← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 175 OF 198

Sashe 175

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin tsananin huci yake fad’in “Kin ko san mai kike fad’a Nabeela... Mahaifiyatace fah a ciki... Kuma ga dikkan alamu taimako take nema, tsananin soyayyar da take min yasa take cewa kada na shiga dan kar abindake cutar da ita cikin gidan ya cutar dani... Who knows meke faruwa cikin gidan..! I’m sorry Nabilah but I can’t just sit back and do nothing... My Mother needs me..!!!” Ya k’arashe yana k’ok’arin kaucarda Nabilah gefe.... Ammi ta kuma d’aura hannunta aka tana sabon ihu...
Cikin sauri Nabilah ta kuma shan gabansa tana kuka take fad’in “Ni zan shiga, you stay right here kaji... Ni zan shiga naga meke faruwa...!!”
Cikin rashin yarda yake girgiza kansa kana yace “Are you kidding me teddy bear...? Ta ya zan barki ki shiga cikin had’ari... Kema kinsan ko mafarki kike hakan bamai yuwa bane... Just stay right here kinji koh...!!”
Janyosa Nabila ta kuma yi tana kuka sosai take fad’in “Bakajin mai Ammi ke cewa ne... Dan Allah ka k’yaleni ni na shiga....!!!”
Wani irin tsawa ya daka mata da fad’in “Nabeeeelaa!!!! Just get out of my way...”
Bata matsa ba bata daina kuka ba... Ammi daga window tana hangosu tana kuka... Lokaci guda taceda Khalid... “Khalid kafin ka shigo gidan inaso kazo na fad’a maka wani abu... ka k’araso nan d’ah nah....!!”
Juyawa yai yana duban Ammi daga yanda take ta ramin window... Girgiza kai kurum yai kana ya nufi kiran Ammi...
Nabilah kaw yana shigewa ta arce a guje ta shige cikin gidan had’ida maida k’ofa ta rife kif... A kid’ime Khalid ya waigo ya nufo k’ofar yana doka mata kira inaaa ko saurarensa batai ba ta nufi kitchen wajen su Ammi..
Dik jijjiga k’ofa da kiran Nabilah da Khalid keyi bata sauraresa ba... Kai tsaye store d’in kitchen ta nufa ta bud’e su Ammi jikinta har lokacin rawa yake....
Ammi na hangota Ta k’araso a guje ta rungumeta tana kuka sosai take fad’in “Na gode... Na gode miki Nabila... Thank you for saving my son... Thank you Nabilah... Bazan tab’a iya biyanki ladan abinda kika min ba....!!!” Ta k’arashe cikin kuka sosai tana mai kuma kifa kai cikin jikin Nabilar...
Nabila dai gaba d’aya wane irin sanyi jikinta yai da ganin irin wannan bak’on al’amari daga wajen Ammi... Cikin sauri kuma Ammin ta mik’e tana fad’in “Maganin... Maganin... Muje mu share kafin ya shigo... Muje muje...!” Ta shiga janyo hannun Nabila tana tambayar yanda tsintsiya da sandar mop yake... Babu shiri Nabilah ta isa ta d’auko tsintsinya da sandar mop... Dik wani lungu da sak’o da Ammi ta barbad’a maganin nan saida suka share tsaf suka goge, Ammi harda bulbula ruwan hypo sosai dan tabbatar da ko burbud’in maganin bazai zauna ba....

Aunty Hanne ce ta fito fuska sharkaf hawaye cikeda borin kunya tazo zata wuce, Ammi ta d’aga mata k’eya tana fad’in “Allah shiga tsakanin na gari da mugu... Nidai daga yau na tuba kema Allah sa ki gane ki tuba Hanne...!”
Aunty Hanne dai mayafi a hannu ta fice jiki a matuk’ar sanyaye...
Ita dai Nabilah sai kallon wannan ikon Allah take... Abu saikace wani a film...
A k’ofar fita ta tadda Khalid wanda ke faman bugu Nabila ta bud’e masa... Tsaye yai yana duban Aunty Hanne cikeda mamaki saikace kazar da aka tsamo cikin ruwan zafi, tafiya ma da k’yar take ga zufa sharkaf jikinta... Cikin muryar kuka Aunty Hanne ke duban Khalid d’in kana tace “Saifullahi wallhi bazan iya kasheka ba kai kasan haka ai...!”
Da tsananin mamaki Khalid ke subanta kana yace “Kisa kuma Aunty..?”
Aunty Hanne na matsan hawaye ta shigesa ko zarafin amsa masa bata samu ba... Khalid ya d’an take mata baya yana kiranta amma inaa ko tsayawa Aunty Hanne batai ba saima Ammi data fito tagajan magajan tana fad’in “Kada ka bita... Ka dawo nan Khalid... K’yaleta Ta tafi kafin tai maka wani mugun abin... Aniyarki Ta biki Hanne... Wllhi idan Khalid ya rasa mata babu abinda zai da d’iyarki... A sauk’a lafiya...!” Ta k’arashe tana tafe hannaye...

