← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 198

Sashe 87

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kauda kanta gefe ta d’anyi kana tace “Kayi hak’uri Ya Hafiz ina maka fatan alkhairi a rayuwarka, Allah kuma ya datar dakai da mace ta k’warai amma badai ni Zulfa’u ba....”

Zuciyar Hafiz ta soma sosuwa, har shine Zulfah ke turning d’insa down, matar da a fari dangin sadaka aka basa, amma Wai yau har shi ke kwantar da kai yana rok’on ta koma gidansa tana sha masa k’amshi bayan yasan deep down tana mutuwar sonsa itama....
Mik’ewa yayi had’ida zira hannaye cikin aljihun wando ya d’an soma takowa gabanta kad’an....
Ta d’ago idanu tana mamakin yanda yai mata tsaye aka ya wani lank’washe wuya harda karkace hula ga hannaye cikin aljihu....
Bud’e baki yai kana yace “Tell it to my face that you don’t love me, you don’t feel anything for me.....” Yayi maganar cikeda gadara...
Itakam ma dariya abin yaso bata yanda har yanzu Ya Hafiz bai daina jin kansa ba kana ta ijiye takardan hannunta tace “Dama can akwai wata soyayya ce tsakaninmu....? Ko ka mance dagani har kai dole aka mana, kuma gudan jinin dake tsakaninmu Allah ya amshi abinsa.... Don haka kamar yanda nace maka kaje Allah ya had’aka da madadina saliha, wacce zata so ka tsakani da Allah....”

Fuzar da iska yai kana yace “Baki amsa min tambayata ba....Ki fito fili ki fad’a min baki sona idan har da gaske babu d’and’anin soyayyata cikin zuciyarki.....”

Shiru ya d’an biyo baya, bata furta komai ba sai k’urama waje guda idanu da tai.....

D’ago kai tai da niyyar magana K’aran horn d’in motar Aunty B ya katseta... Gabanta yai mugun fad’uwa, idanunta sukai rau rau tana mai dubansa, lokaci guda ya mik’e tana fad’in “Ka gani koh... Dan Allah ka fice kafin ta shigo ta taddaka....”

Ko gizau baiyi ba banda kallon k’urilla da yake mata.....
“Ya Hafiz magana nake maka... Dan Allah ka fice before she sees you here....”

Bai kuma cewa komai ba sai juyawa da yai ya soma tafiya, lokaci guda ya juyo yana dubanta itama d’in shi take duba
Hafiz ya furta “I won’t give up on you....” Daga haka sa kai yai ya fice kaman mai shirin tashi sama...

Zulfah ta lumshe idanunta a hankali tana ambaton Allah....

Shiko Hafiz a k’ofar da zai sadaka da cikin gidan suka had’uda Aunty B....
Ta bisa da kallon mai ya kawosa gidanta....
Gaisar da ita ya soma ta dakatar dashi da fad’in “Lafiya mai ya kawoka gidana.......?”
Hafiz ya d’ago idanu yana dubanta... Ta kuma jinjina kai kana tace “Ina saurarenka, mai kazo min gida...?”

“Matata nazo gani....” Ya bata amsa kai tsaye...
‘Yar bazawarar murmushi Aunty Bara’atu tai kana tace “Matarka...? Matarka fah kace....? Ikon Allah.... Ita Sawwamar ce tazo nan gidan...?”

Hafiz ya had’iye wani abu mai zafi kana yace “Matata Zulfa’u....”
Nan ma murmusawa ta kumayi kana tace “Ai bari kaji na fad’a maka Hafiz, Zulfa’u tai maka nisa, nisan da bazaka tab’a samu ba.... A iya sanina Zulfa’u ba matarka bace a halin yanzu domin kaw babu aurenka akanta... Saidai ka shiga jerin masu neman aurenta, amma abin takaicin shine bazaka sameta ba domin kaw wutsiyar rak’umi ya riga yayi nesa da k’asa... Saidai a k’ara gaba amma ba nan ba.... Kaje can Allah had’aka da rabonka.... And to make it clear to you, banso na dake ganin k’afafunka cikin gidana... Ina kuma fatan hakan ya zamto kashedi na k’arshe....”

