← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 187 OF 198

Sashe 187

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga sama tana sauraro murya kamanta Siyama, dan Siyama muryarta mai d’an gwab’i ne sannan irin mutanen nan ne masu magana da sauri sauri....

Jim kad’an taji an bud’e k’ofa, Ijlaal ce ta fad’a jikinta cikeda murna, Nabila ta rungume yarinyar cikeda Farin ciki itama, nan take labarta mata tareda Aunty Siyama suke da Uncle Sameer zasu wuce Kaduna tare, ama Uncle Sameer na mota yana jiransu bai shigo ba... Nabilah ta d’anja hancinta tana tambayarta su Aunty Daula dasu Humaira.. Nan take sanar da ita Aunty B ma Ta wuce Kano yau... Su Daddy dasu Ammi da Aunty Daula kawai aka bari gida... Ijlaal sarkin surutu haka taita cika Nabila da zance dikda yau d’in Nabilar ba wani biyeta take ba dan itama fama da kanta take...

A can parlor kaw zaman Siyama da kad’an saigasu Kubura da Karima Shayibu ya kawosu nik’i nik’i da food warmers, Kubura sai tura Karima gaba take dan bata mance b’aran b’araman da tai jiya ba... Allah ya rufa mata asiri suka tadda Siyama nan gidan dan wllhi da a k’ofa zasu saka su juya... Suka gaidashi Siyama na tambayar waye ya kawosu.. Karima ce ta iya bata amsa Kubura kam tuni ta nufi dining table da flask d’in dake hannunta...

Khalid ya saki tsuka a hankali kana yace “Wai ita Ammi dole sai ta Aiko yarinyar nan ne.. Mai yasa ku baku taho da breakfast d’in ba...?”

Siyama ta d’an dara kad’an kana tace “Kan hanya fah muke nace bara naima Nabilah Sallama, Partner na waje na jiranmu daga nan Daddy zamu biya mu d’auka...”
Khalid yace “Wane Daddyn...?”
“Uncle ba, Daddyn Sameer”

Jinjina kai tai daidai sanda su Kubura suka taho zasu wuce suna yima Siyama Allah kiyaye..
Ta amsa tana zolayar Kubura da fad’in “Mutuniyar na zaci Ammi ta turoki gidan Yayan naki ki masu zaman d’aki ne...” Ai wuf Kubura ta fice kaman wacce ake turata..

Siyama kaw sai dariya take tana duban Khalid da ya sha mur, lokaci guda yake furta “Wllhi ku kesa yarinyar nan tana raina mutane...”

Dariyar Siyama Ta kumayi kana tace “Haba Khalid yo Kubura har abin fushi ne, yarinyar dama batasan maike mata ciwo ba, dik abinda take shiririta ne kawai had’ida k’auyanci da ya kasa sakinta... Kaga bara nai sallama ma Nabilah mu wuce, na bar partner nata jira na...”

Dining table d’in ya nufa yana duba breakfast d’in yayinda Siyama ta nufi upstairs..

Zaune ta tadda Nabilar Ijlaal na faman cikata da zance... Nabila ta d’anyi k’ok’arin gyara zamanta suna gaisawa da Siyamar cikeda mutunta juna,Siyamar nai mata sannu da jiki dan Khalid ya sanar da ita Nabilar bata jin dad’i tana upstairs.. Ita dai Nabilah sadda kanta k’asa kurum tai cikeda kunya...
Siyama taci gaba da fad’in “Toh Nabilah ga amanar baby brother na, a kula min dashi please... Khalid yana sonki, despite dik abubuwan da muka mishi wajen ganin mun rabaku, he never gave up sabida yana sonki... My brother deserve all the happiness in this world... Ku d’in kun cancanci junanku... Ina maku fatan alkhairi da zama lafiya...”
Ta k’arashe hannayensu cikin na juna...
Murmushi Nabilar ma tai kana tace “Mun gode Addah Siyama, ke Allah ya cika gidanki da Farin ciki da kwanciyar hankali...”
Suka kuma rungumar juna sallama... Nabilah ta d’an dafa tana k’ok’arin mik’ewa danyiwa Siyama rakiya...
Saurin zaunarta Siyama tai a hankali tana mai furta “Ina zakije a haka, a’a a’a na yafeki rakiya wllhi... Abinci ma ya kawo miki nan dan bazaki iya sauk’a ba... Ijlaal come let’s go my baby...!”
Ijlaal ta ije wayar Nabila da take game ciki taima Nabilar sallama suka fice Siyama na d’aukeda ita... Basu tadda Sameer parlor ba da alama yana can waje wajen Sameer... Can d’in kaw suka taddasa sukai sallama baki d’aya Khalid d’in na masu fatan sauk’a lafiya....

