← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 129 OF 198

Sashe 129

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mamaki ya kama Khalid “Daddy wani waje zamuje... Ko kaduna zamu koma...?”
Murmusawa kad’an Daddy yai kana yace “Ina zuwa...”
Jim kad’an ya shigo rik’eda wata jaka ya mik’a masa.... “Akwai kaya a ciki inaso idan kai wanka sai ka saka su...”

Mamaki ya cika Khalid, ya kasa yarda da abinda yake gani na faruwa... Daddy bai kuma bi takansa yai ficewarsa, murmushi kwance saman fuskarsa....
Da tsananin mamaki Khalid Ke bud’e jakan... K’irjinsa ne yai wani irin yankewa ganin kayan dake cikin jakan, saida ya kwashe sakanni yana mai k’urama kayan idanu kafin ya soma cirosu...
Shadda ce ‘yar Ubansu, babbar Getznar sai yauk’i da shek’i take, fara k’al mai d’aukan idanu... Saida ya ida cirowa kana ya shiga warwarewa, Babbar riga ce sai ‘yar ciki da wando.. Kallo guda zakaiwa kayan kasan duk mad’inkin da ya d’inka kayan ya k’ware wajen iya d’inka kayan hausawa ta zamani....
Khalid ya fuzar da iska kad’an yana mai kuma juya kayan... Tabbas hasashena ya tabbata Daddy aure zai masa da Yesmin... Toh mai yasa zasu b’oye masa irin haka, shin suna tinanin bazai masu biyayya bane... Abubuwan da suka faru a ‘yan kwanakin suka shiga dawo masa daki daki... Wannan shine manufan Daddy na canza masa lokaci guda... Why Maiyasa Daddy zai masa haka...? Wata zuciya tace ka bishi a haka don tabbatar da abinda zuciyarka Ke raya maka... Zato kawai kake har yanzu tinda bai bud’i baki ya sanar dakai komai ba... Koda yayi wanka umarnin mahaifinsa yai ya shirya cikin wannan manyan kaya na alfarma... Tsaye yai yana kallon kansa cikin full-length mirror, shi kansa wani girma yaga yayi ma kansa had’ida wani k’warjini na musamman, dan har saida ya tsinci kansa da matsananciyar fad’uwan gaba, yanaji ajikinsa yau d’in ranace ta musamman a garesa dikda zuciyarsa dake ayyana masa cewa idan har aurensa da Yesmin ake shirinyi, toh yau d’in zata iya kasancewa rana mafi tashin hankali a rayuwarsa... Ya lumshe dogayen idanunsa a hankali daidai sanda Aunty Daula ta soma knocking k’ofar d’akinsa... Bata izinin shigowa yai yana mai d’an takowa daga cikin closet d’in... Aunty Daula ta shigo sallama saman bakinta tana fad’in ya fito su karya su d’au hanya...
Daskarewa tai tana dubansa yanda ya fito sak ango... Aunty Daula ta gaza b’oye Farin cikinta tana fad’in “Masha Allah Yayansu... Ka fito ras dakai...”

Murmusawa yai kad’an kana yace “Aunty wai meke faruwa ne... Dan Allah ki sanar dani...”

Ta kuma murmusawa a hankali kana tace “Ba’aji mutuwar sarki a bakina ba... Amma before anything, we’re all waiting for you downstairs, Daddy yace baiso mu makara... Muna jiranka...” Bata jira cewansa ba ta fice cikin sauri tana kuma murmusawa...

A hankali ya fuzar da iska mai d’umi kana yasa kai ya nufo k’asa....Su Humy har suna had’e baki wajen cewa “Woow kayi kyau Yaya...”
Ijlal tace “Kaima yau ka zama Daddy ne, ka saka irin kayanshi...” Gaba d’aya suka d’an dara..
Humaira ta kuma cewa “I’ve never seen wanda babban kaya ya mishi kayu irinka ba Yaya.. Pls ka dinga sakawa kaji...”
Murmushi kurum yai had’ida shafa kanta, idanunsa naga mahaifinsa da ya kasa janye nashi idanun daga Barin duban Khalid d’in, ga wani musulmin murmushin Farin ciki saman fuskarsa... Shi kanshi d’an nashi ya masa kyau har ya gaji, ga wani girma da k’warjini na musamman da suka sauk’ar masa... Aunty Daula tana satan kallon d’ah da mahaifin yanda suka zubawa juna idanu gwanin ban sha’awa da tausai... Cikin sauri ta shiga serving Khalid d’in tana tambayar shi idan akwai wani abinda yake so...

