← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 146 OF 198

Sashe 146

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Mamy ta dubi Abba da yai shiru tin bayan shigowarta saima k’ok’arin kamo tashan labarai da yake... Saurin kai hannunta tai ta amshi remote d’in ta kai masa tashar NTA d’in dan lokacin labarun tara ne... Har lokacin nan Abbah bai dubeta ba saima maida hankalinsaga tv da yai dikda cewa da gani bama fahimtar labarun yake ba.... Mamy ta d’an sauk’e ajiyan zuciya sanda takai idanu kan tray d’in abincinsa dake gefe da alama ko tab’awa baiba tinda ita tana hidiman biki Lami ce ke kula dashi ta bata girkin ranakun... K’arasawa Mamy tai ta janyo tray d’in tana k’ok’arin serving d’insa Abbah ya katseta da fad’in “Karki zuba abincin nan Mariya a k’oshe nake...”
Mamy ta d’anyi raurau kana tace “Toh mai kaci ya isheka, gani fah baka ko tab’a abincin ba tintini...”
Jinjina mata kai yai kana yace “Ina sane, kawai na k’oshi ne...”
Mamy tai shiru dan tama rasa abin cewa gaba d’ai, sai sauk’e ajiyan zuciya da tai, a hankali ta d’an kuma muskutawa zuciyarta cikeda tausayin mijin nata lokaci guda take furta “Nasan kana cikin lokaci mai matuk’ar wahala a rayuwarka... Nasan hakan ba abu ne mai sauk’i amma ina rok’onka dan Allah kai hak’uri ka d’auki duk abubuwan da suka faru a matsayin k’addara kaji mijina...!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya wanda ya sanya Abbah juyowa yana dubanta cikeda tsananin tausaya mata, shin wane irin kyakkyawar zuciya Mariya kedashi.... Bayan dik abubuwan dataji ta zab’i ta yafewa wad’annan azzalumai, lallai ita d’in tana zuciya mai kyau...
Sauk’e ajiyan zuciya yai kad’an yana mai k’ura mata idanu... A hankali yakai hannayensa saman nata... Mamy ta d’ago tana dubansa cikeda tausayinsu su duka biyun.... K’wallan da Abbah keta k’ok’arin mak’alewa suka gangaro...
“Ki yafeni Mariya...!” Kalman data soma fita daga bakin Abba kenan...
Mamy ta girgiza kai tace “Dan Allah ka daina bani hak’urin nan haka dukanmu nan abin nan ya shafemu ba ni kad’ai ba, kuma mu godewaAllah da har ya warware mana komai...”
Girgiza kai kad’an Abbah yai “Ke d’in kece kikafi kowa a cikinmu, Mariya wala’alla hakkinki shine ya kamani har mutanen dana aminta dasu sukaimin cin amana mafi muni... A lokacin da Ma’aruf ya b’ace na biyewa son zuciyata naita zarginki da laifi nima, banyi la’akari da halinda kika tsinci kanki a natsayinki na mahaifiya ba, ban kasance taredake nai supporting d’inki ba saima biyema masu laifin da nai muka had’u muka cuzgunama rayuwarki... Zan jima inajin zafin wannan abun a raina...!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya...
Mamy da kanta Ke kife tana matsan hawaye itama, lokaci guda take furta “Wannan duk muk’addari ne daga Allah, mu d’auki hakan a matsayin k’addarar rayuwarmu... Sannan mu godewa Allah da ni’iman da yai mana a yanzu mu daina kuma duba baya...!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya... Abbah yai mata k’uri yana godiya wa Allah can k’asan zuciyarsa da wannan baiwa da yai masa na samun mace irin Mariya...! A hankali ya matsa kusanta ya rungumota cikin jikinsa su duka biyun hawaye suke...!

***

A b’angaren Engr kaw tinda ya isa gida yake nazarin takardan da Akram ya bar masa, ya kasa aminta Muhibba can go this far, ta yaya zata masa haka... Kenan watak’ila tanada masaniya kan yanda Akram d’in ya tafi tinda she’s his accomplice.... Baisan kishin Muhibba yakai wannan peak d’in ba, a had’a baki da ita a yaudare mijinta, mijin da ya d’auki gaskiyarsa da yardarsa ya bata... Ya fuzar da iska a hankali yana mai had’e tafukan hannayensa waje guda... Kaman wacce aka wuntsilota haka ta shigo babu ko sallama bayan ta gama baccin asaranta, dan har ya dawo gidan bata sani ba saida ta tashi ta hangi motar da ya fita da ita a parking lot alamun ya dawo, dik yini zubur d’in nan da Engr yai a waje Muhibbah bata kira taji lafiyarsa ba dikda kasancewarsa mutum mai hada hada da yawa... Kallo d’aya yai mata ya watsar... Ta k’araso tana mik’a had’ida hamma alamun har yanzu akwai bacci a idanunta... Gefe dashi ta zauna had’ida kwantar da kanta cikin jikinsa, cikin murya irinta wanda bacci bai ida sakesa ba Muhibbah Ke fad’in “Excellency na ashe ka dawo, inacan inata bacci I didn’t expect you to be home this early, na zaci meeting d’inku da party chairman yau ne...!” Ta k’arashe tana mai kuma sakin hamma... Jin ko gizau bai kulata ba ya sanyata saurin d’agowa tana dubansa, kasancewar kansa a kife yake yasa bata fahimci halinda fuskar nasa Ke ciki ba saidai ta hangi takardan dake hannunsa wanda ya kifa masa idanu, bata kawo komai ba don a zatonta batada alak’a da takardan....
Murmusawa ta d’anyi tasan dik gajiya Ke damunsa tinda mijin nata bai samun wane isasshen hutu da lokacin kansa sai na mutane... A hankali ta kuma kai hannayenta saman kafad’arsa tamkar mai massage... Cikin salo na kashe murya take fad’in “Excellency na baka son hutu... Waima tsaya, have you eaten..? Should I bring you something to eat...?”
Cikin wane irin razananniyar murya yace da ita “Get your hands off me...!”
Muhibbah data nemi baccin idanunta ta rasa a zabure ta mik’e tana dubansa cikeda tsoro....

