← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 198

Sashe 86

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aunty Lami dake lab’e jikin window wacce tin shigowar Baba Alhaji tazo jikin window d’in ta mak’ale don taji komai, zuciyarta banda k’una da tafarfasa babu abinda yake sanda taga farin ciki da kalan soyayya da Abbah ke nunawa Mamy.... Ta kuma d’ingile k’afa tana aikin lek’ensu yanda ta hango Mamy ta tsiyayawa Abbah ruwan shayi yana sha yana kuma jifanta da kalamai masu dad’in sauraro ga duk wanda ake fad’iwa....
K’walla da takaici sukaima Aunty Lami diran mik’iya, har saida tai datasanin lek’ensu.... Ji take kaman ta isa ta shak’e Mamy ko zata sami sanyi cikin zuciyarta... Duk abubuwan da tai ganin ta dasawa Abbah tsanar Mamy ciki harda salwantar da Ma’aruf sam basuyi aiki ba tsawon wannan shekarun, soyayyar Hannatu sam bazai gushe zuciyar Abbah ba... Hawaye masu zafi suka shiga keto mata sanda ta hangi Abbah na baiwa Mamy shayi ta yanda bakinsa ya goga jikin kofin... Mamy na nok’ewa tana darawa yayinda shi kuma Abbah ke kuma janyota yana mai magana k’asa k’asa wanda bata iya ji.... Shikenan Hannatu Farin cikinta ya dawo,gata da yaranta gaba d’aya a tattareda ita, ga soyayyar miji dana yaranta kai harma da duk wani wanda ke tarayya da ita, itako batada tsuntsu batada tarko, hasalima idan asiri ya bayyana cewa tana d’aya daga cikin wanda sukaso ganin bayan Ma’aruf kashi da shara sai sunfita daraja... Take taji batak’i taga gawan Mamy ba kowama ya huta.... Wani irin jiri ne ya kusa kifawa da ita ganin Abbah tsofai tsofai na nunawa Mamy soyayya da kulawa a shekarunsu na tsufa wanda ita koda wasa ko a baya da takeda k’uruciya sam bai tab’a nuna mata ba.... Ji kake Dimmm ta fad’o daga saman dakalin dake jikin window d’in da take lek’ensu... Babu halin tai ihu don kada su jiyota, ga uban azaba da takeji don da k’yar idan bata cire k’ugunta ba.... Tanajin sanda Abbah ya taso yana lek’en ko wani abin ne ya fad’i... Haka ta matse bakinta da hannayenta da iyaka k’arfinta tana mai tamke idanu had’ida mak’alewa jikin garu don kar ya ganta... Har saida taji juyawan Abban kafin ta lallab’a da jada ciki ta nufi sashenta, Allah ya rufa mata asiri bata ci karo da kowa cikin yaran gidan a hanya ba....

***

Sahariyya da Hajiya su duka biyun tare suke jinya, Hajiy fuska a kumbure ga jiki duk tabo, ita kaw Sahariyya k’afafu a d’aure sabida tun bugun da Hafiz ya mata bata warke daga kariyan data samu a k’afa ba, shi kaw Hafiz yana can asibiti yana nasa jinyar....
Naja’atu ita ce a tsakani tana taimaka masu....
Hajiya taci gaba da fad’in “Wacce duk ta dace Ma’aruf ya zab’eta ta more miji cikinku, gashi gangariya gashi likita....”

Sahariyya dake faman washe baki tai saurin taran zancen Hajiya da fad’in “Ai Hajiya ni zai zab’a ma don nafi dacewa dashi kuma ma ai nice babba ni ya kamata a bashi matsayin mata...”

“K’ya dai tsaya ya zab’a da kanshi cikinku....” Hajiya tace sanda take kuma fifita fuskarta da mahuci....

Sahariyya ta b’ata fuska tace “Hajiya Wllhi gwarama kiyi fatan ya zab’eni don Wllhi duk wacce ya zab’a ba bari mata zanyi ba babu ruwana da cewa ita k’anwatace....”

Tinda suka soma zancensu, Naja’atu dake zaune gefe da lantern tana karatu kasancewar babu wutar nepa batace dasu komai ba sai sannan ta rufe littafinta tace “Addah Sahariyya da ma kin kwantar da hankalinki don indai nice Wllhi bana fatan a lik’ani ga wani namijin da baisona, saikace wacce ake neman kai da....” Ta k’arashe tana mai kuma bud’e littafinta.....

