← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 143 OF 198

Sashe 143

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tasa kai cikeda takaici zata fice dan wani irin haushin mijinta ne ma ya taso mata, wato shima ya munafunceta ne ashe yasan wani sirri da ita bata sani ba, yasan Usman ba d’an Mamani bane amma bai tab’a koda gigin gaya mata ba tsawon shekarun nan da suka jima suna k’ulla makirci tare... Lallai ta yarda namiji ba d’an goyo bane... K’wafa tai tasa kai zata fice dan yau ji take dik wanda ya tink’areta kansa zata huce duk wani takaicinta.... Kaman daga sama Aunty Bara’atu ta hangota zata fice cikin sauri ta k’arasa gaban Haule had’ida shan gabanta, dakakkiyar murmushi saman fuskarta “Haba Haule har zaki fice babu sallama... Akwai sauran buduri fah dan nasan har yanzu bakisan wacece matar Ma’aruf ba... Kuma sai ki tafi babu ko sallama duk irin wannan kwalliya da kika cab’a... Haba Haule ni ce fah AMINIYARKI ta sirri...!” Ta k’arashe tana kuma sakin murmushi kana tace “Ko yanzu Kasuwa ta watse Haule d’ankoli yaci riba... Mariya dai gata nan daram dak’am saidai gani daga nesa ga ‘yanuwanta kewaye da ita, ga d’anta Ma’aruf tareda ita... Bugu da k’ari ga ‘ya’yanta sun samu zaratan Maza na k’warai wad’anda Al’umma Ke alfahari dasu.... Wa gari ya waya yanzu Haule....?....”
Ta kuma murmusawa kana tace “Barka da shiga duniyar k’unci Haule, aci gaba da girban shuka na tabbata duk abubuwan da kikaji kika gani yanzu na gaba sai sunfi d’imautaki.... Sai a tanadi ruwan barekata a gefe na rage k’unci....” Ta k’arashe tana mai kuma murmusawa had’ida juya idanu lokaci guda ta d’agawa Haule yatsa guda tace “Chau.... Aminiyar Sirri..!”

Haba Haule kaman ta yanki Jiki ta fad’i ta mutu ta huta haka nan taji tsaban bak’in ciki dake cazganta... Tanaji tana gani yanda Mamy da ‘yanuwanta suka cika da farin ciki..... Tamkar wacce ake hankad’ata haka ta fice fuuu tanaci gaba da huci tagajan magajan...
Yara Almajirai sai gudu suke a hanya suna kauce mata a tinaninsu mahaukaciya ce sabuwar kamu.....

Wani kayan tashin hankalin had’ida mamaki Haule ta tadda gidanta,gungun ‘yan daudu ta gane shak’e a k’ofar gidan ga mai gurmi da garaya na kad’a masu sun nufi cikin gidan ga wata mata tsakiyarsu lullub’eda mayafi, sai tik’an rawa suke suna kad’a kafad’a da kwankwaso suna tururwan shiga gidanta... Mamaki ya cika Haule tai birki tana kallon ikon Allah Mai gurmi kaw bai fasa kad’awa ba...
Su Amara da ayarinta dake tsakar gidan suna wak’e Sahariyya da ta fice a hayyacinta tana kuka tamkar ranta zai fice ai birki sukai da nasu shagalin ganin iyayensu Sun faso taro.....

***

A can gidan Aunty Bara’atu kaw dik wainar nan da ake toyawa amaren basuda labari, Zulfah ce ma gabanta ya tsananta fad’uwa musamman dataga ango Akram bai kirata ba kuma bataji daga garesa ba gashi Atika ta kira wayan Yusuf taji ko lafiya yafi abinda yafi amma wayar Yusuf bai shiga, itama Atikar dik abin ya soma damunta musamman da sukaga angon Nabilah ya kasa barin gidan, dan koda suka fice da rana rakiya yaima friends d’insa zuwa masauk’i amma gashi yanzu haka ma ya dawo yana jiran Nabilah a parlor.. Haka dai Atika taita bata baki tana cewa lafiya Akram yake in sha Allah.. K’ila dai kan ango ne yai zafi tinda aure ba wasa bane...

