← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 198

Sashe 104

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Gaban Khalid yaci gaba da fad’uwa sand’a ya sa k’afarsa a bakin k’ofar da zai sadaka da main parlor na gidan.... Gabansa bai gama fad’uwa ba saida ya hango dank’areren hoton mahaifinsa manne cikin parlorn gefe dashi wata matace wacce bazata wuce shekaru 39 a duniya ba, wacce sam ratan dake tsakanin shekarunta da Siyama bazai wuce shida zuwa bakwai ba shi kansa bata basa yakai shekara goma ba... Da k’yar yake iya d’aga k’afafunsa yana kutsa kai cikin parlorn.... Wani sabon tashin hankali daga d’aya angle na parlorn ya hango wani hoton da ya kuma d’aga masa hankali... Daddynsa da wancan matar a tsakiyan hoton, yara ‘yanmata guda biyu sun sakasu a tsakiya d’aya bazata wuce shekaru goma ba k’aramar bazata wuce shekaru bakwai ba, fuskokinsu sun cika da annuri.... K’afafun Khalid suka kasa d’aukansa, ji yayi kansa na juya masa cikin sauri ya maidoda dubansa ga Mahaifinsa dake tsaye yana kallonsa...
Cikin rud’ani Khalid ke fad’in “Daddy what is this.... What is all this.... Meke faruwa Daddy.....?”

A hankali Daddy ya dafasa kana yace “Sit down first and try to calm down....”
Girgiza kai Khalid yake cikin rashin yarda da abinda yake gani kana yace “No Daddy... Are you really asking me to calm down after what I’m seeing... Daddy who are these people... Who’s this woman... Tell me Daddy do you really have another family...?” Yayi maganar yana mai k’arasowa gaban mahaifin nasa cikin rashin yarda da abindake faruwa.....
Kasa furta komai Daddy yai sai duban Khalid d’in da yakeyi....
Lokaci guda Khalid ya shiga girgiza kai kana ya soma furta “So is that why you told Ammi neman aurena zakaje...? So bayan Aunt Helen da take America, you have another wife here... Tell me Daddy, be honest with me for once in your life... How many wives do you really have.... Bayan Ammi, Aunt Helen and now ga wata kuma.... Mata nawane kaci amanar mahaifiyata dasu...?!!” Baikai aya ba yaji sauk’an mari da saida ta kaisa k’asa a kumatunsa.....
Khalid ya d’ago dafe da k’uncinsa yana duban mahaifinsa dake tsaye yana sakin huci cikin tsananin b’acin rai.....
Nuna Khalid yake da yatsa cikin tsananin fushi da fad’a yake fad’in “Ban tab’a cin amanar mahaifiyarka ba, kuma idan na auri mace samada guda Ubangijina ya halatta min na auri daga d’aya har zuwa hud’u... If I keep it from your Mum is because I know exactly the type of woman she really is....” D’an sassauta muryarsa yai kana yaci gaba da fad’in “Khalid for the past few weeks na kula kaid’in ba kamar mahaifiyarka da ‘yar uwarka kake ba, zuciyarka tafi nasu taushi da kyau, Khalid wannan shine dalilina na fayyace maka gaskiya sabida akwai rayuwa akwai mutuwa, yau idan bana raye kasan kunada wasu ‘yanuwa...” Ya k’arashe maganar idanunsa na kallon makeken hoton nasu....
Daddy yaci gaba da fad’in “And about Helen banida mata a k’asar Amurka nayi haka ne sabida kar mahaifiyarka ta zargi inada mata cikin k’asar nan, na sani muddin ta sani zatayi komai don ta rabamu shiyasa na karkata hankalinta zuwa nisan duniya can America....
lokaci guda Khalid ya d’ago idanunsa mai zuban hawaye yana duban mahaifin nasa lokaci guda yake girgiza kai yana mai furta “But still that doesn’t justify your actions Daddy, we have the right to know our siblings, Siyama ta cancanci tasan tanada wasu k’annen... Why Daddy...?” Ya k’arashe hawaye na gangaro masa...
Dafasa kad’an Daddy yai kana yace “I wish I can do that son....”

Juyawan da Khalid zaiyi yayi ido hud’u da matar jikin hoton nan, tana takowa tamkar mai tsoron yanda take aje k’afafunta.... Cikin sand’a ta k’araso kusan mijinta, cikeda yanayi na tsoro take duban Khalid d’in kana tace da Daddy cikin sigan rad’a “Why did you bring him here....?”

