← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 198

Sashe 18

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saida ta gama jifansa da harara kafin ta nufesa a fusace.....

Jikin mirror d’in motarsa ya hangeta tana zuwa hasken wutan lantarki ya haske fuskarta wanda bai faye haske sosai ba, tafiyarta kawai zaka gani ka fahimci tayi shirin juye ruwan masifa...

Cikin sauri Khalid ya katse wayar da yake da ‘yar uwarsa Siyama kafin ya juyo domin fuskantar masifatunsa....

“Malam lafiya meye kuma ya kawoka k’ofar gidanmu...? Yama akai kasan cewa nan ne gidanmu...?” Ta k’arashe tana mai d’ora hannaye a kunkumi tamkar mai shirin rufesa da duka....

Tamkar bazaice komai ba haka ya tsareta da idanunsa har saida Nabilah ta soma taarguwa da irin duban da yake mata gashi ita ta kasa jure kallonsa cikin idanu....

Kallo guda zaka mata ka fahimci she’s not comfortable....

Harara ta jefo masa suka kuwa had’a idanu, lokaci guda ta d’auke kanta had’ida doka uban tsaki tace “Banda lokacin tsayuwa a nan, kuma wllhi idan Abbah na ya fito ya taddaka a nan kace wajena kazo zan sa almajiran nan su rakaka da duwatsu....”

Daga haka sa kai tai zata shige saiji tayi ya finciko hijab d’inta ta dawo da baya.....

Tsoro da mamaki ya wanzu saman fuskarta, ta lura wannan baida niyan ficewa daga rayuwarta cikin gagggawa, a hasale take fad’in “Wai don Allah mai kake nema daga wajena, what exactly do want from me....?”

“You wannan know...?”

Ya tambaya yana kashe mata rikitattun idanunsa had’ida murmusawa da gefen baki, lokaci guda kuma ya gimtse kana yace “First of all tambayarki nakeso nayi... Shin a gidanku ba’a koya miki furta sallamawa mutane ba... Ko kuma ba’a koya miki gaida manya ba....?”

Murmushin rainin hankali Nabilah tayi kana ta fad’i cikeda tsiwa “Wannan kuma kanka ya kamata ka tambaya, k’ilan ba’a koya maka daraja mace ba a duk yanda ka ganta... Kuma wllhi ka kuma janyomin hijabi zan maka ihu a unguwar nan....”

Khalid ya kafeta da idanu yana mamakin hali irin na Nabilah...

Sakai tai zata kuma tafiya taji ya ambato sunanta karo na farko sannan batasan ya akai yasan sunan nata ba, take k’irjinta yayi wani irin bugawa...

“Nabeelah....!”

Cak ta tsaya ba tareda ta juyo ba, saida wasu dak’ik’ai suka d’an gifta kafin yaci gaba da fad’in “Idan kinfiso na baiwa Abbanki sak’on ya shiga miki dashi fine zan jirashi ya fito na bashi don na tabbata shi zai tsaya ya saurareni...”

Saurin juyowa tai tana dubansa hannunsa rik’eda envelop fuskarsa babu alamun wasa....

Mamaki ya kamata, wani sak’o ne wannan ita mai ma ya had’ata da wannan mutumin...

Cikin sauri ta dawo da baya tamkar zata kifa da k’asa... Khalid ya saki murmushi wanda idan bashi d’inba babu mai fahimtar yayi....

Wannan karon cikin kwantar da murya take maganar

“Malam don Allah mai kake nema wajena, I don’t know you, bansanka ba bansan mai kake nema a wajena ba, ka kuskureni da mota kamin wanka da ruwan tab’o kaje na yafe maka, amma Dan Allah ka fice a rayuwata, I beg of you please....” Ta k’arashe tana had’e tafukan hannayenta waje guda...

Gyara tsayuwarsa yayi kana yace “Karkiyi tunanin bibiyarki nake... You see this bruise...” ya k’arashe yana nuna mata ciwon goshinsa da Sameer bai jima da masa dressing ba kana yace “Don’t you think I’m too handsome to have it on my face....?”

Dubansa Nabilah tayi baki a sake don batai zaton abinda zaice ba kenan, lokaci guda yaci gaba da fad’in “And my car... Ke tinda kike a wannan lungun naku kin tab’a ganin new brand irin wannan....?”