Da k’yar Nabilah ta kuma ficewa wajen Khalid sai faman ture turen baki take tana fad’in itafah an tak’ura mata... Yusrah tana mata rakiya zuwa k’ofa ta juya tana fad’i k’asa k’asa “A sha love lafiya amaryar Bear...”
Harara Nabilah ta galla mata kana tace “Wai bazaki shigo ba kina nufin ni kad’ai zan shiga...?”
Yusrah ta kuma k’unshe dariyrta tace “Wa ki rufamin asiri kada oga Bear yai jifa dani ta taga... Kedai Ina wajen su Addah Zulfah idan kun gama...”Bata jira cewan Nabilah ba ya juya a guje....
Nabilah na kiranta inaa Yusrah ko waigowa batai ba ta shige cikin gida abinta.... K’irjin Nabilah yaci gaba da bugawa... Amma Yusrah tasan kan tsiya datace zatai mata rakiya ta koma... Zatai maganinta ne.... Ta d’aga kai ta dubi k’ofa tasan yana ciki yana jiranta, wani ikon Allah Wai Khalid ne take matuk’ar jin nauyin Keb’ewa taredashi a yau d’in saikace ba Khalid d’in data saba tsefesa da masifa ba... Da k’yar ta iya saita kanta ta gyara mayafinta ta nufi parlorn sallama saman bakinta cikin muryrta da bai fitowa sosai....
Khalid dake zaune yana shafa wayarsa saurin janye idanunsa yai daga wayar had’ida k’urama k’ofar idanu... Teddy bear d’insa ya hango shirye cikin shiga irinta matan aure, yalwataccen mayafi wanda yakai har gwiwarta, tana sanye cikin leshi golden yellow da yai matuk’ar mata kyau dikda fuskanta kife yake a k’asa... K’uri yai ma k’afafunta yanda take takowa a hankali yana kallon zanen flower na lalle da aka rangad’a mata wanda ya dace da kyakyawar fatarta da ya amshi gyara sosai.... Har yanzu ganin abin yake tamkar mafarki Wai Nabilarsa ta zama matarsa... Haka ya dinga tino tun farkon had’uwarsu da irin gwagwarmayar da suka sha kafin su mallaki juna... Tsan tsan k’aunarta na kuma ratsa duk wani k’ofa na zuciyarsa.... A hankali ya mik’e tsaye sanda ta iso cikin parlorn... Har lokacin kan Nabilah na k’asa ya kasa d’agowa ta dubesa sai bugu da k’irjinta keyi... Khalid ya tako a hankali har zuwa gabanta.. Ganin ya taso ya nufota ya sanyata d’an saurin d’ago fuska sai kuma ta maida kanta k’asa... Ta lura ya sauya shiga shima, half Jampa ce dark ash jikinsa kansa babu hula sai sumarsa da yasha gyara ga k’amshin nan nasa ya cika parlorn gaba d’aya...
Shiko Khalid cikin zuciyarsa cewa yake yanzu haka had’o masifar da za’a masa ake tinda gashi ko gaisuwa har yanzu bai samu ba... Kaman wacce taji zancen zucin nasa nan ta soma gaishesa cikin tsananin sanyin murya wanda har saida ya sanya Khalid jin wani abu na tsagar masa, gaisuwa mai cikeda wani irin ladabi ta masa ba irin wanda ta saba masa a baya ba, tabbas ya kuma yarda sud’in ma’aurata ne... Take yaji kimanta na k’aruwa cikin idanunsa a hankali....
A b’angaren Nabilah kaw har ta cire ran Khalid bazai amsa mata gaisuwarta ba ta sinkayo muryarsa na fad’in “Mu zauna mana first... Ko sauri kike ne....?”
Satan kallonsa ta d’anyi tanaso ta danna masa harara amma ta kasa ga k’irjinta dake matuk’ar bugu.... Bata ankaraba saijin tattausan hannunsa tai saman nata, bugun k’irjinta ya k’aru, tamkar rak’umi da akala haka ta shiga bin bayansa har saida ya zaunarta saman kujera... Shima yai masauk’i ma kansa a gefenta... Ta d’an matsa gefe kad’an tana mai gyara zamanta... Yai kaman bai kula da abinda take ba saima k’ok’arin ciro wayarsa da aka soma kira cikin aljihu da yake....