A hankali shima ya furta “Na cika miki burinki ne zan bari Humaira da Ijlal susan ‘yanuwansu....”
Ta saki murmushi a hankali dukda cewa har lokacin d’ari d’ari take da Khalid d’in
“Sannu da zuwa... Please K’araso ka zauna....” Ta furta a hankali kaman mai tsoron magana fuskarta d’aukeda kyakkyawan murmushi, tana maganar tana k’arasawa cikin parlorn had’ida nuna masa kujera...

Kaman mai tunanin wani abu, fuskar matar a zahiri ya masa kaman ya tab’a saninta wani waje... Samun kansa yai da k’arasawa ya zauna a nan yanda ta umarcesan... Ganin bai gwaleta ba ya sanyata samun k’warin gwiwa, ta dubi Daddy fuska fal fari’a kana tace “I’ll set the table...” Ta k’arashe tana nunida dining area... Jinjina mata kai Daddy yai kana ta wuce kitchen cikeda jin dad’i...
Har lokacin shock d’in bai rabu da Khalid ba.....
Tana cikin had’a plates taji wayarta na k’ara ta k’arasa da sauri ta d’aga still bata daina shirya plates d’in saman dining table ba...
“Da gaske Ya Ma’aruf...? Gaskiya naji dad’i su Humaira zasuji dad’in ganinsu Irfaan sosai, na zaci siyasa ya b’oyeku gaba d’aya...?” Shiru ne ya biyo baya alamun ana magana daga d’aya b’angaren.... A hankali kuma ta nufi balcony tana mai ci gaba da amsa kiran.... Sauk’e ajiyan zuciya ta d’anyi kana tace “Toh Yaya ka sanar da Muhibbar ce....?”
Daga d’aya b’angaren sauk’e ajiyan zuciya ya d’anyi kana yace “Not yet, shiyasa idan yaran sunzo wajenki sai mu samu dama muyi magana....”
Jinjina kai tai a hankali kana tace “Haka ne Yaya, yafi idan ka sanar da ita don aure a sirrancen baida wani amfani tinda gashi nan ni yanda nake fama da nawa auren har yau ya kasa had’amu yayi introducing d’inmu... Ko dashike yau ya kawo min d’ansa kuma ga dukkan alamu bazan samu matsala dashi ba....”
Gyara zama sosai Engr yai kana yace “Daula are you sure you’re happy...? You know you’re my only sister kuma hakkina ne na kula dake koda kina gidan aurenki don nayi rantsuwa ma iyayenmu zan kula dake bayan ransu....”
Hawayene suka ciko idanunta, tasa bayan hannunta ta goge kana ta saki murmushi tace “I’m happy Yaya, I’m very happy musamman yanzu da mijina yake shirin gudanar da al’amra yanda suka kamata....”
Murmushi ya d’anyi kana yace “Gobe in sha Allah yaran suna hanya....”
Daula ta amsa masa da fatan Allah kawosu lafiya kana sukai sallama....

Parlor ta dawo yanda ta tadda Khalid tsaye jikin hotunan yana shafa fuskokin yaran da akace sisters d’insa ne, Daula tai tsaye tana dubansa, lokaci guda taga ya saki murmushi yana mai furta “Who’s Humaira among you and who’s Ijlaal......?”

*Toh fah! Masu iya magana sukace sannu sannu bata hana zuwa... Mai karatu da sannu da sannu tafiya tana kan yin nisa, b’oyeyyun al’amra suna dad’a bayyana, idan mukaci gaba da tafiya a sannun nan zamu kuma gano wasu abubuwan da izin Allah ciki harda tambayar da ya jima yana maku Yawo WACECE AMINIYAR SIRRI...? Da sannu zamuji ko wacece ita da kuma gudunawar da ta bada wajen salwantar da Ma’aruf had’ida sanin dalilinta na aikata hakan... Na gode da yanda kuke hak’uri Kuke bibiyata dukda rashin samun post akai akai....Alkhairan Allah ya kaimaku duk yanda kuke..!*

SameenaAlleeyou📚

*INDA RAI*
_...............DA RABO_

*77*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Chapter 104 · 0% Book details