← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 198

Sashe 122

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sayayya iri guda Mamy taiwa Raihanah da Marliya, jin yarinyar take har cikin zuciyarta... Haka nan Allah ya jefa mata k’aunar yarinyar had’ida tausayinta musamman idan tuna cewa ita d’in marainiyace batada mahaifiya a raye...A hankali ta kuma sauk’e ajiyan zuciya sanda ta jiyo sallama daga parlor tamkar ta ‘Yaruwarta Bara’atu...Mik’ewa tai had’ida amsa sallamar kana ta nufi parlorn.... Aunty Bara’atu ta gani zaune dirshan saman kujera... Gabanta ya tsinke ya fad’i, ta k’arasa a hankali tana mai dafa kafad’ar Aunty Bara’atun...
“Bara’atu...” Mamy ta ambata cikin tsananin sanyin murya...
D’ago kai Aunty Bara’atu tai tana duban Mamy da idanunta da sukai matuk’ar raunana....
A hankali Mamy ta zauna gefenta jikinta na kuma yin sanyi...
“Ke d’in baki kasance mai rauni ba cikinmu... Dik yanda akai akwai abindake damunki... Ki sanar dani ‘yar uwata, shin kinje kinga Yaya Abida ce...?”
Wannan karon d’agowa sosai Aunty B tai tana duban Mamy sai kuma ta kauda fuska gefe, lokaci guda take furta “Mamy haka munaji muna gani zamu bari a aurawa Ma’aruf yarinyar da bai k’auna, kuma munsan yanda mahaifiyarta da ita kanta Sahariyyar suka baida gudummawa wajen tarwatsa rayuwar Zulfa’u... Anya bamu yi kuskuren aminta da wannan auren ba.... Shin bamuda wata hanya da zamu dakatar da wannan aure...?”
Sauk’e ajiyan zuciya Mamy tai kana tace “A koda yaushe mu kasance masu kyautata zato Bara’atu... Kuma babu yanda banyi da Ma’aruf ba cewa karya tilastawa kansa wannan aure amma sai cemin yai yaji ya gani zai iya.. Toh kinga kuwa banida ikon hanawa haka nan mahaifinsa ma... Addu’a ita kurum zamu ci gaba da yi, dik abinda yake alkhairi ne Ubangiji ya tabbatar dashi... Sharri kuma ya kawar mana... Na sani Bara’atu kin damu dani kin damu da ahalina... Hasalima kinfi fifita damuwarmu sama da taki damuwar, gidan duniyar nan babu abinda zan iya biyanki dashi saidai na miki fatan dacewa na kumaci gaba da addu’an Ubangiji ya karkato miki da hankalin mijinki gareki...” Fasali Mamy ta d’anja kana taci gaba da fad’in “Dik yanda ‘yaruwa ta k’warai takai Bara’atu kin kai... Kina tare dani a dik sanda nake tsananin buk’atarki, yayinda ni bani kasancewa taredake lokutan naki buk’atun... Daidai da rana guda baki tab’a juyama d’aya daga cikin ‘yanuwanki baya ba... Kin rik’i amanar Yaya Abida dika cewa tasha tureki daga gareta dik a sabida baki yanke alak’a dani ba, kina nan a tsakaninmu kina nuna mana zallan k’auna.... Ki amshi girman daga garemu, kece kike kula damu a maimakon mune zamu kula dake... Bara’atu bansan ya rayuwata data iyalaina zaya kasance ba da ace na rasaki...” Ta k’arashe cikin tsananin Murya irinta mai kuka...
Saurin rik’o hannayenta Aunty B tai idanunta suna yunk’urin kawo ruwa itama, lokaci guda take girgiza kai tana duban Mamy
“Ki daina fad’in haka Mamy... Abinda ya dace shi nakeyi.... Hakan ce ya kamata ya kasancega ‘yanuwa.... Mamy ina k’aunarki ina kuma k’aunar zuri’arki... Ina kuma fatan Allah yaci gaba da tsareki da kuma ahalinki...Sannan bazan gushe ba ina addu’an Allah ya had’e kan ahalinmu....”
Lokaci guda tasa ‘yar yatsanta ta goge hawayen da ya d’igo mata, take suka rungume juna hawaye na zarya daga idanunsu...
A haka Zulfa’u da dawowarta kenan daga wajen aiki ta taddasu... Jiki a sanyaye tai sallama ta shigo parlorn....
“Mamy.. Aunty..!”
Ta furta cikin tsananin sanyin murya...
Take ko waccensu ta soma k’ok’arin saita kanta....
Aunty B ce tai k’arfin halin d’aura murmushi saman fuskarta, tana mai duban Zulfa’un take fad’in “Wannan zuwa wajen aikin ya kamata a dainashi haka nan... Kamata yai ace yanzu kuna gida a killace daga ke har Nabilar, dama zuwa nai na tattareku ku koma can a soma maku gyara dan mun gama magana da mai gyaran amaren zatazo cikin satin nan....”
Zulfa’u dai murmushin da tafi kama da yak’e tai idanunta naga mahaifiyarta dake matsan sauran k’walla...
A hankali ta isa aje handbag d’inta saman kujera kana ta k’araso tana mai tsaresu da idanu...
“Aunty Wai meke faruwa ne...? Kuka fah na tadda kukeyi...” Tace sanda take zama gefen Mamy da har lokacin bata d’ago sunyi ido hud’u da d’iyar tata ba...
Murmusawa Aunty B ta kumayi kana tace “Yo ba dole muyi kuka ba Zulfa’u... Irin wannan ni’ima da Ubangiji ya lullub’emu dasu, ace zaka aurar da d’oyoyi har biyu lokaci guda kinga kaw ai kuka ya zamto mana dole, kukan farin ciki muke d’iyata....Allah ya cika min buri ya amshi addu’ata bazaki koma gidan wancan shashashan tsohon mijin naki ba, kinga kuwa ai dole na zubda hawayen Farin ciki...” Murmushi tai tana mai duban mahaifiyarta da itama murmushin ne saman kod’edd’en fuskarta...
Allah sarki Bara’atu, ita dai komai sai ta nemo masa mafita, bazata tab’a ganin damuwa a tattareda Mamy da ahalinta ba har sai tasan hanyar da zata biyo dan taga ta taimaka wajen kawar masu da wannan damuwar... Idan da ace duka ‘yanuwa haka suke tabbas da an sami k’aranci gaba da muguwar k’iyayya tsakanin Al’umma....

