← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 198

Sashe 73

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kafin Magaji yayi shiru kuka mai k’arfi ya kufce wa Hafiz... Jikin Magaji yayi sanyi sosai ganin yanda Hafiz ke kuka da iyaka iyawarsa.... Bai hanashi ba bai kuma furta komai ba sai shiru da yayi yana dubansa cikeda tausayawa... Saida Hafiz yayi mai isarsa kana ya tsagaita....
Magaji ya shiga shago ya kawo masa ruwa mai sanyi kana yace “Sha wannan...”
Babu musu Hafiz ya amsa ya kifa kansa bai d’aga ba saida ya shanye tass...
Magaji ya komo gefe da Hafiz ya zauna kana yace “Kayi hak’uri Hafiz ita rayuwar nan gaba d’ayanta daka gani jarabawace, duk wanda kaga yana taka doron k’asa toh fah cikin jarabwar mahaliccinsa yake walau na jin dad’i koko akasinta, Hafiz duk yanayi da kaga bawa na ciki toh ba komai bace face jarabawa, ta ko ina za’a jarabcemu, ta kasuwancimu ne a’a ta iyalanmu ne koko ta lafiyarmu da dukiyarmu, kai komai da kake gani za’a iya jarabtarmu akai, wasu lokutanma har kayi tunanin ko kai kad’ai ake turoma irin wannan jarabawa... Toh fah ba kai kad’ai bane, hasalima idan kaji halin da wani yake ciki zakace naka ba komai bane... Toh shi haka Allah yake gudanar da al’amaransa tsakanin bayinsa, kai k’ok’ari kaci jarabawarka a duk halinda ka tsinci kanka ciki, ba ina cewa lallai sai ka sanar dani abindake damunka bane, amma ka sani a duk lokacin da kake son yin maganar zaka iya samuna, zan saurareka In sha Allah kuma na baka shawari daidai gawardo... Allah shi mana maganin matsalolinmu...” Ya k’arashe yana mai mik’ewa tsaye don attending customer...

Hafiz ya lumshe idanunshi hawaye suka kuma zubowa zuciyarsa nai masa wani irin d’aci, tinda yake a rayuwarsa bai tab’a dayasanin auren Sawwama ba irinta yau, baijin zai iya komawa gida ya fiskanceta a yau sabida tsananin zogi da rad’ad’i da zuciyarsa ke masa, yasan idan ya fuskanci Sawwama a halinda yake ciki yanzu komai ka iya faruwa tabbas zai iya kasheta har lahira, toh amma bazaiso yayi hakan ba sabida wa’azin da Magaji ya masa tabbas ya shiga jikinsa, bazaiso ya kuma wani aikin danasanin ba irin wanda ya taptapka a baya ba... A hankali ya mik’e ya isa cikin shagon ya tadda Magaji kana yace “Magaji kamin alfarma d’aya ka barni na kwana a shagon nan naka don bazan iya komawa gida ba....”
Magaji yace “Ka wuce haka a wajena abokina, gidanmu gidanku ne, ka shigo cikin gidanmu ka kwana har iya lokacin da kake so...”
Hafiz ya dafasa kad’an kana yace “Na gode abokina...”
Magaji ya sakar masa murmushi kafin ya janyo masa kujera ya zauna a cikin shagon....

***

Sallamanta na uku kenan a k’ofar parlorn shiru babu wanda ya amsa, kaman zata juya sai kuma wata zuciya tace ta dai tsaya na wasu dak’ik’ai ko za’a amsa sanin halin matar gidan da yanayinta...
Can jimawa kad’an saiga wata matashiyar budurwa wacce da gani kasan ‘yar aikice ta k’araso ta bud’e had’ida amsa mata sallaman tai mata izinin shigowa...
Aunty Bara’atu ta ida shigowa kana ta tambayi yarinyar ko matar gidan na nan..
Yarinyar ta amsa mata eh tana sama kana ta nufi bene kiran matar...
Kaida ganin gidan kasan anyi wasa da naira sabida tsananin tsaruwa da gidan yayi...
Bara’atu ta d’aga idanu tana kuma k’arewa gidan kallo, cikin zuciyarta take ayyana duk wannan girman gida da had’uwarsa babu magaji cikinta lokaci guda ta rintse idanunta tamkar wacce ta tuna wani abin...
Sauk’owar matar daga bene wacce nake tsammanin matar gidan ne ya sanya Aunty B saurin saita kanta had’ida mik’ewa tsaye...

