← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 198

Sashe 78

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna tafe cikin motar driving kurum yake amma mind d’insa was somewhere else, Shamsu ya kula da hakan don ‘yan kwanakin sam baya gane abokin nasa, yasan definitely akwai abindake damunsa kuma koda bai fad’i mashi yasan it has to do with his wife, tinda yanzu Sameer ya samu iyayensa baida sauran damuwa da ya wuce matarsa, d’an dubansa Shamsu ya kuma ganin yanda yake driving d’in tamkar mai shirin barin gari, a hankali ya furta “Doc please drive slowly kasan banyi aure na ije iyali ba so banyi shirin mutuwa ba ka gane....”

Sameer ya jefa masa harara kana yace “Toh ai ita ba’a mata shiri, shiyasa idan kayi niyya maza kafin k’arshen shekara ka cikawa Mama burinta ka kawo mata sirka...”
Shamsu ya murmusa yace “Na fad’a maka ai na gaji da wannan gorin tsaf zan baku mamaki daga kai har Maman...”

Sameer ya tab’e baki yace “Ba fad’a a baki ba a dai aiwatar sai mu yarda....”

Nan ma murmushin Shamsu yayi kana yace “Yauwa speaking of aje iyali, Wai har yau Siyama bata dawo ba....? Sameer are you ba wata matsala....?”

Kallonda Sameer d’in ya jefa masa ne ya sanyashi d’an yin shiru kana yace “Look I’m sorry, I didn’t mean to intrude kawai na damu dakai ne shiyasa na tambaya....”

Sameer baice komai ba sai d’an duban gefen kwalta da yayi yana mai kuma k’ara speed....Sam bai kulada mutumin dake tafe tsakiyar kwalta d’in ba...
Shamsu ne ya soma hangosa ya shiga salati yana fad’iwa Sameer mutum gabansu.... Sameer ma salati ya soma yana k’ok’arin danna birki had’ida danna hannunsa gaba’a d’aya kan horn amma inaaa ya riga ya hauro saman kwaltan sosai ji kake k’iiiiii k’aran birki ga kuma mutumin da suka bige kwance gefen kwalta......

Cikin sauri suka firfito waje suka nufi mutumin da suka bige wanda ke zube saman kwalta bakunansu d’aukeda ambaton Allah

“Hafiz...!” Sameer ya furta a hankali...
Shamsu ya dubesa yace “Ka sanshi ne...?”

Jinjina kai yai kana yace “Cousin d’inane.... Taimaka min muyi sauri mukaishi asibiti...” ya fad’i yana mai nannad’e hannun rigarsa had’ida sunguman Hafiz Shamsu na taimaka masa, suka sakashi cikin mota kafin suka nufi asibiti mafi kusa.....

SameenaAleeyou 📚

*INDA RAI*
_................DA RABO_

*63*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

NOT EDITED

Mamy ta kuma jan gajeren tsaki a karo na biyu sanda ta kuma dialing wayar Nabilah tajita a kashe, ga magariba ta sako kai, bata saba kaiwa haka a makaranta ba ko dama da take kaiwa magariba computer practical take tsayawa, sannan idan tanada aji 4-6 takan fad’iwa Mamyn sabida karta damu.... Takai dubantaga Marliya da shigowarta parlorn kenan kana tace “Kin sami wayan Yusran...,?”

Marliya ta girgiza kai a hankali kana tace “Na kirata sau biyu bata d’aga ba.... Itama Nabilar na kuma kiranta bai shiga....” Mamy tai k’wafa kana tace “Wannan ai rashin hankali ne, idan ba rashin hankali ba Yo ko wayar k’awarta ba sai ta ara ba tace mana bazata dawo da wuri ba idanma nata babu chaji ne.... Zata dawo gidan nan ta sameni ne...” Ta k’arashe tana mai mik’ewa tsaye...
A k’ofa ta had’uda Zulfa’u wacce da alama daga sashen Mamani ta fito, ganin fuskar Mamyn kawai ya tabbatar mata hankalinta a tashe yake...
“Mamy Nabilar bata dawo ba har yanzu...?” Zulfah ta tambaya cikeda nuna kulawa...

“Inafah ta dawo... So take Abbanku ya kuma tambayana ko ta dawo gida... Wane irin karatu ne har yanzu bazata dawo gida ba, tayi ma kanta yace ta gama karatun...” Cikin fad’a Mamy ke maganar...

