← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 198

Sashe 12

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallo d’aya ya mata yaji zuciyarsa na masa tsananin k’una, wato Muhibbah tasan lagonsa tasan shi wane iri mutum ne, tunda ba wata matar yakedashi ba babu yanda za’ayi ya iya k’aurace mata shiyasa take abunda taga dama don tasan duk fushin da zaiyi zai dawo gareta...

Bata ankaraba taji dakakkiyar muryarsa na fad’in “Tashi ki ficemin a d’aki, kuma kar na kuma ganinki cikin d’akin nan kinajina koh....”

Da tsananin mamaki take dubansa kana tace “Ban gane ba, ni kake kora....?”

“Do I need to repeat myself... Ki tashi ki fice nace..!!” Wannan karon cikin tsananin daka tsawa yayi maganar wanda saida ya figita Muhibbah ta mik’e babu shiri....

“MA’ARUF ni kake kora daga d’akinka, ka mance abinda Baba yace maka akaina...?”

A zuciye yayo kanta yana k’ok’arin kai maita mari sabida tuno tarin kuncin rayuwar data jefasa ciki dukda kyakkyawan alak’arsa da jama’a, bai marenta ba sai sauk’e hannunsa da yayi tamkar ya tuna wani abun kana yace “Get out....”

Kallo ta bisa dashi don bata tab’a ganinsa cikin tsananin b’acin rai irinta yau ba...

Sa kai tayi zata shige tana fad’in “Fine zan fice maka a d’aki amma ka sani nima duk randa ka kwaso buk’atarka ka kawo gareni zan rama, kuma idan akan yara ne ai sunada Nanny mai kuladasu sannan yawan fita da nake ai gani nayi campaign nake maka....”

Bata kai aya ba taji ya damk’ota ya dawo da ita cikin d’akin yana mai ci gaba da huci....

Idanuwansa sun kad’a sunyi jazir yake fad’in “Idan kina tunanin ni Ma’aruf zan nemi wani abu you’re very much mistaken, albarkacin Abbah kike zaune a gidan nan, sannan daga rana mai kaman ta yau ki sani bani buk’atar komai daga gareki, idan kinga dama yawonki ya kaiki har birnin sin babu matsalata ballantana damuwata, gameda campaign kuma I did not ask for your help nor your support, in fact I don’t need any of these from you.... Now, get out.... Get out I said....!”

Ya k’arashe yana nuna mata tangamemen k’ofar d’akin dake bud’e...

Da tsananin mamaki take dubansa kafin tasa kai ta fice zuciyarta na tsananin mata zogi, tana tafe tana mamakin itace yau Ma’aruf Mutallab zai wulak’anta, harda cewa baya buk’atar komai daga gareta...? Tabbas badon tsananin soyayyar da take masa ba da tuni tayi tafiyarta ta bar masa gidansa taji dad’in yawonta da kyau ba tareda fargaba ko tunanin miji ba, tana jin yanda Ma’aruf ya rufe k’ofar d’akin da k’arfin gaske...

Tana isa sashenta ta fad’a d’aki ta d’au waya had’ida kiran aminiyarta Shamzy tana sanar da ita yanda sukayi da Ma’aruf....

***

Har wajajen k’arfe shad’ayan dare baiyi bacci ba, yana nan zaune a parlor yana ci gaba da dialing layinta amma baya shiga...

Shamsu dake tasye jikin k’aramar fridge dake gefen parlorn kallo yabisa dashi jin yanata faman nanata abu guda....

“Com’n Partner.... Pick up your phone....”

K’arasowa Shamsu yayi had’ida zama gefensa ya d’auki remote ya canza daga tashan labaru zuwa na movie kana ya maido da dubansa ga abokin nasa yace “Doc are you sure you’re alright...?”

Fuzar da iska Sameer yayi kana yace “Bazaka ganeba abokina, Siyama has that nasty temper you know, abu k’ank’ani zai b’ata mata rai sannan sam bazatayiwa mutum uzuri ba.... Na tabbata fushi tayi, She is not answering any of my calls... And I miss her... so terribly....”

Murmushi Shamsu yayi kana yace “Then give her space, ka barta ta huce idan Allah ya kaimu gobe you call her again..”

