← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 134 OF 198

Sashe 134

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Haule tace “Yauwa yanzu naji batu....”
Har sun kai k’ofa Baba Alhaji yaja yai birki yace “Toh amma ai Naja’atu da Sahariyya dik abu gudane... Inaga mubar zancen a haka...”
Muguwar kallo Haule ta watsa masa kana tace “Eh lallai na yarda Kai Hafiz ya gada a rashin lissafi.... Dik yanda akai sunada nasu dalilin na canza auren nan, dole mubi kadin lamarin sannan a tinaninka zamu iya tank’wara Naja’atu mu cika burinmu ne.... Ai Sahariyya itace mabud’in cikan burinmu....”
Baba Alhaji ya jinjina kai yace “Kuma kince wani abu.....”
Take suka fice afujajan suka nufi gidan Abbah, kotakan su Sahariyya basu bi ba, gidan biki ya koma gidan rabon dambe... Ana a haka Su Amara suka shigo gidan da baya da baya suna tik’an rawa sun k’ure kid’an wak’ar nan da ake yayi na AURE MARTABA... Dama ba’a gayyaci Amara da tawaganta ba suna shak’e da haushin Sahariyya dan Bikin ko wata budurwa ya tashi a unguwar dole a aikama Amara anko da katinta itada mutanenta toh Bikin Sahariyya su Fa’iza selecting sukai dan haka ba’a gayyacesu Amara ba, koda sukaji an fasa biki suka shigo d’aukan fansa...
Tashin hankalin Sahariyya ya ninku gashi su Amara hidimansu babu mutunci sun sakata tsakiya sai tik’an rawa suke suna mata lik’ida k’osan rogo da suka shigo dashi ciki kwano.....

***
Dikda cewa batasan mahaifiyarsu sosai ba sabida tanada k’anan shekaru Allah yai mata rasuwa tabbas wannan mata tanada fuska irinta mahaifiyarsu.... A hankali taci gaba da takowa tana duban matar wacce keta faman sakin murmushi tana gaisawa da jama’a, d’abi’unta da murmushinta irinta mahaifiyarsu ce... Aunty Bara’atu tasa hannu a hankali tana goge hawayen da suka gangaro mata, Mamy tana hangota ta k’arasa gareta suka rik’e hannayen juna suna ci gaba da kallon Aunty Daula wacce sam bata kula da irin duban da matan Ke mata ba... Mamy ta janyo hannun Aunty B a hankali suka k’eb’e... Lokaci guda suka had’a goshinsu waje guda suna hawaye.... Aunty B cikin rawar murya take fad’in “Fuskar Mama Hajja... Mamy fuskar Mama Hajjah na gani... Tell me Ya Mariya wacece wancar matar...? Shin munada alak’a da ita ne...? Dikda k’ananan shekaru na bazan mance fuskar mahaifiyar mu ba... Ya Mariya wacece matar nan...?”

Mamy tai k’ok’arin saita kanta kana ta shiga share ma Aunty B hawayenta, lokaci guda take k’ok’arin d’aura murmushi saman fuskarta “Wannan matar da kuke waya mai murya irinta Hajja Mama itace wannan Bara’atu... Daula ba murya kawai takedashi irinta mahaifiyarmu ba, harta fuskarta irin tata ce.... Tambayar a nan shin munada alak’a da ita ne... Ko kuwa dai zallan kamanni ce...?”
Aunty B ta dube ‘yaruwar tata kana ta nunfasa tace “Daula ita kad’ai zata amsa mana wad’annan tambayoyi, a hankali zamu santa zamu San asalinta, ta nan zamu fahimci idan ita d’in tanada alak’a da Mahaifiyarmu....”
Jinjina mata kai Mamy tai kana tace “Haka ne...” Muryarta ne ya sark’e sakamakon sauraro hayaniyar Haule da tai daga tsakar gida tana fad’in a fitina sanar da ita uban da yace ai mata wasan k’wallon kwando da yaranta... Baba Alhaji na biyeda ita...

