← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 182 OF 198

Sashe 182

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Baba Alhaji da hawaye ke gangaro masa kuma mik’a hannu yai kaman zai tab’a Hafiz d’in lokaci guda yake furta “Hafiz... Dah na ka yarda dani... Wllhi bazan tab’a aminta da shirinsu ba... Babu yanda na iya ne... Ka yarda dani Hafiz...!!!”
Tinda ya soma magana Hafiz ke binsa da wane irin duba wanda shi kad’ai yasan irin zogin da yakeji cikin zuciyarsa, ya kasa aminta Wai Uba zai yarda a had’a kai dashi a aikata wannan zalunci mafi muni ga d’an cikinsa....
Hafiz na Hawaye yake fad’in “Ban tab’a dana sanin aikata duk wasu munanan abubuwan da na aikata a baya ba irin yau... Kuma ko ba’a kasheni ba naji dad’i sosai a zuciyata sanin cewa kaida Hajiya yanzu kunji zafin a raba d’ah da iyayensa kaman yanda kukayima Abbah... Wannan bai isheku ba Baba kukayi kukasan yanda kuka had’a aurena da Zulfa’u da zigan Hajiya naita muzgunawa Zulfa’u ina azabtar da ita dan kawai cikan burinku na ganin kun cuzguna ma dik wani jinin Abbah... Wllhi nayi danasanin yi maku biyayya tin fari... Nayi dana sanin auren Zulfa’u balle ku samu daman muzguna mata, wllhi da ace tun fari nasan manufarku kenan da ban aureta ba na k’yaleta tai auren soyayya da wanda take so, amma bawa baya tara sani da Ubangijinsa.... Aurena da ita na cikin k’addarar rayuwarmu... Kuma Alhamdulillahi ko yanzu na bar duniya naji dad’i Zulfa’u zata samu rayuwa mai inganci fiyeda wanda tai baya....Haka kurum sabida san zuciya irin taku kuka tarwatsa mana ahali kuka jefa gaba a tsakaninmu....!” Hawaye basu daina gangarowa a idanun Hafiz ba yake ci gaba da fad’in “Yau ga sakamakon dik munan abinda kuka aikata ko nace muka aikata muna gani... Dan haka kada ka kuskura kai yunk’urin cetona... Idan taimako daga gareka ne ka sani bana so...!!!” Ya k’arashe cikin tsananin huci daidai sanda Sawwama ta shigo a birkice... Takalma a hannu d’ankwali a hannu tamkar mahaukaciya sabuwar kamu.... Birki tai ganin Baba Alhaji duk’e yana kuka ga Hafiz nan gabansa magashiyan wanda badon Farin sani da taiwa Hafiz d’inba da zata iya rantsuwa akan bashi bane canzasa akai.... Wani irin jahilar birki Sawwama taja tana d’ora hannu aka... Dik rashin imaninta da futsararta saida ta firgita ta razana da ganin Hafiz... Take jikinta ya d’auki karkarwa.... Ta nufi Hafiz d’in cikin tsananin tashin hankali, lokaci guda take furta “Hafizi na....!!! Hafizina kaine haka... Haka suka maka..??!”

Banda jahilar duba da Hafiz Ke aika mata bai iya komai, hucin hakinsa kurum kake iya saurarowa sabida tsananin b’acin rai.... Tayo kansa gadan gadan... Daidai lokacin da ya ida tsinka igiyar da aka d’aure masa hannunsa da wata fashesshiyar kwalba da ya saci idanun yaran Babban Duna ya d’auka.... Yana nan likimo yana aika mata firgitacciyar kallo tamkar mayunwacin zakin dake kwanton b’auna ga dabban dake farauta..... Tana isowa Hafiz ya shak’o wuyarta da iyakacin k’arfin da Allah ya masa yana fad’in sai ya aikata lahira.... Yayinda Baba Alhaji ya mik’e yai kansa yana fad’in yazo su gudu kafin su Duna su k’araso... Fincika kurum Hafiz yake yana fad’in sai yayi ajalin Sawwama... Daidai sanda suka soma jiyo sautin jiniyan motar polisawa...

