← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 198

Sashe 19

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dashike glass din motar tasa mai duhu ne sam bazata iya gano matuk’in motar ba, ba tareda tsoro ko gudun waye zata gani ya fito daga motar ba taja ta kafe gefe tana jiran fitowar koma wanene don bata tsoron ta kife sannan bata barin saita kwana balle tai tsami....

Had’edd’en saurayi ne maiji da gayu da kyau ya fito daga cikin motar....

Cikin sakanni da basu wuce uku ba ta k’are masa kallo, nan ta kuma tinzira don ta lura irin yaran masu hannu da shuninnan ne marassa tarbiya balle sanin darajan d’an adam wanda tasan akasarinsu sai sun buga shaye shayensu suke d’aukan mota suyita tuk’in ganganci wasuma su dinga kad’e mutane....

Waige waige ya somayi sanda ya fito daga motar amma baiga kowa ba sannan baiga komai ba dashike duhun mangariba ta soma shigowa....

Wata murya mai zak’i cikeda fad’a ne yaji dirarta cikin dodon kunnuwarsa...

“Gani nan behind you....!” Tayi maganar tamkar d’an wasan kokawa dake neman d’an uwansa...

Karkatowa Khalid ya somayi har saida ya waigo zuwa gareta....

Take gabansa yayi mummunar bugawa ganin wata halitta gabansa domin kuwa sam baka gane kalan fuskarta yanda tab’o ya mata dama dama, gashi ta murtuk’e fuska ta d’ora hannu bisa kunkuminta... Nan ya soma tunanin idanba gamo yayi ba toh kuwa shakka babu wannan mahaukaciyace data k’wace daga turu...

Cikin masifa muryar nata ya kuma katse masa tunanin nasa...

“Don kana cikin mota wani na tafiyar k’afa wa ya baka damar ka wulak’antashi.... Ko kuwa dai shaye shayen naka bai fad’i maka gaskiya ne... Kodai baka gani ne aka d’auki mota aka baka a gidanku...?”

D tsananin mamaki Khalid ke dubanta zuciyarsa na k’una, jin k’aramar yarinya na yab’a masa maganganu, nan kuma yayi tunanin ai wannan zai wuya idan tanada lafiyar kwanya ma....

Murmushi ya sakar mata kana yace “Zaki iya gane asibitinku..? Seems guduwa kikai daga asibitin mahaukata koh... Fad’a min sunan asibitin naku I can take you back...”

Nabila ta kuma zuwa wuya jin ya kirata mahaukaciya bayan wanka da tab’o da ya mata... Maimakon ta rama bak’ar maganar da ya fad’i mata sai kallo data bishi dashi zuciyarta na harbawa da sauri wanda ta danganta hakan da tsananin b’acin rai...,

Khalid ya shafi goshinsa yaji jini..... Duban yatsun hannunsa yayi yanda ya lakato jinin kana ya kuma duban Nabila dake ci gaba da huci.....

Kiraye kirayen sallan magrib ne yasa Nabilah jan tsuka had’ida furta “Nan gaba ka dinga kula idan kana tuk’i...”

Tasa kai zata shige Khalid yayi saurin tare gabanta fuskarsa a murtuke....

“Ina kike tunanin zaki tafi da wannan ciwon da kikaji min sannan a tunaninki waye zai gyara min motata...?”

Dab da fuskarta yake maganar wanda hakan ya sauk’ar mata da matsanancin fad’uwar gaba, domin kuwa sam batada tsoro amma wannan mutumin ya firgitata don babu wanda ya tab’a mata irin hakan....

Kasa furta komai tai sai k’ok’arin jada baya da take sannan bata daina aika masa harara ba....

Ganin mutane sun soma fitowa masallaci yasa hankalin Nabila ya kuma tashi kada Abbah ya fito ya taddata a nan, take kuwa wayarta ta hau ruri Mamy na kira....

Murya a tamke tace “Malam ka bani hanya na wuce ai bani nace kake tuk’in ganganci ba...”

Khalid ya kuma yunk’urin matsowa kusanta, jikin Nabila ya d’auki rawa tana k’ok’arin jada baya, fitowarsu Sameer da Shamsu ne ya ceceta hankalin Khalid ya koma garesu.... Tamkar wulk’awar walk’iya haka ta b’ace a wajen....

