← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 198

Sashe 90

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi Khalid ya kumayi had’ida fitar da iska a hankali kana yace “Bazan iya sadaukar da soyayyarki ba teddy bear... You’re the one I love, no one else... I tried amma na fahimci bazan iya ba... I love only you... And I’m ready to fight for you, for our love, for us to be together...”
Wane irin sanyi jikin Nabilah yai tama rasa mai zatace sai k’walla dake k’ok’arin ciko idanunta yayinda Yusrah ke tsaye gefe murmushi kwance saman fuskarta sabida Khalid da soyayyarsa ga k’awarta sun bala’in burgeta.....
Kaman wacce akace ta waiga nan ta hangi Yusrah rungumeda handouts d’insu... Tai saurin k’arasawa kaman zata kifa tana k’ok’arin janyo hannun Yusrah take fad’in “Muje kinji... Zo mu tafi.....”
Dogewa Yusrah take tana fad’in “Mu tafi ina bayan yanzun nan class rep yace malamin bazai shigo ba yace saturday zai fixing class, kowa ya watse ma....”
Khalid ya tari zancen nata da fad’in “Well, in that case inaga muma sai mu wuce gida ai koh.....”
Nabilah ta kasa cewa komai saiko Yusrah da murmushi ya kasa gushewa saman fuskarta ta bud’e baki tana gaida Khalid... Ya amsa mata da sakin fuska fiyeda lokacinda suka soma had’uwa....
Khalid ya k’arashe amsa gaisuwar nata yana mai danna security lock d’in motar sa nan ya bud’e kana yace “Muje koh....” Bai jira amsarta ba ya nufi motar.... Nabilah ta rakasada harara yayinda Yusrah ta shiga janyota tana fad’i k’asa k’asa “Wllhi baki isa kice bazamu shiga ba....”
Hararan Yusran ma tai badon taso ba ta nufi motar Khalid d’in sanin cewa ko tace bazata shiga ba Khalid sai yasan yanda yai ya sanyata shiga....

***

Hajiya Magajiya ta narkawa ‘yarta Sawwama muguwar kallo kana tace “Ashe ke babbar mahaukaciyace ban sani ba, bayan duk uwar rashin mutuncin da kikayiwa Hafiz da ‘yan uwansa kina tunanin zai amsheki a karo na biyu ne... Ai shikenan ya kubce maki domin ita dama guda d’ayace tak...”
Sawwama ta kuma tura baki gaba kana tace “Magajiya wllhi bazan bari Hafiz ya auri wata ba muddin ina numfashi baida wata mata gidan duniyar nan bayan ni.... Ni idanma bazaki kuma tsayamin ba zan wanke k’afata na koma wajen Malamin can da ya mana aikin farko ya shawo min hankali mijina ya karkata zuwa gareni....”
Shewa Magajiya ta saki had’ida rangad’a gud’a da tafe hannaye kana tace “Yanzu ne na tabbata kin cika d’iyata, dama gwadaki nake don mu ba’a jadamu a zauna lafiya bamu kuma sadaukar da fad’a cikin sauri, don haka yanzu na tabbata kin dawo cikin hankalinki.... Tashi mu tafi... Babu boka babu Malam da bala’i wannan karon sai Hafiz ya dawo gareki....”Ta k’arashe tana janyo mayafinta dake shanye saman igiyan shanya.... Fuuuu suka fice itada d’iyarta Sawwama...

Hajiya na baje tsakar gida tana fifita ma ciwonta wajenda bai ida warkewa ba ta sauraro dishesshiyar muryar Magajiya wanda sigari ya gama k’onasa tana banka sallama... Gaban Hajiya Haule ya yanke ya fad’i, cikin zuciyarta take tambayar kanta uwar mai Magajiya tazo yi mata gida...? Bata ida tunanin ba ta hangosu suna tafe uwar na gaba d’iyar na bayanta....

Dafe hannaye a k’irji Magajiya tai ta shiga jero sallalami tana fad’in “Ni haihuwar maguzawa haka jikin naki yayi Haule.... Sannu sannu kinji da jiki.... Ke Sawwama baki sanar dani haka jikin sirkar taki yayi ba... Yo ina nasan jikin naki yayi tsanani haka....”