D’aya daga cikin yaran Duna ne ya shigo a birkice yana fad’in polisawa sunyiwa ginin nasu zobe.... Duna da Magajiya dake tattaunawa na sirri a wani b’angare dake cikin kangon ginin shak’o wuyar Magajiya yai yana fad’in “Kin shirya hakan da polisawa ne... Saida kika bari bamuyi fitowar shiri ba.... K’aryarki tasha k’arya babu wanda ya isa yaga k’arshen Duna...!!”

Magajiya na muzurai yake fad’in “Wllhi ban sani ba... Banida masaniya... Ta ya zan maka haka...? Dan Allah ka yarda dani Babba...!!”

Fincikota Babba yaci gaba da yi bakin bindiga manne gefen kanta har suka k’araso yanda su Hafiz suke... Har wannan lokaci Hafiz bai saki Sawwama ba Baba Alhaji na janyesa.... Yaran Duna kaw tuni Sun fita suna fafatawa da jami’an tsaro, sai bata kashi suke tsakaninsu.... Yau dai rana ta b’aciwa su Babba dan layun da suke amfani dasu su ciza bindiga bata shigarsu harsashi bai kamasu idan jami’an tsaro sun tink’arosu basu fito dasu ba, Take Duna ya kuma lalumar aljihunsa... Nan fah yaji wayam, sai yanzu kalaman Hafiz ke dawo masa cewa sai yayi sanadin Capkesa, Wato wannan shine nufinsa, sace layarsa yai sanda yake k’ok’arin shafasa da burin biyan buk’atarsa dashi... Lallai ya yarda Hafiz shu’umi ne na k’arshe.... Babba Ya Muna laluma yaji da gaske fah babu... Wani irin k’ara ya saki had’ida sauk’ewa Magajiya k’otar bindiga a tsakar kanta wanda saida ya sanyata zubewa a k’asa... Da alama dai dubun Duna ne ya cika....

Sanda ‘yan sanda suka k’araso cikin kangon ginin take suka saitasu da bingoginsu suna fad’in “Freeze... Hands in the air.... No body moves..!!!”

Gaba d’aya d’aga hannaye sukai alamun surrender banda Hafiz da ya zube wajen tamkar matacce... Baba Alhaji yai kansa yana ambato sunansa yana rungumarsa ba tareda yabi takan jami’an tsaro dake k’ok’arin hanasa yin hakan ba... Sawwama ma dai zube take wajen tana numfashi da k’yar sakamon shak’eta da Hafiz yai....

Su Magajiya dasu Duna dik haka suka d’aura hannayensu aka... Su Duna dai Babu layun da za’a ciza a gagari bindigar Jami’an tsaro sannan bata kashi da ‘yansanda sukai da yaransa sun kashe yaransa da dama...
Yau saiga Duna masu uniform sun taso k’eyarsa gaba, gashi d’an tsakurkuri sai shed’ana da mugunta... Gasunk’umin d’an ta’addan da ya gagari jami’an tsaro... Wannan shine fa INDA RAI DA RABO.... Engr dasu Detective Najib ne suka k’araso wajen... Kallo guda Engr yaima Duna zuciyarsa ta tsinke... Tabbas dikda tsufa da shekaru da suka nuna a Fuskar Duna bai mancesa ba... Shine dai wancan d’an ta’addan da yai sanadiyar tarwatsewar ahalinsu... D’an ta’addan da ya tarwatsa ahalinsu Ammansa... Tabbas bazai mance fuskar Duna ba sanda suke nemansu mota bayan mota a lokacin da yake rungume da Daula, hanyarsu ta dawowa daga Jada zuwa Kano.... Lokacin da ya fantsama daji shida Daula yana mai k’ok’arin nema masu tsira daga wajen wad’annan azzalumai...

