Sashe 130
Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Muhibbah dake zaune gefe tana dubansa tamkar ta zuba ruwa a k’asa tasha dan Farin ciki, a hankali ta taso daga yanda take zaune ta iso garesa, links d’in da yake mak’alawa hannun rigarsa ta amsa taci gaba da saka masa, har lokacin tana iya karanto tashin hankali kwance cikin fuskarsa tasan kawai daurewa yake matsayinsa na jajirtacce mai shirin zama shugaba ga d’unbin al’umma...
“Excellency na yanzu auren Khalid dai zaka tafi kenan....?”
Tamkar bazai amsata ba haka yai, saida ya kwashe wasu sakanni kana yace ta mik’a masa turare... Babu musu ta isa gaban dressing mirror ta d’auko turaren, zai amsa ta girgiza masa kai alamun a’a kana ta shiga fesa masa... K’uri kurum yai mata ba tareda ya tankata ba har ta ida abinda take....
Murmushi saman fuskarta tace “Wow yau d’in kayi kyau na musamman mijina karfa kaje kafi ango yin kyau... Ka ganka kuwa...?” Yanda tai maganar sai taso basa dariya, yasan k’ok’ari kawai take to cheer him up... Gefen fuskarta ya d’an shafa kana yace “Toh ni na wuce... Jalo will drive me....”
Muhibbah ta kuma murmusawa kana tace “Toh a dawo lafiya Excellency na... I love you...”
Bai tsaya amsata ba yasa kai ya fice... Aiko yana ficewa tai tsallan murna ta fad’a kan gado tana juyi, Allah mai iko wato dai cikin sauk’i labarin auren mijinta ya shirirnce, lallai ita d’in mace ce mai sa’a... Wayarta dake gefe ta janyo ta shiga neman layin k’awayenta su Shamzy dan yau dole suyi party na murnan nasarar wargaza al’amarin auren mijinta, yau dole ta had’iyi strong k’wayoyi da zasu kaita can sararin samaniya....
Koda Akram ya gama jera lambobin sai akai rashin sa’a babu network a wajen, gashi yana hango d’ayan ya soma motsawa alamun ya kusan tashi, k’irjin Akram ya kuma bugawa, a hankali ya soma lab’ab’awa ya isa jikin wani dutse da yake hangowa.... Cikin sand’a ya samu ya haura saman dutsen,ya shiga k’ok’arin neman service, sai faman jefa wayar sama yake , da k’yar ya samu ya kamo service..... Bugu d’aya a na biyu wayar ta soma ruri....
Engr dake zaune owners corner cikin hamshak’iyar Ford d’insa nan yaga kira na shigo masa da bak’uwar lamba, wayar da yasan mutane k’alilan ke da lambar... Mamaki ya cikasa, ya k’urama wayar idanu har ta kusan tsinkewa kana ya d’aga....
Daga d’aya b’angaren cikin tsananin tashin hankali Akram yake fad’in “Sir... Sir it’s me Akram...You need to hear me out...”
Gaban Engr ya yanke ya fad’i, cikeda karaji ya dakatar dashi da fad’in “You’ve got some nerve... How dare you Akram.... Bayan dik abinda na gani you still have something to say... After making me look like a complete imbecile, after making the fool out of me... After betraying my trust har kanada guts d’in da zaka kirani... Har kana....”
Katse sa Akram dake waige waige yai da sauri yana furta “Sir you have to believe me... Duka wannan makai nakeyi... Sir you need to read that letter nasan baka karanta ba, amma idan ka karanta you’ll understand me... I wrote everything there... Every single thing... Sir please read that note we’re running out of time...”
Girgiza kai Engr yake cikeda rud’ani yana fad’in “What letter Akram.... Wani letter kake magana....?”
Suna maganan network na seizing...
Akram yaci gaba da fad’in “Sir kar ka tab’a mance wannan... Ni d’in zan iya baka rayuwata....Never doubt that.....”D’if wayar ta katse...
Engr yaci gaba da fad’in “Hello..! Hello Akram... Can you hear me... Hello Akram are you there...?” Shiru ba’a babu amsa...
Cikin sauri Engr ya kuma dialing layin... Saidai ji yai bata shiga.... Kalaman Akram sun d’aure masa kai, wane letter kenan Akram ke magana... Take ya tina katin Bikin Akram cikin envelope Yusuf ya kawo masa, he need to go back and check that envelope.... D’an duban Jalo yai kana yace “Jalo juya kan motar... Mu koma gida....”
Cikeda risinawa Jalo yace “Ok Sir....” lokaci guda yabi umarnin ubangidan nasa...
A can daji kuwa sauk’ar k’asar bindiga Akram yaji a k’eyarsa saida wayar ta fad’i ta tarwatse... D’an ta’addan yasa hannunsa duka biyu ya d’ago Akram ya shiga kilansa kaman an aikosa lokaci guda ya shiga janyosa a k’asa yana doka kirama sauran ‘yanuwan nasa yana sanar dasu Akram tried to escape...Aiko gaba d’aya suka tashi a firgice suka nufosu nan suka had’u suka shiga dukan Akram ta ko ina jini na bin jikinsa gwanin ban tausayi....
