← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 198

Sashe 93

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sameer ya d’an gyara zamansa sosai sakamakon tuno buk’atan Baba Alhaji da yayi kana ya soma fad’in “Mummy lafiya kenan zan iya cewa... Amma yanzu duk ba wannan ba Mummy... It’s Siyama.. Siyama itace damuwata a halin yanzu... Mummy I don’t understand her anymore... She’s something else, tinda ta tafi gida bata dawo ba and ko kiranta nayi wasu lokutan ta d’aga wasu lokutan bazata d’aga ba... Maganan da muke dake har yanzu batada labarin na sami biological parents d’ina talk less of introducing her to them... Mummy na fara doubting if Siyama really loves me...”
A hankali ta saki ajiyan zuciya kana tace “Sameer na sanka da hak’uri da barin abu ma zuciya, amma har idan zaka cutu bana goyon bayan kaci gaba da mata uzuri.... Amma mu bar zancen nan har mu dawo k’asar in sha Allah da kaina zanje na samu Faridar ayi mai yuwa idan Siyama zatai zaman aure fine, idan kuma bata shirya zaman auren bane sai mu sani... Ka k’ara hak’uri Sameer, in sha Allahu komai ya kusa daidaita kaji koh...”
Kaman tana dubansa ya jinjina kai kana yace “Mummy kar a mance ai mana addu’a jikin d’aki mai tsarki... Na gode k’warai Mummy na a gaida Daddy ace ina mishi add’uan samun lafiya... Allah yasa a dace ya kuma dawo daku lafiya...”

Ameen Son ta amsa masa dashi kafin ta k’arada “Ka gaishar mun da Mamy da Abbah and your siblings of course, Allah bai yi zamu had’u yanzu ba, amma da zaran mun sauk’a a Nigeria zamu had’u da yardar Allah tinda ta Kano zamu sauk’a... I love you so much Son, never forget that... Nida Daddynka muna sonka.... Allah ya maka albarka ya shige maka lamuranka...”
Cikeda jin dad’i had’ida peace of mind yace “Ameen Mummy nah....”
Sukai sallama har zai katse kiran ta kuma ambato sunansa “Sameer!”
Ya amsa a hankali yana mai jin zuciyarsa tai masa rauni ba tareda sanin dalili ba...
Mummy taci gaba da fad’in “Thank you for coming into our lives... Thnak you for making us happy... Thank you for completing our family... Thank you for giving me that chance to be a mother to you.... Thank you for being that son I always wanted to have.....”
Izuwa lokacin hawayene ke zubowa daga idanun Sameer ji yake tamkar ban kwana Mummy ke masa, a hankali yake furta “Mummy pls stop... Ki daina mun godiya, iyayena haifana sukayi but keda Daddy are my life... Most especially you Mummy, bazan tab’a iya biyanku d’awainiyar da kukayi dani ba Allah ne kawai zai biyaku.... I love you so much Mummy... So much....”. Ya k’arashe hawaye na gangaro masa...
A hankali itama ta goge hawayen da ya zubo mata kana tace “I love you too son.... Allah ya sadamu da Alkhairi...”
Sameer ya amsada Ameen Mummy nah... Jikinsa a matuk’ar sanyaye sukayi sallama... Kwanciya yayi rigingine bisa gado yana tuno rayuwarsa da Mummynsa tun tasowarsa kyakkyawan murmushi kwance saman fuskarsa....

***

Kanshi na bisa cup ya d’aura lips d’insa kenan da niyyan kurb’an ruwan ya sinkayo sallamanta cikin muryar nan nata mai dad’in sauraro, ruwan da bai iya kurb’a ba kenan ya d’go yana dubanta, ta masa kyau sosai har fiyeda lokacinda sukaje mata gaisuwar ta’aziyar rasuwar d’iyarta can gidan mahaifinta....

