← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 198

Sashe 88

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cireta yai daga jikinsa yana mai bintada kallon mamaki ganin abinda bai saba gani ba, Wai shine yau Muhibbah ke biyosa da abinci office.... A hankali ya k’arasa ya zauna saman kujera bai daina binta da duban mamaki ba... Muhibbah ta ije ‘yar mayafinta saman hannun kujeran kana ta isa ta janyo basket d’in ta bud’e zip d’in dake sama ta d’auki plate da serving spoon ta shiga k’ok’arin serving d’insa.... Lokaci guda take furta “I know you must be hungry Excellency na...... It’s your favorite, look... Nasan zakaci s....”

Dakatar da ita yai da fad’in “Wait... I just don’t get it.... Wani kika kawo abinci....? Since when kika soma kawo min abinci wajen aiki....?”

D’an murmusawa tai kana tace “Tun sanda na maka alk’awarin canzawa... Kaga fah nice da kaina na girka maka..... And I’m here to feed you myself....” Ta k’arashe tana mai ci gaba da zuba abincin cikin bowl.....

Girgiza kai yai cikeda takaici kana yace “Drop the act Muhibbah... Kar muyi wannan wasan dake, na sani sarai kinyi hiring cook da take abinci ba ke kikeyi ba, har restaurant d’in da kikaje kikai hiring cook d’in inada labari, kawai na zuba maki ido ne naga gudun ruwanki.... I’m pretty sure canzawa overnight zai maki wahala so na d’ibar maki lokaci na tabbatar shin da gaske kinyi shirin canzawan ko kuwa dai zaki koma ruwa....”

Ta d’an muskuta kana tace “Haba Excellency na Haka ake encouraging mutum, kamata yai kake ganin good side d’ina ba kullum kaita kusheni ba... Wllhi I’m changing for the better, I promise you...”

D’an tab’e baki yai a hankali kana yace “Idan kin canza don kanki Muhibbah don ba mani kikai ba, ki sani ko mai bawa yake aikatawa shi zai accounting kayansa babu wanda zai masa... Kin fahimta....”

A hankali ta jinjina kai kana tace “Haka ne Excellency na.... Dad’ina dakai akwai matsowa mutane Allah kusa shiyasa nake dad’a sonka kuma wannan kyakkyawar d’abi’a taka kad’ai ta isa ta saye zukatan mutane wajen zab’inka matsayin mutumin da zai shugabancesu ya kuma jagorancesu... Allah ya shige maka gaba a duk abinda kasa gabanka Excellency na... Amma kuma banda neman aure idan har yana cikin agenda d’inka....” Ta k’arashe tana dubanshi wanda shid’inma ita yake duba, hab’arsa bisa hannayesa guda biyu ya mata tsuri yana dubanta...

A hankali ya furta “Ita addu’ar taki ta k’arshe bazaki min fatan Allah yamin zab’i ba...”
Saurin mik’ewa tai ta k’araso ta zauna gefensa ta kamo hannunsa guda kana ta shige cikin jikinsa, idanunta a lumshe take furta “I can share you with my children but not with any woman.... Ni Muhibbah ni kad’aice Matar Ma’aruf, haka take a rubuce a zukatan iyayenmu da danginmu.....”

Engr da tuni yayi nisa cikin wata duniyar ta tunani sam bai ida sairaren maganganun da Muhibbah keyi ba...

Duk wannan sabon salon kalallama da take masa ba komai take sonji ba face abinda take zargin mijin nata na b’oye mata, gashi babu yanda batai da wancan mai d’an banzan taurin kan ba yaqi sanar da ita komai, batai zaton zata sami matsala dashi har haka ba, lallai akwai yarda da amana mai tsanani tsakanin Akram da mijinta, amma idan yasan wata baisan wata ba muddin bata sami biyan buk’ata daga wajen mijinta ba tasan ta yanda zata b’ullo masa....

