← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 198

Sashe 102

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A can gidan Abbah kuwa a parlorn Abban Mamani ta ritsa Sameer da iyayensa, ta yanda take shiga bata nan take fita ba, fad’i take “Inyi toh Wllhi sam bazata saku ba, wannan ai gubace ba macen zaman aure ba, ni nasan irin wannan matan barikin sam ba kunya bace dasu.....”
Baba Alhaji ya tari zancen da fad’in “Hajiya ni dama na gama magana ga k’anwarsa Sahariyya zaune gida babu miji kawai sai a had’a aurensu don bazamu zuba idanu wannan yarinya da ya auro matsayin mata ta rainamu ba kuma Mamani ina mai tabbatar miki wannan yarinya da kike gani zata iya rabaki da jikanki a karo na biyu, tun kafin abin yakai nan mu aura masa ta gida kinga mun d’auresa....”
Abbah duban Baba Alhaji kurum yai had’ida girgiza kai, yayinda Mamy ta kasa furta koda kalma guda, har lokacin kanta na k’asa...
Sameer d’ago kansa yai yana duban wan mahaifin nasa da tsananin mamaki.... A hankali ya furta “Baba ku bani dama nayi magana da Siyama please...”
Mamani ta katsesa da fad’in “Yo wani dama, wannan batu naka yayi daidai Alk’ali, yanzu basai anjima ba a soma shirye shiryen biki....”
Abbah ya d’anyi gyaran murya kana yace “Amma Yaya, Mamani bawai nak’i maku bane wannan had’I, kaman yanda Ma’aruf ya buk’ata a basa dama yayi magana da iyalin nasa... Sannan Yaya baku tunanin abinda ya faru damu baya gameda had’in Hafiz da Zulfa’u ya maimaita kansa... Ni dai a ganina da an janye wannan batu...”
Haba nan fah Baba Alhaji ya soma kumfan baki yana fad’in “Toh kinji koh, Mamani... Kinji abinda d’anki yake fad’i koh, a kullum anaso mutum ya kasance mai kyakkyawan zato amma banda Usman... Minene aibun yara na... Maiyasa zai dinga dawo da abinda ya riga ya wuce....Idan har haka ne wannan ya kuma tabbatar min bai d’aukeni matsayin d’anuwa ba kuma wanda yake gaba dashi... Na tabbata da ace d’aya daga cikin yaran Ado ko Wada ne tsaf zai amince amma dashike d’iyata ce shiyasa zai nuna k’yamarsa... Tinda haka ne ni na cire kaina da ahalina daga wannan zuri’a... Usman daga rana mai kaman ta yau ka mance kanada D’anuwa mai irin sunana...!” Daga haka yasa kai zai fice...
Mamani dake hawaye tai saurin tare gabanshi tana fad’in “Shin sai na mutu ne ku sami jituwa tsakaninku...? Shin bazaku mance komai ku rik’e ‘yanuwantakarku ba.... Shin kuna tunanin mahaifinku dake kwance a k’asa zaiji dad’i da ace za’a tayar dashi a nuna masa yaransa sun kasa rik’e zumuntarsu balle su d’aura yaransu bisa... Shin wannan wace irin rayuwa ce mai cikeda rashin yafiya....!” Tai maganar tana mai dafe k’irjinta... A d’ari Abbah ya tashi ya tallafota yana mai bata baki da sanyaya mata zuciya, shima Baba Alhajin kasa fita yai sukai chaa kan mahaifiyar tasu ganin tana numfashi da k’yar...
Sameer da tashin hankali ya nuna sosai saman fuskarsa, tuni ya umarcesu su kwantarta saman kujera a matsayinsa na likita.... Ruwa Mamy ta kawo ta mik’awa Sameer ya shiga baiwa Mamani yana fad’in ta d’auki a hankali....
Mamani ta bud’e idanunta da k’yar ta d’aura kan ahalinta... Baba Alhaji Abbah Mamy da kuma Sameer wanda gaba d’aya sannu suke mata... Bud’e baki tai da niyyar magana, Sameer yai saurin damk’e hannunta had’ida girgiza kai alamun kar tace komai, cikin nutsuwa da kwantar da hankali ya soma fad’in “Mamani bazamuso wani abu ya sameki ba, ban jima da sake had’uwa dake ba, ina fata Allah ya ara mana kwanaki masu tsawo wanda zanyi taredake Kakata... Duk dai ni ne matsalar a nan....” Ya d’ago yana duban Abbah kana ya dubi Mamy ma... Dawo da dubansaga Baba Alhaji yai kana yace “Baba na amince da zab’inka.... Zan auri d’iyarka kuma k’anwata idan hakan zai kawo peace a wannan family d’in....” Ya maido da dubansaga Mamani murmushi kwance saman fuskarta, a hankali ya kuma damk’e hannunta cikin nasa kana yace “Zan auri jikarki Mamaninah... Muna sonki muna son ki kasance cikin k’oshin lafiya da kwanciyar hankali....”
Hawayen Farin ciki ya sauka fuskar Mamani yayinda Baba Alhaji ya shiga Washe baki yana ayyanawa a ransa burinsa ya kusa cika... Abbah da Mamy kallon juna sukai kana suka dubi d’an nasu cikeda tausayawa... Tabbas sun sani d’an nasu sadaukar da farin cikinsa yai ga family d’insu... A hankali Mamy dake danne hawayenta tasa kai ta fice daga parlorn sim sim... Abbah duk’awa yai kad’an ya dafa kafad’an Sameer kana ya furta “Allah ya maka Albarka....”
Mamani da Baba Alhaji a tare suka amsada Ameen Baba Alhaji naci gaba da fad’in ai sai a soma shirye shiryen biki a tsai da rana.....

