← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 198

Sashe 44

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

D’an dubansa tai kana tace “Kaman ka mance Daddy duk abinda nakeso shi yake so, that won’t be an issue besides nayi serving company d’inshi na tsawon shekaru ya kamata yanzu kuma nabi mijina duk yanda zaije, I can’t afford to lose you Partner...” Ta k’arashe murya cikeda shagwab’a...

Har cikin zuciyarsa yake mamakin canzawa da Siyama tai lokaci guda, wata b’angare na zuciyarshi kuwa najin dad’in canzawan da tai dukda cewa har yanzu yanaji kwance k’asar zuciyarsa kaman akwai abinda take b’oye masa, amma sam baiso tunanin nasa yaci galaba a zuciyarsa abinda ya bayyana dashi ake amfani yafi aminta da ya yardarwa kansa cewa da gaske she’s changed tinda gashi har kitchen yau d’in ta shiga tana tambayar Mama ta nuna mata yanda ake wasu abubuwan....

Washe gari Siyamar tai shirin tafiya don Khalid ya sanar da ita da wuri zasu koma Kaduna sabida aiki da ya taso masa, saida ya biya yayiwa Mamani sallama ya kuma cikata da goma na arziki kafin ya wuce d’aukar Siyama, duk wannan bidiri Nabilah batasan Khalid yayi ba don tana makaranta saidai ta labartawa Yusrah yanda taga Khalid jiya gidansu wajen Mamani da yanda suka wanye...

Yusrah dai dariya ta dingayi tana fad’in lallai Khalid ya iya kamun k’afa ta k’arada “K’awata wllhi da gaske yake tinda ya soma biyo gida da kamun k’afa, kekam addu’arki ta amsu ki nemi lahira kawai wannan zankad’ed’en saurayi, ga kyau ga kud’i ga aji ga gayu mai kuma kike nema...”

Banda harara Nabilah bata aika mata komai, takai mata duka da handouts d’in dake hannunta tana fad’in “Ke nake nema, toh ni ina ruwana da duk futures d’in da kika k’irgo maza duk halinsu d’aya ina nan kan bakata bazanyi aure ba..”

Yusrah tace “Daina wannan fatan k’arshen shekara In Allah ya yarda zamukai teddy bear gidan oga bear...!” Nabilah ta kuma kai mata duka su duka suna dariya Nabilah na fad’in “Aifa saidai ku kai masa teddy bear amma bani ba...!” A haka suka rankaya zauren karatu...

***
“Shamsu duk yanda za’ai a unguwar nan nakeso na samu gida tinda kaga Siyama ta dage zata dawo...” Sameer yace yana duban Shamsun...

Jinjina kai Shamsu yai kana yace “Amma gidajen hayan unguwar nan ba taste d’inka bane Dr why not ka nema a wani wajen ga gidaje masu kyau daidai tsarinka da yanayinka, kai idanma kai gidajen hayan unguwar nan sun maka na tabbata Siyama bazata so ba, so kawai mu nema ta wani wajen....

Lokaci guda Sameer d’in ke girgiza kai alamun rashin amincewa kana yace “Kai ina, nifah unguwar nan nakeso duk yanda za’ai kawai ka sama min gida, batun Siyama kuma ai zama ne na temporary bawai permanent ba, nidai kasan yanda za’ai na sami gida a unguwar nan...”

Shamsu dai k’uri kurum ya masa yana mamakin yanda sam Sameer baiso ya bar unguwar, a hankali ya d’an jinjina kai kana yace “Alright I’ll see what I can do...”

“You must...” Sameer ya fad’i yana duba irinta abokan usul...

Shamsu ya murmusa yace “Ok I must...”

Murmushi Sameer d’inma yai yace “Now you’re talking bro....” Kafad’arsa ya rik’o suka shige cikin gidan....

***

*Kaduna*

Kallon mamaki Ammi tabi Siyama dashi tana sallalami “No wonder yaron nan ya mak’ale baida aiki sai zuwa Kano ya maida Kaduna to Kano tamkar zuwa unguwa, ke kuma baki nemi gidansu yarinyar kinga waye ubanta ba...? Domin sanin kanki ne bazan bari ya kawo min ko wacce shirgi ba matsayin sirka...”