Shigowarta parlorn yayi daidai da bugun gate da ake, daga yanda suke suka soma sauraro muryan Hafiz....
Gaban Zulfa’u ya yanke ya fad’i... A hankali ta furta “Ya Hafiz.....”

SameenaAleeyou 📚

*INDA RAI*
_.................DA RABO_

*72*

Tinda ya hangi mota k’irar Mercedes a k’ofar gidan yaji hankalinsa sam bai kwanta aiko kaman jira yake Zulai tana bud’e masa ya soma tambayar ina Zulfa’u.... Zulai ta soma inda inda tama rasa mai zatace masa, tsawa ya darara mata tuni ta shiga ‘yan kame kame, saidi juyawan da zaiyi ya hangi takalman maza k’ofar parlorn, wani abu yaji ya sauk’a masa a k’irji tamkar an ije gingimemen dutse.... Ya watsawa Zulai harara kana ya shige fuuuu kaman zai tashi sama ya nufi parlorn... Kafin ya shige sai ganin Aunty Bara’atu yai gabansa tamkar wacce aka jefota “Karma ka soma wannan tunanin, shige mu tafi” ta nuna masa hanyar waje....
Banda huci da harararta Hafiz baya komai, Ita kuwa Zulfah a can cikin parlor gaba d’aya ta rasa sukuni, hankalinta yafi karkata wajen Aunty B da Ya Hafiz, dikda fira da Yusuf ke k’ok’arin janta dashi bawai fahimtarsa take ba, gaba d’aya ta kasa kunnuwarta ga sauraren tattaunawar Aunty Bara’atu da Ya Hafiz dikda cewa k’asa k’asa Aunty Bara’atu ke maganar...
A kufule Hafiz yace “Amma Aunty Zulfa’u fah da aurenta maiyasa zatake kula wasu mazan....”
Muguwar kallo ta aika masa kana tace “Kaine ka d’aura mata auren... Nace kai ka d’aura mata auren...?”
Hafiz yaci gaba da huci da kumbure kumbure....
Aunty B tai k’wafa kana tace “Shige nace kafin na sunkuceka aka na fiddaka.... Tsaya waima ban maka iyaka da gidan nan ba...?”
Wannan karon gajeriyar murmushi yai kana yace “Haba Aunty ashema Zulfah ta bar gidan nan kenan....”
Aunty B ta gyara tsayuwarta kana tace “Kaga Hafiz shige ka fice tin kafin raina ya b’aci...”
Ya d’ago rinannun idanunsa yana duban Aunty B, ji yake tamkar ya shak’e matar nan data zamto masa shamak’i da farin cikinsa da kuma cikar burinsa... Yana sauraro muryoyinsu yanda suke fira cikin nishad’i da kwanciyar hankali, zuciyarsa taci gaba da masa zogi sanin cewa Zulfarsa ce cikin parlorn nan... Miyau mai d’ankaran zafi ya had’iya kafin ya furta cikin zuciyarsa “This is far from over..” Cikin huci yana mai aiakawa Aunty B duban k’iyayya ya juya kaman zai kifa k’asa....
Aunty B ta murmusa kana tace a hankali “Dama d’aya ce Malam Hafiz kuma kayi wasa da ita, mu zuba nidakai....” Bata bar wajen ba har saida ta tabbata Hafiz ya bar gidan....

Wani lungu ya samu ya mak’ale yana jiran fitowarsu, Aiko mintoci kad’an ya hango munafukar sabuwar k’awar nan tata Atika kaman yanda yake kiranta Munafuka, sun fito sunyoma samarukan nasu rakiya zuwa wajen motar tasu, daga yanda yake yana hango d’aya mai maroon d’in boyal d’in ya kafe Zulfa’u da idanu, zuciyar Hafiz taci gaba da tafrfasa, gashi sosai Zulfah ta masa kyau, tsantsan soyayyarta na kuma azalzalansa, idan za’a mutu bazai daina bikon matarsa ta dawo garesa ba, kuma wllhi da ko wanene ya shirya yak’in neman auren Zulfa’u a karo na biyu....

