← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 198

Sashe 70

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru tai na wasu lokuta kana ta d’ago tamkar wacce aka zabura tace “Aunty Bara’atu..... Aunty Bara’atu will help me... Har muje mu dawo su Mamy bazasu sani ba, zan sanar da Mamy gobe daga sch gidan Aunty B zan wuce idan yaso nida ita sai muje don dai day trip tinda ba wani nisa bane...”

Yusrah tai shiru kana tace “Kenan bazakiyi classes gobe ba...?”

Nabilah ta jinjina kai a hankali tace “Bazan shigo sch ba gidan Aunty B zan wuce, daga nan ma gidanta zamu wuce naje mata da batun don ta kwana dashi although bansan yanda zata d’auka ba....”

Yusrah ta jinjina kai tace “Shikenan Allah ya zab’a miki abinda yafi alkhairi k’awata....”

Nabilah ta amsada Ameen jiki a sanyaye kana suka shige...

Koda suka sami Aunty B da batun da k’yar ta yarda a cewarta bataga dalilin baiwa iyayen Khalid hak’uri da zataje yi ba tinda ba ita tasa ya bijirema buk’atarsu ba... Hasalima zuwan nata ka iya worsen abubuwa... Da k’yar dai Nabila ta shawo kan Aunty B ta amince da buk’atarta...

Har bakin gate Aunty B tai masu rakiya ta kuma basu kud’in abin hawa.... Har sunyi sallama Aunty B ta kirawo sunanta....
“Nabilah...”
“Na’am Aunty...” Nabila ta amsa had’ida juyowa

Takowa Aunty B tai kusanta a hankali kana tace “Yaya Zulfa’u....?”
Dashike tun bayan rasuwar Kausar Zulfah bata dawo gidan Auhty B ba tanacan gidansu...

“Tana nan lafiya, bakuyi waya bane yau....”

Aunty B ta jinjina kai a hankali kana tace “Ki gaidamin ita idan kinje... Yayanku Ma’aruf fah...?”

Nabilah tace “Bai yini a gidan kinsan likita ne....”

Nanma jinjina kai Aunty B kana tace “Allah ya tsare... Yusrah ki gaida Mama kinji koh...”

Yusrah ta amsada “Zataji Aunty mun gode....” Kana suka fice

Jiki a sanyaye Aunty B ta komo cikin gida lokaci guda ta lalumi wayarta dake kan kujera, k’uri taima wani lamba hawaye tab idanunta... ‘Yan uwanta ne batada wanda yafi mata su a rayuwa... Ta sani Yaya Abidah bata ga maciji da Mamy.... Alwashi ta d’au ma kanta In sha Allahu kafin d’aya daga cikin su ukun su bar duniya sai ta daidaita tsakaninsu da taimakon Allah.....

SameenaAleeyou📚

*INDA RAI*
_................DA RABO_

57

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

NOT EDITED

A motar Sameer suka dawo gida gaba d’aya dashike anyi sallamar, Hajiya Mamani an kasa sakin Sameer gaba d’aya gani take kaman zai kuma tafiya ya barsu... Nan ta shiga ‘yan dube dube a d’akin nata cikin shirginta na tsofi da ba’a rasa ba tana neman abin baiwa Sameer... Shiko Sameer sai aikin murmushi yake zuciyarsa nai masa dad’i bai tab’a kawowa nada babban family irin haka ba, matan su Baffah Ado da d’iyoyinsu sukaita shigowa suna gaida Raiha had’ida barkawa Mamani na dawowar Ma’aruf....
Sameer ya yarda shid’in d’an dangine ganin yanda aketa shigowa ganinsa daga k’ofa k’ofa... Da k’yar ya samu ya silale daga sashen Mamani ya nufi parlorn Abbah yanda ya tadda iyayen nasa gaba d’aya, sai sannan Mamy ke tambayarsa gameda matarsa Siyama....

***

A can gidan Baba Alhaji kuwa Hajiya Haule tayi kicin kicin da fuska tana tunanin yanda akai har Ma’aruf ya rayu ya kuma dawo gida wajen danginsa, ko shakka babu Aminiyar sirri ta yaudaresu, amma idan tasan wata batasan wata ba, lokaci yayi da zata fasa k’wan kowa ya sani tinda dai abin ya zama haka....
Baba Alhaji dake cin abincinsa hankali kwance ta kuma watsawa mugun kallo kana ta karkata tai gyaran murya....
“Alhaji wai ni nace ka kaw san abindake faruwa...?”

