← Book details Mundo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 187

Sashe 87

Mundo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin kallo take masa zuciyarta tamkar ta fasa kirjinta ta fito tsabar bakin cikin da ya mamayeta, karan farko data ji bazata iya jure kalaman da yake jefanta dashi ba, tace
Da abinda kake kallona kenan?

Kalaman da kake min kwanaki dalilinsu kenan?

Araab ya sake
aure fuska yace
Kokarin denying kike bayan gashi na gani zahiri?

Hannu kawai tasa ta bu
e motar cikin
acin ran da ita kanta bata san tana dashi ba, kallonta yayi yace
Ina zaki?

Bata kula shi ba ta fita, yayi saurin fitowa cike da mamakin ta, hannu yasa ya riko hannunta ganin ta soma tafiya kan titi, sai yanzu ya kula babu takalmi a kafarta.

Meye hakan kikeyi?

Yaushe kika fara taurin kai ina miki magana bakyaji?

Hannunta ta fisge tace
Please let go of me Ya Araab.
tana sake yin gaba ta cigaba da tafiya.

Mamaki ya kamashi wai yarinyar nan ce take mai magana haka?

Sake fisgota yayi yana dawo da ita baya da karfi
Ni kikewa magana haka saboda kokarin kare martabar aurena da nake da nake kokarin yi?

Kallon sa tayi kawai yaga ta saki wani murmushi tace
Martabar aure ni har yanzu banga muna rayuwa ta aure ba, bansan wace martaba kake magana ba.

Matsowa yayi daf da ita, ya
ago habarta ya saka idonsa cikin nata yace
Shiyasa kike kula wani kenan?

Janye jikinta tayi tare da juya masa baya tace
Tun tasowata dama bansan da
in rayuwa ba, tun tashina nake fuskantar kalubale da zarge-zarge komai nayi bana daidai a idon mutane, sai dai abu
aya yanzu ke sanya naji natsuwa sanin tsakanina da ubangiji." Araab kalamanta yaji sun ratsa shi yace
Dawo ki shiga mota."
Ba tare da ta kalle sa ba tace
Please ka barni naje wurin Kawuna dan Allah koma menene kayimin daga baya amma ina tsananin bukatar ganin sa nasan halin da yake ciki.

Get in ko haka zakije a kasa ba takalmi?

Gefen hannu tasa ta share hawayenta, batasan ta bishi amma ba yanda zatayi dan batasan hanyar komawa ba balle ku
in da zatayi amfani dashi ta koma, haka ta juya ta bude murfin baya ta shiga, sam take jin bata son zama kusa da Araab din, Wani haushi ya sake kama shi yaso mata magana sai ya basar ransa na kara baci tuna haduwarta da Bilal,
Tafiya suke motar tayi shiru kowa da nazarin da yake a zuci, Araab tunani yake ganin me zataje yi wa Kawun nata ko zata sanar dashi ne meke faruwa, idan hakane zai fi so dan ya zama dole ayiwa tufkar hanci tsakanin ta da Bilal.
***************
o motar Araab na parking bakin gidan Jauro, tayi saurin bu
e kofa ta fito fatan ta kawai ta shiga taga Jauro, Araab ne ya rufa mata baya.

Kai tsaye falon ta shiga kamar an jefo ta ko sallama babu, ganin Jauro zaune Salame na gefe suna
an hira jefi-jefi dan yau ya mata kyautar dubu biyar ya samu ku
i na wani aiki da yayi, shine ta
an sake yau suke ta
hira,
Kawu akace baka da lafiya kayi hatsari za
a wuce da kai asibiti yanzu?"
Salame tayi caraf tace
Kaji yar
muguwar fata ki ga masifa akan ki, kin wank jefo mana gida kamar an koroki.

Jauro kallonta yayi yace
Haba Salame ki tsaya mana muji, kinsan dai ba zatayi karya ba.

Tsaki tayi tace
Wannan makirar da bata son mu bata kaunar mu?

Sam bata kula da Araab dake tsaye daga waje ba, tsabar takaicin Mun
o da yadda ta kullace ta, Jauro ya dubi Mun
o yace
Waya sanar dake haka?

Yaya Bilal ne.

Salame ta tashi tsaye tana nuna Mun
o tace
Ke ki fita a idona kinji sharrin naki har ya kai can, a yaushe Bilal yaje gidan da har ya sanar dake, yaron da ko yaje ba barinsa ake ya shiga ba saboda mugun halinki kin samu gidan daula kin yadda dangi?
o tace
Allah Gwaggo da gaske nake, ni kaina bazan yiwa Kawu wanann fata ba, kema kinsani.

Dalla rufe mun baki, kafin na fasa shi.

Araab shiru yayi yana nazari, daga bakin kofa dan duk yana jinsu.

Ganin Araab tai tace
Haba ango ni ko cikaken sunanka ban sani ba ai in da kara ko ita in batada zumunci kai sai ka duba ka dinga abinda ya kamata.

Gaishesu Araab yai, Jauro cikin girmamawa ya amsa, yace
Ashe abinda ya faru kenan?
kawai yace dan baisan me zaice ba.

Bilal yana ajiye Meenal ya biya yasha wiwi dinsa kana ya taho gida, tun daga tsakar gida ya soma jin hayaniya ya shigo yana cewa
Ahh nan kuka taho?

Jauro harararsa yayi yace
Kai akan wane dalili zaka cewa Mun
o nayi hatsari?

Kirji ya dafa tamkar mace yace
Ni a yaushe haba popcy taya zan maka wanann fatan na rasa wama zance sai kai mahaifina tilo?

