← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 198

Sashe 49

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya bata bari takai aya ba tace “Shanye Sarki saidai kar a kuma, kinga nan....” Tai nuni da tafin hannunta kana tace “D’anki na nan sai yanda na juyasa, ko kasheki zanyi bazai tab’a ganin laifina ba saidai ma ya min godiya....” Suka saki shewa itada yaranta...

Mamani da tuni hawaye sun soma zubo mata murmushi tai a hankali kana tace “Dama ita duniya abinda ka shuka shi zaka girba, ko kad’an banji zafin shanye naki d’an da Alahalil kitabi tayi ba... Hakan shine daidai, na kumaji dad’i da Zulfa’u ta rabu da auren wahala in sha Allahu alkhairi na gaba da ita....” Ta juya ta dubi Raihanah da Kausar dake rakub’e gefe guda tace “Ku taso mu tafi kun gama zaman gidan wannan azzalumar....”

Raihanah ta mik’e a tsorace tana rungume da Kausar...
Ai tuni Hajiya ta finciki Kausar tana watsa masu harara take fad’in “Koda wasa idan zaki d’auki jikar naki bisimillah amma wannan jikata ce yanda kikeji Raiha d’iyar d’anki ne haka nakeji Kausar d’iyar Danah ne don haka babu yanda Kausar zata tafi a nan gidan zata zauna...”
Ta maida dubanta ga Raihanah kana taci gaba da fad’in “Ke kuma ki bita idan kinga dama amma ki sani ubanki na dawowa zansa ya d’aukoki, munafukar banza munafukar wofi....” Ta k’arashe tana janyo mata jakan kayanta had’ida jifanta dashi... Taci gaba da fad’in “Idan dai wannan tsohuwar kakar takuce sai kinyi d’andakinsani komawa gabanta domin kaw ba k’aunarku take ba...”

Mamani bata amsata ba don gaba d’aya jikinta a sanyaye yake Sawwama ta gama kashe mata jiki ta nemi fad’a da masifan nata ma ta rasa, kamo hannun Raiha tai suka fice daga gidan, dukda cewa Raihanah bata saba da Mamani ba sannan ta sani Mamani bata son jikokinta ‘yanmata amma har cikin ranta takeji ya fiye mata zaman gidan mahaifinta gaban Hajiya...

A haka suka isa gida Raihana na gane masu hanya....

***

Bayan ficewarsu Sahariyya ta koma gefe ta zauna ta had’e rai sosai donma kar Hajiya tayi tunanin sakata wani aiki tinda Raiha ta tafi, ga wanke wanken da bata ida ba... Tab aiko billahillazi bata isa ta sakata aikin wanke wanke ba saidai tayi da kanta, k’arashe ma mik’ewa tayi ta kad’e bujenta ta shige d’aki....

***

Yesmin tsaye gaban dressing mirror tana kuma shafa yanda Nabilah ta shata mari masu kyau har guda biyu... K’wafa ta kumayi a karo na babu adadi kana tace “Wllhi sai na shayar da ita mamaki, badai a unguwar nan take ba, yazo gidan sauk’i sai tasan ta tari fad’an da yafi k’arfinta... Shegiya d’iyar matsiyata...”

Siyama dake zaune bakin gado tana duban Yesmin d’in sauk’e ajiyan zuciya tai kana tace “yanzu ta ina zamu b’ullo mata....”

Yesmin ta juyo da dubanta gareta kana tace “Ni nasan ta yanda zamu b’ullo mata, badai tace ita maras kunya ba, zamu nuna mata munfita iya bariki da rashin kunya, k’aramace ita a wannan makarantar....”

Siyama ta murmusa kana tace “Ni da police nake tunanin mu kawo mata...”

Girgiza kai Yesmin tai kana tace “A’a ai bata nan zamu b’ullo mata, ta yuyu wannan ta saba kwanan station tinda kikaga haka, tuggu da makirci shine kawai zai rabamu da tsinanniya...”

Siyama ta dara a hankali kana tace “Kinga zo muje kitchen ki sama mana abinda zamuci tinda kinzo na huta order...”
A tare suka fice suka nufi kitchen d’in....

