Sashe 3
Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Toh nace bazaki tafi da ita ba Zulfa’u, harni zakiyiwa gada kan d’iyar d’anah, aikin banza aikin wofi ke wato ga ‘yar boko mai bautan k’asa koh... Shiyasa na k’yamaci aurenki da d’anah wayasani gantalin mi kike tafiya da sunan bautan k’asa, wllhi wllhi Zulfa’u kinji na rantse idan ina raye bazan tab’a barinki kiyi tarbiyan Khausar ba, kuma koba dad’e koba jimawa auren da Ubanninku suka k’ulla tsakaninki da d’anah sai an warware... Annoba dangin tsiya.....Tashi ki fice mun....” Ta k’arashe tana mai janye b’angaren tabarma da Zulfah ke zaune bisa wanda saida ta dungura k’asa, su Naja’atu abin nema ya samu suka kuwa kwashe da shewa....
Hawayen da Zulfah ke rik’ewa suka shiga gangaro mata, a hankali ta mik’e ta fice daga gidan farin hijabinta duk ya b’aci da hawaye.....
*SameenaAleeyou📚*
[25/11, 16:42] +234 703 745 3539: *INDA RAI*
_...............DA RABO_
*03*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
*Dedicated to my Trio♥*
A hankali ta zame hannayenta dake cikin ruwan wanke wanke kana ta saci kallon gefen da Hajiya ke zaune hankalinta yayi nisa wajen tsinewa Zulfah da zuri’arta itada yaranta su Sahariyya....
A can bakin layi ta hangeta tana neman a daidaita, cikin sauri ta k’arasa idanunta na zuban hawaye sabida tsananin tausayin Aunty Zulfah, batasan sanda ta rungumeta sabon kuka na zuwa mata ba, mamaki ya ishi Zulfah jin yanda ta rik’eta tana kuka wanda ko ba’a fad’a maka ba itama nata tarin k’uncin take fitarwa....
K’ok’arin daidaita kanta Zulfah tayi don idan k’arami nayi kai a matsayinka na babba sai kayi k’ok’arin samun k’warin gwiwa...
Rik’eta tayi kana tace “RAIHANAH ki daina irin wannan kukan kanki zaiyi ciwo.... Mai suka miki yau kuma...?”
Budurwa mai kimanin shekaru 17 da ta kira da Raihanah share hawayenta ta shigayi kana tace “Aunty Zulfah abinda suka maki naji zafi, kiyi hak’uri dan Allah, wllhi banji dad’i ba gashi nima sun hanani gaisheki wai ni munafuka ce, kiyi hak’uri Dan Allah...” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya....
Murmushi Zulfah tayi kana ta shiga share hawayen dake kwaranya idanun Raihana kana tace “Raihanah ki daina saka damuwa ma ranki kinji koh, nidake irin tamu k’addarar kenan da Allah yaso jarabtanmu da ita, Allah ya bamu ikon ci... INDA RAI wataran duk wad’annan abubuwan zasu gushe mana su zamto labari kinji koh, kar ki mance duk tsanani yana tareda sauk’i kinji koh... Maza koma gida kafin Hajiya ta fahimci kin fito waje....”
Cikin sauri Raihanah ta jinjina kanta kana sukayi sallama da ‘yar uwarta Zulfah ta koma cikin gida a sace taci gaba da aikinta...
