Sashe 116
Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
***
“Bazan barta ta koma hannun wannan Animal d’in ba Yusuf... I must do something, ai kaji abinda yace, mahaifinsa Ke nuna iko akanta, I know Zulfa’u, nasan akwai abinda Ke holding d’inta back shisa ta kasa barina na turo... Amma wannan karon zan yi iyaka k’ok’arina naga ta bari iyaye Sun shiga maganan once and for all... She’s not safe da wannan lunatic d’inba tareda ita, d’an uwanta ne zai iya kasancewa da ita a koda yaushe... I really need to protect her... Bazan barta da wannan mahaukacin around ba...” Ya k’arashe cikin tsanin nuna damuwa yana mai zagaye parlorn...
Yusuf ya nusa kad’an kana yace “Toh miye abinyi...?”
Wani duba kurum Akram yai masa ba tareda cewa komai ba kana zira hannayensa cikin aljihu...
***
A can gidan su Zulfan ma itada Atika k’ulewa sukai k’uryar d’aki...
Atika ta rapka uban tagumi tana dubanta “Toh ko Aunty B zamu sanarwa, magana ta gaskiya Zulfah Hafiz baida hankali, kar watarana ya miki wani abin kinga yau k’iris ya rage bai mareki bakin kwalta ba, badon Allah ya kawosu Akram ba da bansan ya abin zai kasance ba... Wllhi nidai a nawa shawarin tun wuri gwara ki tsaida miji kafin wannan Baba Alhajin ya kuma zancen maidaki gidan Hafiz...” Ta k’arashe tana mai tab’e baki...
Siririyar iska Zulfah ta fuzar had’ida sauk’e gajeriyar ajiyan zuciya kana tace “Karkiceda Aunty Bara’atu komai, kinsan halinta da d’aukan abu da zafi yanzu sai taje har gidan Hajiya ta taka ma iyayen Ya Hafiz birki, shi kuma Baba Alhaji ba bari zai ba har gida zaizo ya sami Abbah ya d’aga mar hankali a banza... Kawai ki k’yaleni I can handle him...”
Atika dai dubanta kurum take baki a tab’e kaman daga sama suka jiyo ringing d’in wayar Zulfa’u ba kowa ke kira ba illa Akram...
***
KADUNA
Nik’i nik’i take shigowa da akwatin kayan nata sai faman haki take dan tin daga harabar gidan driver ya ije mata, Kubura dake gefen Ostriches tana jefa masu abinci sai cazgan dariyar Yesmin take tana ayyanawa cikin zuciyarta “Madalla Allah shi k’ara...” Ta kuma tintsirewa da dariya tana kuma jefa ma dababbobin abinci, sai Yesmin ta d’ago kai tana harararta sai Kubura tai kaman batasan da isowar nata ba... Yesmin tai k’wafa tana mai ci gaba da jan luggage d’inta....
Cikan murya kaman ta mai wak’a Kubura ke jifarta da habaici sanda ta iso daidai yanda take “Mutum yace bai yinka bai sonka, sai ka gane ka kama kanka... Shidai cusa kai babu k’warjini babban yawa ne... Anyiriri K angon K Khalid angon Kubura kana yafasu muna jin dad’i....”
Yesmin tai birki tana bintada kallon mamaki “Ke da waye kike...?”
Kubura ta shiga waige waige tamkar mai duba wani abin, Yesmin data dad’a k’uluwa tace “Dake nake k’aramar maras kunya, tsaban kin rainani kina ganina da kaya bakisan kizo ki amsa ba sabida kin sami d’aurin gindi daga wajen Ammi koh...?”
Dariyar rainin hankali wannan karon Kubura tai kana tace “Toh wama yasan da zuwan naki, ai ce nake dagani sai dababbobin nan ne a wajen nan...”
Yesmin ta kuma harzuk’owa tana fad’in “Ke ni kike kira dabba...?”
Kubura ta Kuma murmusawa tana wani jijjiga kana tace “Wlhi ba’a bakina kikaji ba...” Tayo kanta gadan gadan a daidai sanda motar Siyama ta sako hanci....
Tana ida parking suka fito itada Laila, dan yanzu kullum Lailar na lik’eda ita...
A guje Kubura ta tafi tana fad’ida Siyama “Oyoyo Aunty na sannu da dawowa..” Ta k’arashe tana amsar handbag d’in Siyamar...
Harara Siyama ta galla mata kana tace “Saikac banga rashin kunyar da kike tsulawa Yesmin ba, kin wani kwaso gudu kin taho nan...”
Yesmin tace “Wllhi cousin yarinyar nan d’aurin gindi ta samu daga wajen Ammi shisa take fetsararta san ranta, wai harda kirana dabba kiji fah...”
Kubura baki a ture tace “Wllhi Aunty Siyama ni bance mata dabba ba, aidai a bakinta kikaji...” Ta k’arashe tana juya idanu...
Girgiza kai kurum Siyama tai kana tace “Bani jakata ki d’auki jakan kayanta ki shigar mata...”
Kubura ta kuma b’ara fuska tace “Kut Aunty gani fah wannan tilin kayan ina zan iya...” Kallon da Siyama ta watsa mata ya sanyata d’aukan ta nufi cikin gida tana mai watsawa Yesmin muguwar kallo...
Siyama ya maido da dubantaga Yesmin kana tace “Wai dawowa kikai ne...? I thought Aunty tace sai bayan biki keda gidan nan...”