SameenaAleeyou 📚

*INDA RAI*
_...............DA RABO_

*93*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Magaji da fitowrsa kenan daga masallaci an ida sallan lisha, yana k’ok’arin bud’e shago ‘yar wak’ensa a bakinsa sai cin karo da mutum yai zaune gefen shagon ga duhun dare da ya soma shiga...Baiji mamakin ganin Hafiz mak’ale wajen ba saidai yanayin da yaga Hafiz d’in ciki ya d’aga mar hankali.... Tak’ure yake gefen dakalin shagon Magaji very miserable, duba guda zaka masa ka fahimci Hafiz ya fice hayyacinsa gaba d’aya, a idanunsa Engr Mutallab yaita alkhairima jama’an unguwarsu, ya tabbata salon munafunci ne kawai irinta ‘yansiyasa...
Magaji ya d’an dubeshi kana yace “Wai dama nan kazo...?”
Bai amsashi ba saima kauda kai gefe da ya kumayi sakamon hasken wutan lantar da nepa suka dawo dashi ya haske fuskan Hafiz.... Zama gefensa Magaji yai yana mai furta “Abokina, hak’uri da saka ma zuciya dangana da amsar k’addaran cewa Zulfa’u yanzu ba taka bace shine kawai zai ficceka.. Amma duk wannan shiga damuwa da tada hankali babu abinda zai haifar maka illa....” Baikai aya ba Hafiz ya katsesa da fad’in “Kaga dalla Malam ya isheka... Idan wa’azi kake so ka tafi bakin masallaci mana ka d’au speaker, ka wani Zo nan zaka cika min kunne, da wanne zanji da k’watan matata na fin k’arfi da akamin ko da wannan surutur naka... Kuma da kake cewa na amshi k’addarar na rasa Zulfa’u kai waye yace maka na rasata kenan... Wllhi sai yanda k’arfina ya k’are, ba yana gadara shi mai neman takaran kujerar governor ba idan shugaban k’asa ya tsaya takara Zulfa’u sai ta dawo gareni... Babu mutumin da ya isa babu wani d’a namijin da ya isa ya mallaki Zulfa’u bayan ni Hafiz not even wannan D’an siyasan, Ka fahimta...?!!!” Ya k’arashe yana mai mik’ewa tsaye yana wani zazzaro idanu tamkar wani k’waro....Magaji ya murmusa a hankali kana yace “Abokina kenan, bakaci yak’i da yaron gida ba kana tinanin zakaci yak’i da uban Gida...? Hafiz lokaci yayi da zaka daina wannan damuwar, yanzu fah Zulfa’u ba sa’ar aurenka bace....!”
Hafiz dake faman danna masa harara jinjina kai yake kana yace “Na jima da sanin cewa baka k’aunar Farin cikina, bari kaji na fad’a maka tsaban kud’insa baya tsoratani, kyautar da yake ma ta riyace nayi imani dan ba har zuciya bane, wa ya sani ma ko d’an k’ungiyar shan jini ne ace a shekarunsa arba’in da ‘yan d’oriya ya mallaki irin wad’annan k’azaman dukiya aima dole ya tafiyarta ta hanyar siyasa tinda bata tsaftacecciyar hanya aka sameta ba dama... Ni dama ban tab’a sonshi ba tuntuni bak’in munafuki...!”
Magaji ya d’an murmusa kad’an “Hafiz kenan ya kamata kasan cewa ba duka ‘yan siyasa bane suka taru suka zama d’aya, komai da kake gani akwai na gari akwai na banza, ko wace irin hark’ace kuwa ba zallan siyasa ba harta cikin malamai akwai na kirki akwai na banza ‘yan kasuwanni ma’aikatan gwamnati da sauransu ka sani na gari basa k’arewa haka na banzan ma, toh ka dainayin kud’in goro kana zagin jama’a domin kaw Allah zai tsayar daku yai maku hisabi, kuma da kake cewa babu wanda yasan source d’in dukiyarsa ka mance shid’in gada yai daga mahaifinsa, ka mance sune masu Mutallab’s Mining company, kamfanin da gaba d’aya west Africa tayi zarra tayi fice bayan wasu manyan kafanonin da suke dashi, idan har zakai masa k’azafin d’an k’ungiyar asiri bakai masa adalci ba..”
Chapter 143 · 0% Book details