Sashe 198
Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
A can b’angaren Mamy kaw,su Ammah dasu Aunty Daula, Mummyn Sameer harma da Ammi sune acan suna nasu bidirin harda Aunty Hanne da Yesmin sunzo... Aunty B ce ta shigo tana sanar da Mamy yanda sukaida Major Kabir Kaita mijinta da a yanzu ya kuma samun matsayi ya dawo gareta yana mai bata hak’uri kan cewa ta bisa cen Lagos tinda yanzu tayi settling family d’in nata kaman yanda ta buk’ata daga garesa wanda hakan ne musabbabin samun sab’aninsu dan cewa tai bazata abandoning family d’inta a halin da suke ciki a baya ta bisa ba, hakan yasa sukaita samun sab’ani toh yanzu dai ga Allah ya karkato mata da hankalinsa.... Su Mamy dasu Daula su Ammah sukace k’warai tabi mijinta dan ta cacanci Farin ciki itama bayan d’inbin SADAUKARWAR da taiwa Ahalinta.... Major Kaita ya shigo ya gaisa dasu ya kuma basu hak’uri da jaddada masu cewa zai kula da ‘yar uwarsu ya kuma bata kulawan da bai bata a baya ba... Farin ciki ya lullub’e ahalin Aunty B bayan dik abubuwan da tai masu basusan da mai zasu saka mata ba tabbas addu’arsu ce zaita isa gareta har yanda take... Nan Aunty B tai baiwa mijinta hak’uri itama dan ko shakka babu tana k’aunarsa... Haka sukai sallama da sauran ‘yan uwa ba’a ida Bikin da ita ba tabi Mijinta Major Kaita suka tafi daga can Lagos d’in zasu wuce k’asar Russia yanda zai gudanar da wani course...
Shagalin biki yaci gaba da gudana bayan an gama koke koken sallama da Aunty Bara’atu babu kaman Zulfa’u wacce take ‘yar gidanta.. Aunty B d’in ta jaddada mata da zaran ta haihu in sha Allahu dik yanda take zata baro tazota ganin grandson ko granddaughter d’inta....
Su Zulfa’u, Siyama, Raihanah harmada Yesmin suka d’unguma suka nufi gidan Baba Alhaji zasu taho da amaren gaba d’aya nan wajen Mamani yanda za’a gudanar da family eve, suka shiga gidan kace kace Haule na lale dasu... Ita kam Yesmin can k’ofa aka barta tana faman danna waya, nan taji taci karo da mutum... Ta d’ago dafe da goshinta tana watsa masa harara... Shima fuska a murtuk’e yake dubanta, kan Hafiz yai aune ta shiga silla masa masifa... Da tsananin mamaki yake dubanta kana yace “You watch where you’re going next time....”
Ta kuma hararsa tana fad’i a hankali “he’s so mean...” Tana maganar tana sosa goshinta...
Juyowa yai kad’an kana yace “Mai kikace....?”
Hararsa itama tai kana tace “Kai mai kaji nace..?”
Ga tsananin mamakinta murmushi taga yayi da gefen bakinsa kana yace “Naji kince he’s so handsome that I couldn’t take my eyes off him...!” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice yana kuma sakin murmushi...
Tsaye tai tana bin bayansa da kallo har ya b’ace mata murmushin da bata san daga ina bane ya kufce mata....
A haka suka fito da amaren yanda suka nufi hamshak’an motocinsu na alfarma dake jiransu waje tareda jagorancin Matar mai girman Gwamna kuma First Lady Zulfa’u....
Bayan sun isa gidan Mamani ne suka tadda draman Mamani da Khalid ya kasa ya tsare yace matarsa bazatci sha daka da Mamani ta bata ba a cewarsa kar yai affecting babynsa...
Mamani ta dangwari k’eyarsa tana fad’in “Kai Haladu bana san iyayi d’in nan Naka... Wato kaima ka iya felek’e toh sai taci nace sai taci... Ungo d’auka kici, Wato kai ga mai mata da d’ah koh... Ungo Ci shadakanki kai waysan mai akaci da cikinka....” Ta k’arashe tana mai mik’awa Nabilah dake masa gwalo tana fad’in “Yauwa Mamani na yau dai bayana kikabi kin gwansa d’an gaban goshi...”
Mamani tace “Ai kema ba sabida ke na bada ba dan tattab’a kunnena dake cikinki na so ne... Kinsan d’an Haladu dole ya zama na gaban goshi na... Gaba d’aya suka dara daidai sanda Su Mamy dasu Ammi harma dasu Haule dik suka shigo za’ai family pictures, Nan Khalid ya fice kiransu Abbah a cewarsa ya kamata ai gaba d’aya...
Jim kad’an kaw suka shigo gaba d’ayansu mazajen harma dasu Engr dasu Sameer su Hafiz... Gaba d’aya sunsha manyan kaya da huluna masu d’aukan idanu gwanin ban sha’awa saikace sun fito daga sallan idi...
Mamani na tsakiya zuri’arta na hallare gewaye da ita hawaye ya d’igo mata tana ayyanawa cikin zuciyarta yau Ina Mahmud Mailafiya yaga wannan kayan Farin ciki... Ko yanzu tabar duniya Alhamdulillah itakam babu abinda zatace sai godiyawa Ubangijinta...Allahu Akbar Zuri’a tai Albarka... Wai akace INDA RAI DA RABO.... Take camera man ya saita camera d’insa don d’aukan wannan kyakkyawan ahali yayinda nima na aje alk’alamina da nai amfani da ita wajen rubuto maku wannan labari mai cikeda abubuwa iri daban daban ciki nace kai nima dai bara na d’auko maku hoton wad’Annan ahali... Take na saita camera d’in wayata nima na d’aukar maku hoton... Nasan su Ahalin SAN suna nan suna jira suga hoton nan dan ga su Sadiya Auwal su Oum Imaan su Fatee Beni su Bintaa su Laweesa su Mrs Deen su Maman Sadiq su Baby Mahe su Nafisa Wala su Maamah su Halima Mekeke su Oum Noor su Zynab Maude su Maryam Mu’az, Maman Hanan, Yasmeen, Hauwa Muhammad, su Bilkeesu,Raheela, su Maryam Muhammad... Su su su kai kunada yawa duk kunsan kanku masu jiran ganin hoton nan... DA RABON kuga hoton yasa na d’auko maku... LOL
ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH!! ALHAMDULILLAH!!!
A nan na kawo k’arshen wannan labari mai taken INDA RAI DA RABO.....Dikkan yabo da godiya Sun tabbataga Allah da ya bani damar kammala wanann littafi cikin kwanciyar hankali bayan dogon zango da aka kwashe ana rubutunsa... Fad’akarwar dake ciki Ubangiji yasa mu amfana dashi, kurakuren dake ciki Allah ya yafemu gaba d’aya... Ameen!
Jinjina gareku dan kun cancanta...
Engr Sholyngaye
Aunty Hasken Annuri
Aisha Amaal Bappah
Sameena Aleeyou Novels(SAN)
Zauren Biebee Isa(ZBI)
Ubangiji ya bar k’auna🤝
Ina kuke Trio😍 AKA Partners💯 littafin nan d’aukacinsa sadaukarwace gareku... Ko ban fad’i ba ku kunsan namijin k’ok’arin da kukai wajen ganin littafin nan ya kammala... Ubangiji ya bar k’auna... Raliya Garba(Rally), Maimuna Mansoor(Anmunah), Aishatu Dahiru Audi(Shawty)....Sonso fillah❤️
Sameena Ke maku fatan Alheri a dik inda kuke🤝
SameenaAleeyou📚