Raihanah marainiyace wacce tun tasowarta take shan azaba da uk’uba wajen kishiyar mahaifiyarta wato Hajiya Asabe, duk wani aikatau na cikin gida Raihanah ta iyashi tun kafin takai yanda take a yanzu, sam Hajiya Asabe bata d’aga mata k’afa dukda cewa mahaifinsu nada rufin asiri dai dai gwargwado yanda zai d’auka masu ma’aikata na cikin gida son ransu, da k’arfin gaske Hajiya kan koresu musamman yanzu da Raihanah ta kuma zama ‘yan mata, ko wadataccen lokacin karatu bata samu kaman yanda sauran ‘yan uwanta ke samu, idan ta dawo daga boko aiki na jiranta haka idan ta dawo daga islamiyya aiki na jiranta, badon mahaifinta na raye ba tabbas da ko makarntar Hajiya bazata bari tayi ba. Duk matan da Baffah Ado kan aura basa jimawa a gidan Hajiya kanyi sanadin tafiyarsu, mahaifiyar Raihanah ce ma ta d’anyi k’argo a gidan ba’a koreta ba dashike Allah yasa akwai rabon Raihanah a tsakani saidai haihuwarta da kad’an mahaifiyarta tace ga garinku, da yawan mutane sunfi danganta mutuwar mahaifiyar Raihanah da saka hannun Hajiya Asabe domin kuwa k’iri k’iri Hajiya ke nuna nata nata ne na wani kuwa ba nata bane haka nan mutanen unguwa ke mata lak’abi da Ramin Kura ‘ya’yanta kawai take so, gaba d’aya gidan tarbiya bai wadacesu ba duk goyon Hajiya garesu, Raiha ita ta fita zakka don harta mijin Zulfah ma shaye shaye yake wai anyi masa auren ne ko zai daina ga hangen ‘yanmata duk budurwar da ya k’yalla idanu kanta sai yace yana so, da anyi magana Hajiya tace sharri akewa d’anta anga shine babban jika na miji a gidan. Mahaifiyar Zulfah da danginta sam basuso auren Zulfah da Hafiz ba amma babu yanda suka iya tuni Baffah Alk’ali mahaifinta ya bada aurentawa Hafiz d’an d’anuwansa, koda mahaifin Zulfah yazo mata da batun batayi musu ba sannan take ta amincewa mahaifinta dukda cewa ga irin halin da Hafiz ke dashi uwa uba ga yarinta da yake fama dashi a lokacin da sukayi auren don dudu bai wuce ratan shekaru uku zuwa hud’u ne tsakaninsu ba., Haka nan Zulfah tayita fama da rashin hankalin Hafiz da sunan biyayyawa mahaifi, tabbas ta sakama zuciyarta Allah bazai tozartata ba tinda yaga niyyanta ta kumayi alk’awarin taka muhimmiyar rawa wajen saita rayuwar Hafiz ya inganta don shine abokin rayuwarta a halin yanzu uwa uba sun soma aje zuri’a.....
Tana tsaye bakin kwalta tana neman abin hawa idanunta sunyi luhu luhu, kalaman Mamani dana Hajiya basu daina zarya a zuciyarta da kwanyarta ba, wad’annan mata guda biyu su sukayiwa rayuwarta karar tsaye mahaifiyar mahaifinta da kuma mahaifiyar mijinta, tabbas ta had’u da k’alubale babba a rayuwarta.... Sam bataji k’aran horn d’in mota daketa faman tashi a bayanta ba, tamkar wacce aka zabura haka ta dawo daga duniyar tunani tana mai k’ok’arin juyawa taga mai wannan horn d’in yawa zai d’agata...
Lokaci guda ta saki murmushi kana ta k’arasa ta bud’e marfin motar b’angaren mai zaman banza....
“Aunty B ina yini...? Allah sa dai gida kika nufa ki ragen hanya....” Duk maganganun da take bata bari sun had’a idanu da matar data kira da Aunty B ba, sai faman sunkuyar da kai take bataso Aunty B taga idanunta da suka kumbura ta fahimci kuka tayi....
“Zulfah....!” Aunty B ta ambaci sunanta cikeda kulawa kana tace “D’ago ki kalleni...”
Kasa d’agowa tayi saima k’ok’arin dad’a kauda fuskar da tayi...
Aunty B bata kuma tsayawa bin takanta ba ta shiga janyo fuskar nata tana ganin yanda idanunta sukayi jazir sukayi luhu luhu abinka da farar mace...
Baki sake Aunty B tace “Gidan Hajiya Asabe kika fito koh, ta maki rashin mutuncin data saba koh...?” Aunty B ta k’arashe tana faman huci...
K’ok’arin girgiza kai tayi had’ida k’ak’aro murmushi kana tace “A’a Aunty, sauri nake zan k’arasa gida na samu na d’aura dinner....”
Aunty B ta tsareta da idanun tausayin d’iyar ‘yar uwar nata na kuma cika zuciyarta lokaci guda tanaji ta shiga gidan Alhaji Ado tayiwa Asabe d’add’aya don gwara su sani Zulfah nada dangin mahaifiya masu k’aunarta....
Lokaci guda Aunty B ta kashe motar kana ta fice tana mai furta “Jirani ina zuwa.....”