Tuni su Marliya da Raihanah sun soma shirye shiryensu, wani d’auki suke kaman ba’a tab’a buki a zuri’ar tasu ba, kodashike dole ma suyi d’auki domin kaw dangin ba’a tab’a Bikin bane tinda auren Hafiz da Zulfa’u da akai a baya shida babu duk d’aya ne, domin kaw biki ne akayi shi ba cikin farin ciki ba, dikda d’auki da suke basa d’aukin Bikin Aunty Sahariyya da Ya Ma’aruf sanin cewa su d’in two different people ne, hasalima tausayinsa suke kamilin mutum irinshi bai cancanci mata irin Sahariyya ba... Dik wannan d’auki da suke sam Naja’atu batayi, babu wanda yasan maike damunta harta Hajiya babu yanda batayi taji meke damun Najah na amma Najah tak’i fad’i mata komai, Sahariyya da k’awarta Fa’iza kaw cewa sukai hassada ce kawai irinta Naja’atu taso ace itace zata auri Ya Ma’aruf ba Addarta Sahariyya ba... Ita kaw Najah bata cewa komai saidai ta tab’e baki, daidai da d’inkin anko d’inta ma bata bada ba, ita kad’ai tasan mai take sakawa cikin zuciyarta..

***

Washe gari tin sassafe Baffah ya tasa k’aninsa mai bi masa a haife wanda ratan shekara d’aya ne zuwa biyu tsakanin su cewa sai ya masa rakiya zuwa Kano...
Baba Ali badon yaso ba yai shirin rakiwa d’an uwan nasa... Suna tafe saman kwalta Baba Ali Ke fad’in “Wllhi badon ka tak’urani ba BillahillAzim bazanje ko ina ba... Kai nifa tin sanda aka soma yima mutane d’iban awakai saman kwalta na daina zirga zirga dik k’aunan yawo irin nawa... Yo Allah na tuba idan mutanen nan sukai wuf dani uban waye zai biya kud’in fansata... Kai ni bama wannan ba, yanda nake fata zalla sai k’ashi suka min bugun zazzab’en dawa ai harta k’asusuwana baza’a samu ba....”
Baffah na dariya yana buga kan steering yake furta “Kai mutumina... Haba Alaji Aliko, Ali zaki mazajen fama...Wai ina kurin da cika bakin ne....”
Baba Ali yace “Kai inaa da ne wllhi....Maza suna daji yanzu...”
Baffah ya kuma tintsirewa da dariya... Wannan na d’aya daga cikin abinda yasa yace Baba Ali ya masa rakiya, don tafiya saida irin su Baba Ali ko babu komai zakaci dariya, Baba Ali irin mutanen nan ne masu k’anan jiki da tsananin barkwanci...
A haka suka isa garin ta Dabo, kai tsaye gidan Engr Ma’aruf Mutallab suka nufa kaman yanda Daddy ya sanarma Engr d’in da zuwan nasu, tuni dama anyi shirin tarabansu... Tarba ta karramawa akai masu a gidan Engr, Muhibbah bata sama bata k’asa sam bazakace itace bace yanda ta kwantar da hankalinta take gudanar da al’amranta... Abin har baiwa Engr mamaki yake tamkar ba Muhibbar da ya sani ba, batun k’arin aurensa sam bai d’aga mata hankali.. Ko dan bataga auren ya tashi gadan gadan bane, maybe shiyasa sam bai dameta ba... Sosai yake jin dad’in canzawar da Muhibbah tai, har k’asan zuciyarsa yake jin dad’in hakan, fatansa Allah sa hakan mai d’orewa ne...