Sahariyya ta harzuk’ota da fad’in “Dilla rufewa mutane baki yarinya, wa zaiga gaye kaman Ya Ma’aruf yace baiso, dama mai zaiyi dake k’arama dake wacce baki jima da soma k’irgen dangi ba, ko a k’afa aka aura masa ke wllhi kwanceki zai ya gudu..... Ni ce nan na dace dashi....”
Ta k’arashe tana juya idanu daga yanda take zaune....

Girgiza kai Naja’atu tai kana tace “Allah shi kyauta ya baki sa’a yasa kada Ya Ma’aruf yace baki masa ba... Dear sister...” Ta k’arashe tana mai kuma duba littafinta...

Haba nan fah Sahariyya ta hau sababiga ‘yar uwarta har saida Hajiya tasa baki.....
“Banaso kuna samu banbancin ra’ayi, gaba d’aya Naja’atu kin zama munafuka.... Kina nema ki juyawa ‘yan uwanki baya, Wai har tarewa kike ki tafi wajen mayyan can Raihanah.... Toh kici gaba kar ki fasa..... Shashashar banza wacce batasan yanda ke mata ciwo ba....”

Da tsananin mamaki Raihanah ke duban Hajiya, har itace Hajiya ke kira munafuka bayan taji bak’in k’ullin da suka shirya itada Alhaji wanda badon tana tsoron rasa iyayenta ba da tuni ta fallasasu kowa ya sani.... A hankali ta girgiza kai cikin zuciyarta tana addu’an shiriya ma iyayen nata...
Ana a haka Baba Alhaji ya shigo tagan magajan sai bambamin bala’i yake....
Hajiya ta tareshi da fad’in “Yaya yaya meke faruwa.... Ya na ganka haka nan.....”

Cikin huci yake furta “Ai komai ma ya faru.... Wai har nine Usman zai dubi tsaban idona yace baiyi na’am da shawarina ba.... Wai shi bazai kuma tilasta yaransa cikin aurenda basa so ba... wata tsiya wata tsiya, ke kijimin yaron nan.....”

Hajiya dake dubansa ido a kanne cewa tai, “Yo ai kaine baka iya ba, cewa zakayi ka bada tinda daga yaran nasa har naka kanada iko dasu, nifa ko ba’a sulhunta auren Zulfa’u da Hafiz ba to fah ya zama dole a had’a auren Sahariyya da Ma’aruf....”

Hajiya bata rufe baki ba Sahariyya tace “Yauwa eh wllhi Hajiya....”
Baba Alhaji ya watsa mata harara yayinda Najah ta mik’e ta bar tsakar gidan sabida tsaban takaici, ta gwammace tasha zafinta a d’aki data zauna sauraren kayan bak’in cikin ahalinta.....

****

A can asibiti wajen Hafiz kuwa bacci yake yana mafarkin abin k’aunarsa Zulfa’u,fuskarsa ta cika da annuri cikin baccin nasa, farkawar da zaiyi sukayi idanu hud’u da abokinsa Magaji....
Magaji ya sakar masa murmushi had’ida masa sannu da jiki.... Hafiz ya amsa yana mai bud’e idanunsa gaba d’aya.... Lokaci guda kuma ya d’an lumshesu kana yace “Batazo ba...?”

Magaji yace “Wa fah....?”

“Zulfa’u...” Hafiz ya fad’i idanunsa na kallon sama....
Girgiza kai Magaji yai kana yace “Wai har yanzu bazaka sarara da tunanin Zulfa’u har ka sami lafiya ba....? Haba Hafiz kodai bakaji abinda likitoci sukace bane.....”
Lumshe idanunsa yai a hankali kana yace “Magaji idan kaga na cire tunanin Zulfa’u toh ka shaida shakka babu na daina numfashi ne... Numfashina yana ficewane tareda tunaninta... Magaji ban tab’a zaton ina k’aunarta har haka ba... Zulfa’u itace rayuwata domin kaw tin daga lokacin data bar cikin rayuwata ban kuma samun natsuwa da kwanciyar hankali da na kasance cikinsu a baya ba... Kai shaida ne...”

