← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 198

Sashe 1

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[25/11, 16:42] +234 703 745 3539: *INDA RAI*
_.............DA RABO_

*01*

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

*Dedicated to my Trio*♥

Cikeda risinawa matashi mai kimanin shekaru 30 a duniya ya d’ago yana duban Dattijon mutumin mai kimanin shekaru 58 zuwa da tara kana yace “But Daddy.....”

Katsesa yayi da fad’in “No SAMEER I don’t want to hear anything, what’s gotten into you Son.... Haba Sameer ni nasan ba haka na tayar dakai ba... Abinda nakeso da kai ka tashi ka tafi gidan Uncle d’inka ka basa hak’uri sannan ka d’auki matarka ku tafi magana ya k’are....”

Jinjina kai yayi kana yace “Ok Daddy I’ll do as you say....”

Murmushi Dattijon yayi kana yace “That’s my boy Allah ya maka albarka....”

“Ameen Daddy...” Ya fad’i yana k’ok’arin mik’ewa had’ida fidda wayar salulansa daga aljihu....

Satan kallon sashen da Mummynsa ke zaune yayi aiko banda uwar harara babu abinda take aika masa.... K’arasawa ya d’anyi had’ida risinawa kana yace “I’m sorry Mummy... I promise this will never happen again in shaa Allah.....”

Jinjina kai tayi kana tace “I hope so, Ace aure ko wata biyar mai kyau bakuyi ba an soma samun sab’ani irin haka ai babu dad’i... Dama naji batu mai dad’i kaji koh...”

A hankali ya jinjina kai kafin ya fice daga parlorn....

Motarsa ya nufa ba tareda ya kula da Malam Sallau dake gaidashi ba...

Ya jima k’ofar gidansu Siyama yana tunanin ta yanda zai soma bada hak’uri don sam hakan ba d’abi’arsa bace idandai ba ma iyayensa bane, a hankali ya rintse idanunsa had’ida furta “Goodness! Where do I start....”

K’aran da wayarsa tayi ne ya sanyasa zaro wayar daga aljihun gaban rigarsa daga d’aya b’angaren Sultan yace “Doc we’ve an emergency here at the hospital, Sameer we need you right away....”

Shafe goshinsa ya d’anyi kana yace “Is my presence really necessary, just do what you can, I’m dealing with another problem here...Please...” ya k’arashe yana lumshe dogayen idanunsa masu yalwan suma....

Fuzar da iska Sultan yayi kana yace “Sameer it’s a boy.... He suffered a multiple deep burns... I’m afraid he’s dying...” Ta cikin wayar yake jiyo sautin kukan yaron wanda k’unan wuta ya masa babu dad’i, cikin sauri Sameer ya juya kan motarsa yana fad’in “I’ll be on my way....” Cikin sauri ya karya kan motar had’ida ficewa daga gidan mai gadi na faman d’aga masa hannu alamun a sauk’a lafiya....

****

*Kano*

Cikin sanyin jiki suka shigo parlorn ko wacce tayi jigum jigum, budurwa mai kimanin shekaru 23 a duniya ne ta soma yab’e baki tace “Wllhi Allah Abbah shi yake biye Mamani take abinda taga dama, haka kurum mata ta tayar da bori wai zata tafi tabi MA’ARUF ni so nake wata rana a barta ta gwada fita nemansa ace yau shekaru 26 babu mutum babu labarinsa toh ta ina zaka soma nemansa, sai anyi magana ace tsufa ke d’awainiya da ita, mtsww...” Ta k’arashe tana jan tsaki....

D’ayar mai kimanin shekaru 19 tace “Wllhi Adda Nabila ni bana ganin laifin Baffah Wali idan ya fice mata a giya, kiga dai duk jikokin gidan nan rankatataf d’inmu ban cire kowa ba harda ke mai sunanta bata damu da kowa ba kullum damuwarta Ma’aruf yaron da tun yana shekara 4 ya b’ace sai anyi magana itada Mamy suce INDA RAI DA RABO, Allah na tuba da ace yana raye tsawon shekarun nan ai da ya bayyana mana....”

