Sashe 183
Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kasancewar jami’an tsaro sun gewaye wajen da igiyoyi na tsaro da gudanar da bincike yasa Haule bata samu daman tsallaka fence d’in ba.. Tana nan tsaye tana jimamin Ta yanda zata hango Hafiz d’inta.... Can ta hango wani kaman shi saman gado mai suffar keke irinta motar d’aukan majinyata Wato ambulance.... Haule ta rikice ta nufi wajen a d’ari tana ambato sunan Hafiz d’inta... Saidai sam kwance kawai Hafiz yake tamkar bai numfashi dan tuni ma jami’an lafiya dake taredashi cikin bayan ambulance d’in soma k’ok’arin d’aura masa na’urar oxygen dan ceton rayuwarsa... Haule hannaye bibbiyu aka take kuka... Yayinda Engr ke tsaye gefenta yana bata baki had’ida k’arfafa mata gwiwa cewa ta kwantar da hankalinta Hafiz zai sami lafiya da izinin Allah....
Haule dai kuka kurum take tana fad’in Hafiz kada ya tafi ya barta.. Can ta hangi Baba Alhaji dasu Sawwama dasu Magajiya an taso k’eyarsu hannayesnu rufe cikin handcuffs.... Tai kukan kura ta nufesu tana tsine masu albarka... Babu kaman Baba Alhaji da a cewarta dasa hannunsa aka tasamma hallak’a d’ansu...
Taci gaba da kuka tana fad’in “Bazan tab’a yafe maka ba Alhaji.. Ka cuceni ka zalunceni... Wannan shine sakayyar da zaka min bayan shekarun da muka kwashe muna tare... Mu k’ulla tare mu warware tare, amma rana tsaka kabi wad’annan tsinannun Allahn ka amince a salwantar da rayuwar d’anka gudan jinjnka... Allah ya isa tsakanina da kai...!!”
Baba Alhaji na kuka sosai yake fad’in “Haule wllhi ba laifina bane ki yarda dani... Wllhi tilasta min akai... Amma kinsan bazan tab’a yiwa Hafiz haka ba... Haule ina son d’ah na ina son d’anmu... Ki yafe ni Haule na...!!!”
Haule na kuka take fad’in “Kada ka sake kiransa d’anka dan babu uban da zaima d’ansa na cikinsa haka kan wata shashashar mace.... Wllhi nayi dana sanin aurenka da duk wasu muggan abu da muka k’ulla tare a baya...!” Ta k’arashe tana mai kuma fashewa da kuka....
Engr dai sadda kansa k’asa kurum yai zuciyarsa na masa rauni... Wannan shine k’arshen dik wanda yace zai gina rayuwarsa kan zalunci... Akwai darussa masu yawa a rayuwar wad’annan ahali ta ko wanne b’angare.... Tabbas mahak’urci yana tareda riba, yau gashi su Mamy da sukai hak’uri har k’arshen mutumin da yai sanadiyar mutuwar mahaifinsu da tarwatsewar ahalinsu Allah ya nuna masu... Gashi yau an capke Duna dik ta’addancinsa, yau ga Baba Alhaji da matarsa mutanen da suka tasamma salwantar masu da d’ansu yaron da baiji ba bai gani ba sabida son zuciya irin nasu yau gashi su da kansu suna tuhuman juna da d’aura alhakin salwantar da nasu d’an a wuyan juna... Kaico irin wannan rayuwa... Ubangiji ka kiyashemu aikin dana sani da son zuciya...Ameen...
Haka aka wuce dasu Magajiya aka jefasu bayan hilox yanda akewa criminals... Za’a haura da Baba Alhaji kenan ya hangi Abbah daga gefe idanunsa sunyi matuk’ar raunana... Baba Alhaji ya sadda kansa k’asa cikeda nauyin d’an uwan masa, lokaci guda ya rok’i d’an sandan cewa ya basa sakanni yai magana da d’an uwansa... Da k’yar d’ansandan ya k’yale Baba Alhaji yai magnar mintina da basufi biyu ba da Abbah...