***

KADUNA

Tun sassafe ta tashi tanata faman kintsawa da shike yau take komawa Abuja, gashi da masoyinta Khalid zatai tafiyar gaba d’aya bata sama bata k’asa... Taso su tafi da motarsa amma shi yace sam saidai subi train.... Ba hakan taso ba tafiso shi yayi driving ya kaita har gida amma babu yanda ta iya don tasan tana provoking d’insa abu mai sauk’i ne yace bazai tafiyar ba kuma, don haka dole take lallab’ashi...
Wata had’edd’iyar leshi d’inkin doguwar riga da yasha tsaga har kusan cinya ta saka, saiko d’an mayafi data rufe gashinta babu d’ankwali akan nata kana iya hango kitson gashin kanti dake kan nata..... Rigar ta matseta sosai tamkar tai numfashi ya b’arke, badon tsago mai tsawo da aka masa ba ma zai iya b’ekewa, sannan rabin k’irjinta a waje yake.....Ta shigo d’akin Ammi da k’yar tana mai doka kirawa Ammin....
Khalid dake zaune gefe saman sofa dake a cikin d’akin wulak’antaccen kallo ya bita dashi baki a tab’e....
Ta sakar masa murmushi tana mai fad’in “Ina kwana My Kay...”
Bai amsata ba sai cewa da yayi “Yanzu ke a haka kinyi shigar mutunci kenan har kuke kiran wata Karuwa.... Tsakaninki da Allah dake da ita wayafi kama da sunan da kuka dangantata dashi....?”

Yesmin tai kicin kicin da fuska...
“Tambayarki nake....?” Ya kuma fad’i yana dubanta...
Baki a ture ta shiga duba jikinta kana tace “Haba my Kay what’s wrong with my clothes... 21st century fah muke.....”

Jinjina kai yai kana yace “I see... Kinsan Allah, kinji na rantse maki bazan had’a hanya dake da wad’annan ‘yan iskan kayan jikin naki ba.... Don ni ba d’an iska bane...”

Mamaki ya cika Yesmin ganin dai Khalid a waye yake, maiyasa zai mata haka ko don bai sonta ne.... Duban kanta ta kumayi kana tace “Nidai gaskiya su nake son sakawa...” Ta d’an murmusa tace “Kodai kishina kake MyKay....”

Ya watsa mata muguwar kallo kana yace “God forbid..! Ai idan kinji ana kishin mutum ana sonsa ne....Kiyi yawo tsirara ma idan kinso, ko a kwalata... Nidai what I know shine bazan had’a hanya dake da wannan shigar taki ba, Don nima sai ai tunanin d’an hanu ne... Idan kinga dama kin canza don kanki idan baki canza ba don kanki....” Ya k’arashe yana mai mik’ewa ya nufi sashen mahaifinsa don yimasa sallama....

K’atutun bak’in ciki ya tokari mak’oshin Yesmin, tai sakare a wajen har Ammi ta fito daga bayi ta taddata... Ammi ta tambayeta maike faruwa bata sanar da Ammin ba saidai kafin su tafi saida ta koma ta canza shiga wanda ya d’anfi wancan shigar tata...

Daddy ya sakawa Khalid albarka da fatan sauk’a lafiya, ya k’arada “Sama’ila zai ajeku a train station d’in....”

D’an jim Khalid yai kana yace “Dama Daddy motata tana wajen Baffah zai k’araso ya ajemu, akwai yanda zamu biya tareda Baffan ne....”

Jinjina kai Daddy yai ya kuma saka masa albarka kana sukai sallama... Wajen Amminsa yaje ya mata sallama itama taita masa kashedin saura yaje ya nuna halinsa ma iyayen Yesmin ya nuna masu dole aka masa baison d’iyarsu.... Jin mahaifiyar tasa kurum yayi amma shi kansa bai tunanin abinda yake shirin yi daidai ne....

Ammi tai masu sallama gaba d’aya had’ida shi masu albarka kana Baffah yazo ya kwashesu....

Saida suka isa har tashan jirgin, ya tabbata Yesmin ta shiga ta zauna a kujerarta kana ya fito ya kirawo layin Baffah......
Baffah na tafe yaga kiran Khalid, ya d’aga yana tambayarsa ko mantuwa yayi....
Khalid yace “Kana ina...?”
Baffah yace “Gani na shige Sterling bank kad’an....”

Khalid yace “Dawo da baya...”
“Ban gane in dawo da baya ba... Mai ka mance Khalid... Shinma Wai ba yaznu zaku tashi ba...”