K’aramar cikinsu mai kimanin shekaru 16 tace “Ahtoh sai anyi magana tace Babban Jika... Mu da yake Yayanmu uwa d’aya uba d’aya ma bamu kaita damuwa b.....” Had’iye kalaman nata tayi cikeda k’unk’uni tana duban wacce ke faman narka mata mugun kallo da alama bata jima da shigowa parlorn ba

“Aunty Zulfah ina yini....”

Gaba d’aya sauran biyun suka juyo suna duban sashen da k’anwarsu ke gaisuwa....

Ganin yanayin Addar tasu wacce ke sanye cikin kayan Bautar K’asa ya sanyasu shan jinin jikkunansu....

Ba tareda ta amsa gaisuwar tasu ba fuska a tsume tace “Mamy fah...?”

Nabila mai bi mata a haife ne tace “Suna can sashen Mamani suna bitan karatunsu na aikin lallashi...”

Girgiza kai kurum Zulfah tayi kana ta nufi k’ofa zata fice Mas’udah mai bin Nabila a haife tayi saurin katseta da fad’in “Allah Aunty Zulfah Mamani abinda take yayi yawa naga dai idan da akwai wanda b’acewar Yaya Ma’aruf zai damesa bayan Mamy da Abbah toh ya kamata ace sai kece tinda ranar da aka haifeki ranar Yaya ya b’ata....”

Nabila ta k’arada “Shiyasa Mamani tafi tsanar Addah sama da kowa a jikokinta a nata tunanin sanadiyar haihuwar Addah Yaya ya b’ata...”

“Ya isheku haka...!” Zulfa’u ta katsesu kafin taci gaba da fad’in “Ku bazakuyi hankali ba, ana cewa yaran Abbah sunfi kaf yaran gidan nan tarbiya amma kuna nema ku shafawa iyayenku bak’in fenti... Sai mai idan Mamani ta nuna damuwarta kan missing grandchild d’inta, badai jikanta bane toh ina ruwanku, idanku baku damu dashi ba sabida baku sanshi ba sai ku k’yaleta ita ta nuna damuwarta, wllhi kunji na rantse kar na sake zuwa gidan nan naji kuna k’anan maganganu kan wannan al’amari kunajina koh...”

Ciki ciki suka amsa kafin Marliya k’aramar cikinsu ta k’arada “Aunty Zulfah yau ina kika baro Kausar naga baki kawota nan gida ba yau....”

Harara kurum Zulfah ta watsa mata kafin ta fice ta nufi sashen Mamani....

****

*Kaduna*

Fitowarsa kenan daga surgery wayarsa dake bisa teburinsa ta d’au ruri.... Dafe kansa yayi ganin mai kiran ba kowa bace illa Mummynsa sannan ta kirasa yafi sau a k’irga, shaf ya mance bai kashe wayar salulansa ba sanda zai shiga aikin domin kuwa akasarin lokuta idan zai shiga aiki kashe wayarsa yake donma kar a nemesa....

A hankali ya d’aga wayar had’ida zama cikin kujeransa....

Kafin ya sami zarafin magana Mummy ta soma balbalesa....

“Sameer ya maka kyau, nace ya maka kyau... Da ka fice zaka gidan Hajiya Faridan gidan uwar wa ka tafi....? Shine sabida tsabagen wulak’anci zaka barsu suna jiranka, ko kasan cewa harta Alhaji Madi bai fice ba ya tsaya jiran zuwanka amma ka kama ka watsa mana k’asa a idanu.... Ya maka kyau Sameer nasan haka zakayi wllhi da ban bari an baka auren Siyama ba....”

Tinda ta soma magana bai katseta ba har saida takai aya, a hankali ya soma fad’in “Mummy calm down please, this isn’t good for your blood pressure.....”

A hasale ta kuma cewa “Don’t ask me to calm down, jininan ma ya hau mana duk ba kaine sila ba....”

A hankali ya shafi goshinsa can k’asan mak’oshinsa ya furta “Goodness..!” A fili kuwa cewa yayi “But Mummy cikinku babu wanda ya damu yaji daga gareni, babu wanda ya damu if I’m also suffering, Mummy this isn’t easy for me either.... Kin sani Mummy kinsan ina son Siyama kuma auren soyayya mukayi.... Kwana biyun nan bansan meke damunta ba... Amma koma meye na miki alk’awari I’ll save our marriage cos I still love my wife, l love her so much...” Ya k’arashe cikin sanyin murya....