***

Mamani ta lura da yanda Raiha ke d’ari d’ari da ita, tausayin yarinyar ya cika mata zuciya...
“Raihanatu sunanki koh....?”
Raihanah ta jinjina kai a hankali alamun eh....
“Kodai kece Halimatu takwaran tawa..?” Nanma a hankali ta jinjina kai alamun eh kana ta k’arada ni ce...
A fili Mamani ta furta “Alhamdulillah da ya kasance ba’a cikin wad’ancan watsattsun d’iyoyin Haulen aka sanyamin takwara ba... Ki saki jikinki kinji koh, nan gidanku ne... Da Manu da Sarki duka ‘ya’yana ne don haka nan ma gidan Babanki ne kinji koh...”

Raihana ta k’ak’aro murmushi a hankali tace “Toh Mamani....”

“Yauwa Raihantu... Kinci abinci kuwa...?”

Shiru bata amsata ba, Mamani ta fahimci bataci abincin bane, flask d’in dake gefe wanda aka kawo daga wajen Baffah Wada ta janyo ta mik’a mata tace maza taci mai isanta, shinkafa da wake ne da mai da yaji....

Mamani ta mik’e ta nufi d’aki abubuwan data aikata a baya sai dawo mata suke, yanzu idan ba’a sami Zulfa’u ba itama tamada kamisho tunda tana d’aya daga cikin masu aibantata da muzantata da k’untatawa rayuwarta... Allah dai ya bayyanar masu da Zulfa’u ta nemi yafiyar yarinyar nan don bazataso ta mutu da hakkin Zulfa’u akanta ba.... Da wannan tunani ta zauna jiran dawowan d’anta Abbah... A haka bacci yayi gaba da ita...

Raihanah kuwa tuni ta shiga tattarewa Mamani d’aki, ta gyare mata ko ina yayi tas tas gwanin ban sha’awa, tai wanke wanke ta goge ko ina, harta dangin kayan kallo su tv stand saida Raiha ta goge ko ina ta saka roomfresh waje ya d’auki k’amshi kaman ba d’akin tsohuwa ba, kiraye kirayen Sallahn azahar ya tada Mamani, mamaki ya cikata ganin ko ina a gyare bacin tasan yaran Baffah Wada da k’yar akeyi dasu suzo su gyara dama Marliya ce mai shigowa tai mata idan batada karatu....

Nan fah Mamani taga aikin Raiha ya zarce duk wanda ake mata, ita kad’ai sai murmushi take tana fad’in “A’a ikon Allah.. kaji yarinya d’iyar albarka... Oh ashe dai d’iyoyi mata rana ne dasu...” Tai maganar a hankali kana ta lek’a d’aya d’akin ta hangi Raiha na sallah cikinta nan ma tas tas kaman bashi ba...
Ta kuma sakin murmushi cikeda jin dad’i kana ta nufo waje don gabatar da alwalan azahar sai shan mamaki take don harta taakar gidan tas ta share ta gyare...

Mamani ta hangi kujeran zamanta nayin alwala a goge tsaf harda buta a gabanta, ta isa ga kujeran ta dafa ta zauna tana mamakin ina aka samo mata sabon buta... Saida ta d’aga tace “Au ikon Allah ashe dai butarce dai tawa...” K’al Raihanah ta wanke butar ta cika mata ruwa mai d’an d’umi bamai sanyi k’au ba...
Mamani sai mamaki take tana ayyana hankalin yarinyar cikin zuciyarta....

***

Wajajen k’arfe biyar ya fito daga office, tafe akan hanyarsa ta komawa gida ya hangi motar Abbah na k’ok’arin shiga gida, bazai iya shigewa ba tareda ya tsaya sun gaisa da Abbah ba, daga can yayi parking ya sauk’o ya nufi motar Abbah wanda shima tuni yayi parking d’in sakamakon hango Sameer d’in da yayi....

Cikeda risinawa yake gaida Abbahn, Abbah ya amsa masa kaman ko yaushe, fuska fal fari’a...
“Malam Sameer an taso aiki kenan...?” Abbah ya tambaya murmushi kwance saman fuskarsa...
Sameer da shima murmushin ne kwance saman fuskarsa yace “Eh Abbah an taso, ya kasuwa...?”

“Alhamdulillah... Mun gode Allah, ya wajen aikin naka... Anata fama da jama’a koh...?”

