← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 198

Sashe 97

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Suna tafe tana d’an jan k’afar tata da bai ida warkewa ba tana sak’e sak’e da zullumin waye yazo d’aukanta har islamiya.... Bata ida tunanin ba ta hangosa gefen malamansu kansa kife bisa wayar salulansa, yana sanye cikin k’anan kaya, navy blue check wato riga mai zanen gidan dara long sleeve, haka jeans d’in jikinsa ma blue d’in ne, da matuk’ar wuya kaga Sameer da t-shirt idan dai ba check bane, akasarin kayan nasa check ne masu dogayen hannu da masu gajerun hannu, ta yanda da yawa wasu a asibitin nasu ma suke banbancesa kenan, wasu har lak’abi suke masa da Dr-check, duk ranan juma’a kuwa shigar dogayen kaya yake harda hula, saiko wani zubin yakan saka suit musamman idan zai halarci wani taron....
Wani irin muguwar fad’uwar gaba Raihanah taji, ko mai yasa Ya Ma’aruf zaizo d’aukarta...? Sai kuma ta soma tunanin Salma nurse mai mata dressing tasha sanar da ita irin k’aida da kaffa-kaffa da Dr Sameer ke dashi dashike akasarin hiran da Salma zata mata akan Sameer d’in ne, Salma batada zance saina Dr Sameer dukda cewa shid’in baisan tanayi ba...
Kanta a k’asa ta k’araso tana gaida sauran malaman, suka amsa mata da sakin fuska had’ida mata sannu da jiki, ta d’an maidoda dubantaga Sameer wanda har lokacin idanunsa nakan waya.... A hankali ta furta “Ya Sameer ina yini....”
Ya amsa mata a tak’aice kana yace “Ki k’arasa mota ina zuwa...”
Jinjina masa kai kurum tai kana tace “Toh..” A tak’aice....
Saida ta d’anyi nisa da tafiya kafin ya ida abinda yake cikin wayar kana ya k’araso yaiwa malaman sallama...
Tana nan tsaye jikin mota taji k’aran security lock alamun an bud’e motar, Aiko shid’inne ya k’araso fuskarsa sam babu walwala, bata tab’a ganinshi cikin yanayi irinta yau ba...
K’asa k’asa take dubansa, tana jin sanda yace “Shige muje....”
Babu musu ta bud’e marfin motar ta shige a d’arare,sai faman cije leb’e take a hankali bata son ya fahimci halinda take ciki don gaba d’aya wandon islamiyan nata data saka ya sosa ciwon ya fama kad’an....
Yana kunna motar sautin karatun Alk’ur’ani mai girma yaci gaba da tashi cikin muryar Sheik Sa’oud Shureim, da alama karatun yake saurare dama, ga wani k’amshi na musamman dake tashi cikin motar tasa, haka kurum taji wani irin nutsuwa ya sauk’ar mata cikin zuciyarta, da gefen idanu take satan kallonsa har wannan lokacin babu walwala saman kyakkyawan fuskarsa... Ta janye idanunta a hankali zuciyarta nabin k’ira’ar cikin suratu Yaseen yayinda ta maida dubanta gaba d’aya zuwaga window.... K’arar ringing d’in wayar salulansa k’irar Samsung shi ya sanya Sameer rage sautin karatun Alk’ur’anin.... Ya d’aga wayar wanda daji kasan daga can asibitin nasu ake nemansa.....
Cikin muryarsa mai cikeda charisma da dad’in saurare yake fad’in “Ni kuma gashi bana kusa, ina Awwab yake... Contact him mana....”
Magana akai daga d’aya b’angaren sai jinjina kai da yai yana furta “Ok ok gani nan zuwa, prepare the patients....” Daga haka bai kuma cewa komai ba sai canza hanya da yai.....
Raihanah ta dubesa da tsananin mamaki ganin ya canza hanyar gida, kaman yasan duban nasa take nan ta sinkayi muryarsa yana fad’in “Meyasa kika fita ba tareda sanina ba...?” Batakaiga basa amsa ba ya kuma jefo mata wata tambayar “Salma bata sanar dake k’a’idojina bane wanda duk patients d’ina dole subi wad’annan k’aidojin....?”
Sai sannan ya d’an cire idanunsa daga kwalta ya kaikaito kad’an yana dubanta, gani yai idanunta a k’asa tana wasa da ‘yan yatsuna hannunta, a hankali ta furta “Kai hak’uri Yaya bazan sake ba....”
Maida idanunsaga tuk’in dayeke yai ba tareda ya kuma cewa komai ba saima d’an k’ara volume d’in karatun da yai sakamakon ragewa da yayi sanda zai amsa waya...
Raihanah ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali had’ida lumshe idanu, ita duk damuwarta ma hanyar asibiti taga sun nufa ne, kenan ba yanzu zasu koma gida ba... Haka nan dai idanunta na lumshe taketa bin sautin karatun cikin zuciyarta da sam batasan bakinta na furtawa ba....
Sameer yakai dubansa gareta yaga yanda bakin nata ke furta karatun a hankali idanunta masu yalwan girma a lumshe, bai tab’a samun daman k’arema fuskarta kallo ba sai yau, Raihaan kaman yanda shi yake kiranta, bata a layin mata masu haske sannan kai tsaye bazaka kirata b’ak’a ba, hancinta ba mai tsawo bane hasalima ya d’an baje kad’an daga k’asa, full lips gareta dikda cewa bakin nata madaidaici ne kana iya hango d’an tudu kad’an da bakin nata kedashi haka nan tanada yalwan idanu da dogayen gashin ido wanda ya k’ara ma idanun nata kyau sannan tanada lostawar kumatu wanda ko magana take zakaga suna lotsawa karatun da take bi yanzu ma sai faman lotsawa suke, daga nesa ma bazakai mata kallon kyakkyawa ba harsai ka matso kusanta, haka nan suke ita da Nabilah sam basu d’auko haske irin na sauran family members d’in nasu ba, ita Raihanah kam ma bata ragewa mahaifiyarta komai ba sam bata kama da dangin Baba Alhaji wannan yasa kamanninta ya fita daban da sauran ‘yan gidan..... Shiyasa ma Haule ke mata lak’abi da dangi mayu...
Tana jin alamun tsayawa ta bud’e idanunta, nan ta gansu a farfajiyan asibitin.....
Sameer ya bud’e central lock kana ya mik’a hannunsa bayan motar ya d’auki wasu files da farar labcot d’insa...
“Muje...” Kalmar da ya fad’i mata kenan....
Babu musu ta kama marfin motar ta fice tabi bayansa cikin sauri ga yanayin tafiyar tasa sassarfa ne ita gashi gaba d’aya tafiyar nata d’ingisawa ne...
Yana tafe ma’aikatan asibitin na jefo masa gaisuwa duk yanda ya shige...
Saida zai d’auki wata hanya ya tunada Raihanah... Juyowa yai yana dubanta yaga tana jan k’afarta da k’yar da k’yar.... Tsayuwa yai yana observing d’inta kana ya girgiza kansa a hankali, yasan hakan ka iya faruwa... Saida ta k’araso kusansa kanta a k’asa, duk a tsarge take ganin yanda ya k’urawa k’afarta idanu, hannu yasa ya amshi jakar islamiyar nata yana mai furta “Give me that....” Ita dai sakar mishi kawai tai tana mai tambayar kanta ko maiyasa ma ta fito da jakar oho dama barinta tai a mota...
Wani office taga ya bud’e masu wanda ga dukkan alamu mallakarsa ne....
Ya shige ciki tabi bayansa, Office ne maiji da lafiya gashi ya had’uda gayu don mai office d’in ya k’ure wajen tsafta da gayu... Tai tsaye sororo yayinda Sameer ke jikin table yana duba laptop d’in dake bisa table d’in... Saida har ya gama abinda zaiyi ya juyo ya ganta nan tsaye sai rarraba idanu take kaman taci kud’in aika....
Sofa dake gefe ya mata nuni dashi kana yace “Ki zauna acan...”
Babu musu tai yanda yace....
Tana gani ya tattari wasu takardun da labcot d’insa ya nufi k’ofa, har yakai k’ofa ya juyo ya d’an dubeta kana yace “Idan zakiyi sallah ga bathroom and akwai abin sallah a gefen wancan drawer d’in... I won’t take long kinji... Ki jirani a nan...”
Cikin sauri ta shiga mana masa kai sai faman muzurai take...
Har ya kuma juyawa zai fice ya d’anyi birki ya kuma juyowa, kai tsaye jikin k’aramar fridge dake a cikin Office d’in ya nufa ya bud’e ya ciro goran fresh yogurt ya ije gefenta, daga haka bai kuma cewa komai ba ya fice cikin sauri had’ida jan k’ofar office d’in....
A daidai k’ofa ya had’uda Awwab yana fad’in “Dama zuwa nai na fito da kai don ance min ka iso ka nufi Office....”
Suna tafe cikin sassarfa Sameer yake fad’in “Wai dama kana nan shine sai an nemoni...?”
Suna nufa wata k’ofar Awwab ke fad’in “Ai tinda kaga an dage a nemoka is serious kuma ba mutum d’aya ba kusan three patients ke jiranmu, na shiga na gansu gasu yara abun babu dad’in gani, Allah ka tsaremu daga sharrin wuta duniya da lahira..”
Ameen Sameer ya amsa dashi daidai sanda suke isowa d’akin theatre d’in....