Tana ida fad’in haka ta danna lock wa motarta ta nufi cikin gida....
Hafiz ya bita da kallo tamkar wanda ruwa ya shanye, da k’yar ya iya d’aga k’afafunsa ya fice daga gidan....

Wani mugun kallo Aunty B ta watsawa Zulfah dake mata sannu da zuwa, kana ta shige d’aki ba tareda ta amsata ba... Zulfah ta dafe kanta a hankali tana ambaton Allah, ko shakka babu tasan Aunty ta had’uda Hafiz ne a hanyarsa na ficewa daga gidan....

***

Bayan sun fito daga taron jama’an ne suka d’an samu keb’ewa, abinka da mutumin da jama’a ke matuk’ar so, da k’yar Engr ya samu ya silale daga dandatson jama’an dake fatan samun kujerar muk’ami ta gwamna da yake nema....
Ya cire hularsa ya shiga fifita da ita, kana iya hango kwantacciyar sumarsa da suka jik’e da zufa, dukda AC dake hurawa dashike lokacine na tsananin zafin rana.....Akram ya k’araso rik’eda wata ‘yar takarda hannunsa kana ya mik’ama ubangidan nasa cikeda risinawa...
Ya amsa yana mai murmusawa lokaci guda yana mai duba takardan...
Baiso ya fahimci halinda yake ciki don haka k’ok’arin saita kansa yayi kana ya soma koro masa bayani....
“Rankashi dad’e duk wani bayanai gameda ita da zan iya samu suna k’unshe cikin takardan nan.... Sannan k’asa kad’an lambar wayartace.....”

Engr ya jinjina kai a hankali, murmushin bata gushe saman fuskarsa ba...
Lokaci guda ya soma furta “Na gode k’warai Akram....”
Akram ya girgiza kai yana mai furta “Ka wuce haka a wajena your Excellency, bacin duk abubuwan daka min a rayuwa, ina fata watarana nima nayi abinda zan saka maka....”

K’uri Engr ya masa yana mai son karantar yanayinsa.... D’an aje takardan yai saman table dake gabansa kana yace “Akram... Akwai matsala ne... Akwai abindake damunka ne wanda baka sanar dani ba...?”

Akram ya d’an k’ak’aro murmushi had’ida girgiza kai yace “Babu... Babu komai your Excellency.... Zan iya tafiya... Zanje na duba idan jama’anmu kowa ya sami motar shiga....” Ya k’arashe maganar yana mai mik’ewa ya nufi k’ofa.....

Engr ya kirawosa ya dawo da baya.... Kansa a k’asa,don ko duban idanunsa baisonyi bacin abinda Muhibbah ta bijiro masa dashi....

“Zauna....!” Engr yace yana mai dubansa....
Babu musu Akram ya zauna....
Gyara zama Engr yai kana yace “Banso kana d’aukan duk wasu abubuwan da nake maka a matsayin watarana zaka biyani, cos to me you’re my younger brother.... You’re not only an employee Akram... You’re family.....”
Akram yai saurin d’agowa yana duban Ubangidan nasa... Engr ya jinjina masa kai a hankali kana yace “So babu ramuwa tsakaninmu kaji koh....”
Akram ya jinjina kai a hankali...

Engr yaci gaba da fad’in “Inaso ka wakilceni a wajenta, ma’ana inaso ka soma gabatar dani kafin na gabatar da kaina.... Amma banso ka sanar da ita ko ni wanene har sai nan da wani lokaci... For now zan dinga kiranta a waya amma kai zaka dinga zuwa a madadina.....”
Banda bugu babu abinda k’irjin Akram keyi.... Mai yasa yana k’ok’arin manceta da yunk’urin cireta cikin zuciyarsa Engr zai masa haka... This will be hard for him... Gashi babu hali yace masa a’a... Shin kodai ya sanar dashi gaskiya ne cewa sunyi tarayya wajen son mace guda ne....?