Babu shiri Aunty Bara’atu da Mamy suka dubi juna... Aunty B tace “Mamy meke faruwa...?”
Girgiza kai Mamy tai kana tace “Wllhi ban sani ba, amma kaman muryar Hajiya Haule nakeji... Muje muji ko menene...”
A d’ari suka nufo tsakar gidan saidai yanayin da sukaga Hajiya Haule ciki saida ya firgitasu, fuskarta gaba d’ai kwalliyar ta cab’e, janbaki ya koma kumayi gazal dasu mascara sun zagwanyo zuwa kumatu, tamkar wata dodanniya haka Haule ta juya, ga uwar d’amara data sha uwa zata tashe, uwa Uba ga d’aurin zaninta daidai k’wanjinta ya tsaya saikace mai haye wuta, ga sumarta da sunan anyi retouching dik na shirin biki sun mimmik’e wasu na kallon gabas wasu na kallon yamma saikace wani k’aho....Sai tsima take tana tsalle, Lami kanta da taga Haule a haka saida taja birki ta koma da baya tana dafe k’irji, dan da ace a hanya taci karo da Haule a haka shakka babu zatace gamo tai... Shiko Baba Alhaji sai wani muzurai yake yana sab’a babbar riga....

Mamy da tsananin mamaki take duban Hajiya Haule kana tace “Hajiya lafiya na ganki haka... Meke faruwa ne....?”

Hajiya na jijjiga take fad’in “Inafah lafiya Mariya... Mijinki ya mana wasan k’wallon kwando da yara wacce aka baiwa d’ansa daban wacce ya aura masa daban....”
Mamy da Aunty Bara’atu suka dubi juna....
Girgiza kai Mamy tai “Ban gane ba Hajiya Haule... Mai kike nufi....?”
Duban mijinta dake tsaye bayanta gaho tai kana tace “Kai mata bayani yanda zata fahimta kai mata bayanin yanda k’aninka ya raina mana hankali, mun baiwa d’ansa auren Sahariyya ya aura masa Naja’atu... Toh bazata saku ba dole a warware wannan aure a maida kan Sahariyya....”
Sai sannan Aunty Bara’atu ta murmusa kana ya matso kusan Haule.... Murmushi bai bar saman fuskarta ba take fad’in “Da gaske Hajiya Haule... Toh amma meye abin tashin hankali, naga dai Sahariyya da Naja’atu duk abu guda ne... Maiyasa kuka dage sai Sahariyya ce zata auri Ma’aruf... Shin kunada wata b’oyeyyiyar al’amari ne da bamu sani ba Haule....? Ko kuwa dai akwai wani abinda kuke shiryawa ne...?”

Huci Haule taci gaba da yi tana rarraba idanu lokaci guda take fad’in “Ke Bara’atu ki shiga taitayinki, babu ruwanki a wannan magana, ‘ya’ya dai ‘ya’yana ne kuma kuma mu ba Naja’atu muka baiwa Ma’aruf ba, Sahariyya muka bada kuma dole, ya zama wajibi a warware wannan auren yanzu ba sai ‘yan d’aurin aure Sun gama watsewa ba a d’aura aure da Sahariyya kowa ya shaida....”
Kaman daga sama suka jiyo muryar Mamani tana fad’in “Auren da Allah ya riga ya k’ulla babu d’an adam d’in da ya isa ya warware... Kuma dama su munafukai ranan jin kunya na nan na zuwa masu....!!”