Kai a k’asa Baba Alhaji ke furta “Ka yafeni Usman... Ka yafe min dik abubuwan da nai maka.... Hak’ik’a naso tarwatsa ahalinka sabida son zuciya da k’yashi da hassada irin nawa, sai gashi Allah ya tsare maka ahalinka sabida shi baya mulki da zalinci... Yanda naso tarwatsaka sharrina ya koma kaina... Na tarwatsa nawa ahalin da kaina... Babu wanda zaiso ya sake d’aga idanu ya dubeni cikin iyalaina... Babu wanda zai yarda cikinsu cewa bazan tab’a yiwa Hafiz haka ba...! Usman ka yafeni... Wllhi wannan hakkinka ne Ke bibiyata... Naso na salwantar da Ma’aruf tun yana k’arami... Na tilastawa Mamani ta tarwatsa farin cikin dake tsakaninka da matarka Mariya ta hanyar d’aurawa Mariya laifin b’acewar Ma’aruf... Na kuma tilasta mata had’a auren Hafiz da Zulfa’u ba don komai ba sai dan na tabbata ahalinka babu kwanciyar hankali a tattaredasu.... Usman duk wad’annan abubuwan ni ne nan na tilastawa Mamani yinsu, tsangwamar Mariya da yaranta idan har tana so sirrinta na cewa ba ita ta haifeka ba ya rufu... Idan ba haka ba zan sanar dakai komai... Ba komai yasa nai haka ba sai dan sanin cewa kana matuk’ar k’aunar Matarka Mariya kuma ta haka ne kawai zan ganka cikin k’uncin rayuwa... Idan har ka rasa kwanciyar hankali da zaman lafiya cikin gidanka da iyalanka nasan tamkar rayuwar kawai kake amma Farin ciki ya k’aurace maka... Na kuma had’uda mata shed’aniya irin Haule sai na kuma samun wata dama...!” Baba Alhaji dake kuka sosai ya kuma had’e hannayensa waje guda yana rok’on yafiyar Abbah da ko d’agowa ya kalli Baba Alhajin ya kasa... Shin mai ya tsare masa da tsanani a rayuwa da har zai masa irin wannan k’iyayya... Ashe d’an uwa zaiso ya jefa rayuwar d’an uwansa cikin garari irin haka... Kai kaicon rayuwa mai cikeda tarin hassada k’yashi da mugunta... Ko duban Baba Alhaji Abbah bai iya yi ba sabida zuciyarsa dake tsananin suya da d’aci had’ida rauni... Yana jin sanda d’ansanda ya tasa k’eyar Baba Alhajin... Bai daina bud’e murya yana fad’in Abbah ya yafe masa ba had’ida cewa “Usman kamin rai ka d’aukar min lauya kada ka bari a yanke min hukuncin laifin da ban aikata ba na rok’eka Usman..!!!”
Abbah dai rintse idanunsa kurum yai wasu irin hawaye masu d’umi suka gangaro masa....
Ganin yayi weak sosai yasa Engr K’arasowa ya tallafesa, gaba d’aya tausayin Abbah Mamy da Zulfa’u sun cika zuciyar Engr dan a gabansa Baba Alhaji yaita confessing muggan abubuwan da yaiwa d’an uwansa.... Ace d’an uwanka ne yai maka irin wad’annan abubuwan, baida buri face ya ganka ka tagayyara... Shin mai za’ai da k’iyayya hassada da gaba...Kaicon zuciya mai cikeda wad’annan cututtuka....
Engr bai bar wajen ba saida ya sanya one of his men ya maidasu Mamy gida... Itakaw Haule dama cikin ambulance d’in da aka d’auki Hafiz ta shige, sanin cewa magaifiyarsa ce ita shisa basu hanata ba... Tareda ita aka nufi asibitin...
Daga bisani ne su Engr suka nufi police station d’in yanda zasu bada nasu statement d’in, Engr ya kuma filing wani case akan Duna... Toh Duna kanma dama nemansa ake ruwa a jallo dan haka cases d’in dake bisa wuyarsa ma bazasu lissafu ba, D’an ta’adda ne da hukuncin kisa ya hau kansa koda ma ba’aje kotu ba ballantana kuma aje.... Tsabaragen ta’addancin Duna bazai yuwu a Detaining nasa a nan police station kafin a shiga kotu ba dole aka tafi da Duna prison dan ajesa a police station na nufin an basa lasisin escape ne....
