← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 176 OF 198

Sashe 176

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yesmin ta d’ago tana duban Khalid, kafin tai maganan Khalid ya girgiza mata kai kana yace “Is ok Yesmin... Ki sani ni ban tsaneki ba kuma inasonki a matsayinki na k’anwata, wannan soyayyarce a tsakaninmu bata aure ba kinji koh... Kuma inaso kisa ma ranki cewa kinfi k’arfin wulak’ancin ko wanne d’ah namiji... You’re beautiful, you’re strong and you’ve your love ones beside you... So never allow someone to look down on you kinji koh... Kar ki tab’a bada k’ofa ma wani namiji ya rainaki... Da sannu zaki samu wanda zai maki irin k’aunan da kika cancanci a nuna miki....”

Yesmin na murmushi hawaye na kuma gangaro mata take furta “Na gode Ya Khalid... Thank you so much...!”

Gaba d’aya annuri ne ya cika fuskokinsu, Yesmin ta isa ga Ammi suka rungume juna, lokaci guda take fad’in zataje ta duba Mummynta sannan ta tabbata itama ta tuba ta dena biye biyen malaman tsubbun da take, dan tana fata wannan abu da ya faru ya zama idan da wa’azi a gareta itama....

Farin ciki ya wanzu, rahamar umabgiji ya lullub’esu... Zukata sun cika da salama, saidai Allah son Barka da fatan Allah ya baiwa Daddy lafiya ya fuskanci wannan ahali nashi mai cikeda aminci.... Koda su Ijlaal suka dawo daga sch haka Aunty Daula taita introducing d’insu ma Ammi, Ammi na rungumarsu, Allah sarki mai za’ai da k’iyayya da gaba... Allah ka wadatamu da soyayya sadaukarwa da kuma yafiya....
Aunty Daula tsaye tai Daga k’ofa tana hangen su Humaira da Ijlaal yanda suke tsalle jikin Ammi suna zuba mata surutu a dole labari suke bata...
Aunty Bara’atu tai k’uri ma ‘yar uwar tata murmushi kwance saman fuskarta... Lokaci guda Aunty Daula ta waigo tana duban Aunty B d’in... A hankali ta tako gareta had’ida rungumeta... Lokaci guda take furta “Shin mai zanyi ba taredake ba ‘yaruwata....? Ban san da kalaman da zanyi amfani dasu wajen nuna miki godiyata ba Aunty Bara’atu... Da ace ‘yanuwa zasu zama irinki tabbas da duniyarmu Ta cika da alkhairi....” Cikin tsananin rawar murya taci gaba da furta “Thank you so much... ‘Yaruwata.... Thank you for uniting my family...!!”
Cikin sauri Aunty B ta rungumeta tana mai furta “Kukan nan ya isa haka Daula... Hakan shi ya kamata ‘yan uwa suyi... Family d’inki nawa ne... Idan ya falling apart tamkar nawa ne yai haka idan ya dunk’ule waje guda tamkar nawa ne ya dunk’ule waje guda... Allah ya had’e kan dik wani family da suke fuskantar barazanar tarwatsewa waje guda....!”
Suka kuma rungumar juna...

Khalid ne ya hauro upstairs da sauri yana fad’in ina suke...Gaba d’aya su Ammi su Aunty Daula suka nufosa suna tambayar lafiya ko wane abin ne ya sami Daddy...

Murmushi ya kasa Barin fuskar Khalid lokaci guda yake sanar dasu “Ammi.. Aunty... Daddy regained consciousness, he’s out of coma, Alhamdulillah...!!” Ya k’arashe yana rungumar mahaifiyarsa cikeda Farin ciki...

Haba nan fah aka shiga hamdala da gode ma Allah... Wani sabon Farin ciki ya riskesu... Ammi tace “Ai sai mu tattara mu d’unguma mu tafi asibitin gaba d’aya...
Hakan kaw akai suka d’unguma k’wansu da k’wark’watansu dan hardasu Ijlaal yau suka nufi asibtin, Siyama ce dake Kaduna kawai bata a wajen.... Idan Kaga wannan ahali dole kaima kai masu farin ciki.... Yau d’in rana ce ta musamman a garesu....

