← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 160 OF 198

Sashe 160

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fincika Hafiz ma yai kana yace “Da ace baka soma d’aura idanunka kan matata Zulfa’u ba dik da hakan bata faru ba, da yanzu ina tareda matata... Nayi warning d’inkacountless time amma bakaji ba yanzu ga halinda muka tsinci kawunanmu ciki... You’re at fault here...!”

Da tsananin mamaki Akram ke duban Hafiz kana ya kuma zabura yana fad’in “Kai har ka isa.....! Don’t you dare throw the blame on me, dak’ik’ancinka da jahilcinka shi ya kawomu nan... Ka kasa fahimta wa’adin zaman k’addarar Zulfa’u da kai ya k’are... Kuma dama na fad’a maka ita d’in ba tsararka bace, kuma nima ba tsarata bace.... Amma yanzu na tabbata ka fahimci hakan.... Bari kaji na fad’a maka, koda ace na kamun da son Zulfah a baya... The moment da na fahimci Boss d’ina is into her as well na janye zuciyata amma ban janye k’afafuwata da makamai na ba domin kaw mashi nake yak’in.... To keep his reputation clean nai haka dan nasan yanda kake mahaukacin nan muddin akace His Excellency ne mai nemanta zaka ruining komai from the very start, na tabbata zaka had’a kai da ‘yan adawa da wannan doluwar matar tasa ku taru ku b’ata sunan his Excellency shisa nayi playing game d’in.... Ka fahimta....!” Ya k’arashe yana mai ware idanunsa gaba d’aya....

Hafiz yai shiru tamkar wanda ruwa ya shanye... A hankali ya shiga jinjina kai tamkar wani k’adangare, lokaci guda ya tsartar da miyau wanda Ke gayraye da jini daga bakinsa kana yace “Yanzu na fahimci komai....”

Akram da bai daina aika masa harara ba yace “Tinda ka fahimci komai yanzu sai musan yanda zamuyi mu fidda kanmu daga wajen nan Kafin mutanen nan su cimma burinsu akanmu....”

Hafiz ya buga uban tsaki kana yace “Ta ya zamu iya fita daga dajin da Duna ya gama kewayeta da sihirinsa.....?”

Akram dake aika masa harara yace “Allah shi zai fiddamu....!!!” Daga haka babu wanda ya kuma cewa komai cikinsu sai sak’e sak’e da suke cikin zukatansu....

***

Saida ‘yansandan suka tabbata sun binciki dik wani wanda keda alak’a ta kusanci da Hafiz saida suka masa tambayoyi, hankalin Haule ko ba’ace ba yai matuk’ar tashi, babu Hafiz babu dalilinsa ga ‘yansanda na binciken yanda yake, ga Sahariyya kwance babu lafiya danma Allah ya rufa asiri k’unan bai shiga sosai ba... Haule dafe kanta tai da duka hannayenta biyu tana duban officers kana tace “Rankashidad’e wllhi wannan sharri ne d’ah na ba d’an ta’adda bane... Wllhi sharri ne kumin rai kar ku kulle min d’ah a gidan yari wllhi shi ba d’an ta’adda bane....!” Ta k’arashe tana mai fashewa da kuka had’ida zube gwiwoyinta k’asa hannayenta duka biyu dafe da kanta....

Magajiya dake gefe tana jijjiga fad’I take “Ranaka shidad’e kowa ya kwana da sanin cewa Hafiz ya lashi takobin hana auren Zulfa’u yuwuwa dan haka zai ko menene dan ganin Akram bai auri Zulfah ba, kuma kowa shaida ne dik abinda Hafiz ke k’ullawa tare yake k’ullawa da wannan makirar uwar tasa....Rankashi dad’e a halin yanzu rayuwar d’iyata kanta na cikin had’ari a matsayinta na matar wannan d’an ta’adda ku taimaka ku zak’ulo Hafiz dik yanda ya shiga ya fita kafin ya hallak’a nawa d’iyar.....” Ta k’arashe cikeda nuna damuwa....
Haule da hawayen idanunta suka kafe gaba d’aya dan jin irin sharrin da ake k’ullawa d’anta gaban idanunta... Cikin sauri ta zabura zatai kan Magajiya take fad’in “Amma ke wannan ‘yar wuta ce.... Ko a labarin munafukai masharrantar farko ban tab’a cin karo da irinki ba....”
Magajiya ta mak’ale bayan Officer tana fad’in “Yallab’ai ka gani koh.... Ka yarda itada d’anta duk ‘yan ta’adda ne tinda gashi nima tana yunk’urin hallak’ani...”