***
Kan kace mai ‘yan d’aurin aure sun soma hallara, gidan Abbah ya soma cika da bak’i ‘yan d’aurin aure... Abbah sai sab’a babbar riga yake yana tarban mutane, gaba d’aya k’ofofin babban parlornsa aka hangame... Dik wannan d’awainiya na amsan bak’i da yake bai saka d’an uwansa Baba Alhaji a idanunsa ba saiko sauran k’annensa su Baffah Wada da Baffah Ado saiko Hafiz da bai sama bai k’asa bakinsa ya gaza rufuwa, jinsa yake ko aurensa na fari baiyi Farin cikin da yake ciki a yau ba... Sai wannan nan nan da Abbah yake, su Baffah Wada har mamaki suke irin kwalliyar da Hafiz ya chab’a Magaji abokinsa ma abin mamaki yaketa basa, gashi karaf abokansa ya gayyata, koda Mukhtari ya tanbayesa baya kishi Zulfah wani zata aura sai ce masu yai su tsaya suyi kallon show yanda auren Zulfah zai tashi daga kan munafukin d’an siyasan nan ya dawo kansa... Su Mukhtari dasu Magaji dai kallon ikon Allah kurum suke suna mamakin anya abokinsu bai sami tab’in hankali ba, ta ya za’ace ranar aure an sauya shek’a an dawo kansa... Hafiz yace sudai suyi kallo kawai....
Huzaifah yace “Munaji muna gani muna kuma saurare angon Zulfa’u....” Gaba d’aya abokan suka sa dariya idan ka d’auke Magaji da zuciyarsa ta kasa natsuwa... Anya ba wani mugun abin Hafiz ya k’ulla ba dan yasan yanda ya d’auki Akram da muguwar gaba....Fatansa dai Allah sa ba abinda yake tinani bane....
***
A can gidan Baba Alhaji kaw tuni Hajiya tasa an k’ure mata kid’a dan cewa tai a banbance gidan biki da gidan makoki, harta kwalliyar nan irinta zamani saida Hajiya tasa aka tsara mata itama, ga wata uwar gwaggwaro da aka d’aura mata dan cewa tai yau d’in na musamman ne, gidan shak’e yake da k’awayenta ana tayata murna yanda kasan itace amaryar.... K’awayen Sahariyya kaw su Fa’iza sai dad’a d’aura Hajiya suke keken aljanu suna haukatata suna fad’in irin kyaun da tai....
Najah ta kuma kai dubantaga mahaifiyarta yanda take tik’an rawa tsakar gidan, a hankali ta lumshe idanunta had’ida sauk’e nannauyan ajiyan zuciya... Saida takai k’ofar gidan kafin ta kuma huyowa ta dubi Hajiya, cikin zuciyarta take furta “I’m sorry Hajiya... Ki yafeni....” Daga haka sa kai tai ta fice a gidan....
Sanda ta isa sashen Mamani ta tadda ‘yanmatan gidan sai gugan ankonsu suke tare a parlorn Mamani, su Raihanah su Marliya dasu Sadiya... Sai kacaniya ake baka ma d’aukan zancen kowa sabida yanda hayaniyarsu ya cika wajen....
Najah ta k’arasa tana tambayar Raihanah Mamani...
Raihanah tace “Inaga suna can wajen kitchen itadasu Umman Kazaure kije dai ki duba....” Ta kuma duban Sadiya tace “Sadiya dan Allah ga rigata a goge min...”
Sadiya ta d’an jefa mata hararan wasa tace “A nawa....?”
Karaf Marliya tace “Chab aiko Ya Ma’aruf ne zai biyaki kinsan patient d’insa ce ya hanata aiki....”
Gaba d’aya suka sa dariya Karima na fad’in “Chapd’i aiko ku rufa mata asiri kafin Addah Sahariyya uwar kishi tajiku...
Marliya ta tab’e baki tace “Yo ba sai taji d’in ba wake tsoronta ince dukanmu nan Yayanmu ne, sai mai dan ya nuna kukawarsa akan Raihanah...”
Ita dai Raihanah batace komai ba sai girgiza kai da tai ta janyo hannun Najah tana fad’in “Muje na tayaki neman Mamani....”
A can hanyar k’ofar da zai sadaka da sashen Abbah suka hango Abban tareda Mamani da alama muhimmiyar magana suke tattaunawa... Daga yanda suke k’arasowa suka soma jiyo muryar Abban na fad’in “Wllhi Mamani bansan yanda Yaya ya tsaya ba, abin nima ya bani mamaki ace auren yaranmu nawa har uku ga nashi guda amma ko k’yallinsa babu... Toh ina yaje a irin wannan rana mai matuk’ar mahimmanci....?”
Mamani tace “Alk’ali kasan halin d’an uwan naka, yanzu haka wani sabgan ya shiga amma ina mai tabbatar maka zuwa jimawa zaka gansa....”
Abbah yace “Toh Allah yasa...”
Juyowar da zai ya tarar Naja’atu da Raihanah na gaidashi cikeda risinawa...
Abbah ya amsa masu da sakin fuska, suka gaida Mamani ma....
Ganin dai suna tsaye kaman da magana a bakinsu yasa Abbah cewa “Ya dai yarana akwai wani abin ne...?”
D’an duban Raihanah Naja’atu tai ga k’irjinta dake bugu kana tace “Abbah dama Mamani nake nema...”
Abbah yace “Toh toh kuce Kakar taku kukazo gaidawa ashe ba Abbah ba...”
Gaba d’aya suka d’an saka dariya kana Raihanah tace da Najah bara taje taji halinda gugan kayanta Ke ciki....
Mamani ta dubi Naja’atu tace “Yaya dai ke ‘yar gidan Haule... Inji lafiya...?”
“Lafiya Mamani magana dama nake so na maku...”
Abbah da tuni ya sab’a babbar riga zai shige Naja’atu tai karaf tace “Abbah maganar harda kai...”
Abbah ya juyo cikeda mamaki, itama kanta Mamani mamakin ne ya cikata...
Abbah yace “Toooh, amma lafiya kuwa Naja’atu koh...?”
Naja’atu tace “Abbah akan b’acewar Ya Ma’aruf ne... Abbah nasan su waye suka b’atar dashi, kuma har yanzu ma sunada wata shiri...””