Cikin taku irinta mata masu ji da kansu da isarsu matar ke takowa cikin parlorn, saida ta iso tsakiyar parlorn tana mai ci gaba da k’arewa Aunty B kallo kana tace “Bara’atu mai ya kawoki gidana... Na zaci ta maki iyaka da nan ne kaman yanda na mata iyaka da yanda nake...”

Aunty da kanta ke k’asa ta share k’wallan dake k’ok’arin kawowa idanunta kana tace “Yaya mun yini lafiya...?”
“Baki amsa min tambayata ba Bara’atu...” Matar ta kuma fad’i
Sai sannan Aunty B ta d’ago tana dubanta kana tace “Zuwa nayi na fad’a miki Ma’aruf ya dawo...!!!”

SameenaAleeyou 📚

*INDA RAI*
_................DA RABO_

60

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

NOT EDITED

Cikin wani irin yanayi matar da Aunty B ta kirada Yaya ta d’ago tana dubanta, ta d’auki lokaci mai d’an tsawo tana duban nata kana tace “Ma’aruf...?!!”
Aunty B ta jinjina kai a hankali....
Tak’aitaccen murmushi matar tayi kana tace “Toh mai nawa ciki... Mai ya shafeni da zakizo musamman don ki sanar dani....?”
Tasan hakan ne zai iya faruwa amma batai k’asa a gwiwa ba tace “Yaya karki mance kusanki da mahaifiyarsa, ki dubi girman Allah ki mance komai ki shirya da ‘yaruwarki, ita rayuwar nan babu tabbas, yau kaine gobe ba kai ba.... Kuma nayi imani badon kin mata iyaka da gidanki ba itada zuri’arta da zaki ganta, ko baki ganta ba nayi imani zata turo ‘ya’yanta.... Yaya girma muke ba k’ank’ancewa ba don Allah mu aje komai duk wasu abubuwa da suka faru a baya mu rik’i junanmu don bamu da wanda yafi mana junanmu....”

“Kin gama.....?”
Yaya Abida tace..
Aunty B ta d’ago tana dubanta....
“Toh idan kin gama ki tashi ki fice min a gida....” Cewar Yaya Abida dake hakince saman kujera....
A hankali Aunty B ta duk’a ta d’au handbag d’inta kana ta dubi ‘yar uwar tata tace “Yayah zan wuce... Bazan gushe ba ina rok’onki kimin wannan alfarma guda d’aya....”
Yaya Abidah ta d’ago tana dubanta, Aunty B taci gaba da fad’in “Ki sassauta zuciyarki ki rungume ‘yan uwanki ki tuna bakida wanda suka fisu....” Daga haka Aunty B bata kuma cewa komai ba ta fice ta bar Yaya Abidah nan tsaye tana mai rakatada kallo har ta b’acewa ganinta....