***

KADUNA

SameenaAleeyou📚

*INDA RAI*
_................DA RABO_

*110*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

NOT EDITED

Mummy da Raihanah sukai masu tarba, yanzu kam Raihanah Ta k’aware sosai a fannuka daban daban da ya shafi tattalin gida da na iyali, dole ne ma Mummy ta zage dantse wajen koyawa matar Sameer tattalin iyali da kula dan bazataso a maimaita abinda akai da Siyama ba... Wajajen isha suke shirin tafiya gidansu yanda Sameer ya zaunar da Siyama yake sanar da ita cewa yanzu basu kad’ai bane...
“Siyama a lot of things have to change, but I want you to always remember that I love you... Dan nayi aure ban daina sonki ba Partner... Har yanzu dai ked’in ce Siyamata.. My partner...!” Ya k’arashe yana kamo hannayenta cikin nasa...

Murmushi Ta saki a hankali kana tace “Partner, na fahimci komai, kuma in sha Allah zaka sameni ina mai yi maka biyayya... Dik abubuwan da nayisu a baya bazanyi repeating d’insu ba yanzu in sha Allah, nai maka alk’awari... Iyakacin abinda nakeso shine ka yafe min... Please forgive me Sameer..!!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya...
Yai mata k’uri yana dubanta k’aunarta na ratsa zuciyarsa, a hankali ya furta “Come here..!” Ta k’arasa cikin jikinsa tana mai lumshe idanu...

Bayan Mummy ta ida shirya Raihanah da yi mata ‘yan nasihohi da tsananin mamakinsu Siyama suka gani ta k’araso ta kamo hannayen Raihanah lokaci guda take furta “Are you ready... Welcome to our home Raihanah...!”
Raihanah ta d’an d’ago idanunta masu zuban hawaye tana duban Siyama...
K’ak’aro murmushi Siyama tai kana tace “Partner yana jiranmu, Mummy idan kin mana izini zamu tafi...!” Ta k’arashe cikin rawar murya dikda hawaye dake k’ok’arin gangaro mata...

Lokaci guda Mummy ta isa ta rungume Siyama cikeda tausayin Siyamar take sanya mata albarka dan yau d’in harta gafaran Raihana saida Siyama ta nema.... Mummy ta had’esu su duka biyun ta rungume tana kuma saka masu albarka had’ida ‘yan nasihohi, shin wa zai kaita Farin ciki idan matan d’an nata suka had’e kawunansu haka suka zauna lafiya, tabbas zaman lafiyarsu shine cikan buri da kwanciyar hankalin d’anta Sameer....

