← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 168 OF 198

Sashe 168

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yarinyar ta soma isan Siyama... Kasa korinta tai sai amsar spoon d’in da tai ta soma bata a bakin kaman yanda ta buk’ata... Su dai su Nabilah da Humaira daga yanda suke zaune suna kallon drama Ijlaal da Siyama... Sai bata a baki take tamkar ba Siyama ba.... Idan tai wani shiriritar har darawa kad’an Siyama keyi... Bata San dalili ba amma haka kurum taji yarinyar ta tsaya mata a rai....
Har saida tace mata ta k’oshi kafin ta daina bata... Yarinyar ta mik’e ta d’auki picture d’insu tana k’ok’arin d’agawa alamun tanaso Ta maidasu wajen zamansu....
Siyama ta dubeta kana tace “Wait, what are you doing... Put that down zaiji maki ciwo....”
Yarinyar ta turo baki tace “So nake na maida...”
Siyama ta k’araso ta amshi picture d’in kana ta lank’aya... Ta dubi yarinyar tace “Happy....?”
Jinjina mata kai tai tana murmushi kana tace “Inaso ai mana dake da Ya Khalid da Humy da Aunty Beels... Wait, kema kinada miji ne... Ina yake...? Do you have children...?”
Wannan karon wani irin bugu k’irjin Siyama yai... Tai k’urima yarinyar kana ta waigo tana duban dining area yanda sukai idanu hud’u da Nabilah.... Siyama ta rasa mai zatace da yarinyar dan ba kowa ya fad’o ranta ba face Sameer...
A hankali ta mik’e kana ta Shafa kan Ijlaal tace “Good night beautiful...!” Daga haka bata kuma bi takan kowa ba ta haye upstairs yanda ta tadda Ammi ta tasa Aunty Daula gaba da fad’in ta nuna mata d’akin mijinta dan nan ne masauk’inta....
Siyama tace “Ammi please that’s enough... Zamu iya kwana nidake da Yesmin a guest room ba sai kinje d’akin Daddy ba please....”

Wani irin wawan kallo Ammi ta watsa mata kana tace “Toh sannu uwata... Nace bazan kwana a guest room d’inba... D’akin da suke cin amanata ciki, nan zan kwana....”
Ita kanta Siyama saida kalaman Ammi suka d’an mata nauyi.. Ta girgiza kai kad’an tace “Haba Ammi that’s enough please...!”
Ammi ta kuma hayayyak’ota yayinda Aunty Daula ta girgiza ma Siyama kai alamun ta k’yaleta kawai... Kaman yanda Ammin ta buk’ata haka Aunty Daula ta bud’e mata d’akin Daddy harda kawo mata sabon bedsheet... Ammi tace waye take jira ya shimfid’a... Babu musu Aunty Daula ta shimfid’a mata... Ta haye kan gadon tana mai rakata da bak’ar harara....

A b’angaren Siyama tana isa d’aki wayarta ta d’auki ruri Sultan ne mai kiranta....

Dik yanda taso danne zuciyarta abin yaci tura, cikin ‘yar daburcewa tace “Sultan.... You are kidding me right...? Kaga nifa yanzu har tsoro kiranka Ke bani....”

Sultan yai k’asaitaccen murmushi Daga d’aya b’angaren kana yace “Idan kinaso Ki tabbatar ma idanunki, Ki bar dik abinda kike Ki taho Kaduna gobe... Ni kuma zan maki jagorancin zuwa ganin abinda baki tab’a zato ba balle tsammani.... The surprise of your life....!”

Siyama ta mik’e zunbur daga zaune kana tace “Sultan Wai dan Allah meke faruwa ne...? Ka sanar dani please... I can’t wait till tomorrow, I don’t have that kind of patience....!”

Murmusawa Sultan ya kumayi kana yace “Na fad’a miki Siyama, is a surprise... Idan har kinaso Ki sani ki baro dik abinda kike kizo Ki gani da idanunki dan banso a baki labari zaifi kyau idan kika gani with your own eyes... Kin daisan bana k’arya....!” Ya k’arashe yana shu’umin murmushi lokaci guda ya katse kiran....
Hankalin Siyama idan yayi dubu ya tashi, gaba d’aya ta kasa zaune ta kasa tsaye... Toh menene Sultan zai nuna mata.... Menene haka da tsanani....? Taci gaba da bubbuga wayarta saman tafin hannunta tana mai zagaye d’akin.... A haka Ijlaal ta turo k’ofar ta ganta.... Siyama tai tsaye tana duban Yarinyar....
Ijlaal tace “Aunty, you couldn’t sleep...? Do you want me to hug you...?”