Jinjina kai Sameer yayi kana yace “Wai yaushe zakayi aure ne...?”

Tak’aitaccen murmushi Shamsu yayi kana ya kurb’i ruwa yace “Lokaci muke jira Sameer, May be k’arshen shekara....”

Sameer ya jinjina kai kana yace “Toh Allah sa gaskiyar kenan wannan karon...”

Shamsu ya kuma darawa had’ida mik’ewa yana fad’in “Zancen kakeso Doctor....”

Sameer ya jefa masa pillow yana fad’in “A daina yaudaran yaran mutane haka nan ayi k’ok’ari a nutsu waje guda, first thing tomorrow morning kafin na fice Surgery zan samu Mama da batun, zaka sani ne mayaudarin banza kawai...”

Banda dariya Shamsu baya komai har ya shige d’aki, jimawa kad’an Sameer ya mik’e shima ya kashe kayan kallon ya nufi d’akin da aka masa masauk’i gefe da na abokinsa Shamsuddeen.....

Misalin k’arfe 8:am suka fito a tare daga sashen Mama zasu wuce aiki, Sameer sai dariyar sille Shamsu da Mama tayi yake, dole ne itama taso taga tilon d’anta ya ajiye Iyali amma sam aure baya gaban Shamsu... A haka har suka shige motocinsu Shamsu na shak’e da Sameer ganin yanda ya biyewa Mama suka masa tas...

Kallo ya dinga bin ginin unguwar dashi yanajin wani sanyi cikin zuciyarsa, baisan dalilin jin hakan ba amma can k’asan zuciyarsa ji yake tamkar ya tab’a zuwa wajen, ko wucewa ko wani abu mai kama da haka, gashi dai unguwar mai yawan jama’a ne da hayaniya ba kaman unguwannin da ya taso cikinsu ba tsawon rayuwarsa, dukda hayaniya da yawan jama’a dake cikeda wannan unguwa sai yaji dad’in unguwar da kwanciyar hankali fiyeda tunaninsa, da k’yar ya karb’i tayin Shamsu ya sauk’a gidansu da niyyan yin kwana biyu kafin ya samu nasa apartment d’in don da hotel ya nufa amma Shamsu fir ya hanasa a dole yazo gidansu ya sauk’a...

Shamsu abokin Sameer ne wanda sukayi makaranta tare a can k’asar India, a lokacin baida amini sai Shamsu harta gidan da suka kama GIDA GUDA ne, iyayen Shamsu sunsan Sameer haka iyayen Sameer sunsan Shamsu, hasalima Shamsu idan ya tafi Kaduna gidansu Sameer yake sauk’a shiyasa wannan karon Shamsun ma ya dage sai Sameer d’in ya sauk’a nasu gidan....

Haka Sameer yayita bin unguwar da kallo murmushi kwance saman kyakkyawar fuskarsa yanajin natsuwa sosai cikin zuciyarsa.....

***

Tana zaune gefensa yana karyawa cikin shirinsa na tafiya kasuwa sai faman zuba santi yake tana jin dad’i da sanyi har cikin zuciyarta, gradually burinta suna kan cika.... Sai faman murmusawa take tana kwarkwasa...

Abbah ya kuma tand’e hannunsa kana yace “Zuba min kunun rabin kofi, Aunty Lami tayi yanda yace Abbah ya shiga kurb’an kununsa yana lumshe idanu...

Kaman daga sama suka jiyo sallaman Mamani rungume da turmin zanin da Aunty Lami ta kawo mata daren jiya, sai faman wage baki take tana ci gaba da k’waza sallama dukda cewa sun amsa mata sallaman nata....

Tuni Aunty Lami ta shiga murmusawa tana kuma sadda kai k’asa had’ida gaida Mamani...

Cikin sakewar fuska Mamani ke amsata tana fad’in “Lafiya lou sirkar arziki, nazo nuna ma d’ana abin arzikin da akewa uwarsa ya shaida...”

Aunty Lami ta kuma murmusawa tana fad’in “Haba Mamani wannan ai ba komai bane ni uwa na d’aukeki.....”

Mamani tana amsa gaisuwar Abbah take fad’in “Kaji koh, kaji d’iyar albarka abinda take fad’i, uwa ta d’aukeni....”