Sameer ya d’an shafa kai yace “Alhamdulillah... Toh Abbah zan wuce a huta gajjiya...”

Abbah da duk had’uwansu da Sameer bai fatan abinda zai rabasu cikin sauri ya tari Sameer d’in da tuni ya nufi motarsa da fad’in “Amm Dr nace ba ko zamu shiga kaci abinci.... Akwai fura mai kyau ma sai a dama maka...”
Sameer baison ce masa a’a sabida tsananin nauyin mutumin da yakeji d’an k’ak’aro murmushi yai yace “Ai Abbah ban jima da cin abinci a wajen aikina ba...”

Annurin fuskan Abbah ya d’an ragu, kaman zaice shikenan ka huta gajjiya sai kuma yace “Ko furan kasha Dr, tanada kyau sosai musamman nasa a dinga kawo mani...”

Sameer ya d’an kuma shafar k’eyarsa babu yanda ya iya bazai iya jada Abbah ba sabida tsananin ganin girmansa da yake....
Cikeda risinawa ya amsada “Toh..To Abbah...”

Cikin jin dad’i Abbah yace “Yauwa ko kaifah maza shigo da motar taka cikin gareji...”

Babu musu Sameer yayi yanda Abban yace, suka nufo cikin gidan tare...

Aunty Lami da fitowarta kenan daga sashen Abban don ita keda girki ta gama jere abinci kenan, nan ta hangosu sun jero suna tahowa Sameer rik’eda ‘yar jakkan Abbah....
Gabanta ya yanke ya fad’i, shikenan kullum kusancinsu k’aruwa yake, cikinta ya murd’a lokaci guda....
A daburce ta nufi sashenta tana tunanin abinyi, Aminiyar Sirri zata kira ko kuwa Haule...
Gadai Ma’aruf har cikin gida yauma, ga kuma dama ta samesu domin kaw itace da girki...
Hannunta rik’eda wayar salula ta rasa wace zata kira cikinsu, shawarin wa zata d’auka cikinsu...
Lokaci guda ta yanke shawarin kiran ko wacce cikinsu don jin yanda zasuyi da Ma’aruf...
Hajiya ta soma kira ta sanar da ita abindake wakana...
Ai babu wata wata Hajiya tace tasan yanda za’ai tai amfani da wannan dama ta zuba masa guba yaci su huta, itakaw Aminiyar Sirri cewa tayi “Yanzu ke banda abinki Lami kika saka masa guba yaci kindai san babu wacce za’a kama saike, ita Haule da take tinziraki kiyi hakan ai tasan ba kamata za’ai ba tinda ba ita ta bashi abincin ba... Nidai shawari ki bari abi komai a sannu...”

Lami ta amsada “Kumafah hakane gaskiyarce Aminiyar Sirri... Zanyi yanda kikace d’ain...” Daga haka sallama sukai tana mai ci gaba da kaikomo cikin d’aki...

Nabilah dake lab’e bakin k’ofa bata jiyo komai ba sai AMINIYAR SIRRI... Nanata ta dingayi cikin zuciyarta, Aminiyar Sirri....
Cikin sauri ta fice daga sashen ta koma can k’uryar d’aki ta shiga neman layin Aunty B...
Bugu biyu a na uku Aunty B ta d’aga...
Cikeda damuwa Nabilah ke sanar da ita sabon sunan da ta jiyo daga bakin Aunty Lami Aminiyar Sirri...

Shiru Aunty B tai kaman mai nazari kana tace “Aminiyar Sirri...? Toh mai hakan yake nufi...?”

Nabilah tace “Abinda naji kenan Aunty, and ga dukkan alamu matar da take waya da ita itace Aminiyar Sirrin... Aunty could it be possible Aminiyar Sirri itace ta taimakawa Aunty Lami wajen ganin bayan d’an uwana Ma’aruf...?”

Nanma shiru Aunty B batace komai ba, saida ta d’an d’ibi wasu dak’ik’ai kana tace “Watak’ila hakan ne Nabilah...”

“Toh wacece wannan aminiyar sirrin...? I need to find out who she’s...” Ta fad’i tana mai jaddada kalamanta...

Aunty B tace “Kodai itace wacce kike ganinsu tare ma’ana Hajiyar Hafiz....”
Chapter 49 · 0% Book details