Zulfah ta d’an sauk’e ajiyan zuciya kana tace “Kiyi hak’uri Mamy in sha Allah lafiya lou take, kinsan wasu lecturers d’in sam basu san yakamata ba babu ruwansu da lokacin sallah wasu kuma ba musulmai bane so a mata uzuri Mamy...”

K’wafa Mamy ta kumayi kana tace “Ai bazasu hanata yin waya ba... Idan kuma Abbanku ya kuma tambayan ko ta komo gida sai kije ki masa wannan bayanin tinda ita batada hankalin ta d’aga waya ta kira mutane...” Ta k’arashe tana mai nufan kitchen bata daina sababi ba....

Marliya da Zulfah suka dubi juna suna masu jinjina lamarin....
“Bani layin Yusran na kuma kira....” Zulfa’u tace tana mai duban‘yar uwar tata... Cikin sauri Marliya ta mik’a mata wayar dake hannun nata...
Zulfah ta d’auki number d’in kafin ta soma dialing...
Wayar sai faman ringing take ba’a d’aga ba... Har ta kusa tsinkewa kafin aka d’aga, muryar k’aramar yarinyace take fad’in “Hello bata kusane ta saka wayar a chaji ne....”
Zulfa’u tace “Wannan ba wayar Yusrah bane....?”
Daga d’aya b’angaren yarinyar tace “Eh wayartace amma bata kusa ne...”
Zulfah ta jinjina kai tace “Ta dawo daga makaranta kenan...?”
Yarinyar tace “Eh tinda rana ta dawo...”

Duban Marliya da tai mata k’uri Zulfa’u tai kana tace “Toh shikenan sai anjima koh, idan Yusrah tazo kice mata Zulfa’u Addar Nabilah ce ta kira...”
Yarinyar ta amsa mata kana ta kashe wayar...

Jigum jigum sukai suna tunanin ta yanda zasu soma sanar da Mamy cewa k’awar Nabilah ta jima da komawa gida... Marliya tace “Addah kodai mu sanar da Mamy halinda ake ciki, kinga fah dare ya riga yayi, bamusan wane hali ‘yar uwarmu ke ciki ba....” Ta k’arashe fuska d’aukeda damuwa...

Shiru Zulfah tai tamkar mai tunani kana tace “Marliya na rasa ta yanda zamu fara b’ullowa lamarin ne, gashi anjima kad’an nasan Abbah zai kuma tambaya muddin bai ganta ba... Toh idan dai bata makaranta ina take... Toh ko kinada layin sauran abokan nata ne...?”

Marliya ta girgiza kai tace “Ai batada shirgin k’awaye kinsan halinta not everybody can stand her... Ita Yusrah dai itace d’aya k’awarta da na sani kuma coursemate d’inta ce komai tare sukeyi... Toh idan dai sun jima da tashi ita ina taje....?” Batakai aya ba muryar Mamy ya katseta da fad’in “Ban gane ba.... Ta baro makaranta tuntuni...? Toh ina ta tsaya....?”

Zulfah ta d’an gyara murya tace “Mamy ki kwantarda hank.....” Bata ida maganar ba wayarta ya d’auki ruri... Lambar Yusrah da yanzu ta kira ake kuma kiranta....

Zulfah tai saurin d’agawa cikeda damuwa... Daga d’aya b’angaren Yusrah tace cikin ‘yan kame kame bayan sallama “Em em ina yini Addah Zulfah...”

“Lafiya lou, Yusrah ce....?”
“Eh itace dama bana kusa ne d’azun...”
“Eh haka k’anwarki tace... Yusrah nace ko kuna tareda Nabilah ne... Munata kiran wayarta baya zuwa gashi dare ya sako kai already....”
Yusrah ta soma fad’in “Eh ai amma mun tashi ita sai ta wuce gidan Aunty Bara’atu.... Akan haka muka rabu, amma ku kira wayan Aunty B d’in suna tare....”

Nannauyan ajiyan zuciya Zulfah ta sauk’e kana taceda Yusrah “Toh shikenan mun gode Yusrah zan kira Auntyn yanzu....” Ta ida maganar tana mai duban Mamy da Marliya.....