Siyama ta tab’e baki had’ida yatsina fuska “Tab ai wllhi Ammi saima kinga yarinyar low class da ita wacce idan akace min Khalid zai kalli irinta matsayin mace zanyi musu, kwatakwata she isn’t his type, wllhi Ammi sai kinga yarinyar Yesmin ta d’arata a komai, bak’a k’irin da ita balle nace kyaune ya tsole idanunsa toh babu ko d’aya... Wannan ma kunya zakiji azo bikin one and only son d’inki aga wannan kucakar ya d’auko... Wllhi Daddy ma bazai bari ayi wannan shiriritan dashi ba...” Ta k’arashe tana cakalan grapes d’in dake hannunta cikin bowl ta tsinken toothpick....

Jinjina kai kurum Ammi take tana tsuma ita kad’ai, Khalid na nema ya tozartasu ya jajab’o masu d’iyar matsiyata, banda sakin huci bata komai, ta kuma kai dubanta ga Siyama wacce ke cin grapes d’inta hankali kwance kana tace “Shikenan duk kun watse kunyi garin Kano kun k’yaleni, shi yana can yana neman auren da ba yuwa zaiyi ba kekuma zaki tattare kibi mijinki toh ni kuma ku barni da wane tinda shi uban naku nacan wajen matarsa wata k’asar daban...”

Dariya ta kufcewa Siyama ta aje bowl d’in hannunta tana fad’in “Wai Ammi ba kece mai bani shawarin nabi mijina a baya ba, toh yanzu na yanke shawarin binshi kaman yanda kikaso a baya zan aje aikina...”

Ammi ta rakata da mugun kallo had’ida tab’e baki “Ke ni dama aurenki da Sameer bawai ya kwantamin bane tun farko don dai kawai keda mahaifinki kunfi k’arfina ne, mai za’ai da maras asali...”

Siyama ta d’an tab’e baki tace “Ammi nifa I don’t care koma baida asali all I know is that I love him, besides baida wani mummunan hali...”

“Ke dalla can rufemin baki, sanda kika haifu aka d’aga idanu aka kalli yaranki akace ina dangin mahaifinsu mai zakice..? Ko kuma yaran su girma su tambayeki su waye iyayen Babansu wane explanation zaki basu...?”

Siyama tai shiru tamkar mai nazari tana duban wani b’angaren...

Ammi ta kuma jinjina kai tace “Ina horonki da haihuwa da mutumin nan dukda nasan haihuwa ba ra’ayinki bane amma kada ki bari soyayya ta kaiki ta baroki, ya kalallameki da dad’in baki ki haifa masa yaran da a baya zakizo kina danasani, tun ba’aje ko ina ba ya rinjayeki kin aje aikinki zaki bishi, shin waima wane irin apartment ya kama maku...?”

Siyama da gaba d’aya jikinta yai sanyi a hankali ta sauk’e ajiyan zuciya “Oho Ammi don’t know gaskiya but koma wane iri ne I’m pretty sure to my taste zai kama, saima kinga unguwar da yake zama Ammi asubahin fari Almajirai ke tashinku a bacci... Gosh! So annoying, waima don gidan da yake d’in nada d’an fasali...”

Ammi ta jinjina kai tace “Toh kinga abinda nake fad’i maki koh... Amma idan kinason binshi a haka fine kijeki...”

D’an tsuke baki Siyama tai ba tareda ta kuma cewa komai ba, nan ta b’atar da zancen da tambayar Ammi yaushe Daddy zai dawo...

***

A satin Sameer ya sama masu gida a nan cikin unguwar, gidane madaidaici mai k’unshe da madaidaitan d’akuna guda biyu wanda basu faye girma ba sai parlor da kitchen a cikin parlorn saiko d’an wajen wanki da shanya dake a wajen kitchen d’in....

Banda yatsina fuska Siyama bata komai, ita da yace mata ya sama masu gida a zatonta gidan gaske ne ashe wannan abin ne wanda ko BQ bazata amsa ba....