Abbah da tun bayan b’acewar d’ansa Ma’aruf da k’yar ake ganin murmushinsa sai gashi nan yana murmusawa a hankali kana yace “Lami kawo mata abincin...”

Kafin Aunty Lami ta basa amsa Mamani ta katse sa da fad’in “Wa ai nikam ‘yar gata ce don ina tunanin kafin naka ya iso gareka nawa ya riga isa gareni...”

Aunty Lami ta kuma sakin murmushi tana fad’in “Dole mu kula dake sosai Mamani ko don mu samu albarka rayuwarmu tayi kyau....”

Haba nan fah Mamani ta kuma washe baki cikeda jin dad’i....

Mamy dake tsaye jikin k’ofar kasa shigowa tayi sabida tsananin sanyi da gwiwoyinta suka mata, take taji hawaye na neman ciko idanunta, a hankali tasa kai ta juya had’ida komawa d’akinta don ji tayi sam bazata iya shiga ba, tausayin kanta ne ya kamata sanda ta zauna saman gado had’ida rapka uban tagumi da duka hannayenta biyu hawaye na gangarowa saman k’uncinta.....

SameenaAleeyou📚
*INDA RAI*
_...............DA RABO_

*12*

Tsaye take tana linke kayan wanki da bata jimada shigowa dasu ba, sam duba wayar mijinta ba d’abi’arta bace, hasalima sai wayar ta k’araci ringing d’inta koda baya kusa bazata d’aga ba sannan bazata duba ba har sai yazo da kansa ya d’aga ko kuma ya samu missed calls, wannan d’abi’ace da mahaifiyarta ta horasda ita domin samun zaman lafiya mai d’aurewa a gidan aurenta....

Sau biyu kenan ana kira batakai dubanta ga wayar ba har ta k’araci ringing d’inta dukda cewa wayar a gefen kayan da take linkewa yake, jin ana sake kira yasata kai dubanta ga k’ofar band’akin ko zai fito amma shiru saima k’aran zuban shower da take iya jiyowa ga uban sauti da ya k’ure a d’aya wayar tasa domin d’abi’arsa ce tun yana matashi idan zai shiga band’aki sai ya k’ure sautin wak’a har yayi aure bai daina, tayi tayi ta hanasa wannan d’abi’a amma abu yaci tura k’arashe ta yanke shawarin tayasa da addu’a...

Tunaninta guda kodai Hajiya ce mai kira, k’ilama zatace azo a d’auki Kausar ce, take taji farin ciki ya mamaye zuciyarta annashuwa da annuri sun cika fuskarta sakamakon tuno d’iyarta da tayi....

Cikin sauri tayi jifa da rigar da take linkewa ta suri wayar tana duban screen d’in, dukda lamba ce kawai babu suna hakan bai hanata tunanin k’ila d’iyarta bace, jiki har na rawa Zulfah ta d’aga wayar ta k’ara a kunnenta ba tareda tace komai ba ga k’irjinta dake faman lugude...

Daga d’aya b’angaren cikin tsananin fad’a Sawwama ke fad’in “Dole kaki d’aga wayata munafukin Allah ta’ala, shine zakace min babu komai tsakaninka da Zabba’u toh yau k’wai ya fashe har hoton d’akin da kuke watsewa a hotel an nuna min, wllhi wllhi Hafiz idan kana tunanin zaka iya fooling wannan shashashar matar taka toh ni baka isa ba wllhi sai na danna maku rashin mutunci daga kai har Zabba’un zaka zo ne ka sameni....”

Daga haka katse wayar tayi cikin tsananin b’acin rai da huci...

Zulfah dake rik’eda wayar tamkar gunki ko motsawa ta kasayi, maganganun Sawwama ke ci gaba da yawo cikin kwanyarta, ta kasa motsawa haka nan ta kasa ijiye wayar har lokacin wayar na mak’ale a kunnenta...

A haka Hafiz ya fito daga bayi ya hangeta rik’eda wayarsa tamkar wacce aka dasa, take zuciyarsa ta shiga masa zafi domin idan akwai abinda ya tsana a rayuwarsa shine a d’aga masa wayarsa....
Chapter 12 · 0% Book details