Washe gari sassafe Nabilah ta dira gidan Aunty B, Aunty Bara’atu batai mamakin ganin Nabilar da safe ba don tasan Nabila da kafiya akan duk abinda tai niyya.... Jigum tai a d’aki tana ida shiryawa zuciyarta naci gaba da sak’e sak’en anya tayi dai dai kuwa...? Anya hakan ya dace ta biyewa Nabilah suyi tafiya bada ilimin mahaifanta ba....? Ta lumshe idanunta a hankali tana kuma tunanin lamarin, a hankali ta sauk’e ajiyan zuciya taci gaba da shirinta domin kaw alk’awari ta d’aukarwa kanta da yardar Allah Mamy da ahalinta bazsu kuma shiga k’unci ba matuk’a tana raye wannan shine dalilinta na ajiye Zulfa’u a gidanta a lokacin da suka rabu da Hafiz sannan zatai iyaka k’ok’arinta wajen ganin Mamy da Ya Abida sun shirya koda ace wannan shine abu na k’arshe da zata aiwatar a rayuwarta... Muryar Nabilah ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi... Tai saurin yafa mayafinta had’ida d’aukan jaka da mabud’an motarta kana ta fito ta iske Nabilah a parlor....
“Kinyi breakfast ne....?” Aunty B ta tambaya sanda take gyara zaman mayafinta tana mai duban kanta jikin madubin consul...
Jinjina mata kai Nabilah tai a hankali kana tace “Nayi Aunty... Ke kawai nake jira....”

Aunty B ta jinjina kai a hankali tana mai k’arewa Nabilar kallo kana tace “Nabilah are you sure of this....?”

Sauk’e ajiyan zuciya Nabila tai hawaye na k’ok’arin ciko idanunta take fad’in “Aunty this is the only way....”
Aunty B ta jinjina kai kana tace “Kinaso muje...?”
Nabila ta jinjina mata kai a hankali alamun eh...
Nan ma kad’a kai Aunty B tai kana ta kamo hannayenta tace “I’m here for you kinji koh.... Ko meye zai faru.... You have your Aunt kinji koh....”
Nabilah ta jinjina kai a hankali kana tace “Na gode Aunty....”
Aunty B ta sakar mata murmushi kana suka sa kai.....

***
Da idanu guda take k’are masa kallo yanda yake shiryawarsa cikin tsanaki, babu abinda ya canzu cikin d’abi’unsa saima k’warjini da kyau da ya k’ara mata, ita kanta ta sani tana son Ma’aruf tana tsananin k’aunar mijinta, wasu lokutan takan rasa maiyasa take masa abubuwan da take masa, kodashike abune a fili, mijinta mai son kula da tarairayane ita kuma sam bazata juri wannan ba, mijinta maison nitsartsiyar macece mai kula da duk wani nauyi da hakki na rayuwar aure da Allah ya shar’anta ga duk wata mace mai aure sauk’esu amma ita sam bazata iya sauk’e wad’annan hakkin ba ciki harda kulada yaransa da tarbiyarsu wanda yaran nan yaranta ne amma ta sani sam basu gabanta kuma bazata iya sauk’e masu hakkinsu dake kanta ba a matsayinta na mahaifiyarsu, fita yawonta da gantalinta ma bazasu barta... Mijinta mai son mace mai killace kanta a gidane kaman yanda Alk’ur’ani mai girma yace _Kuma Ku zauna cikin gidajenku kada kuke fita irin yanda jahilan farko suke fita_..... Duk wad’annan abubuwa da mijin Muhibbah keso matarshi ta kasance cikinsu sam Muhibbah ba haka take ba hasalima d’an kwanaki biyu da tayi a gidan ba tareda ta fita ba duk sai taji babu dad’i...

Mik’ewa tai zaune tana faman mutsuke idanu alamun bacci, ganin yaci gaba da sabgan dake gabansa ba tareda ya kulata ba ya sanyata mik’ewa ta tako a hankali ta tsaya bayansa, a hankali ta rungumesa ta baya had’ida d’aura hab’arta saman kafad’arsa guda tana mai kallon fuskokinsu cikin madubi....
Fuska babu walwala yake k’ok’arin kaucewa yana mai ci gaba da abinda yake, lokaci guda yake furta “I’m running late, people are waiting for me....” Ya k’arashe yana mai d’aura agogo a hannunsa....
Chapter 73 · 0% Book details