“Idan bazaka dawo bane ka fad’a min....”
Girgiza kai kurum Baffah yai kana ya karya kan motar ya koma da baya...

Yesmin tanaji ana announcing tashin jirgi abin ya dameta ganin Khalid bai dawoba bayan ga wajen zamansa a gefenta, ta mik’e tana lek’elek’en cikin jirgin... Gabanta ya shiga bugun tara tara ganin bata hango ko k’yallin Khalid ba.... Gashi babu halin ta fice don tuni jirgi ta soma tafiya... Tamkar ta tsuguna wajen ta runtuma ihu haka taji sabida tsaban bak’in ciki.. Batasan sanda hawaye suka soma sauk’a mata ba... Lallai yau ta yarda Khalid ya cika babban d’an rainin hankali da wayo... Haka tanaji tana gani jirgi ya tashi da ita babu Khalid babu dalilinsa....
***

Baffah na isowa ya masa k’uri shaye da mamaki kana yace “Ina Yesmin d’in....?”

Dafa marfin motar yai kad’an kana yace “Ka gane ka hau taxi ka koma gida please....”

Mamaki ya cika Baffah... Fitowa yai daga cikin motar kana yace “Ban gane ba... Toh Wai ba tare zaku tafi ba....”
Khalid bai amsa shi ba sai shigewa cikin motar da yayi mazaunin driver ya aje hularsa gefe d’aya Seat d’in... Ya d’ago ya dubi abokinsa Baffah kana yace “Allah sadamu da Alkhairi, sai munyi waya....”

Khalid na k’ok’arin rufe motar Magaji yai saurin rik’e marfin motar kana yace “Khalid Wai meye haka... What exactly do you mean... Ina Yesmin...? Ina ka nufa...?”

Dubansa yai kai tsaye kana yace “Kano.... Shikenan kaji... Zaka iya barina na shige....”

Girgiza kai kurum Baffah yai kana yace “You’re unbelievable Khalid... Shine ka bar Yesmin d’in ta tafi ita kad’ai... Haba Khalid, I thought zakabi umarnin iyayenka da gaske....”

Kallo ya watsa masa kana yace “Da nace zan aureta ai biyayya na masu, ko ita k’aramar yarinyace da sai na d’auketa na maidata gida...? Tinda ba cewa nayi na fasa auren ba kaga ban bijirewa umarnin nasu ba, ai.... Kana iya barina na tafi....? Banso rana yamin... Idan kuma zakajene bisimillah...”

Girgiza kai kurum Baffah yai kana yace “A sauk’a lafiya... Allah ya tsare hanya...”
Khalid ya amsada Ameen had’ida janyo marfin motarsa ya rufe... Baffah na kallon yanda ya kwashi motar da k’arfin gaske ya bar wajen.... Addu’a kurum Baffah ya rakasa dashi kafin ya soma saka hannu yana taran taxi....

***

Abbah yai shiru yana sauraren d’an uwan nasa da ya gama harzuk’a sabida rashin samun goyon baya da yayi daga Abban.... Baba Alhaji ya mik’e yana mai ci gaba da fad’in “Shikenan Usman.. Kaje ka rik’e ‘ya’yanka... Ai iyakacina kake son nuna min... Yayi... nace yayi daidai Usman.....”

Dai dai lokacinda Sameer yai sallama, sam baiji dad’in yanayin da ya tadda mahaifin nasa da kuma yayan mahaifin nasa ba... Ko gaisuwar Sameer Baba Alhaji bai sami zarafin amsawa ba sai duba da bisa dashi kana yai ficewarsa tamkar zai tashi sama...
Sameer ya k’arasa kusan mahaifinsa had’ida duk’awa ya gaidashi...
A hankali ya amsa masa yana mai k’ok’arin k’ak’aro murmushi had’ida d’aurawa bisa fuskarsa....

Sameer ya d’an dubi yanayin mahaifin nasa kana yace “Abbah lafiya....? Meke faruwa...?”

Abbah ya murmusa a hankali kana yace “Babu komai Ma’aruf... An shigo... Za’a wuce aiki kenan...?”
Chapter 88 · 0% Book details