SameenaAleeyou📚

*INDA RAI*
_................DA RABO_

*69*

Akram na ficewa Engr yaci gaba da juya takardan hannunsa, har lokacin murmushi ne kwance saman fuskarsa... Idanunsa ya sauk’a kan lambar wayar da aka kawo masa a matsayin nata, ya d’auki lokaci mai d’an tsawo yana duban lambar wayar tamkar wani mai niyyar haddace lambar.... Ya d’an sauk’e ajiyan zuciya kad’an had’ida fuzar da iska... Wayarsa dake aje gefensa yakai dubansa ga fuskar wayar, nan ma saida ya jima yana duban wayar tasa kafin yasa hannu ya d’auki wayar, ya shafi screen d’in wayar ya kawo haske... A hankali ya soma loda lambar wayar cikin tsanaki a wayar tasa.... Koda ya gama jera lambobin saida ya tsaya ya d’auki lokaci yana tunanin abinda yake shirin yi... This is not like him, bai tab’a zata rana irinta yau zata riskesa a rayuwarsa ba bayan duk zaman hak’uri da yayi da Muhibbah ko ince yake kanyi.... Anya kuwa ba damuwa yake shirin k’aro ma kansa ba kan wanda yake ciki da matarsa Muhibba...? What if itama ta kasance kaman Muhibbah ko ma worse than Muhibbah....? Yayi saurin shafar sumarsa a hankali kana yace toh amma according to Akram yarinyar ‘yar gidan tarbiyace kuma rashin dacen miji tai a fari wanda yayi sanadiyar mutuwar aurenta....
Ya d’an mik’e tsaye a hankali yana zagaye tangamemen parlorn mai d’aukeda kujeru kusan set uku.... Idanunsa suka sauk’a ga tangamemen k’ofan glass da aka k’awata parlorn da ita, yana hango mutane yanda suke faman kai komo wanda da dama fitowarsa suke jira.....
Ya kuma tsurawa lambar idanu, samun yatsarsa yai yana mai dialing lambar da ya gama lodawa a wayarsa da sunan lambar yarinyar kenan....

Zulfah na faman baiwa Aunty B hak’uri gameda riskan Hafiz da tai a gidan wayarta ta d’auki ruri.... Ko takan wayar batabi ba ita dai damuwarta Auntynta ta bar fushi da ita...
Aunty B ta d’an aika mata harara kana tace “Ki amsa kiran nan da ya ishemu ya cika mana kunnuwa...”

Zulfah ta d’an turo baki gaba tace “Nidai bani amsawa Aunty sai kince kinyi hak’uri....”
Dariya taso bata kana tace “Naji nayi... Maza tashi ki amsa kiranki....”

Zulfa’u ta rungumeta da sauri cikeda farin ciki tana mai furta “Ko kefa Aunty na...” Har wayar ta tsinke kafin aka sake kira....
Aunty B tace “Ni d’agani kada ki k’arasani... Gwara dai na sanar dake don wllhi idan giyan soyayya ya d’ibeki Hafiz ya hure maki kunne kika kuma aurensa saidai ki nemi mai tsaya maki badai ni Bara’atu ba kuma ba ‘yar uwata ba.... Ki amsa kiran nan haka...”

Zulfah na murmushi take fad’in “Ba dolenki ki tsaya min ba Auntyna... Kinga wata lamba ce bansan mai ita ba, banson d’agawa kardai Ya Hafiz ne....”

Aunty B tace “Ki dai d’aga kiji koma waye, it might be something urgent....”

Zulfa’u ta d’aga wayar da sallama tana mai k’arawa a kunnenta....

Wani abu yaji yana tsargar masa cikin zuciyarsa sanda muryar nata ya daki dodon kunnensa, tabbas itace Muryar da ya saba saurare ne a radio.... Daga can b’agaren kuwa Zulfa’u taci gaba da fad’in “Hello... Assalamu’alaikum... Wake magana...? Hello....”

Shiru ba’a amsata ba.... Muryar matarsa Muhibba da ya sauraro tana shigowa ya katse masa hanzarinsa... D’if ya katse kiran ba tareda yace komai ba.... Muhibbah ta k’araso yayinda Suwaiba maid d’inta ke biyeda ita rik’eda basket d’in abinci nik’i nik’i.... Batai wata wata ba ta k’arasa ta rungume mijin nata tana fad’in “Excellency na nayi kewarka, mutanen nan basa barinka ka huta... Jibi duk yanda ka rame kai bak’i....”Ta dubi Suwaiba tace ta ije abincin a wajen ta fice, Suwaiba tai yanda tace....
Chapter 87 · 0% Book details