Raihanah ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali kana ta sami daman k’are ma ofishin kallo, takai dubantaga lallausar carpet d’in da k’afafunta ke bisa tana mai ayyanawa cikin ranta _Wannan ma ai ya isheni sallah basai na d’auko abin sallah ba_ don already lokacin magrib ya kusa....
K’ofar da ya nuna mata matsayin bathroom nan cikin office d’in ta nufa, saidai hoton da ta hanga saman table d’insa cikin k’aramar frame ya mugun jan hankalinta, ta k’arasa jikin table d’in tana mai k’arema hoton kallo, murmushi saman fuskarta ta d’auki hoton tana duba, ko ba’ace ba wannan ce matarsa, sunyi kyau har sun gaji sannan sun bala’in dacewa da juna, duk yanda gayu yakai wannan mata tasa takai sannan ko ba’ace ba kasan suna matuk’ar k’aunar junansu.... Sun mata kyau har sun gaji... Ta jima tana duban hoton kafin ta maida ta aje saman table d’in.... Can gefe kuma jikin gini an k’awata wajen ne da tarin Awards and Medals na shaidan d’inbin nasarori da ya samu, nan ta k’arasa tana bi tana karantawa d’aya bayan d’aya, duk wanda ta karanta sai ta saki murmushi hardai ta jiyo ana kiran sallah daga masallacin cikin asibitin, nan ta nufi bathroom d’in tayo alwala kaman yanda ya nuna mata....
Har ta ida sallan magrib babu Sameer babu dalilinsa....
Haka nan tai zaune ta rabka uban tagumi tana zaman jiran tsammani....
Chapter 97 · 0% Book details