Shidai Khalid gaba d’aya bai wani iya cin abincin ba, ya k’agu baiji shirin Daddy akansa ba... Aunty Daula ta dubi su Ijlaal da suka ida cin abinci tace maza suje Karima ta ida shiryasu, idan zasuyi fitsari ma duk suyi kafin su d’auki hanya.. Itama dai mik’ewa tai dan ta lura d’ah da mahaifin suna buk’atan kad’aicewa suyi magana...
Dining area ya rage saura su biyu, Khalid sai juya spoon yake cikin mug, da ganinsa kasan hankalinsa bai jikinsa... Kaman daga sama saijin hannun Daddy yai saman nashi...
Ya d’ago a hankali yana duban mahaifin nasa
A hankali Daddy yasa duka hannayensa ya kamo kafad’un Khalid ya mik’ar dashi tsaye suna fuskantar juna....
Murmushi saman fuskar Daddy, kana iya hango kwantattun k’walla cikin idanunsa lokaci guda yake furta “You look very handsome my son.... Kai d’in a yau zaka kuma cika babban mutum, idan ban tab’a fad’a maka ba Khalid toh yau zan fad’a maka... I am very proud of you Son, kai d’in ka cika d’a mai biyayya... Na gwadaka ta hanyoyi daban daban kuma duk kaci jarabawarka.... Ko yanzu na bar duniya nayi imani kaidin zaka iya kulamin da ahalina... Allah Ubangiji ya maka Albarka, ya albarkaceka da zuri’a d’ayyiba masujin k’an iyayensu da yi masu biyayya kaman yanda kai mana....Ina kuma fata zakai Farin ciki da zab’in da nai maka da kuma hukuncin da na yanke a gareka...”
Izuwa lokacin zuciyar Khalid tai rauni sosai.... Cikin sauri ya kamo hannayen Daddy, cikin k’ok’arin dakewar murya dukda rauni da yakeji daga can k’asar zuciyarsa ya soma fad’in “Daddy dik abinda ka yanke akaina kayi daidai... Kuma bazan tab’a questioning d’inka ba... And zaka sameni ina mai yi maka biyayya.. I know you love me and bazaka zab’a min abinda zai cutar dani ba....Na sani our family isn’t perfect, we have our differences, if there’s one thing da mutum bazai zab’a ba shine family d’inshi... We don’t choose our family... Haka Allah yake gudanar da al’amarinsa... Saidai mu wayi gari mu ganmu tareda mutanen da yaso ya ganmu dasu ya kuma zab’a mana a matsayin family d’inmu... Daddy inaji a cikin zuciyata cewa nid’in mai sa’a ne da Allah yasa na kasance d’anka.... Thank you for everything Daddy....”
Hawayen da Daddy Ke mak’alewa suka ziraro, lokaci guda ya rungume d’ansa sosai cikin jikinsa yana jin k’aunarsa na ratsa zuciyarsa...
Aunty Daula dake hangosu daga kitchen share hawayen da suka gangaro mata, tausayin d’ah da mahaifin ya cika zuciyarta....

Murmushi Daddy ya sakar mashi yana mai gyara masa zaman hularsa kana ya warware agogon dake d’aure hannunsa ya shiga d’aurawa Khalid d’in da kanshi... Murmushi kwance saman fuskarsa, shima Khalid d’in murmushi yake...
Daddy yaci gaba da fad’in “There... Now you look even more handsome...”
Khalid ya kuma sakin murmushi kana yace “Na gode Daddy...”
Shafa fuskarsa Daddy yai kana yace “Khalid a yau zamu tafi amsar aurenka da macen da Allah ya zab’a maka a matsayin abokiyar zama... Are you happy...?”

K’ak’aro murmushi yai dikda tsananin bugu da k’irjinsa keyi kana yace “Yes... Yes Daddy... I’m very much happy...”
Kana ganin yanda yai maganar zaka fahimci k’arfin hali ce kawai...

“Well, sai mu d’au hanya kar mu makara...” Ya k’arashe yana mai kiran matarsa Daula...