Jinjina kai Mummy tayi cikeda jin dad’i kana tace “Yauwa D’an Albarka haka nakeson ji maza ka wuce gidan Uncle Madi d’in daga asibitin zanyi waya wa Hajiya Faridan na sanar da ita aiki ne ya rik’eka a asibiti amma gaka nan zuwa....”

Bai iya amsa Mummy ba har suka ida wayar, mik’ewa yayi had’ida d’aukar wayarsa da key ya nufi duba patient d’insa kafin ya fice...

Sam baisan Siyama nada kishi haka ba, ya kamata ta fahimci yanayin aikinsa da kuma za’a iya kiransa emergency ko wani lokaci.....

A farfajiyan gidan ya iske Alhaji Madi zaune saman kujeru na shak’awata jarida rik’e a hannunsa, don haka kai tsaye cikeda risinawa ya nufi sirkin nasa kuma amini ga Daddynsa...

Daga can d’an gefe ya durk’usa kana ya soma gaida sirkin nasa.... Fuska babu walwala ba kaman yanda ya saba masa d’inba ya amsa...

Sameer ya d’anyi gyaran murya kana yace “Uncle dan Allah ayi hak’uri bana gida Siyama ta fice kuma koda na kira layinta bata d’aga ba amma In sha Allah hakan bazai k’ara faruwa ba...”

Cikeda k’osawa Alhaji Madi ya amsa da “Allah sa kada hakan ya kuma faruwa, a dinga kulawa Sameer, kasan cewa muna tsananin k’aunar Siyama kuma bamu k’aunar ganin kukanta, sanin kanka ne Sameer my children are my life, I can do anything for them ko menene, Siyama da Khalid sune farin cikin rayuwata ka fahimta...”

A hankali Sameer ya jinjina kai kana yace “Ayi hak’uri Uncle za’a kiyaye In sha Allah....”

Alhaji Maina ya kuma jinjina kai had’i da bud’e shafi na gaba a jaridar tasa kana yace “Ka k’arasa ciki ka samu matar taka....”

Cikeda risinawa ya kuma mik’ewa had’ida godiyawa Alhaji Maina kafin ya nufi sashen Ammi mahaifiyar Siyama....

“You know what sis... I think you’re been too impulsive....”

Matashin Saurayi mai kimanin shekaru 26 ya fad’i yana mai duban Addar tasa wacce ratansu shekara guda ne tak....

Pillow dake gefenta ta d’auka ta jefi dashi kana tace “You stay out of this Khalid... Ni ba sa’arka bace...”

Fitoda manyan idanunsa masu rikita ‘yanmata yayi kana yace “Oh really Sis.... Alright, fine, ni shawari kawai nake badawa, stop being so paranoid, your husband would never cheat on you, I know Sameer so well, kuma da kika aureshi kin mance wanene shi, kin mance wa kike aure...? Well, Incase you forgotten Sister, he’s a Doctor, a surgeon for that matter... Emergency zai iya faruwa ko wane lokaci kuma za’a kirashi, so sister dear you’ve to get this through your head.... Ok...” Ya k’arashe yana janyo bakin gelan kitson kalaba manya dake zube kanta...

Duka ta kai masa yayi saurin kaucewa a daidai sanda sukaji sallaman Sameer....

Daskarewa Siyama tayi had’ida lumshe idanu sakamakon jiyo k’amshin mijinta da tayi wanda tayi kewarsa a kwana guda tak...

K’arasawa Khalid yayi yana fad’in “Yauwa gwara da Allah ya kawoka, you better take your wife with you before she breaks all my bones da wannan hannun nata....”

Murmushi kurum Sameer yayi kafin ya mik’awa Khalid hannu sukai masabaha...

Bayan sun gaisa Khalid ficewa yayi ya bar ma’auratan guda biyu...

Kaman munafuki ya k’arasa cikin parlorn yana mai sand’a idanunsa kan matarsa tsan tsan k’aunarta na d’awainiya dashi....
Chapter 1 · 0% Book details