← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 193 OF 198

Sashe 193

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Babu b’ata lokaci suka nufi gidan Hajiya Rabi d’iyar Hajiya Marka marigayiya k’awar Mamani.... Mamani tana hango Abbah sabon kuka ya kece mata... Allah sarki shima Abban kukan yake sosai lokaci guda ya tafi ya rungumeta yana kuka sosai yake fad’in “Mamani mai yasa zaki tafi ki barmu... Munsha wahala sosai wajen nemanki... Mai yasa zaki gujemu Mamani na...!”
Cikin muryar kuka Mamani ke fad’in “Usman bansan da wasu idanu zan dubeka ba... Abinda na b’oye maka tsawon rayuwarka abu ne mai girman gaske d’ah na.... Nayi kishi sosai irin na jahilcin zamin da nida mahaifiyarka amma Allah shine shaidata haihuwa itace tai sanadiyar mutuwar Harira... Usman ka yafeni idan na b’oye maka dika wad’annan d’ah na....” Ta k’arashe tana kuka sosai....
Abbah ya kuma kamo hannayenta yana hawaye lokaci guda yake furta “Na yarda dake Mamani, kuma tabbas da ace zaki kashe mahaifiyata da nima kin had’a dani amma kika d’aukeni kika bani duk wani kulawa da uwa ke baiwa d’anta... Shin ta yaya zan mance duka wad’annan... Mahaifiyata haihuwata kawai tayi amma kece duk wani d’awainiyata tin ina tsumman goyo har izuwa girmata, hakan bazai tab’a shafewa a idanuna ba... Zanci gaba da yiwa mahaifiyata addu’an samun rahama har tsawon rayuwata sannan kema zanci gaba da baki matsayin mahaifiya da nake baki tin tasowata... Babu abu guda da zai canza Mamani na....!” Ya k’arashe murmushi saman fuskarsa hawaye naci gaba da gangaro masa....
Mamani ta tallafi fuskarsa tana hawaye sosai lokaci guda take furta “Tabbas ba sai ka haifi d’ah ya zamto Naka ba... Na yarda da wannan kalma da hausawa me cewa D’ah na kowa ne... Kada kaga yaro ka wulak’antasa ko Allah ya k’addari rik’onshi ya fad’o hannunka kai masa rik’on sakainan kashi, bakasan waye zaka mora a rayuwa ba, d’an wani sai yai maka abinda Naka d’an bai maka ba... !”

Abbah na hawaye yake jinjina kai kana yace “Mamani tare muke da ‘yanuwana... Zamu d’aukeki mu koma gida gaba d’aya...!”
Mamani ta d’an sarara da kukanta kana tace “Kana nufin harda Alhaji..?”

A hankali Abbah ya jinjina mata kai yana mai duban k’ofa yanda su Baba Alhaji dasu Baffah wada suka sako kai cikin d’akin... Mamani tana ganinsu a haka sabbin hawaye suka shiga zarya a fuskarta... Haka Baba Alhaji ya duk’a yana kuma neman gafarar Mamani harmada Abbah... Allahu Akbar hawayen Mamani suka gaza tsayuwa yau ga ‘ya’yenta a had’e waje guda, gasu nan sun yafi juna, mai yafi wannan Farin ciki, ko yanzu Ubangijinta ya kirayeta ya cika mata burinta taga irin wannan rana.. Yanzu batada buri da ya wuce ta sami Mariya da Zulfa’u ta nemi nasu yafiyar...
Haka su Abbah sukaita godiyawa Hajiya Rabi kana suka d’unguma suka koma gida gaba d’aya cikeda Farin ciki... Kan kace mai labari ya zaga family Mamani ta dawo... Kowa sai murna da San Barka yake... Mamani ta nemi yafiyar Mamy dama yaranta, rayuwa ta koma kaman da harma fiyeda da, Wai zo Kaga murna wajen Raihanah da Sameer, har sai aka rasa wa yafi murna... Su Nabilah ma sunyo waya daga Abuja Khalid yace bai isa ba dole su taho Kano su gaida Mamanin Haladu....Lol

Mamani da kanta taje taiwa su Zulfah murna ta kuma nemi yafiyar Zulfah, Engr da baisan Mamani sosai ba yanata d’an mata surkunta nan ya fahimci Mamani kam babu ruwanta da wani surkunta... Ya cikata da goma na arziki harda kyautar sabuwar mota dal aka dawo da Mamani gida... Sai kuka Mamani take tana fad’in yau dik Ta dalilin Zulfa’u ta samu wannan d’aukaka... Rayuwa kenan, d’an hakin daka raina wataran shike tsone maka idanu... Dik yanda D’an adam yake kada ka rainasa Allahn da ya haliccesa shi Yasan mai ya aje wajen....

Bayan dawowar Mamani Mami Ta rok’i Abbah kan yaje ya maido da Aunty Lami, da fari yak’i yarda da hakan har saida Mamy taita masa magiya tana nuna masa yanda ya yafema kowa itama ta cancanci yafiya tinda ta gane kurenta, sannan dik Abinda ya faru muk’addari ne daga Allah, hakan tuntuni na rubuce...
Da wad’annan batu na Mamy Abbah ya yarda suka tafi har k’auyen su Aunty Lami tareda Mamy...

Aunty Lami ta rame tai bak’i ta fita hayyacinta kaman ba ita ba, zaman k’auye surfe da daka ma kawai sun isheta gashi gidansu mahaifinsu malamin zaure ne wanda bayan rasuwarsa Almajiran basu bar gidan ba sauran matan Babanta da wasu daga cikin yayyensu maza sun ci gaba da kulada almajiran dan haka wahala ce tsantsan ta tadda a wannan gida... Aiko tana ganin su Abbah haka ta duk’a ta dinga kuka tana rok’onsu yafiya musamman Mamy....