***

Kai da Kaga Hafiz Kaga ango, sai watsa k’amshi yake yasha wanka cikin dakakkiyar shaddarsa, bakinsa kaw ya gaza rufuwa tamkar gonar auduga, Sawwama dai bata tankasa ba har ya ida shirinsa, koda yace mata babu fatan Alheri sai ce masa tai fatan alherin kenan ta gama masa da ta had’asa dasu Babba Duna.... Ya isa yai kissing goshinta yana murmusawa kana yace “Tabbas kin bani gudumawar da tafi ta kowa....Bazan tab’a mantawa ba, nai miki alk’awari...”

Murmusawa tai kana ta mik’e ta d’au mayafinta dake lank’aye saman k’ofa...
“Rakiya zakimin...?” Ya tambaya yana dubanta...

Murmusawa tai kad’an kana tace “A’a kaje bikinka...”

Hafiz ya d’anyi rau rau da idanu cikeda shagwab’a kana yace “Bazaki raka mijin naki tarbo k’anwarki ba... Kinsan fah kece Yayar....”
Nanma murmusawa tai kana tace “Zanso nai maka rakiya amma nima wani auren zan tafi... Mahaifiyata da mijina zasuyi aure rana guda...”
Da mamaki Hafiz ke dubanta kana yace “Kina nufin Magajiya yau take aure...?”

Jinjina masa kai tai kana tace “K’warai kuwa, Kaga dole na tafi can na k’yaleka da amaryar ka kusha shagali nima na taya nawa mahaifiyar nata shagalin....”

Ya murmusa ya shafi fuskarta kana yace “Kice ina mata fatan alheri, kuma nayi murna sosai... Daga baya zanzo har gida nai mata murna...”

Sawwama ta jinjina kai tace “Zan isarda sak’onka in sha Allah...” Daga haka sakai tai abinta ta fice, tabar Hafiz shi kad’ai sai shafan hab’a yake yana sakin murmushi.....

***

Cikin dabara ya samu ya tsinka igiyar da tin jiya yake k’ok’arin b’allata da akai amfani da ita wajen d’aure masa hannu...Hannayensa gaba d’aya sunkuwa b’aci da jini alamun yaji jiki wajen kwancen hannun... Ya waiga yaga har yanzu dai masu tsaron nasa bacci suke basu farka ba dan jiyan tatil sukai da barasa, tinani ya somayi, mai zaiyi yanzu, idan yace zai gudu a wannan daji da baisan yaya aka shigo dashi ba baisan ta ina zai soma bi ba, baisan wata hanya zai soma bi ba tinda kanshi cikin buhu aka shigo dashi... Ya dafe kansa kad’an yana tinanin abinyi, kuma dole yai acting very fast kafin su tashi, aljuhun d’aya daga cikinsu data d’an zame ya hango wayar salula... Ya sauk’e ajiyan zuciya a hankali kana ya lab’ab’a ya d’auki wayar da k’yar da sand’a....
Dubawa yai yaga chaji ya kusa k’arewa one percent ne... Dole yai dik yanda zai yayi making call d’in cikin sauri....

SameenaAleeyou📚

*INDA RAI*
_................DA RABO_

*87*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Kasancewar k’aramar wayace yasa Akram baisha wahala wajen bud’eta ba, sauri yake ya shigar da lambobin dan sai warning battery d’in yake masa yana nuna alamun low battery....
Wani ikon Allah lambar da ko nashi lambar waya bai haddace kamanshi ba sai yaji yana k’ok’arin kufce masa tsaban tashin hankali da ya tsinci kansa ciki... Ga wayar gab take da d’aukewa gaba d’ai danma Allah yasa Nokia akwai amanan rik’e chaji ne.... A hankali ya soma k’ok’arin saita kansa yana jera lambobin a natse....

****

Tsaf ya ida shirinsa cikin manyan kaya dan tuni Daddy ya sanar dashi cewa yau ake d’aurin auren Khalid, sam bai kawo gidan da Khalid Ke neman aure gidansu Zulfa’u bane, all he knows shine Akram ya yaudaresa zai kumayi k’ok’ari ya mance da komai, dan haka ya yanke tafiya auren Khalid maimakon amsawa Akram aure kaman yanda Akram d’in ya buk’ata ta bakin abokinsa Yusuf....
Chapter 129 · 0% Book details