Da tsananin mamaki Khalid ya waigo yana duban mahaifiyarsa, lokaci guda Ammi ta k’araso gareshi a guje ta shiga Shafa jikinsa tana fad’in “Babu abinda ya sameka dai koh....!!”

Khalid da mamaki ya kasa sakinsa girgiza kai kurum yake cikeda rashin yarda kana yace “Wai Ammi Wai meke faruwa ne... What’s all this....??”
Kasa magana Ammi tai sai rungumesa da tai hawaye na gangaro mata... Lokaci guda take furta “Khalid ka yafe ni... Ka yafe min d’ah nah..” Ta k’arasa ta janyo Nabilah ta had’esu duka biyu ta rungume tana fad’in su yafeta... Gabaki d’aya taananin mamaki ne ya cikasu....

Ammi na tsakiyarsu rungume dasu suka nufi cikin gidan, Nabilah da Khalid basu daina duban juna ba suna duban Ammi cikeda mamaki... Shigarsu gidan da kad’an su Aunty Daula dasu Aunty Bara’atu suka dawo....
Har lokacin Ammi hawaye take tana neman gafaran su Khalid....

Su Khalid basu ida shan mamaki ba saida sukaga Ammi ta nufi gaban Aunty Daula da k’irjinta ke tsananin bugu, ga mamakin Aunty Daula hannayenta Ammi ta kamo tana hawaye sosai take fad’in “Ki yafeni... Ki yafeni Daula... Nayi niyyar maki mugunta sai reshe ya tashi juyawa da mujiya... Na gina miki ramin mugunta keda ‘ya’yanki sai na tashi afkawa ciki nida nawa d’an.... Da ace yau na rasa Khalid tabbas da nima halak’a zanyi... Daula ki yafeni, wllhi na yarda abinda shuka a duniya shi zaka girba...” Take Ammi ta labarta masu dik abinda ya faru babu abu guda k’wakk’wara data b’oye masu...
Yesmin dake kallon wannan tashin hankali wani irin kuka mai tsuma zuciya ta fashe dashi... Aunty Daula ma kukan take had’ida kamo Ammi dake k’ok’arin duk’awa ta hanata k’arasawa...... Lokaci guda suka rungume juna suna hawaye sosai... Aunty Daula fad’i take “Ki daina bani hak’uri Ammi kema tabbas ba’a kyauta maki ba... Amma tuni Allah ya hukunta hakan... Ni baki min komai ba wllhi kuma nafi kowa jin dad’i da Allah ya k’addari kika fahimci hakan... Ubangiji ya yafe mu gaba d’aya ya kuma tashi kafad’un mijinmu..!”

Allah sarki duk wanda zaice bai kuka ba a parlorn nan sai wanda baida zuciya cikin k’irjinsa... Gaba d’aya baka jin komai sai sautin fitan kuka a hankali, harta Aunty Bara’atu saida k’walla ya zubo mata had’ida tausayin Ammi... Kai harta Kubura da Karimatu dake lab’e Daga k’ofar kitchen saida sukai hawaye... Allah sarki babu abinda yafi zaman lafiya yafiya da yad’a soyayya sama da k’iyayya dad’i a duniya... Hak’ik’a wane irin sanyi da aminci ne ya sauk’a a wannan ahali had’ida sakeenaah....