Duk yanda sukaida Yusrah ta fad’i masu, ran Mamy idan yayi dubu ya b’aci, wace irin rashin hankaline wannan... Kan wane dalili Nabilah zata kama hanya ta tafi gidan Bara’atu ba tareda sanin kowa ba...? K’wafa ta kuma yi a karo na babu adadi kana taceda Zulfah tai mata kiran wayan Aunty B...

Zulfah ta danna nan ma bai shiga... “Bai zuwa Mamy....”
Jinjina kai Mamy tai kana ta nufi d’aki sauk’inta ansan yanda take yanzu...
Ita kaw Aunty Lami sai safa da marwa take tsakanin sashenta da sashen Mamy badon komai ba sai don ace ta nuna damuwarta itama....
Zulfah da Marliya dubanta kurum suke sam basuso Mamy tana fayyace mata cikinta gaba d’aya, don suma haka kurum bawai sun gama aminta da matar bane, tamkar tana b’oye wani abin haka suke gani....

Basu suka shigo garin Kano ba sai wajajen k’arfe takwas na dare, masallatai duk sun fito daga sallan lisha.... Kana ganin Nabilah zaka fahimci hankalinta a tsananin tashe yake, tasan a daidai wannan lokaci, lokaci ne da Abbanta ke zaune parlornsa kewaye da ‘ya’ayensa, idan baiga guda ba sai ya tambaya... Shikenan zata saka Mamynta a magana, donma yanzu Abbah ya sassauta da wasu halayyan nasa...
Aunty B takai dubantaga Nabilah wacce gaba d’ai take dame kana tace “Relax daughter, ki kwantar da hankalinki zan shiga naiwa Abbanku bayani ta yanda zai fahimta kinji koh....”

Nabila tai saurin dubanta kana tace “Aunty ce masa zakiyi ga yanda naje...?”

Aunty B ta girgiza kai tace “Ya za’ai nace masa haka, wannan between us ne, our little secret.... Ni dai kawai nasan mai zan fad’i masu daga shi har Mamyn taku.... Kinji koh... So ki kwantar da hankalinki idan Ina nan in sha Allah bazakuyi kuka ba...”

Nabilah ta murmusa tace “Na gode Auntynmu....”

***

A can asibiti kuwa har wannan lokaci Hafiz bai farka ba.... Gaba d’aya Sameer a dame yake, hankalinsa gaba d’aya na tashe... Duk wasu abubuwa da Hafiz yayima k’anwarsa bai hanasa jin tausayin Hafiz d’in ba musamman da shike shine ya bigesa....
Likitoci suna kansa yayinda shida Shamsu suke reception sai faman safa da marwa yake....
Shamsu ya mik’o masa ruwan gora yana k’ok’arin calming nasa....
“Doc try to calm down....”
Saurin katsesa Sameer yai da fad’in “How could you ask me to calm down.... Shamsu mutumin nan fah d’an uwana ne kuma ba fata ba yanzu idan hakan ta zamto silan ajalinsa zan jima inajin zafin hakan, domin gani zankeyi tamkar ni na kashesa.... Shamsu Hafiz can’t die.... He just can’t....” Ya k’arashe yana mai zama bisa benchi had’ida rufe bakinsa da duka hannayensa biyu cikin tsananin mutuwar jiki....

Shamsu ya zauna gefensa yana buga kafad’ansa guda a hankali yake furta “Bazai mutu ba in sha Allah.... Ka kwantar da hankalinka friend and pray for him kaji koh....”

Sameer ya lumshe idanunsa a hankali ba tareda ya iya furta koda kalma ba...

***

KADUNA

Daddy na zaune parlornsa Ammi na gefe faranti dambun kaza gabansa yanaci suna fira Khalid yayi sallama... Ammi ce ta amsa masa sallaman nasa kana ya shigo jiki babu laka...
Daga can gefe ya zauna kana iya hango d’an rama da duhu da yayi a ‘yan kwanakin... Kansa a k’asa ya soma gaida iyayen nasa.....

Ammi ce ta amsa masa Daddy kam ko kallon kirki bai ishesa ba....
Ya dubi Ammi tai masa alamu da idanu kan ya baiwa mahaifin nasa hak’uri...
Khalid ya d’an muskuta kana ya soma fad’in “Daddy kayi hak’uri....”
D’aga masa hannu yai alamun dakatarwa kana yace “Mai ya dawo dakai gidan nan....?”
Chapter 78 · 0% Book details