‘Yansandan suka janye Haule daga kan Magajiya suka watsarta gefe suna mai fad’in zasu tafi yanzu amma zasu dawo kuma dole su saka idanu kan Haule sabida ita kad’aice zatai kinking d’insu to Hafiz.....

Haule zubewa tai a wajen tana kukan nadama da bata tab’a yin irinsa ba a rayuwarta.... Koda wasa bata tab’a hasasho irin wannan musiba da yake ciki a halin yanzu ya tunk’arota ba.... Kaicon rayuwa mai cikeda tarin son zuciya... Lallai yau ta kuma yarda makirci makaranta ne mai k’unshe da azuzuwa iri daban daban... Ta kuma yarda da wannan hausar da akace duniya tafi gabaruwa iya jima....

Naja’atu dake rakub’e gefe tana kuka sosai, k’arasowa tai ga mahaifiyarta tana fad’i cikin kuka “Hajiya lokaci yayi da zaki yada makaman yak’inki Ki tuba kibi Allah Ki yarda shikeda cikakken iko akan komai....!”
Haule na tsananin kuka wanda bata tab’a yin irinsa ba ta rungumo Najah tana ci gaba da fad’in “Naja’atu Yayanku Yayanku Najah... Najah sun k’ullawa Hafiz d’ina sharri.....!”

Ta zabura da sauri tana janyo rigar Baba Alhaji take fad’in “Alhaji karka bari wannan azzalumar da d’iyarta su k’ullawa d’anmu sharri... Kai kanka kasan Hafiz ba d’an ta’adda bane koda ace yanada muguwar zuciya... Alhaji ka taimaka kaje kaima jami’an tsaro magana... Laifin garkuwa a k’asar nan ya zama babban laifi karka bari a kama d’anmu da ita....!”

Fincikewa Baba Alhaji yai yana watsa mata muguwar kallo daga yanda take duk’e k’asa “Uban da ya aikesa ya aikata laifin... Dama tinda naga ya nace sai ya maida Zulfa’u nasan cewa bak’ar zuciyarsa da yayi gado a wajenki bazai barsa ba, dan haka tsuntsun da ya janyo ruwa shi ruwa ke bugu, babu hannuna ciki... Wayasani ma ko tare kuka k’ulla kedashi tinda dama kowa ya sani bak’ar makirace ke....!”
Magajiya na murmushi ta shiga janyo Baba Alhaji tana fad’in “Muje Dalin Dalin... Muje karma ranka ya b’aci kaji koh....!”
Ta waigo tana duban Haule dake duk’e tana duban mijinta cikeda al’ajabi kaman ba tare suka jima suna k’ulle k’ullen makircinsu ba..... Magajiya tai mata gwalo had’ida kashe mata idanu guda ta janyo hannun Baba Alhaji yabi bayanta kaman wani soko....

Haule dake duk’e wajen wane irin kuka ne mai ban tausayi taji na fito mata, Sahariyya da akai komai gaban idanunta itama, kuka ta fashe dashi daga yanda take kwance mai ban tausayi.....

****

Tsaye Engr yai cikin parlorn yana amsa kiran jami’an tsaron, bayan sun ida wayar ne yaji shigowarta tana tafiya tana karo da k’ofa ita kad’ai.... Mamaki ya cikasa ganin irin yanayin da Muhibbah ke ciki na tsananin maye.... Engr yayo kanta da sauri ganin zata kifa a k’asa garin tangad’i.... Saurin tallafota yai yana binta da kallon mamaki....
Murya can k’asan mak’oshi yake furta “Maye.... Muhibbah...!!”

