dasu shirya aurama Sameer Sahariyya dasu Hajiya da Baba Alhaji sukai don su cimma burinsu na kawar da Ma’aruf a karo na biyu...
Tinda ta soma magana hawaye ke zarya a fuskokinsu gaba d’aya... Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un... Wannan wane irin al’amari ne, idan ance Haule da Lami zasuyi haka bazaiji mamaki ba sabida kishi...Amma Baba Alhaji fah... Ta yaya d’an uwansa zai masa haka...? D’an uwansa na jini... Yana ganin yanda suka rayu shekara da shekaru cikin k’unci da alhini na rashin d’ansu.... Shin wace irin rayuwa duniyar yau ta tsinci kanta ciki... Ace d’an uwanka na jini zai aikata maka mugun aiki irin wannan... Kaicon rayuwa mai cikeda mugunta da k’iyayya had’ida muguwar hassada da k’yashi.... Mamani dafe k’irjinta dake tsananin mata zafi kurum tai tana mai girgiza kai idanu a lumshe ga hawaye dake gangaro mata, lokaci guda take furta “Sun cutar damu... Sun zalunci baiwar Allah Mariya...Sun rabata da gudan jininta tsawon shekaru... Sunsa mun d’auki laifi gaba d’aya mun aza mata tsawon shekarun nan... Mariya ki yafeni... Ki yafe min baiwar Allah.....!” Ta k’arashe cikin tsananin kuka...
Naja’atu ma kuka take tana furta “Mamani Abbah ku yafeni... Tin kwanki naso sanar daku amma na kasa, banida k’arfin Zuciyar yin hakan har sai lokacinda nake tinanin lokaci ya k’ure... Ku yafeni su d’in iyayena ne...”
Saurin rungumota Mamani tai kana tace “Baki makara ba Naja’atu... Wannan sadaukarwa da kikai Kika zab’i ki sanar damu gaskiya dikda sanin cewa sud’in iyayenki ne, Ubangiji Allah ya saka miki da gidan Aljannah, ya baki rayuwa mai inganci a gidan duniya... Kuma yanzu da mukaji gaskiya jikana bazai had’a iri da Haule ba... Tashi kije abinki Allah ya miki albarka... Kinyi abinda ya dace...”
Jiki a sanyaye Naja’atu ta mik’e ta fice...
Mamani ta dubi Abbah tace “Ma’aruf bazai auri d’iyar Haule ba kaji na fad’i maka....”
Abbah ya jinjina kai ba tareda ya iya koda duban mahaifiyar tasa ba...
lokaci guda ya soma k’ok’arin Mik’ewa yana fad’in”Zanje na bada auren Nabilah da Zulfa’u, shi kuma Ma’aruf an fasa nasa auren....”
Dakatar dashi Mamani tai da fad’in “Babu aure guda da za’a fasa...”
Abbah ya dubeta da tsananin mamaki... Jinjina masa kai tai tace “Ince dama sabida ni ya amince da auren d’iyar wajen Haule...? Toh na tabbata dik wanda zan canza masa da ita baza’a sami matsala daga garesa ba... Kuma ina fatan hakan ya zame masa Alheri ya kuma izna da ishara gasu Haule....”
Jinjina mata kai Abbah yai kana yace “Dik yanda kikace Mamani...”
***
A yayinda ya rage saura mintoci a soma d’aurin aure su Khalid suka samu isowa, har yanzu ya kasa daina jinjina lamarin cikin zuciyarsa yana ganin abin tamkar mafarki... Ta ina layinsu Teddy Bear zai b’ace masa dikda cincirindon mutanen da yake hangowa tin daga bakin layin nasu... Ya dubi Daddy dake zauna gefensa Jafaru driver d’insa na jansu yayinda motar su Aunty Daula da yara Ke biyedasu... So yake ya tambayin Daddyn amma ya kasa saima sakin wani irin ajiyan zuciya da yakeyi... Like shin mafarki yake ko gaskiya, idan har mafarki ne baya fata a katse masa wannan mafarki nasa har sai yaga abinda ya kwancewa buzu nad’i... Shin dama aurensa da Nabilah Daddy Ke shiryawa all this while... Waidai da gaske ne abinda yake ganin na shirin faruwa...? Bai gama shan mamaki ba saida yaga su Baffah da wasu tsiraru cikin abokansu sun k’araso sunaima Daddy sannu da isowa... Khalid kaw aikama Baffah wata muguwar kallo yai wanda yake nufida ka jira had’uwarmu.... Baffah dai k’unshe dariyarsa yake yana kuma yima Daddy sannu da sauk’a, Khalid sai b’alla masa harara kurum yake yayinda sauran friends d’insu su Misbahu D’anisa suka k’araso suna zolayan ango... Ga wani annuri na musamman dake haska fuskar Khalid d’in....