Mamaki duk ya cikasu ganin Khalid da ciwo a goshi ga kuma motarsa a fashe...

“Subhanallahi wai hakan ta faru ne...? Na kiraka naji baka d’aga ba I thought ma rasa gidan kayi kuma sai naji baka d’aga ba...” cewar Sameer cikeda kulawa

Gajeren murmushi Khalid yayi kana yace “Na d’an sami accident ne...”

Shamsu ya cab’e zancen da fad’in “Ai idan ka shigo unguwar nan kawai ka d’aura hannunka saman horn idanba haka ba kayita kuskuren bige yaran kenan don iyayensu sakesu suke tamkar shanu....”

Sameer yace “Ai sai muje asibiti a dubaka....”

Khalid yayi saurin girgiza kai yace “No no basai munje asibiti ba ko a gida zaka min dressing doc...”

“Are you sure basai munje ba...?” Sameer ya kuma bid’a

“Yeah I’m sure Dr...”

Khalid ya fad’i yana murmushi had’ida waigan ta inda yarinyar can tabi wacce ko k’yallinta bai kuma gani ba, cikin sa’a ya hangi wulk’awan hijab d’inta ta shige gate d’in wani gida... Harda sauk’e ajiyan zuciya Khalid yayi don da ace ta b’ace masa baisan ta yanda zai samota ba a wannan unguwa mai tarin gidaje...

Masallacin ya bisu shima domin gudanar da sallan magrib...

Daga sahun da Abbah yake ya hangi bayan Sameer, take yaji zuciyarsa na masa wani irin sanyi ya k’udirin niyyan da zaran an ida sallah zai cimma saurayin nan ya tambayeshi sunan shi saidai hakan bata samu domin kuwa ana ida sallah ya nemi saurayin cikin masallacin ya rasa nan ma jikin Abbah a mace ya komo gida....

***

Ta yanda Mamy ke shiga bata nan take fita ba, haka taiwa Nabila tas akan daren da tayo a unguwa, Nabilah sai ture turen baki take tana fad’in “Amma dai Mamy kiga fah yanda na dawo gidan nan jagab da tab’o koma tausayina bakiji ba kuma baki tunanin ko lafiya nake ba... Mamy fah motar k’iris ya rage bata bigeni ba shine mai motar ya wankeni da ruwan tab’o...”

“Rufe min baki sakarcin banza, rashin hankalin da kika tsaya yaja hakan ya sameki ai, banda sakarci tun yaushe ya kamata ki dawo gida sai yanzu, itama Bara’atun ai hankali bai isheta ba dama... C’mon ni wuce ki cire wannan kaya kafin ki b’ata min waje.... Sa’arki d’aya Abbanku bai tambayi ina kike ba...”

Fuuu Nabilah ta shige d’aki yanda ta tadda Marliya na aikin gyaran wardrobe d’insu wanda sanda zata fita tai d’ai d’ai dashi wajen neman hijab....

Marliya na mata welcome Sisi ko takanta batabi ba ta fad’a toilet, Nabila ta fita zakka cikin yaran Mamy gata batajin magana gata batason aikin gida idan kaga ana aiki toh Marliya ce wai donma Mamy na tak’ura mata, ita dai barta da masifarta....

Babu yanda Sameer da Shamsu basuyi ba Khalid ya tsaya yaci dinner koma ya bar motar tasa gobe da safe bakanike yazo ya duba amma fir yak’i ya tak’ura tafiya zaiyi yanda ya sanardasu da safen zai mik’a motar wajen gyara...

Gidan da yaga ta shige nan ya nufa yanda ya tadda wasu Almajirai zaune daga can gefen gate d’in gidan alamun wajen tamkar wajen zamansu ne.....

Daga can gefe yayi parking kafin ya fito yana zira hannaye cikin aljihun wando sai wani faman yatsina fuska yake...

Yaro guda ya kira cikin almajiran kana ya tambayesa ko yaga shigan wata yarinya cikin gidan d’azu bada jimawa ba...