Sameer ya k’araso ya rungumeta ta baya yana fad’in “Partner ya kikaga gidan ya miki...?”

Yatsina fuska ta kumayi kana tace “You call this a house..? Wait waima dan Allah Partner waye ya baka shawarin kama wannan gidan, of all gidajen hayan dake garin nan ka rasa apartment d’in da zaka kama mana sai wannan, nibama wannan ba gaskiya unguwar baimin ba...”

Tinda ta soma magana ya hard’e hannaye had’ida lank’washe k’afa dake jingine jikin k’ofa yake yanai mata wani irin duba fuska babu walwala...
“Zaki iya zaman gidan ko bazaki iya ba...?”

Taji tambayar tai mata wani banbarak’wai gaba d’aya tamkar an canza mata Sameer d’inta, da a bayane ta tabbata da saidai abi nata zab’in amma yanzu gaba d’aya duk ya canza kaman bashi ba...
Tai kicin kicin da fuska ba tareda ta amsa shi ba, bai kumabi takanta ba yayi ficewarsa...

Siyama data cika tayi fam zama tai cikin kujera tana tunanin abinyi ita datasan hakanema da bata soma cewa zata dawo garin ba, bak’in ciki bai gama gauraye mata zuciya ba saida ta jiyo muryar Almajirai sahu sahu suna rangad’a mata bara tamkar ta d’aura hannu aka ta kurma ihu haka taji...
A hankali ta zamo saman carpet tana furta “Na shiga uku ni Siyama what have I got myself into...” K’aranda wayarta tai ya dawo da hankalinta, a hankali tasa hannu ta d’aga wayar Laila ce mai kiran nata....

SameenaAleeyou📚

*INDA RAI*
_................DA RABO_

*36*

*©Sameena Aleeyou....✍🏽*

“K’awata ya najiki haka.... hope all is well with you....?” Laila tace daga d’aya b’angaren....

Siyama na zaune dirshan saman carpet take fad’in “Laila na kawo kaina halak’a...”

“Ban gane ba... Wani abin Sameer d’in ya miki ne...?”

“Komai ma yamin, ke kinga gidan da ya ijeni ne, anya ba ramuwar gayyar abinda nai masa yakesonyi ba, if not na tabbata babu abinda zai zaunar da Sameer a wannan gida.... Wllhi bazan iya zaman wannan environment d’inba....”

Laila ta sauk’e ajiyan zuciya tana mai furta “Ya gane kin zubda ciki ne ko kuwa kin bud’e baki kin fad’a masa da zai maki wannan horon...?”

Siyama ta shiga girgiza kai tamkar Lailar na kallonta kana tace “Babu abinda ya gane, kuma kinsan bazan tab’a bud’e baki na fad’i masa ba, duk wannan rigimar dai kan pills ne da ya gani.... Gaba d’aya kaman an canza masa rayuwarsa da tunaninsa..”

Laila ta jinjina kai tace “Toh ke kuma yanzu wanne shawarin kika yanke, zaki daina shan maganin ko kuwa....?”

Fuzar da iska Siyama ta d’anyi kana tace “Wllhi I’m lost Laila, gaba d’aya ma yanzu bansan wanne zanyi ba, kinsan dai inason Sameer so na gaskiya....”

Laila ta jinjina kai tace “Na sani amma dai ki duba maganar Ammi da kyau k’arshe kece za’a bari da kayan kunya, nidai a nawa shawarin kici gaba da shan pills d’inki har lokacin da asalin Sameer zai bayyana miki, idan kinji kina iya haihuwa dashi fine sai ki saki jiki kiyita zubo masa ‘ya’yaye har yanda kike so tinda ra’ayinsa na haihuwa ya rinjayeki, idan kuwa kikaji asalinsa abin k’yamatane shawari ki nemi tsira ma kanki kisan yanda zakiyi ki guntile aurenshi dake, shawari ne...”

Siyama ta zaro idanu waje tana fad’in “Laila na raba aurena da Partner fah kike nufi...?”
Chapter 44 · 0% Book details