D’agowa tai a galabaice cikin tsananin maye tana dubansa, lokaci guda ta tintsire da dariya tana mai nunasa da ‘yar yatsa take fad’in “Wai da gaske ka auri wannan kucakar yarinyar....? Ma’aruf da bakinka kake fad’a min kayi aure....??” Ta kuma fashewa da dariya tana mai ci gaba da layi, har lokacin Engr na rik’eda ita yana duban ikon Allah, abinda yakeji wai Wai akwai mata mashaya sai gashi nan har cikin gidansa..... K’ok’arin janyota zuwa cikin parlorn ya soma amma tak’i shigewa sai faman nunasa da yatsa take tana fad’in “How... dare you... Ma’aruf.... How could you.....?” Tana maganan tana nunasa da yatsa tana tangad’i.... Lokaci guda hawaye suka soma gangaro mata sanda taci gaba da fad’in “You’ll never be Happy Ma’aruf... Nai maka.... Alk’awarin bazan tab’a barinku ku kasance cikin farin ciki ba.....is a promise.... Kuma bari kaji na fad’a maka, bazan bar maka ‘ya’yana ba... I’m leaving with them, kaima ka sani ni ba matsiyaciya bace... Inada dukiya... Kuma dik k’asar da nakeso mu rayu da yarana zan tafi dasu.... Horon da zan maka kenan shine bazaka sake sakasu a idanunka ba..... Wannan alk’awarine....!!!” Ta k’arashe tana mai zubewa cikin jikinsa alamun bacci yayi gaba da ita....
Azata yai a kafad’arsa ya haura da ita sama d’akinta... Saman gado ya shimfid’ata had’ida gyara mata kwanciyar.... Yai zaune gefenta had’ida k’ura mata idanu tausayinta na d’awainiya dashi... Ya sanya ma ranshi zafin kishi ne ya sanyata aikata abinda ta aikata, baiji har cikin zuciyarsa ta jima tana ta’ammudi da miyagun k’wayoyi.... Sauk’e ajiyan zuciya yai had’ida k’urama drawer dake gefe idanu.... Kaman wanda aka sinkaya ya k’arasa ya janyo drawer d’in.... Gabansa ne yai mummunar fad’uwa sakamakon ganin tulin gidajen kayan maye da akai amfani dasu suna zubowa.... Mamaki ya cika zuciyarsa ya shiga d’aukan ledoji da kwalayen yana gani mamaki da fargaba fal zuciyarsa..... Cikin sauri ya kaikato yana duban Muhibbah dake bacci wasted zuciyarsa na kuma tsinkewa, lokaci guda yaci gaba da juya kwalayen yana ambaton Allah a hankali... Hakan na nufin Muhibbah ba wai yau bane ta saba ta’amuddi da miyagun k’wayoyi kenan... Ya dafe kansa a hankali yana mai karanto innalillahi.... Zuciyarsa naci gaba da harbawa... K’aran shigowar sak’o cikin wayarta da ya jiyo daga cikin jakkanta ya sanyashi saurin janyo jakkan kana ya ciro wayar... K’ura ma sak’on idanu yai zuciyarsa na kuma tsinkewa...
Bash ne ya turo mata sak’on yana sanar da ita rana iti yau zasu fitar da huge amount of chocolates ta shagonta so ta zama ready.....

Ya karanta yafi sau abinda yafi yana nanata chocolates cikin zuciyarsa... Haka kurum yaji kalmar chocolates bai kwanta masa ba tinda yasan Muhibbah Manyan shagunan kayan k’arau na mata takedasu har guda biyu babu wani shagonta da ya danganci abin ci.... Ya kuma juya wayar yana mai kuma karance sak’on.... Take wani tinani ya fad’o masa, yai saurin k’arasawa ya d’auki yatsarta ya shaga jikin wayar nan wayar ta bud’e.....
Chapter 160 · 0% Book details