Daga yanda suke lab’e jikin window wani irin dad’i ne ya dabaibaye zukatansu... Haule tamkar tayi jifa da sandar hannunta ta buga tsalle haka taji, shikenan yanzu basuda wata matsala, Ma’aruf ya amince zai auri Sahariyya wacce a wajensu daidai take da ajalinsa... Ko wannan shu’umar matar bata basu had’in kai ba ga d’iyarsu zatai masu komai...

Lami ta janyota suka koma gefe... Shewa suka saka had’ida tafe hannaye.... Haule ta gyara sandarta tace “Ke ni dama wannan shegiyar matar tasa da ganin yanda take kallon mutane nasan bazamu samu wani qofa ta wajenta ba... Yanzu komai zai zo mana cikin sauk’i....”
Lami ta sauk’e ajiyan zuciya kana tace “Anya kuwa Haule... Toh mai zai faru idan d’iyarki ta juya mana baya... Kuma nayi imani babu macen da zata sami wannan had’edd’en saurayi ta salwantar da rayuwarshi... Anya kinaga Sahariyya bazata fara son Sameer ba...?”

Tsuka Hajiya taja kana tace “Uwar soyayya ce, yo sai mai, ai ita kanta bazata san tuggun da muk’e had’awa ba, ke nida mijina mun riga mun gama tsara komai, kinga idan Sahariyya ta auri Ma’aruf zamu sami k’ofa mai sauk’ine wajen tsunduma cikin rayuwarsa, idan bamu cimma burin hallak’asa ta wannan ba, ma’ana idan ya haye tuggunmu ko asirinmu yazo ya tonu daga baya kinga abin zaizo mana da sauk’i tinda mun zama sirakansa....”
Lami ta d’anyi shiru tamkar mai nazari kana tace “Toh ni kuma fah... Da wane ido Alhaji Usman zai kalleni....?”
Haule ta murmusa kana tace “Toh Banda abinko ai naki tonan sililin mai sauk’i ne akan Aminiyar sirri... Idan har za’a yafewa Aminiyar Sirri kinga kenan ya zama dole a yafe miki tinda duk kusanci da Ma’aruf tafimu..... Kinga idan wannan aure ma ya tabbata zamu had’asu fad’ane yasu yasu mu had’e mata baki mu d’aura duka laifi akanta... Kinga shikenan mun had’asu fad’a mun fita da fitarmu...”
Lami ta shiga juya maganganun Haule tana jinjina basira irinta Haule kana tace “Kai amma kin birgeni Haule, Wato idan baka iya kama b’arawo ba shi b’arawo sai ya kama ka... Wannan shawari tayi daidai Hajiya Haule....”
Haule ta dara kana tace “Babu wani shegen bokan da zai sake ci mana kud’i tinda duk Malamin da muka kai masa koke ce mana yake abu a duhu, da makirci kawai zamu kauda Ma’aruf a karo na biyu mu kuma b’adda Aminiyar Sirri tinda amfaninta ya k’are mana....”
Shewa suka kuma sawa had’ida tafe hannaye, duniya tai masu dad’i...