Tai far da idanu “Excellency na mai kuma ya faru.... Ko wani ne waje ya b’ata maka rai...?” Ta k’arashe tana zaro manyan idanunta.... Bata ida razana ba saida ya d’ago fuska, nan ta hango tsananin b’acin Rai dake kwance cikin idanunsa... K’irjinta ya shiga bugawa ta soma tinanin kardai dubunta ne ya cika Engr ya san tana shan drugs... Toh amma she’s been very careful bata basa wani k’ofa da zai fahimci hakan ba tinda shi bama mazauni bane, Toh kodai yasan itada k’awayenta safaran miyagun k’wayoyi shine sana’arsu... Wata zuciya tace kai da zai sani da tuni ya Sani k’ila dai wani abin ne daban....
Muryarsa ne ya kuma dawowa da ita daga duniyar tinaninda ta tafi...
“Why did you do that...? How dare you lie to my face...?!” Ya k’arashe cikin wata irin murya mai razanarwa yayinda Muhibbah ta shiga willi willi da idanu k’irjinta naci gaba da bugu.....

SameenaAleeyou📚

*INDA RAI*
_................DA RABO

*94*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Take ta soma rau-rau da idanu tamkar mai shirin kuka, lokaci guda take furta “Haba Excellency na wani abin nayi ne... Kodai wani ne ya b’ata maka rai wajen taro....?”
Tsaye ya mik’e yana dubanta sosai kana ya mik’a mata takardan dake hannunsa...
Gaban Muhibbah yai wani irin yankewa ya fad’i, toh wannan kuma takardan minene...? Ta tambayi kanta, ta kuma d’agowa tana dubansa, gani tai ya tsume sosai babu alamun wasa a tattare dashi, ga idanunsa da suka kad’a sosai alamun b’acin rai...
Ta k’ak’aro murmushin da tafi kama da yak’e “Excellency na wannan kuma na menene...?”
“Ki karb’a ki karanta sai kimin bayanin dalilin da ya sakaki sikata abinda kika aikata, and don’t you dare lie to me....!”
‘Yan hanjinta suka kuma kad’awa gashi ya tsareta da idanunsan nan masu firgita marassa gaskiya...
“Ki karb’a nace..!!!” Ya kuma fad’i cikin daka tsawa Wannan karon...

Jiki har na rawa Muhibbah ta amshi takardan ta soma karantawa, k’irjinta na bugun tara-tara... Wato Akram tona masu asiri yai wajen Engr, lallai tayi wauta data yarda Akram can betray Engr... Jujjyya takardan ta shigayi tana fad’in “Excellencyna ban fahimci komai ba fah ni... What’s all this...?” Ta k’arashe cikin murya mai kalan tausai...
Girgiza kai yai kad’an yana dubanta kana yace a hankali“The nerve...! Har kinada k’arfin gwiwar k’aryata abinda kika karanta yanzu... So tell me where’s Akram... Since you’re his ally na tabbata kinada masaniyar yanda ya tafi fad’a min ina yake....!”
Muhibbah ta kuma turo baki kana tace “Ni dai wllhi bansan yanda yake ba... I have no idea....”
Engr ya kuma jinjina kai kana yaci gaba da fad’in “So, are you happy now...? Kina farin ciki tinda kin lalata auren mijinki....? Fad’a min kina farin ciki da hakan...?” Ya k’arashe yana mai tsareta da idanu...
Yatsina fuska tai kana tace “Toh mai kake tinani Excellency na... Na zauna na zuba idanu ka kawo min wata mata cikin gidan nan, kaima kasan da nace maka na amince dan banida option ne, kuma da na fahimci kunyi tarayya da Akram wajen sonta sai nai amfani da wannan damar, haba Excellency na, wannan yarinyar ba class d’inka bace... How in the world ma zaka soma neman aure kana takara da yaronka... Ai ni taimakon ka ma nai na rabaku cikin salama, Kaga ‘yan adawanka na siyasa bazasu sami abin tsegumi ba...”
Tsawan da ya daka mata ya sanyata had’iye sauran maganganun nata... Ya kuma takowa gabanta kad’an kana yace “Don’t you dare talk about her like that ever again, wannan ya zama gargad’i na k’arshe... Don’t push me to the wall Muhibbah....!” Ya k’arashe yana mai rab’awa ta gefenta ya nufi bathroom da niyyan d’auro alwala....
Muhibbah ta juya idanu had’ida yin jifa da takardan, a fili taja wani uban dogon tsaki kana ta tintsire da dariya tace “Ko a yanzu dai ni ce da riba tinda baka aureta ba batun auren yabi ta shanun sarki... Ma’aruf kenan, ai gidan duniyar nan baka da mata sai ni Muhibbah...!” Ta kuma tintsirewa da dariya kana ta kad’a k’afarta ta fice tana wani juya jiki take fad’i a hankali... “Idan ka matsu dani ka biyoni har b’angarena...”

***
Chapter 146 · 0% Book details