Khalid shi ya soma shiga d’akin Daddy yanda ya hangi Daddyn kwance bisa gadon sa ta jinya, wannan karon an rage yawan na’uran da suke taimaka ma lafiyar nasa....
Cikin murya irinta majinyata Daddy ke furta “Khaleed... My son, come here...!” Ya k’arashe yana k’ok’arin d’ago hannun nasa yana mik’ama Khalid....
Khalid da hawaye suka wanke masa fuska da ganin Daddy yau ya bud’e idanu na magana har na ambato sunansa... Abu ne da yai zaton shikenan bazai sake gani ko ji daga Daddyn nasa ba... Lallai Ubangijinsa ya cika abin godiya.... Cikin sauri Khalid ya isa ya damk’e hannun Daddy, yana hawaye sosai yake furta “Daddy... Daddy ka tashi.... I thought I was going to lose you Daddy..!!” Ya k’arashe yana mai kifa kansa gefe kafad’a Daddy da babu bandage.... Daddy ya d’ago d’aya hannun nasa da k’yar maras cannula kana ya dafa kan Khalid kad’an yace “Khalid I’m sorry... Na Barka da abubuwan da bazaka iya warwarewa ba... Na barkada d’awainiyar da ba taka ba.... Khalid d’ah na ka yafe min kaji.... Na sani it wasn’t easy for you... Ni yafi cancanta na had’e kan iyalaina ba kaiba... Ka yafe min kaji d’ah na.. Kai d’in ka cika d’ah na gari kuma mai biyayya....”
Cikin sauri Khalid ya d’ago kansa yana duban Daddy da idanunsa masu zuban hawaye, lokaci guda yake furta “No Daddy.... Babu abinda kayi... Wannan hukuncin Ubangiji ne shi ya k’addari hakan.... Fatanmu shine Allah ya k’ara maka lafiya...” lokaci guda Khalid Ke murmushi kana yaci gaba da fad’in “Daddy yau inada babban Albishir a gareka....”
Lokaci guda Khalid ya mik’e ya isa ya bud’e k’ofar... Yayinda Daddy yai k’uri yana kallon masu shigowa....
Wani irin zabura yai kaman zai mik’e daga saman gadon ganin masu shigowar... Khalid yai saurin k’arasawa ya rik’esa yana fad’in ya kwantar da hankalinsa....
Ga tsananin mamakin Daddy murmushi ya gani saman fuskokin Matansa guda biyu Farida da Daula... Yai saurin d’ago kai yana duban Khalid kana yace “Shin abinda nake gani gaskiya ne Khalid..?”
Khalid ya jinjina masa kai a hankali kana yace “Gaskiya ne Daddy... Abinda kake gani haka ne...!”
A hankali Daddy ya lumshe idanunsa siriryar hawaye ta gangaro masa...A hankali ya ware idanun nasa yana mai furta hamdala ga Ubangijin rahama a bayyane.... Ya juya b’angaren dama yaga Ammi na sakar masa murmushi hannayenta saman nasa hannun dake wannan b’angaren siririyar hawaye bisa fuskarta itama, ya kuma juyowa b’angaren hagu nan ma Aunty Daula ce tayi yanda Ammi tai... Kafin yai magana Ammi tace “Daddyn Siyama kai shiru haka nan you’re still weak..!”
Aunty Daula ta jinjina kai tace “Haka ne Dr yace banda yawan magana...”
Ya kuma kallonsu duka biyu yana murmushi shi kad’ai yasan kalan farin cikin da yake ciki... Suna a haka Khalid ya kuma shigowa d’aukeda Ijlaal a kafad’arsa hannunsa guda kuma rik’eda Humaira nan suka shigo suka gaida mahaifin nasu suna fad’in irin kewarsa da sukai... Daga nan su Nabilah dasu Aunty Bara’atu ma dik suka shigo suka gaida Daddy...
Wayar Siyama ne dai Khalid bai samu ba gashi ya d’anja sosai balle ya kira Sameer ya sanar dashi dan dikda baida tabbacin Siyamar Kadunan Ta tafi yasan babu yanda zatace face wajen Sameer d’in a irin wannan yanayi na tashin hankali da suke fuskanta...
Ammi ce ta sanar dashi sunyi waya da Hajiya Fatahiyya ta sanar da ita Siyamar na Kaduna... Hakan yasa hankulansu kwanciya....
***