Izuwa lokacin Nabilah ta gama isa wuya, ta lura wannan d’an rainin hankalin wulak’anci kawai yazo ya mata... Zatai magana ya mik’o mata envelope d’in yace “I want you to take look at this....” Yayi maganar yana bud’e envelop d’in.... Lokaci guda yaci gaba da fad’in “This is a list of all the expenses on the car that you’ll need to cover... Take... Karb’a mana....”. Ya k’arashe yana d’aura takardan saman hannunta....

Huci kawai Nabilah keyi sanda tabi takardan da kallo, Khalid ya kuma murmusawa kafin ya nufi motarsa yana fad’in “Make sure kud’in sun zama ready kafin na bar garin nan only then zan fice a rayuwarki kaman yanda kika buk’ata....”

Kallo ta bisa dashi da gaske motarsa ya nufa ya barta da zungureriyar takarda cikeda zeros, cikin sauri ta take masa baya, zamansa cikin motar da wuya yajiyo k’aran keta takarda, da tsananin mamaki ya juyo yana dubanta...

Tas ta keta takardan kafin ta watsa masa cikin motar nasa tana fad’in “Bazan biya ba, ai bani nace kayi tuk’in ganganci, kuma wllhi ka sake zuwa k’ofar gidan nan duk abinda ka gani kai ka jiyo....”

Tana ida fad’in haka tasa kai tayi shigewarta cikin gida... Su Sadiya da Mamanta Karima suna lab’e suna gulma Nabilah tazo shigewa nan kaw suka sha jinin jikinsu don sarai tasan sun jima wajen suna kwasan gulma....

Tsuka ta buga had’ida furta aikin kenan, tasan tinda Sadiya da mamanta suka ganta Mamani taji wannan batu an gama amma ita yanzu bata Mamani take ba damuwarta wannan d’an rainin hankalin ya fice mata daga rayuwa.....

***
Yau bayan an ida sallan asuba Sameer ma zama yayi kaman yanda yaga dattijan unguwan suna zama d’aukan karatu wanda ya danganci wasu littafan na addini...

Sosai abin ya birge Sameer, yanaso yaga mutum na neman lahirarsa ba duniya kurum ba kaman yanda nasa iyayen suka d’ora rayuwarsa bisa neman duniya zalla, ya lura da mutumin da ya gyara masa mota kwanaki biyu da suka shige, dukda cewa mutumin ba mutum bane mai yawan magana hankalin Sameer ya kwanta dashi...

Bayan an ida karatu, Sameer ya k’arasa ya gaida liman kana yabi sauran dattawan d’aya bayan d’aya suna gaisawa da yazo kan Abbah fari’arsa ta k’aru, shima Abban sai yaji wani shauk’i na d’ibansa na ganin saurayin....

Shi kanshi Sameer d’in ya lura da yanda Abbah yaji dad’in gaisar dashi da yayi tareda alamun bai mance shi ba, tare suka fito daga masallacin Sameer ya gyarawa Abbah takalmansa ya saka...

Suna tafe Abbah ya dubesa fuska d’aukeda murmushi kana yace “A nan unguwar kake ne...?”

Sameer ya d’an girgiza kai kana yace “A’a zuwa dai nayi Baba, asalina mutumin Kaduna ne iyayena da dangina duk suna can, aiki ya kawoni garin nan nake zaune gidansu Abokina, gidan Marigayi Alhaji Sa’adu Sharubutu... Munyi karatu tareda d’ansa Shamsudden...”

Abbah ya jinjina kai jiki a sanyaye tabbas babu yanda za’ai wannan saurayi ya zama nasa d’an hasashensa ne kurum ya basa hakan, baisan dalili ba amma har cikin ransa yakejin wannan saurayi da ya sanar dashi sunansa Sameer...

Har k’ofar gida Sameer ya rako Abbah kana ya masa sallama, ya lura da yanda yanayin Abban ya canza tinda ya basa tak’aitaccen labarinsa...

Sameer yasa kai zai shige Abbah ya kirawo sunansa....

Dawowa da baya yayi cikeda risinawa,

Abbah yace “Idan bazaka damu ba kazo muci abincin dare a gidana...”