Sahariyya dake zaune parlor ne ta d’ago labule don ba iya fitowa zatai ba har yanzu kariyarta bata ida warkewa ba, daga yanda take zaune ta bud’e murya tana fad’in “Ke tsohuwar ‘yar bariki koda wasa, karkizo nan ki mana salo, ince d’iyar taki itace sanadiyar ciwon Hajiya.... Yanzu kun d’ibo k’afafu babu kunya ta tasoki gaba zaku kawo wa mutane fitsara....”
“Keee kul ahir d’inki....!” Sawwama ta dakatar da ita kafin taci gaba da fad’in “Koda wasa ba’a zagi mahaifiyata a kwana lafiya... Tambayi tsohuwarki kiji dalilinda ya kwantar da ita jinya.... Yanzun nan zan karye miki d’aya k’afar taki ki zama gurguwa da kyau.....”
Zuciyar Sahariyya banda tafarfasa bata komai, batasan sanda k’walla masu zogi suka ciko idanunta ba jin kalan maganganun da Sawwama ke yab’a mata gashi babu halin ta tashi ta rama... Ta rarumo takalmin gefenta ta jifa masu tana ci gaba da zaginsu.... Sawwama tayo kanta gadan gadan Magajiya ta rik’eta tana fad’in “K’yaleta ‘yar albarka, da daidainka kake fad’a wa zai fad’a da nakasasshe, ai tsakaninmu da mai nakasa saidai sadaka... Kinga Hajiya Haule gaisuwa mukazo da ban hak’uri had’ida ban gajiya a matsayinki na uwar mijin d’iyata.....”

Batakai aya ba Haule dake tururi ta katseta da fad’in “Wllhi ko a hanya Hafiz ya kuma nuna yasan d’iyarki baki zan masa.... Ku fice man a gida kafin rayukanku su b’aci.....” Ta k’arashe tana huci kaman wata zakanya....

Shewa Magajiya tai had’ida juyi tsakar gidan kana tace “Ai baki Sani ba Haule, Hafiz da Sawwama ai auren zobe sukai idan kinga sun rabu toh ki rubuta d’anki ne ya mutu....”

Haule da k’irjintake tsananin suya cikin kufula ta soma rarrafowa zatayo kan Magajiya daidai nan Baba Alhaji yai sallama....

Tuni Magajiya ta saita kanta ta shiga janyo mayafi tana sinne kai ciki, murmushi kwance saman fuskarta ta duk’a tana k’ok’arin gaidashi, tai idanuma d’iyarta ma ta duk’a gaida Baba Alhaji itama.... Nan kuwa ya saki fuska sosai yana amsa masu ganin an duk’a ana gaidashi a cikin gidansa, don tun bayanda Raihanah ta bar gidan rabonsa da yaga an masa irin wannan gaisuwar a cikin gidansa saiko yanzu da Najah ta koma saliha....
Hajiya Haule ta saki bakida hanci tana kallon salon makirci....

Nan Magajiya taci gaba da jajanta ma Baba Alhaji abinda ya faruda Hajiya Haule ta kuma bada hak’uri kan abinda Sawwama tai da tabbacin haka bazai kuma faruwa ba.... Tai ma Sawwama idanu nan Sawwama ma ta shiga bada hak’uri harda kuka tana fad’in sharrin shaid’an ne ba halinta bane...
Baba Alhaji da gaba d’aya jikinsa yai sanyi nan ya shiga amsan hak’urinsu yana fad’in ai babu komai duk d’an adam ajizi ne..... Haba nan fah Hajiya ta fashe da kuka tana fad’in “Alhaji yanzu yarda kayi da makircin wad’an nan... Wllhi munafunci ne ba har zuciya bane..... Na shiga uku ni Haule....”

Baba Alhaji ya dakarta da ita da fad’in “Haba Haule, tinda sunzo sun tako har yanda kike sun nemi yafiya da afuwa mai zaisa bazaki yafe masu ba, kowa ya cancanci dama ta biyu.....”

