← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 198

Sashe 114

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

D’an dafa fuskarta kad’an yai suna shak’ar numfashin juna kana yace “Ji nake kaman kar na tafi na barki Daula...” Yai maganar yana mai rik’o hannayenta su duka biyun suna fuskantar juna....Murmushi ta sakar masa kana tace “INDA RAI wata rana zamu kasance tare gaba d’aya babu b’oye b’oye like a one big happy family, In sha Allah...”
Murmushi bai bar saman fuskar Daddy ba ya kuma kai tafin hannunsa ya shafi gefen fuskarta na dama kana yace “I can’t wait for this moment to come... Ina rok’on Allah yasa Yana nan kusa...”
Su duka biyu sukai k’uri suna duban junansu na d’an wani lokaci kana Daddy yace “Ni zan wuce Kaduna, duk yanda abun ya kasance zan kiraki na sanar dake komai, for now inaso ki gama sayyayan duk wasu abubuwa da ake buk’ata,akwai number k’anwar mahaifiyar ita Nabilar da Sameer ya tura min sai ki kirata ku tsara komai ki kuma tambayeta wasu abubuwan...”
Aunty Daula ta jinjina kai tace “Shikenan, zan kirata in sha Allah sai mu tsara komai...”
Hannayensa Daddy ya bud’e mata kana yace “Come here...”
Cikeda kunya ta k’arasa ta shige cikin jikinsa... Suka k’ank’ame juna tamkar su dawwama a haka ba tareda wani abin ya gitta tsakaninsu ba, haka Aunty Daula ta rabu da mijin nata cikeda bege da alhini...

***

Gaba d’aya yau d’in Yusrah bata gane kanta ba, ta kuma zama wata sukuku da ita haka nan, har suka fito daga second class d’in tana nan haka sukuku, babu wani abinda ta fahimta, ganin abin take tamkar a mafarki Wai ita ake batun aurensu da Khalid kuma har an saka rana lokaci guda dana Yayanta Ma’aruf, abinda yafi bata mamaki shine tinda akai maganar auren Khalid bai nemeta ba, bai kuma sanar da ita komai ba.. Mai hakan yake nufi...? Ta lumshe idanunta a hankali tana mai zama bisa carpet d’in masallacin..
Yusrah da tuni ta d’auro alwala zama tai gefenta tana zira safarta dara cire sanda zatai alwala lokaci guda take maganawa Nabilar... Ganin hankalin Nabilah bai tareda ita ya sanyata d’an dungurinta kana tace “Ke Wai meyene haka, tin safe kike haka nan... Wai meke faruwa ne, kinga d’azu a class k’iris ya rage wannan d’an rashin mutuncin bai koreki daga ajinsa ba, wai dan Allah meke damunki....?”

Idanu Nabilah ta zuba mata kana ta sauk’e ajiyan zuciya kad’an tace “Wai aurena ake shirye shirye... Could you imagine...”
“No.... Are you serious...!” Yusrah tace sanda take mik’ewa tsaye cikeda murna harda sakin k’aran murna gaba d’aya ta mance masallaci suke har saida Nabilar ta janyota had’ida d’aka mata duka tace “Ke bafah a class kike ba....”
Yusrah ta zauna tana mai ci gaba da fad’in “Ke Wai da gaske kike....? Aure with who....?” Lokaci guda kuma taci gaba da murmushi tana nunata da d’an yatsa take fad’in “Wllhi da shine... I’m certain dashi ne.... Haladu na Mamani... Wayyo angon teddy bear... Allah yayi, wllhi dama kunyi masifar dacewa...”
D’an tsuka Nabila tai kana tace “Bansan misa Abbah ke hanzarin ya aurar dani ba saikace na tare masa wani abin...Kuma shi d’an rainin hankalin ko wayarsa ban sake ji ba ko ma waye zai jida kai oho....” Tai maganar cikin fad’a...
Yusrah na murmushi ta dafata kana tace “Kan ango yayi zafi toh ki kirasa kiji lafiyarsa mana....”
Wani uwar hararanda Nabila ta b’alla mata ya sanyata had’iye sauran zancen... “Kar Allah sa yayi lafia idan sai na kirasa, kema kinsan idan za’a shekara a haka bazan kirasa ba, kuma bazan nuna masa nasan komai gameda batun auren ba... Ke ni haushi ma yake ban wllhi...” Ta k’arashe tana mai mik’ewa tsaye da zummar d’auro alwala... Yusrah ta murmusa tace “Ah lallai na yarda abin yazo... Allah huci ran Amarya...”
Harara Nabilah ta galla mata ba tareda ta kuma cewa komai ba don harga Allah wani irin mugun haushin Khalid d’in takeji...