Yaron ya d’an tsaya tamkar mai nazari.... Tuni sauran almajiran sun k’araso wajen sabida sun zata sadaka mutumin zai bayar kar a bawa guda cikinsu su rasa...

Daga yanda suke tsaitsaye rungume da kwanukan baransu d’aya yace “Ba Nabilah bace uwar masifa ta shige har muna k’ok’arin mata dariya tayi wanka da tab’o...”

Sauran sukace “Tab wa ka tab’a gani yazo wajen wannan masifaffiyar inaga dai cikin sauran yaran gidan ne..”

D’ayan ya kuma cewa “A’a Garzali itace kawai ta shige da mangariban nan...”

Zasuci gaba da musu Khalid yace “Ku dakata, sunanta Nabila...?”

A tare suka jinjina kai had’ida furta “Eh sunanta kenan uwar masifa...”

Khalid ya jinjina kai kana yace “D’ayanku ya shiga ya min sallama da ita..”

A tare yaran suka kalli juna fuskokinsu cikeda tsoro...

Khalid ya kuma dubansu cikeda mamaki kana yace “Tsoro kukeji..?”

D’aya wanda yafisu k’ank’anta yayi saurin jinjina kai had’ida furta “Zata iya hanamu zaman wajen nan idan muka shiga hark’arta, babu mai iya koda gaisheta ne cikinmu sabida masifarta...”

Khalid ya Kuma jinjina kai kana yace “Karku damu bazata maku komai ba tasan da zuwana....” Ya k’arashe yana mai saka hannu cikin aljihu...

Sadakan kud’i ya basu wanda tsaban mamakin yawan kud’in basusan sanda suka soma had’e baki wajen cewa bari suyi masa iso da ita ba... Sai zuba masa godiya suke tsananin tausayin yaran na d’awainiya dashi, yaran da basu wuce ace suna makaranta ba, wasu ba takalma wasu kayan duk a b’arke... Sosai suka baiwa Khalid tausayi sanda yaji suna fad’in abubuwan da zasuyi da kud’in da yanda zasu b’oye kada matar Malam ta gani ta k’wace.. Wasu na fad’in zasu sai takalmi wasu na fad’in sun samu kud’in karin kumallo na sati guda koma fiyeda haka...

Kasancewar jikinta ya b’aci yasa tai wankan darenta mai iyanin ta sauya shiga cikin kayan bacci, suna zube parlorn Mamy suna kallon tashan wasan kwaikwayo lokaci guda suna cin tuwo itada Marliya Mamy na gefe tana ci gabada yiwa Nbilah fad’an rashin natsuwarta...

Cin tuwon kawai Nabila take tasan yau sai gari ya waye Mamy ta daina d’ago maganar gashi ba itace a d’akin Abbah ba, babban abinda yafi bak’anta mata rai shine yanda ake cewa tai koyi da k’anwarta Marliya...

Sallaman yaro almajirine ya katse Mamy yanda ya sanar dasu ana sallama da Nabilah a waje...

Tuwon da Nabilah kenan bata had’iyeba ya tsaya mata a mak’oshi....

SameenaAleeyou 📚
*INDA RAI*
_..............DA RABO_

*19*

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*

Mamaki bai saki Khalid ba ganin gidansu Nabieela suka nufa, har k’asan ransa yake jin dad’i don dama nan yayi niyyan zuwa ya danna mata wani wulak’ancin kafin ya tafi tinda itace silan kwanansa har biyu a garin.....

Marliya ce ta masu iso har parlorn Abbah, Khalid sai dubanta yake yana hango tsananin kamanninsu da Nabila gashi dai ita wannan ga dukkan alamu saliha ce kuma mai hankali ba kaman wancan uwar bala’in ba....

Haka kurum Sameer yaji yarinyar ta kwanta masa sai murmushi yake yana dubanta yanda take kaikomo da kayan ciye ciye da shaye shaye gabansu....

Tambayarta sunanta yayi ta d’ago a hankali tana dubansa kana tace “Marliya...”

Sameer yace “Sannu koh Marliya mun gode.....”

Kanta a k’asa tana murmushi ta fice....
Chapter 19 · 0% Book details