Magajiya ta murmusa jin nasaran da suka samu kana ta isa kusan Hajiya ta kuma duk’awa ta kwanto da kai kusanta sosai, cikin sigan rad’a take furta “A makarantar makirci ajin farko kike har yanzu Haule... Babu boka babu Malam mu zuba kowa tasa ta ficcesa....” Ta d’ago tana duban Haule da hawaye suka wanke mata fuska ta shiga gogema Haule hawayen tana furta “Ki daina kukan nan haka nima duk sai kisa naji kukan.... Muyi hak’uri da juna don mahaillicinmu ma muna masa kure ya yafe mana... Ko ba haka ba Alhaji....” Ta k’arashe tana duban Baba Alhaji had’ida kashe masa murya...
Cikin sauri ya jinjina kai yace “K’warai kuwa.... Kar kiji komai Hafiz zai maida matarsa d’akinta in sha Allahu....”

“Laaaaa! Shikenan shikenan sun asirce min miji..... Wllhi wllhi kinci uwar k’arya Magajiya.... Wllhi....” Batakai aya ba Baba Alhaji ya katseta da fad’in “Haba Haule... Wane irin taurin zuciya ne haka... Duk wanda ya kwantar da kansa ya baka hak’uri sai ka amshi hak’urin nasa... Ku tashi kuje komai ya shige da izinin Allah....”

Magajiya ta kuma murmusawa tana duban Haule kana ta mik’e tana kuma sinne kai cikin mayafi, sai faman murmusawa take da bakinta gefen hak’orin makkanta, k’asa k’asa yake duban Baba Alhaji kana tace “Toh mun barku lafiya Alhaji... A dai k’ara hak’uri, yaran ne ka haifesu baka haifi halinsu ba.....”
Baba Alhaji sai Washe baki yake yana satan duban Magajiya da kalan murmushin da take masa har suka fice yana mai tabbatar masu Hafiz ya maida matarsa an gama.....

Har lokacin idonsa naga k’ofa Hajiya kaw bata daina dubansa baki sake ba.... “Alhaji! Alhaji!! Har saida ta ambato sunansa a karo na uku kafin ya maidoda dubansa gareta yana fad’in “Barin k’arasa ciki... Ina Naja’atu ya kawo min abinci na.... Ke Naja’atu....” Ya k’arashe yana bud’e murya alamun yana neman Najah.....

Sahariyya da akai komai a gabanta tsorone ya fara cika mata zuciya tana tunanin kardai abinda Hajiya ta shuka ne suka soma girba....

Da rarrafe Haule ta nufi d’akin mijinta tana fad’in “Amma Alhaji ka bani mamaki....”
Yana mai kwab’e babbar rigarsa ya katseta da fad’in “Da nayi mai....?”

Haule ta kuma sakin baki tana duban ikon Allah kana tace “Au bama kasan mai kayi ba Alhaji... Yanzu kai bazaka iya tantance makirci da akasinsa ba... K’iri k’iri kasan wancan shed’aniyar da d’iyarta makirici ne zalla ya kawosu ba komai ba.... Ko ka mance haka mukayi ma K’aninka da matarsa, ka mance irin wannan hak’urin muka basu.....”

Murmushin ko inkula Baba Alhaji yai mata kana yace “Banda abinki Haule shikenan kowa sai ya zama irinki... Sabida d’abi’arkice makirci shiyasa kike ganin kowa makiri ne.... Tinda sun gane kukurensu ni inaga ai shikenan Hafiz ya maida matarsa itama Zulfa’un sai ya had’esu duka biyu....”
Baikai aya ba Hajiya ta katsesa da fad’in “Wllhi k’arya kenan, wannan watsesstiyar d’ahna ya gama zaman aure da ita.... Wannan tsaf zata kar mutum... Wllhi badai Hafiz d’ina ba....”

Da wutsiyar ido ya dubeta kana yace “Akwai wani Hafiz d’in ne.....? Na gama magana Hafiz zai maida iyalansa don sakin baida wani alfanu cikinsa......” Daga haka band’aki ya shige ya bar Haule tana sallalami tana mamakin Yaushe Baba Alhaji ya soma mata musu... Lallai Magajiya bata zauna kurum ba da shiri ta shigo mata gida... Dik yanda za’ai ya zama dole ta tashi tsaye ta sami lafiya ta koma wajen bokanta kafin komai data mallaka su kufce mata.....

***
Chapter 90 · 0% Book details