Araab kansa ne ya sake
aurewa, Bilal ganin Araab ya kalli Mun
o yace
Haba Babe ba sai kinyi karya ba dan kare kanki akan haduwar mu.

Araab idonsa ya runtse yana jin wani zafi a ransa tamkar ya kaiwa Bilal naushin da ko da wasa ba zai kara kiranta babe ba, ya dake yana dunkule hannun sa.

Ganin yanayinsa da Jauro yayi ya sa ya tashi ya zabgawa Bilal mari, ya nunashi da yatsa yace
Bana son shashancin banza da wofi wallahi ka shiga hankalin ka, idan baka fa
a mata ba haka kawai ba zatayi karya."
ah ya da haka, daga ya fa
i gaskiya, karya ne ba son junansu suke ba, har an saka musu rana kayi kulla kulla kaga kudi aka canza zance." Jauro mamakin Salame ya kamasa sosai yace
Ki ji tsoron Allah Salame." Tsaki tayi tace
Gaskiya ce ba
a so kuma sai an fa
a ehe!

Ta juya kan Bilal tace
Kai wuce ciki muje, haka kawai baza'a saka a gaba ba.

A ranta ta kuduri ba zata kyale Mun
o ba tasan tabbas Bilal zai aikata amma haushin abinda ta mata yasa ta mata haka, sannan tace
Mu zuba ni dake bani zakiyiwa bakin cikin ba samun arziki ba kema ba zaki zauna kici shi ba wallahi
Tayi kwafa.

Jauro kallon Araab yayi wanda zuciyarsa ke wani zafi, yana tsugune ya dunkule hannayensa, Mun
o kam na gefe sai hawaye take na jin sharrin da suke kulla mata shikenan zasu kara saka Araab yana mata kallon yar
iska,
Dan Allah kada ka
auki maganganunsu, ina da kyakkyawan shaida akan Mun
o ba zataci amanar auren ka ba, haka wallahi babu soyayya tsakaninta da Bilal, kayi hakuri ka
auke ta ku koma gida, nagode sosai da kulawa.

Araab kai kawai ya jinjinawa Jauro dan shi kansa bai gama tantance a wane yanayi yake ba, Ya juya ya fita Mun
o tabi bayansa tana jin
duniyar ta mata zafi lokaci
aya, yayin da wani sashe take jin haushin kallon da Araab da ke mata mumunan zato.

Araab suna shiga falo ya saka key, ya nufo inda Mun
o take wacce tayi hanyar
akinta, hannu ya kai ya jawota da karfi yana mata wani irin mugun kallo yace
Ana ganinki shiru shiru ashe kin wuce tunanin me tunani, wane baki gare ki yanzu na kokarin bada kariya ga ganki?

Juya masa baya tayi tace
Allah shine shaidata, bansan me zance ba balle na bada kariya.

Ta wuce abunta bata jira ya sake cewa komai ba, Araab wani irin huci yake ya koma kan kujera falo ya zauna tare da
aura tafin hannunsa kan goshin sa yana jin yadda kansa ke sara masa, shi yarinyar nan kewa magana haka?

Sa
arsu Ikram?

Shi babu yaro karamin ma daya rainashi kamar ta.
o kuwa
aki ta shiga ta fa
a kan gado ta saki wani irin kuka mai cin rai.
***************************
Meenal rai kwal ta isa gidansu farin cikin plan
inta ya tafi daidai, daga ganin yadda Araab ya fisgi Mun
o tasan ba za
a kwashe lafiya ba.

Bata tarar da kowa gidan ba, sai mai aikin su, hakan yasa ta wuce
akinta ta kwanta, dama duk bayan kwana biyu Mumy nasa masu aiki su gyara
akin su wanke toilet gudun kar yayi k
ura sosai.
in wanka tayi ta kwanta taja bargo dan son nunawa iyayenta bata da lafiyar, Mumy da Alhaji Hussain tare suka fita ya nuna mata wani shago da ya
auka haya zai zuba kaya, ita dai kawai ta nuna masa farin cikinta a zahiri ne amma a ba
ini fargaba ce a ranta na yadda yake kashe ku
i ba tare da yasan meke faruwa ba, hatta wani filinshi siyarwa yai.

Suna dawowa gida a falo suka zauna, Meenal taji dawowarsa wayarta ta jawo tama Mumy text
Kizo
akina Mumy na dawo bani da lafiya sosai."
Ido ta zaro tamkar zasu fa
o kasa tace
Kin dawo?"
Bata san maganar ta fito fili ba,
Wacce ta dawo?

Alhaji Hussain ya tambaya yana kallon ta, bata da wani zabi tace
Meenal." Zumbur ya mi
e yace
Meenal ta dawo?

Akan wane dalili?

Tana ina?

Yai maganar duk a rikice.

Mumy cikin sanyin jiki tace
akinta.

Cikin damuwa na ganin yanayin Alhaji Hussain na
acin rai sosai,
Meenal Meenal Meenal
ya soma kwala kiranta cikin daga murya.

Tsoro ne ya shigeta bata san sanda ta dirko daga gadon ba ta fito falo, bai tsaya jin komai ba ya soma kikkifa mata mari, mari uku ya mata a jere, ya rufeta da duka gaba
aya ya fita hayyacinsa, yace
Uban wa ya dawo dake ba tare da sanin mu ba?

Kasa magana tayi sai kuka,
Zaki bu
e baki kiyi magana ko sai na b
alla ki?"
Kukan ta na karuwa tace
Yaya Araab na biyo.

Ba tare kuke dashi acan ba?
Chapter 87 · 0% Book details