Magaji ya jinjina kai a hankali kana yace “Duk naji wannan amma ka d’ibar mata lokaci kaima ka sami sauk’i tukuna....”
Wata duba Hafiz ya watsa masa kana yace “Inaga dai baka fahimci abinda nake nufi bane... Na k’agu su sallameni a wajen nan na tafi na maidoda matata... Nifah idan basu sallameni cikin satin nan ba Toh fah gaskiya zan sallami kaina....”

Magaji ya d’an murmusa kana yace “Lallai ka sami sauk’i abokina tinda har kake fad’in haka...” Shigowan Likita ya katse masu zancen....

***

Koda Aunty Lami ta isa d’aki da k’yar da jin jiki, nan ta nemi man zafi ta shafe kwankwasonta yanda ta buga, ga k’afarta guda da tuni tayi fushi ta kumbura abu kaman wasa....

Bayan kwanaki biyu aka sallami Hafiz ya koma gida, a b’angaren Baba Alhaji da Abbah kuwa sam babu sararawa a batun da Baba Alhajin yazo dashi, gaba d’aya ya d’aure Abbah da jijiyoyin jikinsa, Allah ya sani bai kasance mai tirjiya da tsaurin idanu ga na gaba dashi ba, Abbah irin mutanen nan ne da idan na gaba dasu yace ga yanda za’ai toh fah bai iya tsallakewa sannan bai iya cewa a’a, har yanzu dai bai fayyace ya wacce ya baiwa Sameer cikin yaransa ba sannan shima Sameer d’in sam baida wannan labarin, a b’angaren Zulfa’u kuwa Aunty Bara’atu dole ta kuma d’auketa daga gidan ta maidata nata gidan ganin idan ta barta gaban Abbah da Mamy Baba Alhaji na kuma sake aura mata Hafiz wanda a yanzu kusan baida buri da ya wuce yaga ya kuma mallakar matarsa Zulfa’u....

Yau tana zaune tsakar gida tana duba wasu takardun, shirin da zata gudanar safiyar washe gari idan Allah yakai rai sai jin ana knocking tai.... Tasan kuma dai ba Aunty bace ta dawo don da itace da horn d’in motarta zataji.... Kira ta shiga rangad’awa Safinatu mai aikin Aunty B, Jim kad’an Safinatu ta iso tana fad’in “Gani Aunty Zulfa’u....”

Zulfah tace “Ki duba gate kaman knocking ake...”

Safinatu ta amsa kana ta shige duba gate....

Zulfah ta maida hankalinta kan aikin dake gabanta.....
Tana cikin duba wani k’aramar takarda ne a hannunta tana rehearsals kawai sai hango k’afafun mutum tai yana shigowa.... Tai saurin d’agowa don tabbatarwa don tasan shi kad’aine mai irin wad’annan k’afafun....Tai saurin rintse idanunta cikeda takaici don ko jiya ma saida ya bita har wajen aikinta...

Safinatu ta k’araso tana fad’in “Aunty Zulfa’u nace dashi Aunty Babba bata nan amma yace shi wajenki yazo....”
Zulfah ta jinjina kai kana taceda Safinatu “Jeki kawai....”
Safinatu ta shige abinta....

Take ta had’e rai tamkar ba Zulfa’un da ya sani ma’abociya sakin fuska da son mutane ba....
“Ya Hafiz mai kuma ya kawoka gidan nan fisabilillahi... Sanin kanka ne idan Aunty ta dawo ta taddaka gidan nan bazai maka kyau ba ko nace bazai mana kyau ba....” Ta k’arashe maganar tana mai warware gyalen abaya dake d’aure kanta ta yafe shi zuwa kafad’unta...

Farar kujera dake gefe ya zauna bisa kana yace “Wannan itace irin tarban da zakiwa mijinki...?”

Girgiza kai Zulfah tai kana tace “Kana mancewa nifa ba matarka bace... Don girman Allah ka daina bibiyata kayi zamarka da matarka Sawwama don gaskiya ni dai kam bazan koma gidanka ba....”

Hafiz ya mata tsuri yana dubanta kaman ba Zulfa’un da ya sani ba kana yace “Kar ki sake kiran wancan ballagazar da sunan matata... Matata d’aya ce nan gidan duniya, kuma kece Zulfa’u.... Karmu wahalar da kanmu na sani munason juna.... Wllhi a shirye nake na sake aurenki Zulfa’u, I’m ever ready....”
Chapter 86 · 0% Book details