Siyama da batasan dalilin zuban hawayenta ba cikin sauri ta bud’ewa Ijlaal hannayenta tana fad’in “Please hug me....!”
Cikeda tausayawa Ijlaal ta tafi ta rungume Siyama dake hawaye... Sosai Siyama ta k’ank’ame yarinyar tana jin wane irin rauni cikin zuciyarta....
A haka suka kwanta cikin jikin juna har bacci yai gaba dasu, Yesmin data shigo ta gansu haka k’ebebe ta tsaya tana kallon ikon Allah... Cikin zuciyarta take ayyana cewa anya wannan yarinyar ba mayya bace, jibi dik k’in yara irin na Siyama amma lokaci guda ta manne ma Siyama, har tana k’ok’arin jefa mata rauni cikin zuciyarta.... Lallai dole tasan abinyi kafin soyayyar yarinyar yai tasiri zuciyar Siyama....

***

Nabila dake zaune ta kasa bacci dan har yanzu babu Khalid babu dalilinsa... Sai juyi take gefen Humaira dake baccinta hankali kwance... Jin kaman motsi daga downstairs ya sanyata mik’ewa zunbur ta zira hijab kana ta nufo k’asa....

A Daidai k’ofan d’akinsa ta hangesa zai shige... Yaja ya tsaya had’ida sakar mata murmushi wanda ko ba’a ba tasan na k’arfin hali ne... Gaba d’aya itama sai taji zuciyarta ya kuma mata rauni, tsananin tausayinsu gaba d’aya na ratsa ta..... Ga k’walla da suka ciko idanunta... Ganin haka ya sanyashi saurin k’arasowa gareta had’ida rungumeta... Kaman jira take nan ta saki mashi kuka a hankali.... Khalid ya rik’eta sosai yana fad’in “Is okay teddy bear I’m here now....!” Gaba d’aya shima da k’yar yake maganan, dan saida hawayen da yake k’ok’arin maidawa ya d’igo masa....
Cikin murya mai tsananin rauni Nabilah ke fad’in “Where have you been...?And meyasa kaki d’aga any of my calls... You’ve got me worried you know....!” Ta k’arashe hawaye na kuma gangaro mata....
A hankali yai mata masauk’i a gefen jikinsa yana mai furta kana suka nufi cikin d’akin nasa yana mai furta “I’m sorry teddy bazan sake ba kinji love...!”

Yesmin da Kubura da suke lek’en wad’annan masoya kusan gware sukai garin lek’e ba tareda sun ankare ba, dan Kubura bata tsammaci ganin Yesmin ba haka Yesmin d’inma bata tsammaci ganin Kubura ba....

Yesmin ta saki k’ara tana kame goshinta yanda sukai gware da Kubura....
Cikin sauri Kubura tajada baya had’ida danna switch d’in wuta tana mai furta Wayyo nayi gamo... Dan Yesmin ta shafe fuskarta da mayukan gyaran fata na bacci.... Ganin Yesmin ce ya sanyata jan uban tsuka itama Yesmin d’in tsukan taja Kubura na dariya tana fad’in “Ya kikaga Kajal da Sharupkan sun birgeki koh... Ai kawai ki d’au ta Annabawa oga Khalid sai gani daga nesa k’walelenki.....” Ta k’arashe tana gwalowa Yesmin had’ida tintsirewa da dariya....
Yesmin dake faman huci a d’ari tai upstairs ta shiga bugun k’ofar Ammi tana fad’in ta fito ta gani....
Babu shiri Ammi ta fito tana mustuke idanu... Su AuntB da Aunty Daula ma fitowa sukai jin bugun k’ofan da Yesmin keyiwa Ammi... Yesmin bata jira komai ba ta shiga janyo hannun Ammi tana fad’in “Ammi gayacan mayyan nan a d’akin Khalid zata lashesa....”