A hankali ya fito daga mab’oyar tasa ya nufosu, Atika da ba wani saninsa tai ba amma hangosa da tai saida gabanta ya fad’i don ba komai ta hango saman fuskarsa ba face tashin hankali tsagwaranta....
Cikin sauri Atika ta soma fad’in “Ka kar ka damu Oga Akram ka samu k’awata an gama in sha Allahu...”
Yusuf yai karaf yace “Yauwa k’anwata nasanki da k’ok’ari aci gaba da k’ok’arin shawo mana kan gimbiyar....”
Baikai aya ba suka sinkayo muryar Hafiz yana fad’in “Baza’a shawo kan nata ba bak’in munafuki....”
Gaba d’aya suka juyo suna duban Hafiz wanda keta faman hure huren hanci yana cika....
Gaban Zulfa’u ya yanke ya fad’i yayinda Yusuf yace “Kaikuma waye....?”
Hafiz yai wata k’asaitacciyar murmushi kana ya dubi Zulfah da gaba d’aya tashin hankaline ya nuna a fuskarta kana yace “Au dama baki fad’a masu kinada miji ba, basusan cewa ke d’in matar aure bace....?”
Yusuf ya d’an murmusa don ya gane Hafiz tsaf tsohon mijin Zulfah ne kuma sun had’u kwanaki a gidansu Zulfa’un sanda sukaje mata gaisuwar rasuwa....
Takowa Yusuf yayi kusansa kad’an yana k’are masa duba daga sama zuwa k’asa, dab fuskar Hafiz ya matso da tasa fuskar kafin ya rage murya yace “Tsohon miji zakace, a halin yanzu Zulfa’u ta mai rabo ce....” Ai baikai aya ba Hafiz dake tururi yakai masa shak’a a wuya yana mai furta “K’arya kake wllhi tawace har abada...!”
Zulfah da Atika suka zaro idanu waje cikeda tashin hankali ta k’arasa tana fad’in “Ya Hafiz dan Allah ka sake shi, kar kaji masa ciwo....”
“Rufemun baki munafukar banza munafukar wofi wacce batasan komai ba sai cin amana, kin had’e kai da wannan Kawaliyar k’anwar uwar taki kuna cin amanata....”
Tinda Zulfa’u take Hafiz bai tab’a k’ona mata rai irinta yau ba, Aunty Bara’atu yake kira Kawaliya.... Batasan sanda hawaye suka soma gangaro mata ba, ta kasa katab’us yayinda Atika tai saurin rik’ota....
Akram ya d’ankai dubansa gareta yaga hawaye na zubo mata, duban Atika yai kana yace “Ki shiga da ita ciki...” Babu musu Atika ta jinjina masa kai kana ta janyo Zulfah tamkar rak’umi da akala suka shige cikin gida....
Maidoda dubansa ga Hafiz Akram yai kafin ya tako har gabansa yasa hannu ya cire hannayensa daga wuyar abokinsa kana yaceda Yusuf “Ba girmanka bane fad’a da mahaukaci, lets go....”
Hafiz ya saki Yusuf yana k’ok’arin rik’o Akram saidai hannu guda Akram yai amfani dashi wajen damk’e hannun Hafiz d’in da ko motsata ya kasa.... Murya a dake yake furta “Komai nada iyaka... Yanada kyau kasan madakatarka a rayuwa.....!” Daga haka jifa da hannun Hafiz d’in yai suka shige mota... Akabar Hafiz da sosa hannunsa yanda Akram ya murd’e masa... Yana ganin yanda suka kwashi mota suke shige suka bar masa k’ura....
Suna tafe Akram na sak’e sak’e cikin zuciyarsa, hukuncinda ya yanke yayi daidai, yafi kyau shid’in ya nemi auren Zulfa’u don baijin zai bari His Excellency yayi takara da wannan lunatic d’in....
Chapter 93 · 0% Book details