A b’angaren Aunty Daula kaw tinda suka iso wannan gari gabanta ya tsananta fad’uwa, gaba d’aya wani iri takejin kanta ta rasa maike mata dad’i, a yayinda su Daddy suka shige babban parlorn Abbah Aamiru d’an wajen Baffah Wada yaimasu Aunty Daula jagoranci zuwa sashen Mamy, k’irjin Aunty Daula ya tsananta fad’uwa... Haka sukaita gaida mutane ‘yan biki hardai suka k’arasa cikin parlorn, yanda wasu Gwaggwanyen su Zulfa’u na can Kazaure suka tarbi su Aunty Daulan da Mamy basuma ganta ba abinka da hidiman biki...
***
A can parlorn Abbah kaw auren Nabilah da Khalid aka soma d’aurawa, sanda kunnuwan Khalid ya jiyo masa ana d’aura aurensa da Nabilah a hankali ya lumshe idanunsa, can k’asan zuciyarsa na samun wani natsuwa da bai tab’a samun irinta ba, siririyar hawaye ta gangaro daga idanunsa guda... Daddy dake dubansa taisayin Khalid d’in ya kamasa tabbas d’an nasa yasha gwagwarmayar soyayya... Allahu Akbar wannan shine INDA RAI tabbas DA RABO... Yau d’in Allah ya cika ma d’ansa wani babban buri cikin burikansa... Fatansa Allah ya albarkaci sabuwar rayuwar da d’an nasa ya tsinci kansa ciki a yau d’in....
Wani ikon Allah shine har wannan lokaci babu labarin zuwan masu auren Zulfa’u, abin har ya soma damun Abbah, ya waiga nan ya waiga can, ya dubi Baffah Wada su d’anyi magana k’asa sannan ya dubi Baffah Ado ma, su kansu duk abin ya damesu...
Hafiz ya k’araso had’ida ciro sadakinsa cikin aljihun babbar riga yana fad’in “Abbah na fad’a maka dama wannan d’an siyasan wllhi babban mak’aryaci ne yaudarar Zulfa’u kurum yai Abbah... Abbah ni ne mijin Zulfa’u, ni d’an uwanta ne Abbah... Abbah wllhi muna k’aunar junanmu ka taimaka ka maida aurenmu... Abbah kar mu bari mahassada su mana dariya...”
Mamaki ya cika illahirin mutanen dake wajen... Kallo ya koma kan Hafiz da Abbah, wani irin al’amari ne tamkar film suke gani na faruwa....
Tamkar gunki haka Abbah ya zubawa Hafiz idanu... Hafiz yaci gaba da sab’a babbar riga yanayin kalan tausayi dan jama’an wajen su tausaya masa... “Abbah Zulfa’u matata ce... K’addara ta rabamu kuma yanzu ma k’addara zata maida aurenmu... Abbah please ka duba lamarin nan ko dan ‘yanuwantakanmu kar ka bari bare suji kanmu.... Abbah ka dubi girman Allah kaji tausayinmu ka maida aurenmu... Wad’annnan mutane ba zuwa zasuyi ba...”
Baffah Wada da takaici ya ishesa nan ya katse Hafiz da fad’in “Kai Hafiz bamu son shashanci kanaji koh... Ya ranar auren yarinya zakazo da wani batu wanda hankali bazai kama ba... Mu k’ara masu lokaci Suna nan tafe na tabbata...”
Hafiz ya kuma sab’a babbar riga tamkar zararre ya isa gaban Baffah Wada yana fad’in “Baffah wllhi manemin auren Zulfa’u gawurtaccen mak’aryaci ne nai maka imani idan zamu kwana a nan bazai bayana ba, domin kaw aikinsa kenan Yaudara....”
Baffah Wada ya girgiza kai yace “Bama san hauka Hafiz ka tashi ka daina wannan rashin hankalin Naka...!”
Cikin tsananin huci Hafiz Ke duban Baffan nasa yana fad’in “Baffah dana kune ‘yan bak’in ciki kar matata ta dawo gareni...Toh Allah ya nuna min kuma kana gani za’a maida aurenmu... Idan ba mayaudari bane toh ina yake maiyasa bai bayyana ba, maiyasa bamuga masu amsar masa auren ba...Ina suke idan da gaske ne...?!!!”
Kaman daga sama suka jiyo wata murya mai cikeda k’warjini tana fad’in “Gamunan mun iso....!!”
Ba Hafiz da tuni ya daskare ba harta su Abbah da tsananin mamaki suka juyo suna duban bakin k’ofa....
SameenaAleeyou 📚
*INDA RAI*
_.................DA RABO_
*88*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*