Mamy tace “Babu komai Lami Allah ya yafemu gaba d’aya, yasa wannan ya zamto wa’azi a gareki da masu hali irin naki...”
Aunty Lami sai jinjina kai take tana hawaye had’ida da kuma neman gafararsu.... Wani irin kima da darajan Mamy ne suka k’aru a idanunta.... Daga bisani suka d’unguma suka komo gida, har lokacin Aunty Lami a d’arare take....

***

A b’angaren su Zulfa’u kuwa tuni an gama processing visa d’insu, cikin kwanakin suka d’aga zuwa k’asa mai tsarki, kafin su tafi saida Engr ya kaisu duba Muhibbah gaba d’ayansu harda Zulfa’u da yaran... Muhibbah taita masa godiya tana rungumar yaranta, Ta kuma dank’a amanansu hannun Zulfa’u dan batada haufi Zulfa’u zata rik’e mata su da aminci... Haka suka tafi Muhibbah na cikeda kewarsu danma Ta soma karatun Islama a nan prison d’in, idan ka ganta ma bakace ita bace, babu shan k’waya babu ta’ammudi da miyagun k’wayoyi daga ita har Shamzy yanzu sosai suka rungumi sanin addininsu....

Sauk’arsu a k’asa mai tsarki aka wuce da Ammah asibitin ta dan dama tin suna Nigeria an riga an ida dik wani abinda za’ai.... Nan Ammah ta buk’aci Engr ya d’auki matarsa su tafi wani wajen su keb’e tinda ita a nan Gata nan ga yaran ga kuma Hajjah sannan ga Akram ma... Tana ganin zai kyau idan sukai amfani da wannan dama suka d’an tafi wani wajen kafin su koma Nigeria ya soma hidiman office... Tamkar Mahaifiyar tasa Ta shiga ransa, burinsa kenan su d’anyi amfani da wannan tsakani shida matarsa su kasance tare....
Babu wani b’ata lokaci ya sai masu tikitin k’asar Maldives, Akram shi yai masu processing komai cikeda ladabi had’ida girmamawa....
Washe gari suka d’aga zuwa k’asar Maldives..

***
MALDIVES

*Anantara Dhigu Maldives Resorts*

Ita dai tinda suka iso wannan k’asa mai d’inbin Ni’ima take jinta tamkar wani duniyar ta daban suke, Wai dama akwai irin wad’annan wajaje a fad’in duniyar nan... Kai lallai ganin wannan waje ra’il aini ya kuma sanyata tsarkake Ubangijinta a zuciyarta wanda ya k’agi halittar wannan waje da yafi dacewa da a kirasa da Aljannar duniya... Ikon Allah Wai ita Zulfa’u yau dai gata a island nan tsakiyar tsibiri abinda take gani a talabijin da hotuna yau gata cikinsa, Daidai da d’akinda take ciki tsakiyar ruwa yake, ruwanda view d’insa ma kawai kwanciyar hankali yake haifar maka had’ida wane irin natsuwa cikin zuciya.... Ta kuma juyi saman gadon da aka k’erasa da zallan itace akai masa wane irin kwalliya da shell, komai dai a wannan waje abin birgewa ne, ga wani irin ni’imtaccen iska na kad’a dik wani kafa na jikinta.... Laushin bargo da bedsheets ya kuma sanyata lumshe idanu tana sakin wane irin murmushi a hankali... Tinda ya bata kayan da zata sanya idan tai wanka bata kuma ganin gittawansa ba, tadai daure Ta kuma mik’ewa tana duban kanta jikin full length mirror dake nan cikin d’akin wanda akai masa kwalliya da shell shima.... Rigace bak’a doguwa wanda tafi kama data turawa... Ta d’an murmusa kad’an Wato yau irin shigar da yake so ya gani jikinta kenan... Wata zuciya tace “Yanayin wajen bana saka atampa bane k’ila shisa ya kawo miki wannan ki saka.... Ta kuma sakin murmushi a hankali tana mai gyara sumarta ta d’auresa cikin bakin mayafin rigar, ita kanta tasan babu Wai tayi kyau Masha Allah son kowa kin wanda ya rasa... Kyaun da ita kanta bata tsammaci tana da irinta ba.... Tana nan tsaye wayarta ta kuma yin k’ara... A hankali ta isa saman gadon tana duba wayar... Gabanta ne yai wani irin tsinkewa ya fad’i... ‘Mr Unknown..’ Sunan da ya soma zuwa zuciyarta kenan.... Tai saurin bud’e sak’on tana karantawa.... Gabanta ya kuma tsinkewa...
_Nasan kina son sanin ko ni wanene..._ Wannan shine sak’o na biyu da ya shigo....
Zulfa’u har ta soma tsorata tana tinanin toh ko dai gamo Tai ne... Tayi zaton wannan bawan Allah ya daina turo mata anonymous messages d’insa tin ranar aure sai kuma ga wani yau... Ta had’iyi miyau da k’yar dan bata fatan abinda zai kawo mata cikas ga wannan sabon rayuwa mai cikeda Ni’ima data tsinci kanta ciki... Bata ida tinanin ba wani sak’on ya kuma shigo mata...
_Idan har kina son sanin ko ni wanene ki biyo wannan k’ofa da kike hango beautiful ocean d’in nan daga wajen...._
Chapter 193 · 0% Book details