Ganin yanayin da Aunty B ta fice a motar gashi ta nufi kwanar gidan Baffah Ado yasa gaban Zulfah yankewa ya fad’i, a d’ari ta sauk’a ta takewa Aunty B baya tana rok’onta tayi hak’uri tazo su tafi, ai idan gyalen Aunty B ya amsa itama zata amsa sai faman watsa sauri take yawa wacce ake tinzirata....
Hajiya dasu Sahariyya sun saka Raihanah a gaba suna tambayarta gidan uwar wa ta fita gulma, Hajiya ta dubi Naja’atu dake tsaye bakin famfo ta rik’e kunkumi tana jira mahaifiyarsu ta basu izini su lakkad’i Raihanah kana tace “Najah jeki d’auko min dorinar nan don ubanta tinda bazata fad’a ba....”
Cikin muryar kuka Raihanah ke fad’in “Hajiya wllhi Allah babu yanda naje dan Allah kiyi hak’uri....”
“Bazanyi ba munafuka, badai kin rainani bane har zan sakaki aiki ki tsallake ki fice, yi sauri Najah.....” Ta k’arashe tana janyo wuyar Raihanah a dai dai sanda Aunty B ta banko k’ofar tsakar gidan ta shigo....
Jifa da Raihanah Hajiya tayi kana ta maido da dubanta ga Aunty...
Huci kurum Aunty B keyi kana tace “Hajiya Asabe kiji tsoron Allah ki tuna abinda kayiwa d’an wani za’ayiwa naka, kuma ‘ya’ya mata gareki gidan aure zasu tafi kuma bakisan wasu irin sirkai zasuyi arba dasu a gidan aurensu ba, bama wannan ba gameda Zulfa’u ki sani Zulfah ‘yar dangice bazamu zuba ido kicigaba da muzantata kina wulak’antata ba, aike abin ki gode mata ne don idan ba itaba babu mai auren wannan d’an naki... Kodashike ba laifinki bane Uwar mijinki ta bud’e maki k’ofa kiyiwa Zulfah haka amma ki sani idan a baya mun zuba maku ido yanzu bazamu zuba miki ido ki ci gaba da cin zarafinta ba, d’anki yayi kema kiyi wad’annan marassa ta idon yaran naki suyi....”
Tinda ta soma magana Hajiya ke k’yarma tana dubanta, yaran suka hayyayok’o Najah ta janyo bokatin wanke wanke Sahariyya ta finciki bulalar hannun Hajiya da sunan zasu daki Aunty B...
Murmushi kurum ta sakar masu tana mai gyara tsayuwarta tace “I dare you to try it, k’anan marassa kunya,... Na rantse da Allah maras kunyar data fasa cikinku, daga yau kun gama rashin kunya...”
Sahariyya tayi saurin sauk’e hannunta sanin mijin Aunty B Soja ne, Najah ce tayi kanta gadan gadan Hajiya tayi saurin raba tsakaninsu tana fad’in “K’yaleta k’yaleta Auta...” Ta maida dubanta ga Aunty B kana tace “Bara’atu kinyi kad’an ki shigo har cikin gidana kimin rashin mutunci, amma tinda haka kika zab’a mu zuba nidake....”
Tsaki Aunty tayi kana tace “Abinda kuka iya kenan, nidai na fad’a miki ki sakar ma Zulfah mara a mutunce, da da yanzu ba d’aya bane....” Daga haka sa kai tayi ta fice daga gidan had’ida buga masu k’ofa.....
Najah sai faman fincika take tana fad’in “Haba Hajiya haba meyasa baki barni na cirewa matar nan rashin kunyarta ba, sai me don mijinta Soja wllhi Allah Hajiya da baki barni na gurji hak’waranta ba baki birgeni ba....” Ta k’arashe tana mai jifa da bulalar hannunta had’ida wucewa d’aki fuuu....
Hajiya ta kama farar kujera dake ijiye tsakar gidan ta zauna da k’yar zuciyarta naci gaba da tafarfasa...
Sahariyya ta zauna gefenta tana tausarta, ita kuwa Raihanah ma iya cewa Allah ne ya ceceta, cikin sand’a ta wuce d’aki....
***
Har suka iso layin unguwarta bata daina tunani da fargaban abinda Aunty B ta aikata a gidan Hajiya ba, dubanta Aunty B tayi bayan ta ida parking kana ta dafata
“Zulfa’u...!”