D’agowa yayi yana dubanta kana yace “Meke faruwa kuma....?”

Gyara zama ta kumayi kana tace “Bakada labarin dawowan d’an d’an uwanka...?”

Gyara zama ya kumayi had’ida aje cokalin hannunsa kana yace “Ban fahimceki ba Haule....”

Hajiya Haule ta kuma tab’e baki tace “Yo ai bakada amfani a wajensu shiyasa ba’a sanar dakai ba, basu d’aukeka bakin komai ba, sam Usman baya darajaka baya baka girman da ka riga ka fishi, bacin haka ace an doshi sati guda da bayyanar Ma’aruf amma babu wanda ya sanar dakai.....?”

Sauran abincin dake bakinsa ne ya kusa k’waransa... Ya kuma duban Hajiya Haule yace “Haule kinaso kice min Ma’aruf ya dawo gida bayan duk shekarun nan da aka d’iba baya nan....?”

Hajiya Haule ta jinjina kai tace “K’warai kuwa.... Ma’aruf ya dawo...”

Baba Alhaji yai shiru na d’an lokaci kana yace “Shine babu wanda ya sanar dani.... Usman bai fad’a min ba....”

Hajiya ta kuma yab’e baki tace “Toh yaushe kuwa zai fad’a maka tinda ba amfani kakedashi a wajensa ba, ita kanta mahaifiyar taku k’ark’ashin kulawarsa take yo ba dole ba, gaba d’aya ya amshe girman naka, ‘yan uwanku girmansa suke gani ba naka ba tinda ya yanka masu matsuguni a gidansa, yanzu gashi ance Ma’aruf babban likita ne kuma iyayen rik’onsa da alama masu kud’i ne sosai, na tabbata Mamani babu abinda zatai dakai yanzu balle ‘ya’ayanka zaka kuma zama maras amfani a wajenta....” Ta k’arashe tana mai k’ura masa idanu.....

Shiru yayi na wasu lokuta kalaman Haule na kuma tasiri a zuciyarsa... Lokaci guda ya mik’e ya hau zira takalma...
Haule ta mik’e tana k’ok’arin rik’esa take fad’in “Ina kuma zaka....?”
Ba tareda ya dubeta ba yace “Zanje naga d’an d’anuwana....”
Bai kuma saurarenta ba ya fice cikin sauri tamkar zai kifa k’asa, wani abu na yawo cikin zuciyarsa...

Hajiya Haule ta rakasada mugun kallo har ya fice kana ta buga tsuka tayi shigewarta d’aki...
Najah dake zaune can gefe a idonta akayi komai sauk’e nannauyan ajiyan zuciya tayi kana ta furta a hankali “Hajiya ina fatan babu saka hannunki a b’acewar Ya Ma’aruf....” Ta k’arashe tana mai lumshe idanu a hankali kafin ta mik’e don gabatar da sallar la’asar, tana idarwa tayi shirin islamiya abinta, tanajin Sahariyya da Hajiya na d’ibe mata albarka wai ta zama munafuka ta koyo salon munafunci ko kulasu batai ba ta fice abinta tanai masu addu’ar shiriya...
A can islamiyar ta had’uda Marliya yanda Marliya ke sanar da ita cewa an sallami Raihanah ta dawo gida, Najah tace zasu tafi tare idan an tashi ta duba jikin ‘yar uwar tata..,
Sosai abin kewa Marliya dad’i ganin yanda lokaci guda Allah ya shiryi Naja’atu ta dawo daga rakiyansu Hajiya....

***

Abbah da Mamy na zaune parlor suna firansu na mata da miji gwanin ban sha’awa Baba Alhaji yayi sallama, Mamy ta mik’a hannu ta janyo mayafinta ta rufa kafin Abbah ya basa izinin shigowa dukda ba jiran izinin nasa yake ba, da gadara ya shigo yana watsa masu kallo...
Mamy ta gaidashi ya amsa a ciki...
Abbah yace “Yaya kaine a tafe, sannu da shigowa....”
Baikai aya ba Baba Alhaji ya dakatar dashi da fad’in “Dakata Usman kada ka sake cemin Yaya... Ai baka d’aukeni matsayin Yayan ba.... Na tabbata har cikin ranka bakak’i ace kaine d’ah na fari a gidan nan ba, duk wasu d’awainiya da suka kamata ace ni ne nan na d’aukesu ka d’auka ka yafa ma kanka ba don komai ba sai don ka zamto abin tink’aho da alfahari a dangi koh, kana neman ka k’wace girman da Allah ya riga ya bani... Toh duk yinka Usman na rigaka zuwa wannan duniya kuma nine d’ah na fari a wajen iyayenmu kuma kai baka isa kayi komai akan hakan ba....” Ya k’arashe yana mai dukan k’irjinsa cikeda zafin rai....