Tinda Engr ya sako k’afa a k’ofar ofishin Zo Kaga yanda manema labarai kesonji daga bakinsa duba da yanda ya jajirce a matsayinsa na d’an k’asa mai kishin k’asarsa ya kawo k’arshen wannan d’an ta’adda da ya gagari Al’umma... Sam Engr bai b’oye masu cewa ba shi kad’ai yai wannan yak’i ba harda su Hafiz su Akram Wanda suka sadaukar da rayukansu dan a kame wannan hatsababibin d’an ta’adda....
Kame Duna ba k’aramin Martaba da d’aukaka ya k’arawa Engr ba, dan tuni labari ya karad’e ko ina, hartaga jamk’iyarsu sunyi matuk’ar alfahari dashi tin ma bai d’ale karagar mulki ba yake sadaukarwa da jajircewa wajen ganin al’umman k’asarsa sun zauna lafia... Toh inaga ya hau kujerar mulki... Kai daidai da jamk’iyar adawa saida suka jinjina masa.... Jama’an gari kaw ya k’ara samun karb’uwa a wajensu dikda yace sam shi ba don haka yai ba.... Da jagorancin Akram aka tafi dajin Babba Duna aka kub’utar da d’inbin jama’an da ya sacesu ya ijesu dan amsar kud’in fansa Daga iyalansu.... Zo Kaga farin ciki wajen jama’a... Kan kace mai labari ya karad’e k’asa ko wane kafan yad’a labaru breaking news d’in da ake nunawa kenan.... Kame Duna ba k’aramin nasara bane dan zai bada dama ya zak’ulo duk wasu wanda suke mu’amala dasu na sace mutane da yin garkuwa dasu dan amsar kud’in fansa tinda bazai yarda ya tafi k’asa shi kad’ai ba ciki kaw harda gurb’atattun k’usoshin gwabnati da ake had’e bakin dasu akeyin wannan ta’asa.... Allah ka kawo mana k’arshen wannan ta’addanci a k’asarmu baki d’aya.. Ka yalwatamu da aminci da zaman lafiya had’ida shuwagabanni adilai masu jin k’an al’ummansu... Ameen Ya Rabbi..!
Detective Najiba ne ya k’araso yanada Engr ke tsaye yana amsa waya wanda ko ba’a fad’i maka ba da sahibarsa ce sakamakon wane irin annuri da ya cika fuskar tasa... Saida Najeeb ya jira Engr ya ida wayar kafin ya k’araso gareshi ya risina yace “Sir, it’s confirmed... Muhibbah tana d’aya daga cikin manyan Drug dealers na k’asar nan... Shagunanta ana saye da cinikayyan kayan maye a b’oye.... Sannan tanada wasu shaguna a nan mak’wafciyar k’asarmu Wato Kamaru yanda suma aka smuggling miyagun k’wayoyi.... Sannan ta tabbata a gobe zasu fitar da kaya Ta wannan shagon nata na saida sark’ok’in mata.... Daga nan zamu executing plan d’inmu and capture them..!”
Ya k’arashe yana mai nuna masa wata video na sirri da ya samu daga jikin CCTV footage na babban kantin Muhhibar....
Jikin Engr yai mugun sanyi ganin yanda ake tsaga soson gidan ‘yankunnaye ake jera muggan k’wayoyi sam bazaka zaci akwaisu ciki ba sai idan ka sani....Wato ta haka suke snuggling k’wayoyin ta yanda baza’a gane ba.... Take yaji wasu irin k’walla suna ciko idanunsa... Saurin mik’awa Najeeb wayar yai yana mai barin wajen cikin sassarfa.... Najeeb ya bisa da kallo cikeda tausayawa...
***
A b’angaren Muhibbah kaw sai faman tsinuwa take tana ashar sabida plan d’insu bai working ba, Engr da tawagarsa basu fita taron campaign ba... Komai ya rushe mata ya ruguje, taso ganin downfall d’in Engr a yau... Taso a nuno fuskar Engr Ma’aruf MUTALLAB a yau a matsayin gurb’ataccen d’an siyasa mai b’ata matasa mai d’aurasu akan turban ta’amuddi da miyagun k’ wayoyi sai gashi Shamzy ta kunna mata TV yanda ake hasko fuskarsa a matsayin jan gwarzo mai k’aunar Al’ummarsa da k’ok’arin kawo sauyi a k’asarsa.....