Abinka da wanda sam bai faye zama ba bacin gaisuwa da sukaidasu Baffah bai kuma saka su idanunsa ba, hidimominsa da sabgogin gabansa sunada yawa...
Dik kyau da tsari da gidansu Khalid kedashi sai sukafi santin wannan gida da aka sauk’esu, kai da gani kasan Nira ta tsufa hannun masu wannan gida, sashe guda na bak’i aka masu masauk’i babu abin buk’atar da babu... Baba Ali ya fito yana k’arema tangamemen sashen da aka masu masauk’i kallo, “dank’ari mak’ari Wato dai gida ne saikace otel d’in k’asashen turawa” Yai maganar yana kewaye k’ayattacen swimming pool dake a b’angare guda cikin sashen....
Harda buga tsalle yana ihu yake fad’in “Kai Baffah ai sai kace min tafiyar k’asan waje zamuyi tikitin jirgi ne kurum ya rage mana.... Kaga gida tamkar a turai.... Wai ma tsaya meye alak’an mutumin nan dasu Khalid ko d’iyarsa yake nema... Nima na samu amin connection tinda naga auren yanzun dik connections ne....”
Darawa Baffah yai kana yace “Wllhi idan zaka sakamin bindiga bansa alak’an Daddy da wannan mutumin ba, kasan manyan mutanen nan k’ila ko kasuwanci ko siyasa ta had’asu tinda Engr Ma’aruf cikakken d’an siyasa ne mai neman takaran kujerar Governor...”
Jinjina kai Baba Ali yai kana yace “Hakk’un... Ai cewa nake nan ne gidansu yarinyar da sai nace ashe da Ammi batasan waye d’anta Ke nema ba tinda nasan halin matar sam tak’i jinin talaka...”
Dubansa Baffah yai kana yace “Har yanzu ma batasan da batun auren ba kuma nasanka da zuba da b’arankan baki Ali, dan girman Allah na rok’i arzikin ka ko Khalid kada yasan wannan batu balle ya isa ga mahaifiyarsa...”
Baba Ali ya zaro idanu waje “Toooh babban magana... Wannan wane irin aurene haka b’oyewa tamkar wani abin k’i... Naga dai aure shelansa ake ba b’oyesa ba....”
Baffah yace “Babu ruwanka kaidai kawai kayi abinda na sakaka....”
Hannu yasa yaja fatun bakinsa alamun ya ja masu zip ya saka masu sakata kana yace “Bakada matsala my lips are sealed...”
Baffah ya jinjina kai yace “Good...!”
Zuwa dare suka kira Sameer suka sanar dashi suna Kano, Sameer yace babu matsala gobe idan Allah yakai rai zai masu jagora zuwa gidansu don dama shi suka kira suka sanar dashi zasuzo gaisuwa a madadin Khalid tinda Daddy ya aike Khalid d’in wani waje bazai sami zuwa ba sannan ga lokacin biki na kuma k’aratowa....
Chapter 122 · 0% Book details