Ammi ta dafe k’irji tana fad’in “Na shiga uku ni Farida kauce bani hanya....!” Ta ture Yesmin ta nufi downstairs tamkar zata kifa....

Aunty B da Aunty Daula suka dubi juna cikeda al’ajabin hali irin na Ammi, dik sahun da suke ajeta ta zarta tinaninsu....

Dafe da fuskarta yake furta “A lokacin da aka d’aura aurenmu na zaci shikenan yak’in ya k’are mana... Ashe akwai saura a gaba... Nabilah I can’t wait for all of this to end and to finally be with you... Mu biyu nidake a wata duniya mai dad’i da babu hatsaniya cikinta.... Na k’agu na nuna miki irin k’aunarda nake miki teddy bear...!” Ya k’arashe yana mai kuma tallafo fuskarta da duka hannayensa biyu, su duka biyun suna duban cikin idanun juna cikeda shauk’i.... Kaman daga sama suka soma jiyo ana bugun k’ofar da k’arfin gaske... Mamaki ya cika fuskokinsu... A zabure Khalid ya mik’e yana mamakin k’arfin hali irinta mai bugun k’ofar nan....
A zuciya yaja k’ofar saidai kafin yakai ga magana sukai idanu hud’u da mahaifiyarsa sai faman jijjiga take... Lokaci guda take k’are masa kallo... Yana sanye cikin inner black v neck saiko three quarter mai ruwan shud’i... Ammi tace “Ina take....?!”
Jin muryar Ammi ya sanya k’irjin Nabilah saurin bugawa... Tai k’ok’arin janyo hijabinta ta zira, sai faman muzurai take....

D’an sosa kunnensa kad’an yai kana yace “Wace kenan Ammi...?”

“Ka fini sani... Ina take nace...?!”

“Ammi wayace miki tana nan...?!”
“Zaka matsa ne ko kuwa...?!” Ta kuma fad’I cikin daka tsawa..
Girgiza kai kurum yake murya a shak’e yak’e furta “You’ve went too far...!!”

Turesa gefe tai tana fad’in “Kaucemin kafin na had’a dakai...” Tuni ta fad’a cikin d’akin tana fad’in “Ina kike munafuka...?!”
Khalid yai saurin take bayanta yana fad’in “Ammi you can’t do this...!”
Harara ta watsa masa tana kuma watsa wa Nabilah dake tsaye kanta a k’asa muguwar kallo....
“Zo ki fita munafuka...Fita nace...!”
Ta k’arashe tana k’ok’arin janyota... Khalid da mamaki ya kasa sakinsa saurin rik’o hannun Nabilah yai, cikin tsnanin k’unan rai yake furta “Ammi We’re not doing anything wrong here... After all, She’s my wife, and you can’t just barge in......”
Baikai aya ba Ta katsesa da fad’in “Kamin shiru nace... Minafiki...!” Ta kuma duban Nabilah dake tsaye hawaye na d’igo mata kana tace “Kin kasa hak’uri har ku tare ne shine bari ki biyosa... Dangin marassa kunya, gadon k’anwar uwarki mai aure mazan mutane kikai ba laifinki bane...Wuce ki fita kafin na fitar dake....!”
Sosai Nabilah ke kuka ta shiga k’ok’arin b’anb’are hannunta Daga rik’onda Khalid yai mata... Yak’i sakinta saima damk’e hannun nata da yai sosai har kaman zai ji mata ciwo sabida yanda ransa yakai k’ololuwa wajen b’aci.. Duban Ammi kurum yake da idanunsa da suka gama rinewa zuwa ja... Nabilah kaw na kuka sosai taci gaba da k’watan hannunta Daga rik’onda Khalid yai mata...
Ammi dake ci gaba da huci bud’e murya tai kana tace “Khalid idan baka sakar mata hannu ta fice ba wllhi kaji na rantse maka zaka nemi wata uwar amma ba ni ba...!”
A hankali ya saki hannun Nabilah jin kalaman Ammi na k’arshe...
Nabilah da kanta ke kife cikin hijabi ta fice da sauri tana ci gaba da kuka....
Chapter 168 · 0% Book details