Koda ta koma gida ma Mamy da Aunty B ta tadda nan suna zancen, fuska a tamke ta gaidasu don gaba d’aya har mutanen gidan nasu haushi suke bata, ji take kaman ta nufi parlorn Abbah ta sanar dashi cewa itafah bata amsa auren Khalid ba toh amma rashin kunyar nata baikai nan ba, Koda ta iska Marliya a d’aki tsiya ta dinga mata musamman data fahimci ko labarin Bikin bata k’aunar ayi...
A can parlor kuwa Aunty Daula ce ta kirawo layin Aunty B Dan su samu su tattauna maganar kawo lefe da sauransu...
Da sallama Aunty Daula ta soma cikin siriryar muryarta mai dad’in saurare... Wani irin fad’uwan gaba Aunty Bara’atu ta tsinci kanta ciki ba tareda sanin dalili ba......

SameenaAleeyou 📚

*INDA RAI*
_................DA RABO_

*81*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Sun ida wayar sun samu matsaya kan cewa ranan biki ma’ana ranan d’aurin aure sai su taho da lefen gaba d’aya, wani ikon Allah harta Mamy ma wani irin yanayi ne mai wuyan fasaltuwa ta tsinci kanta ciki sanda tai maganada abokiyar zaman mamar Khalid, muryarta baida maraba data marigayiya mahaifiyarsu, tamkar marigayiyace ke magana haka nan sukaji sautin muryar...
Aunty B ta numfasa ta dubi Mamy tace “Muryar matar nan sai ya min kaman nasan mai irinta amma na kasa gane ina san mai irin muryar...”
Sauk’e nannuyan ajiyan zuciya Mamy tai kana tace “Muryar Hajja Mama naji a tattareda matar can... Babu abinda ya raba muryarta data mahaifiyarmu....”
Numfasawa Aunty Bara’atu tai kana tace “Allah mai iko, shisa na kasa gane ina nasan mai irin muryar ashe dai irin muryar Mama Hajja gareta, kinsan ni ban wani san Mama Hajja sosai ba ina k’arama Allah yai mata rasuwa....”
Take fuskar Mamy ya soma sauyawa, abubuwan da suka faru a wancan shekarun suka shiga dawo mata, k’walla masu zafin gaske suka ciko idanunta, dafa hannayenta Aunty B tai kaman zatace wani abu sai kuma ta kasa don ko shakka babu dukda juriya irin tata itama d’in sai ta kasa magana, zuciyarta tai rauni sosai, a hankali ta mik’e ta nufi waje ba tareda ta iya furta koda kalma ba....
Aunty Lami dake lab’e tana dubansu, murmushi ta saki a hankali tana mai ayyanawa cikin zuciyarta “Muddin Aminiyar Sirri tana tsakani bazaku tab’a kasancewa cikin farin ciki ba koda kuwa zaku nunawa duniya cewa cikin Farin ciki kuke, can a k’asar zuciyarku bazai kasance haka ba domin kaw wata gyambo ce da batada magani can k’asar zukatanku...” Ta kuma murmusawa kafin ta juya sad’af sad’af ta koma sashenta...

***
Chapter 114 · 0% Book details