Yesmin tai kicin kicin da fuska tace “Wllhi bazan iya va cousin, I’m dying to see my Kay, bazan iya kwanakin nan ban ganshi ba...” Daidai sanda idanunta suka sauk’a kansa ya fito daga sashensa waya manne kunnensa, yana sanye cikin shiga ta k’anan kaya Red shirt da yayi tsananin fito da kyan fatarsa, gaban rigar an rubuta _Mango_ da ruwan zinari sai faded jeans, k’afafunsa sanye suke cikin takalmi k’irar sandals kalan bak’i.. Ya mata kyau matuk’a wanda har su Siyama da Laila suka shige cikin gida bata fahimci hakan ba....
Kaman wanda akace ya juya ya hangota ta kafa masa idanu tamkar tsohuwar mayya....
SameenaAleeyou📚
*INDA RAI*
_................DA RABO_
*82*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Cikin ranshi yake furta wannan yarinyar idan mayyace ta kama mutum toh harta b’argon dake cikin k’ashinsa sai ta lashe.... Kaman daga sama ya jiyo muryarta tana fad’in “My Kay badai fita zakai ba...?”
Mamaki ya hanasa furta komai, Yesmin ta d’an murmusa a hankali tana juya idanu kana tace “Yi hak’uri ko gaisawa bamuyi ba na tsareka da tambaya....”
Batakai aya ba ya katseta “Ke wai ke wata irin mayyace... Wai tsaya ma what’s your class of degree....?”
Ta dubesa da mamaki sai kuma ta murmusa ta mance tambayar da ya mata ta farko saita biyun take yunk’urin amsa masa “I graduated with second class upper...Ashe fah bakaje grad d’ina ba su Ammi ne sukaje....”Tai maganar tana kuma yauk’i had’ida juya idanu....
Gajeren murmushi yai wacce tafi kama data takaici kana yace “Aka sai maki result dai, don a ajin dak’ik’ai ban tab’a cin karo da babbar dak’ik’iya irinki ba, da kina gane karatu kaman yanda kikace da baki tsaya b’ata lokacinki wajen mutumin da sam baisan kinayi ba... And let me remind you this... Wllhi wllhi... Kinji na miki rantsuwar musulmi, kika kuskura kika sake ki yarda aka aura miki ni Khalid Mainasara a matsayin miji, sai kinyi nadamar da baki tab’a irinta ba tinda kika fad’o duniya.... So advisably ki sami Ammi tinda gaki nan Allah ya kawoki ko nace nacinki ya dawo dake, ki rok’eta ta taimake ki ta rufa miki asiri ta janye wannan auren shiriritan da take yunk’urin had’awa... Dan wllhi kika sake kika yarda kika biye mata akai wannan auren, na miki alk’awarin ganin dark side d’ina da duk duniyar nan babu wanda ya tab’a ganin sa.... It’s a promise...!” Yana ida fad’in haka bai jira cewarta ba yasa kai yai ficewarsa yana kuma making call....
Yesmin tabisa da kallo hawaye tab idanunta, wannan wulak’anci na Khalid ya isheta, inama zata iya ciresa cikin zuciyarta da tayi hakan ko dan samun farin cikinsa ne, amma hakan bamai yuwa bane, zataci gaba da juran duk wani wulak’ancinsa tasan wuyarta suyi aure ne tuni zata koya masa yanda zai k’aunaceta... Ta saki murmushi a hankali had’ida goge hawaye mai d’umin da ya ziraro mata....
Fitowar Siyama da Laila kenan zatai rakiyawa Lailar ta hangi Yesmin tsaye tana faman goge hawaye ta k’urawa motar Khalid dake ficewa daga gidan idanu.... Sallama Siyama tai da Laila, dan mai d’aukar Lailar waje yai parking, kana Siyama ta k’araso wajen Yesmin... K’uri tai mata tana duban yanda take matsan k’walla....
Siyama ta dafata a hankali kana tace “Wa ya sakaki kuka cousin...? Tell me was it Khalid...?” Cikin sigan lallashi Siyama tai maganar
Yesmin ya kuma goge hawayenta tana mai jinjina kai ga tsananin rawa da muryarta keyi “Who else cousin...? Sauk’ata kenan, amma irin tarbar da zaimin kenan.... Tell me please cousin, Am I really a bad person... Why is it so hard for him to understand how much I love and care about him... Wllhi ina son Khalid fiyeda yanda nake son kaina cousin...” Ta k’arashe sabbin hawaye na ziraro mata...
Numfasawa Siyama tai kana ta d’an dafata kad’an “Yesmin ba laifinki bane dan Allah ya jarabceki da sonsa, amma kema bak’in nacin tsiya ne dake dole ki hau masa kai, karfa ki mance a train station yai tafiyarsa ya k’yaleki last rabuwarku amma har kin kuma kwasan k’afafu kin dawo masa, Ke ko ‘yar ajin nan ta mata baki d’an ja ne, kiga dai nida Sameer dikda na sani muna matuk’ar son juna nakan d’an basa space dan in nuna masa matsayina da darajata a wajensa amma ke ko yaushe sai ki bari Khalid yaita cin kashinsa akanki, toh wllhi ki farga dan in ba haka ba, hardai kina nan da wannan halin nacin tsiyar naki kika auresa a haka sai ya gasa miki gyad’a a tafin hannu, I know Khalid so well, girma ne ma ya d’an canzasa, sanda muke k’uruciya babu wanda ya ragarma toh wllhi kiyi hattara ki d’an koyi jan aji koda d’an kad’an ne....”
Baki a ture Yesmin Ke dubanta kana tace “Banja ajin ba ya cazga min wulak’anci balle naja masa, ni wllhi idan dai akan my Kay ne saidai na yarda banida ajin...” Ta k’arashe tana mai nufan cikin gida....
Siyama ta murmusa a hankali kana tace “Allah ya baki sa’a...”