SameenaAleeyou📚

*INDA RAI*
_................DA RAO_

*76*

Marliya da Nabilah ya tadda a parlor sunyi jigum sakamakon hawaye da suka gani fuskar Mahaifiyarsu dawowarta daga parlorn Abbah, duk a tunaninsu hakan ya faru ne dalilin zuwan Siyama matar Ya Ma’aruf....
Sameer ya dubesu yanda sukai jigum jigum kana yace “Ina Mamy...?”

Sai sannan sukaji shigowar tashi, suka had’a baki wajen cewa “Sannu da shigowa Yaya..” Kana Nabilah ta amsa tambayar tasa da cewa “Mamy tana d’aki tun d’azu tak’i sanar damu meke damunta....”
Marliya ta k’arada “Kuma tace mu fita mu bata waje she wants to be alone...”

Shiru yai tamkar mai nazari kana ya jinjina kai yace “I’ll check on her...” Bai jira cewarsu ba ya nufi corridor da zai sadaka da d’akin.... Saida yai knocking da sallama saman bakinsa kana ya nemi izinin shiga...
Saita kanta ta d’anyi had’ida goge hawayen fuskarta kana ta masa izinin shiga....
Tai k’ok’arin d’aura murmushi saman fuskarta tana nuna masa wajen zama...
Idanunsa akanta ya k’araso ya zauna kana ya sadda kansa k’asa... Zuciyarsa sai faman tafarfasa take sanda ya tuna kalan rashin mutunci da Mamani tace Siyama tayi a gidan, kansa na kife k’asa jijiyoyin goshinsa sunyi rud’u rud’u, shi kad’ai sai dunk’ule hannunsa yake yana murzasu, kaji tsoron mutumin da bai faye saurin fushi ba, idan yayi fushin nasa babu kyau....
Mamy ce ta katse shirun nasa da fad’in “Baban Abbah an shigo...”

Sameer ya d’ago jajayen idanunsa wanda siririyar hawaye ke sauk’a ya sauk’esu kan mahaifiyarsa.... Ganin hawaye idanun d’an nata sai ya kuma d’aga hankalin Mamy, tai saurin tasowa daga wajen zamanta ta dawo yanda yake, hannayensa ya kamo ta rik’e kana tace “Na sani ka yanke hukunci mai tsauri ma kanka,... Ma’aruf idan baka son wannan aure da suke shirin maka dan Allah ka barni na tsaya maka d’ana for the first time, bana buk’atan komai face Farin cikinka.... Kaji d’ahna....” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya....
Rungume Mamy yayi lokaci guda kuka mai k’arfi ya kufce masa... Wanda har saida yasa jikin Mamy yin sanyi.... Cikin muryar kuka yake “I’m sorry Mamy... Dan Allah ku yafe min.... Ban tab’a danasanin auren Siyama irinta yau ba... Amma Mamy na muku alk’awari Siyama bazata sake tozartaku ba, ku yafe min....!!!” Ya k’arashe cikin shesshek’ar Kuka....
Jikin Mamy a sanyaye ta d’ago fuskarsa tana fad’in “No Ma’aruf, matarka bata tozartamu ba, kasan Kakarka akwai tsufa a tattareda ita shiyasa, rashin fahimtace kawai, kuma wannan shine zuwarta na fari... Amma idan mukace ta tozartamu mun mata k’age... Tasa hannu tana share hawayen da suka wanke masa fuska wanda ya koma jazir kana tace “Don’t take any drastic measure kaji koh, ka zauna kayi magana da matarka na tabbata zakuyi sorting komai, ai bata san damu ba, itama abun yazo mata ba zata ne... So ka bata dama da lokaci ta san family d’inka kaji d’ahna....”
Chapter 102 · 0% Book details