Gaba d’ai juyawa sukai suna duban Mamani dake k’arasowa Abbah na tafe gefenta, idanunsa k’yam kan d’an uwansa Baba Alhaji yanai masa wani irin duba da idanunsa da suka kad’a sukai jazir...
Haba nan fah Haule ta soma shan jinin jikinta... K’ak’aro murmushin yak’e tai kana tace “Au Mamani baki fahimta bane...”
“Sakani na fahimta Haulatu...” Mamani tace tana mai kuma k’arasowa...
Haule taci gaba da fad’in “Wato abinda faruwa jikarki Sahariyya an yaudareta an maida sadakinta na k’anwarta Naja’atu...”
Murmusawa Mamani tai kana tace “Kinyi kuskure Haule, sadaki dai tabbas na k’anwar Sahariyya ya juya amma kuma ba jininki ba....”
Tashin hankali da ba’a saka masa rana.... Da tsananin mamaki Haule ke duban Mamani, murmushin da yafi kama da yak’e ta soma yi... “Kin mance ai Naja’atu jinina ne... Kuma itace k’anwaga Sahariyya....”
Baba Alhaji da hantar cikinsa ke tsananin kad’awa duban mahaifiyar tasa yai kana yace “Mamani Wai meke faruwa ne... Meke faruwa ne a nan... Kai Manu mai ka aikata da ‘ya’yana..? Waye ya baka izinin canza auren yarana...?” Ya k’arashe yana mai isa gaban Abbah cikeda tsananin huci... Shima Abban huci yake yana duban cikin idon d’anuwan nasa, he can’t believe d’anuwansa na jini zai aika masa irin wannan mummunan aiki.... Cikin karaji Abbah yake fad’in “Ka bani mamaki... Ka bani mamaki Yaya.... Shin har kanada k’arfin halin kallon cikin idona....?”

Jikin Baba Alhaji ya soma sanyi yayinda Haule da Lami suka soma duban juna, hawaye masu tsananin d’umi suka shiga gangarowa daga idanun Abbah sanda yaci gaba da fad’in “For years.... Shekara da shekaru kana kallon yanda nida matata muke shan wahala, kana ganin yanda mahaifiyar tasha wahala amma sabida son zuciya irin naka ka zab’i Kaga mun rayu cikin k’unci da d’aurawa junanmu laifi... Yaya ka fad’a min shin mai na tab’a yi maka da tsanani...? Shin k’oyayyar da kake min har yakai ka rabani da gudan jinina....? Shin wane irin zalunci ne wannan....?”

Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.... Kalaman da illahirin mutanen wajen suke nanatawa kenan a zuciyarsu, sauk’in abu mutanen dake wajen duk na gida ne Gwaggwanyen Kazaure ne saiko Aunty Daula dake d’aki da alama bata ma San wainar da ake toyawa ba, tana dai jiyo kaman hatsaniya daga waje amma da shike ta kasance mace maras shiga hurumin da bai shafeta ba shiyasa ma bata fito ba.....
Su Haule da Lami kaw da za’a tsaga jikinsu tabbas da zai wuya a sami jini sabida yanda suka daskare sakamakon jiyo irin kalaman dake fitowa daga bakin Abbah... Kenan hakan na nufin asirinsu ne ya tonu ko kuwa....?
A daburce Baba Alhaji ya soma fad’in “Kai Usmanu yanzu rashin kunyar naka har ya kai ka dubi tsaban idanuna ka dinga jifata da sharruka irin wannan had’ida wasu kalamai marassa kan gado bayan cin amanan da ka min na canza auren yarana da kai.... Ni ban ma san mai kake nufi da wad’annan kalaman naka ba...!!” Kan ya kai aya Mamani dake zuban hawaye ta katsesa da fad’in “K’arya kake ka sani.... Kasan komai Alhaji Alk’ali bazai maka sharri ba... Kaida wad’annan azzalumai biyu ku kukai sanadiyar rabuwarmu da Ma’aruf...” Tai maganar tana nuna Hajiya Haule da Aunty Lami dake faman rakub’e rakub’e tana raba idanu kaman mage a ruwan zafi, ga wane irin gumi dake faman keto mata....

Mamy data tari zancen kaman wani sauk’an guduma kasa fahimtar komai tai sai bin mutanen dake wajen da idanu da take, take kanta ya shiga huya mata, ita bama ta fahimci abindake wakana ba...
Chapter 134 · 0% Book details