Aunty B ta k’araso ta kamo hannun Ammi da na Aunty Daula tana hawaye itama kana tace “Alhamdulillah...! Mijinku zaifi kowa Farin ciki idan yau ya tashi ya wayi gari ya ganku haka... Yau Allah ya cika masa burinsa...!”
Ta juyo tana duban Aunty Daula sosai kana tace “Daula banida haufi akan zakiyima abokiyar zamanki biyayya a matsayinta na wacce ke gaba dake a haife da kuma a zamantakewar aurenku...”
Cikin sauri Aunty Daula ke jinjina kai tana hawaye alamun tabbas hakane...

Aunty B Ta maida dubantaga Ammi kana taci gaba da fad’in “Toh nima dai zan rok’i yafiyarki Ammi... Amma kafin nan inaso na sanar dake zuciyata taji wasai sanin cewa abokiyar zaman ‘yaruwata ta fahimci gaskiya kuma ta gane cewa Allah shikeda cikakken iko akan komai ba boka ko Malami ba... Allah shike k’addarawa kuma shike badawa ya kuma hana ga wanda yaso... Boka ko Malami basu isa suyi maka abinda Allah bai maka ba.. Basu isa su hana faruwan abinda Allah ya riga ya hukunta ba...”
Ammi na hawaye take jinjina kai tana fad’in “Wannan haka ne Bara’atu.. Wllhi na yarda kuma na tuba tuba na gaskiya..!”
Aunty B tace “Alhamdulillahi... Tinda kin fahimci haka... Yanzu zan sanar daku dik yanda abin ya faru...!”
Gaba d’aya sukai jigum suna duban Aunty B had’ida saurarenta....

Nan Aunty Bara’atu ta labarta masu dik yanda abin ya kasance... Sukaita al’ajabi wannan hikima irin na Aunty B da hangen nesanta... Lallai ita d’in ta cika jajirtacciya wacce takai a yaba mata... Cikin salama ta wargaza mugun nufin su Ammi kuma tayi k’ok’arin karkatoda hankalinsu da tinaninsu zuwaga fuskantar gaskiya da kuma k’auracewa sab’o...

Kubura da shashashanci daga yanda take tsaye ta k’yak’yace da dariya tana fad’in Inama tana wajen.... Ganin kowa yaimata zuru yana dubanta ya sanyata had’iye sauran dariyarta had’ida kame bakinta da duka hannayenta biyu saidai ita kanta Ammin dariya sosai abin ya bata musamman data tina yanda take rok’on gafara...
Shiko Khalid d’an darawa yai kad’an kana yace “Aiko da na shigo kin rasani gaba d’aya kin huta...”
Ammi ta janyo hannun Nabilah tana fad’in “Toh ai ga savior d’inka kana tafe tareda ita, yanzu na yarda na tabbata banida matsala indai wannan heroin d’in tana tareda kai....!” Ta k’arashe tana mai rungumo Nabilah dake sanne kai had’ida k’unshe dariyarta cikin jikinta....
Gaba d’aya wannan karon d’an darawa sukai kana Ammi taci gaba da fad’in su Khalid da Nabila su yafeta kuma in sha Allahu bazata sake zama matsalaga rayuwar aurensu ba... Su Kubura babu kai nan ta had’e hannayenta biyu waje guda ta shiga tafawa ita dole nuna murnanta take Ammi zata k’yale Khalid yai rayuwarsa da matarsa cikin salama, dan ita ko bata samesa ba ta gwammaci ta gansa yana rayuwa cikin Farin ciki...

Yesmin kaw jikin a sanyaye ta k’araso ta duk’a gabansu tana hawaye sosai, lokaci guda take rok’on Khalid da Nabilah gafara.... Hannayenta biyu had’e waje guda take ci gaba da fad’in “Ya Khalid dan Allah ku yafe min, ku yafe min dik abubuwan da nai maku... Especially you Nabila... Dan Allah ku yafe min, na yarda Allah shike jefa soyayya cikin zukatan mutane... Na yarda haka Allah yaso ya gina soyayyar junanku cikin zukatanku... Ku yafe min katsalandan da naitayi ma rayuwarku da tak’ura maku da k’ok’arin raba tsakaninku... Dan Allah ku yafe min...!”
Nabilah ta janyo hannayen Yesmin tace “Ban tab’a rik’eki ba cikin zuciyata Yesmin... Allah ya yafemu gaba d’aya... Nima ki yafe min wasu abubuwan da nai maki...” lokaci guda Yesmin ta rungume Nabila tana hawaye sosai...
Chapter 175 · 0% Book details