Lokaci guda yaji k’walla na ciko idanunsa da tuni sun kad’a sunyi ja.... A daidai lokacin da Jami’an tsaro suka taso k’eyar babban d’an ta’adda wanda ya shahara ya kumayi k’aurin a fannin garkuwa da fashi da makami a fad’in k’asa baki d’aya Engr ya k’araso garesu had’ida masu umarnin su tsaya...
Babu musu suka tsaya suna masu bin umarninsa domin kaw shid’in shi yai dik k’ok’arinsa wajen ganin an capke Duna an kuma ceto Hafiz kaman yanda yaiwa Akram alk’awari....

Duna ya d’ago jajayen idanunsa yana duban Engr dasu.... Engr dake tsananin huci d’an rank’wafo da kansa yai kad’an dan Duna sam baida tsawo, hannayen Engr hard’e a baya yake furta “Ka gane ni...??!!”

Duna ya kauda kai gefe... D’aya d’ansandan ya buga masa bakin bindiga a k’eya yana fad’in “Yi magana mana..!!!”

Duna yai wani salo da harshensa irin yanda yakeyi kana yace “Ba kaine d’an takaran mujerar gwabna a k’ark’ashin jamk’iyar Adalci party ba...!”

Engr na tsnanin huci yake furta “Ba wannan nakeso ka tina ba...!”

Duna ya kumayin salo da harshensa tamkar tsohon maye ba tareda yace komai ba.... D’ansanda ya kuma darara masa tsawa yana mai buga masa bakin bindiga... Dakatar da d’ansanda Engr yai Ta hanyar d’aga hannu kana ya kuma duban Duna cikin tsananin karaji yake furta “Nasan zaka iya tina Wani Soja a can garin Jada wasu shekarun baya da yaso ya kawo k’arshen ta’addancin ka... Ka kasheshi kabi iyalansa zaka hallak’a... Nasan zaka iya tina Sanda Iayalansa suke tsere maka a tashar mota... Akwai wani yaro cikinsu da kuma k’aramar yarinyar ta goye... Nasan ka tina... Nasan ka tina komai yanzu..!!!” Ya k’arashe hawaye na tsarto masa...

Duna yabisa da kallo shaye da mamaki kana yace “So you’re that boy..!”

Engr ya jinjina masa kai kana yace “And that boy is your downfall... Yanzu zaka girbi abindaka shuka..!!! Ku d’aukeshi daga nan..!!!” Ya k’arashe yana mai kauda kai gefe had’ida k’ok’arin saita kansa sakamakon hawaye dake k’ok’arin ciko idonsa... Juyowar da zai sukai ido hud’u da Mamy wacce basu jima da isowa ba,da alama taji tattaunawarsu da Duna... Kuma itama taso ta ganeshi cikin wad’ancan ‘yanta’ddan...

Mamy na hawaye tana duban Engr, lokaci guda take furta “Ma’aruf... Shine wannan...Shine ya kashe Mahaifin mu... Bazan tab’a mance wannan bak’ar fuskar tasa ba... Shine..!!” Kuka yaci k’arfin Mamy yayinda Haule Ta matso ta rik’eta sosai jikinta a matuk’ar mace itama...

Jinjina mata kai Engr yai yana k’ok’arin daidaita kansa kana yace “Yes Mamy... Shine wancan d’an ta’addan... D’an ta’addan da yai sanadiyar rugujewar ahalinmu...Yau Allah ya kawo k’arshensa shima... Zai kuma girbe abinda ya shuka..!”
Ganin kukan Mamy na k’aruwa ya sanya Abba d’an janyo hannunta kad’an ya nufi mota da ita yana fad’in “Muje ki zauna Mariya... Kukan nan ya isa haka... Yau an kama wanda ya kashe Baba kuma za’a bi maku hakkinku.... Allah baya barin zalinci ya tabbata...!” Haka Abbah yaita bata baki har suka isa mota...
Yayinda motoci jami’an tsaro sukaci gaba da zarya a wajen...
Chapter 182 · 0% Book details