Mummy na tsakiyarsu suka k’araso parlorn yanda suka tadda Sameer da Ijlaal suna zaune suna jiran fitowarsu, Ijlaal na zaune bisa laps d’insa, a hankali ya mik’e yana duban kyawawan matan nashi yanda Mummy ke tsakiyarsu rik’eda hannun ko wacce daga cikinsu....
Wasu irin k’walla ne yaji suna k’ok’arin ciko idanunsa, shin dama irin wannan rana na zuwa...? Which of the Favours of your Lord will you deny..!
A hankali ya tako har gabansu rik’eda hannun Ijlaal, lokaci guda Mummy ta d’ago hannayen nasu ta dank’a saman na Sameer... Ita kanta Mummy hawaye ke gangaro mata, a hankali take furta “Sameer these two beautiful women amanace a wajenka, kar ka tab’a manta wannan kaji d’ah na... Ubangiji ya maku albarka ya yakwataku da zaman lafiya da kwanciyar hankali... Allah ya albarkaceku da zuri’a d’ayyiba....”
Tinda Mummy ta soma magana kan Raihanah na k’asa hawaye na d’igo mata yayinda Siyama ta kafe Sameer d’in da idanu itama hawayen take... Sameer yai k’ok’arin saita kansa kana ya rungume Mummy yana mai furtawa a hankali “Thank you for everything Mummy.... I can’t ever repay you for everything you’ve done to me.... I’ll always hold you here...!” Ya k’arashe yana mai nuni da k’irjinsa...
Kumatunsa ta d’an kama irin yanda take masa tin yana yaro kana tace “Silly... Oya kuje dare yanayi....”
Gaba d’aya murmusawa sukai kana suka kuma yin sallama... Har mota Mummy tai masu rakiya yanda Siyama da Ijlaal suka shige baya yayinda Raihanah Ta shige gaba Doctor Sameer Ke driving...
Hiran Ijlaal da Siyama shi yai keeping nasu company cikin motar dan Amarya Raihanah kam bata iya cewa komai, tinda ta shige motar kanta kife yake tana twisting ‘yan yatsunta....
Saida suka biya mall ya d’anyi masu window shopping had’ida d’an abubuwan tab’awa kana suka nufi gida... Wani ikon Allah Wai Siyama ce ta zage damtse tana ta kintsa gidan, dik yanda Raihanah taso tai aiki Siyama ta kasa ta tsare ta hanata, suka tsuke da riga da wando itada Ijlaal sai faman aikinsu suke, Ijlaal d’in ta dage ita taya Siyama take.... Rabin aikin nasu wasa ne,Ijlaal ta d’an yarfawa Siyama ruwan dake hannunta tana fad’in “Catch me if you can...!” Haba nan fah Siyama tai jifa da sandar mop ta shiga bin bayan Ijlaal a guje, yarinyar sai k’yak’yata dariya take suna zaga parlorn....
Ba Sameer da shigowarsa kenan yai tsaye yana dubansu cikeda jin dad’i harta Raihanah dake k’ok’arin taimaka masu da aikin sosai suka bata sha’awa tai tsaye tana dubansu saikace uwa da d’iya... Ganin Sameer da tai ne ya sanya gabanta wane irin fad’uwa, tai saurin mak’alewa jikin staircase tana lek’ensu daga nan...
Aiko Siyama na hango Sameer tai wajensa a guje had’ida watsa masa ruwan hannunta itama... Taci gaba da bin Ijlaal a guje tana fad’i wa Sameer shima ya kamata idan zai iya....
Aje bags d’in hannunsa yai ya shiga folding hannun rigarsa yana mai furta “Let’s see Partner...!” Take ya shiga bin bayansu shima yanda suka ci gaba da zagaye parlorn gaba d’aya... Tsantsin moping ya kusa kada Ijlaal ta fad’o kan Siyama yayinda Sameer ya tarosu gaba d’aya suka fad’o kansa... Gaba d’ayansu suka ci gaba da k’yak’yata dariya Ijlaal na fad’in she won....
A kunne Siyama ke rad’a masa “Partner muje ka shirya...!”
Duban idanunta ya d’anyi, tai k’ok’arin k’ak’aro murmushi tana mai jinjina masa kai....
A tare suka mik’e ita dashi kana ta dubi Ijlaal tace “Princess wait for me here, abar aikin nan haka sai na dawo... Just watch your cartoon ok...!”
Jinjina mata kai Ijlaal tai yayinda Sameer ya bud’e shopping bag guda ya ciro mata ice cream yana mai fad’in asha kad’an kar ai mura... Ta amsa tana tsalle had’ida masa godiya....

***
Chapter 187 · 0% Book details