KADUNA

Washe gari da k’yar Siyama ta farka dan daren jiya ba wani baccin kirki Ta samu ba bayan ta ida sallan asuba ne ma bacci b’arawo yai gaba da ita, K’uri tai ma gefen gadon wajen kwanciyar Sameer tana ganin kaman zata ganshi kwance wajen... Ta lumshe idanunta a hankali wasu hawayen suka ziraro mata....K’ila ma yana can tareda ita, tinanin da yazo zuciyarta kenan... Kuka mai k’arfi ya kuma kufcewa Siyama, sosai Ta rungume pillow tana kuka mai tab’a zuciya...
Ko takan wayarta batabi ba har wannan lokaci, dan gani take Tamkar Sultan ne mai kiran nata... Bathroom ta fad’a tai wanka nan d’akin Sameer d’in komai na buk’ata akwai, bathrobe d’insa tai amfani da, ta jima tana shak’an k’amshin shower jell d’insa da tai amfani da... Lokaci guda ta nufi closet d’insa ta shiga bin kayansa da kallo lokaci guda take shafasu d’aya bayan d’aya... Siyama ta kuma sa hannu tana goge hawayen dake kuma gangaro mata... Taita tina rayuwarsu na baya a cikin gidan... Da k’yar ta tafi nata d’akin ta shirya... Koda ta fito parlor duban dining area tai sai tana ganin kaman zata hangosa ya fito daga kitchen yana fad’in ‘Partner breakfast’s ready...’ Ta saki murmushi a hankali,Sameer ita ya kamata ta tabbata yaci abinci kafin ya fice wajen aiki amma a b’angarenta ba haka bane Shine yake tabbatarwa taci abinci kafin ta fice aiki... Sameer wane irin miji ne da tayi imani samun irinsa a wannan zamani yakeda matuk’ar wahala... Ta kuma share hawayen da suka gangaro mata... Jiki a sanyaye Ta nufi kitchen dan nema ma kanta abinda zata saka a cikinta...

**

Yana cikin d’aura agogo Raihanah Ta shigo sallama saman bakinta, sanye yake cikin jampa ruwan k’asa da yai matuk’ar amsarsa...Ganin yanayinsa ya kuma sanyaya mata gwiwa... Kanta a k’asa ta gaidashi, ya amsa idanunsa naga abinda yake.... A hankali take furta “Mummy ce tace na dubaka ko lafia taga baka fito ba...”

Shiru na d’an lokaci har kaman bazai amsa ba sai kuma ta sinkayo muryarsa yana fad’in “Daddy ya fito...?”

Jinjina masa kai tai alamun eh... Sameer ya jinjina kansa ba tareda cewa komai ba yana mai brushing sumarsa gaban dressing mirror, ya mik’a hannunsa yana k’ok’arin d’aukan hularsa dake saman drawer a wajen, nan hular ta subce ta fad’i k’asa, baikaiga d’aukowa ba ya hangeta Ta duk’a ta d’auko masa, kanta a k’asa take mik’a masa, bai amsa ba saima k’ura mata idanu da yai yana karantarta... ya kula yau d’in mood d’inta a b’ace yake.... hannayensa biyu yasa ya tallafo fuskarta had’ida k’ura mata idanu... Cikin sassanyar murya yake furta
“Hey...What’s wrong... Did something happen...?” Ya tambaya yana tallafe da fuskar nata..

Ganin Ta kasa magana saima hawaye dake k’ok’arin gangaro mata ya sanyashi saurin kamo hannunta suka zauna saman kujera... Hannayenta ya kamo cikin nasa had’ida k’ura mata idanu...

SameenaAleeyou 📚

*INDA RAI*
_................DA RABO_

*106*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

NOT EDITED
Chapter 176 · 0% Book details