Sameer ya fad’ad’a murmushinsa kana yace “Kai Baba na gode matuk’a da wannan karammawa In sha Allahu zanzo...”

“Amma Baba wani hanzari ba gudu ba shin zan iya zuwa da abokina Shamsu..?”

Abbah ya jinjina kai yace “Kazo da duk mutanen da kayi niyya Malam Sameer ni na gayyaceku...”

Sameer ya jinjina kai cikeda jin dad’i kana yace “Godiya muke Baba In sha Allah zamuzo...”

Abbah yace “Ka kirani Abbah haka yarana ke kirana...”

Sameer ya kuma jinjina kai had’ida furta “Abbah...!”

Ba Sameer d’in kawai da ya tsinci kansa cikin wani irin yanayi harta Abbah saida yaji wani shauk’i na sauk’ar masa...

Fuskar Abbah kurum zaka kalla ka fahimci na cikin farin ciki, Mamy ta lura da hakan saidai bata tambayesa ba, yinin ranan zubur Abbah cikin farin ciki yake, Mamy na hankalce dashi ba abin ta tambayeshi ba ta janyo wani abin don ba kasafai yakeson yawan tambaya ba tun bayan b’acewar Ma’aruf, don haka taja bakinta ta d’inke..

Da yamma da zai fita yace da ita sunada bak’i a shirya masu sauk’a..

Babu musu Mamy ta amsa mishi had’ida mishi a dawo lafiya, as usual a ciki ya amsa mata...

Shamsu sai mita yakewa Sameer cewa shi babu ruwansa da kowa a unguwar ba abinda zai kaisa wani gida dinner, da k’yar Sameer ya shawo kan Shamsu ya yarda zai rakasa, Khalid da yazo masu sallama ma aka had’a dashi sam yak’i shikam a cewarsa yanada wajen zuwa, Khalid d’in ne ya basu ride sanda zai koma...

Ganin gidan da suka nufa ya sanyasa canza ra’ayi ya bisu suka d’unguma zuwa gidan gaba d’aya....

SameenaAleeyou 📚
[12/01, 22:08] +234 703 745 3539: *INDA RAI*
_...............DA RABO_

*17*

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*

Cak Nabila ta tsaya tana kuma jin sauk’ar ruwan tab’on nan a jikinta wanda ya wanketa har fuskarta... Tayi k’ok’arin bud’e idanunta da harta suma tab’on ya tab’a... Babban abinda yafi bata takaici shine da alama shashashan matuk’in motar da ya mata wannan aika aika baisan yayi ba....

Kallo tabi motar tasa dashi wanda yake ruwan shud’i k’irar Mercedes, duk duniya babu wanda ya tab’a mata wannan wulak’ancin, lallai wannan mutumin da gani babban d’an rainin hankali ne wanda baisan mutunci tinda baisan ya tsaya ya bada hak’uri.... Zuciyar Nabila taci gaba da tafarfasa, kasancewar hanyar unguwar cike yakeda kwarai da k’wazazzafo yasa sam motar bai b’ace ma ganinta ba, tamkar mai neman wani abin haka ta shiga waige-waige..., Can ta hangi wata dutse, tuni ta k’arasa ta d’auki dutsen tana mai ci gaba da huci da tafarfasa...

Cikin sassarfa ta kusan isa ga wannan had’edd’iyar mota data mata mummunar wulak’anci da babu wanda ya tab’a mata irin hakan..,

Daidai gate din gidan da yake tunanin nan ne gidan da Sameer ya turo masa address yayi parking motar naci gaba da diri still idanunsa kan wayarsa da alama layin Sameer yake nema...

Khalid bai ankara ba saijin sauk’an ringimemen dutse yayi daidai glass din k’ofar glass din dake saitinsa na matuk’in mota...

Tuni wayarsa ta zame yai saurin kare fuskarsa da hannayensa yana karanto innalillahi... Saidai tuni glass din ta sameshi a goshinsa yanda ta tarwatse lokaci guda....

Cikin tsananin tashin hankali had’ida firgici ya finciki marfin motar nasa ya fito yana rarraba idanu don ganin maike faruwa dashi., tsawa ya sauk’a masa ko kuwa bomb ne ya kuskuri tashi dashi...
Chapter 18 · 0% Book details