Abbah bai tankasa ba har ya gama kana yace “Yaya ka zauna mu gaisa tukuna...”

“Aw mahaukaci wanda baima san abinda yake ba ka d’aukeni kenan, kasa su Ado sun rainani duk basu ganin girmana sai Naka shine yanzu bari ka nunawa d’anka Ma’aruf bani da daraja a gidan nan koh, ban tashi sanin cewa ya dawo ba sai yau... Sabida kafi k’arfi ka nuna masa cewa kanada Yaya koh, sabida ka sami d’aurin gindi daga wajen mahaifiyarmu koh...?”

Abbah na girgiza kai yake fad’in “Ba haka bane Yaya... Dama naso na d’aukeka na kai maka shi har gida n......”
Dakatar dashi Baba Alhaji yayi da fad’in “Bana buk’atar bayananka... Ina Ma’aruf d’in yake.....?”
Sai sannan Mamy da kanta ke k’asa tace “Ya fice amma inaji ba nisa yayi ba....”

Baba Alhaji ya kad’a kai kana yace “Dama idan ya dawo maza yaje gida ya sameni....”

Mamy ta jinjina kai tace “In sha Allahu za’a sanar dashi...”
Ko amsa bai basu ba ya fice ya nufi sashen Mamani kaman wani zai kifa....

Aunty Lami dake lab’e ta murmusa cikin zuciyarta tace “Aikin k’awata Haule yayi kyau kenan... Yanzu zan kirata na labarta mata don nasan wannan ba komai bane illa makircinta....” Ta k’arashe tana kuma sakin murmushi...

Mamani ta had’e fuska tayi kicin kicin tana aika masa mugun kallo....
Baba Alhaji yaci gaba da fad’in “Mamani kin kasa gane duk wannan sharrin d’an uwanane, ya rabani dake, ya rabani da ‘yan uwana su Ado yanzu yanaso ya d’auke d’iyata ya rabani da Raihanatu... Tinda an sallameta ta shige mu tafi gida Ta k’arashe jinyar acan.....”

Tsegege Mamani ke dubansa kana tace “Gafara kamin shiru shanyayye wanda Haule da bokayenta suka gama dashi... Toh bazata koma ba, nace bazata koma ba, ince sanda tana asibitin Haule ta hanaka kaje ka dubata sai yanzu ne zakazo kace ta koma gida... Salon Haule da asararrun ‘ya’yanka su k’arasata koh... Toh wllhi kaji na rantse ko bayan rainane ka d’auki rik’on Raihanatu ka maida hannun Haule Allah ya isa ban yafe maka ba....”
Baba Alhaji ya d’ago yana dubanta cikeda mamaki....
Mamani tace “K’wari kaji baninda nace ai... Tashi ka ficemin ka koma wajen Haule ka k’are can....”
Haka Baba Alhaji ya mik’e ya fice yana mai aikawa Raihanah da idanunta ke k’asa mugun kallo

Hawayene ke zuba a idanunta, kalaman Mamani akan mahaifinta yana mata zafi sosai, ko babu komai ko yaya yake tasan mahaifinta ne kuma bazata canza hakan ba....Kuma tabbas kalaman Mamani kayi tasiri a rayuwarsa...

Mamani ta dafata tace “Yaya dai Raihanatu jikin ne.....?”

Raiha ta girgiza kai a hankali tace “A’a Mamani....”
Mamani ta kuma dafata cikeda tausayawa tace “Karki damu kinji bazan tab’a bari Alhaji ya maidaki gaban Haule ba kinji koh....”
Raiha bata iya cewa komai ba sai sadda kai k’asa data kumayi...
Mamani ta mik’e tana fad’in “Ohni Halimatu toh yanzu waye zaike wanke ciwon naki gashi mun riga mun dawo gida, naga lokacin wankin ciwo naki yayi....”
Chapter 70 · 0% Book details