← Book details Mundo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 187

Sashe 1

Mundo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Root Entry
WordDocument
0Table
Data
Normal
Default Paragraph Font
Normal Table
No List
(MAI HAKURI)
Na Zee Yabour
Ayusher Muhd
RUGAR JIJJI
Hayaniya ke tashi ta ko'ina wanda ta karad'e rugar, mata da yawa ta k'aramin ginin katangar gidajen su suke lek'e, a duk sanda kaga hayaniya irin wannan to tabbas ba lafiya ba, sannan matsalar dai mutum
aya ke jawo ta.

Yau ma hakan ce ta kasance, gungun maza ne sanye cikin falmaran da akai da yadi, daga yanda suke hargagi ka
ai zaka shaida sun shirya ma fitina haka ransu a matuk'ar b'ace yake, Kowannen su
auke
da makami yake wanda ke nuna alamar sun shirya lahanta wanda ya tab'o su.

Daga masu fatanya, sai wasu d'auke da gora, wasu da adda.

K'ananan mazan dake cikinsu sune masu d'auke da muciya, wani ma murfin tukunya ya kinkima.

Shigar su da fuskarsu ka
ai zaka kalla kasan fulani ne (Hmm mutanen mu)
Uku daga ciki ne suka fad'a cikin gidan.

Matan dake zaune tsakar gida sukayi saurin fad'awa bukar su, kowaccensu na neman wurin b'oyo dan ganin mazan nan cikin yanayin nan kadai zai tabbatar maka ba lafiya ba.

K'aramin gida mai ginin laka da bulo na kasa suka ja burki suka tsaya, suna zazzare ido suna aikawa junansu sakon yanda zasu farma abin, ba tare da b'ata lokaci ba suka soma kaiwa randunan kasar dake waje bugo ji kake tass, tana fashewa ruwa na zubowa, suka sake nade hannu suka fara sarar sandunan dake jikin ginin wanda ake shanye ko kuma a d'aure tunkiya in anada bukata, yi suke tamkar zasu ruguza ginin, gidan kewaye yake da bukkoki wanda yawancinsu iri daya ne, sak ginin ainihin fulanin ruga.

Gaban bukka d'aya suka nufa, Cikin hargagi suke kiran sunan "MUN
O!!"
Cikin karaji da ihu suke ta ke kiran sunan kai kace zasu fito da makogaransu.

Yarinya ce yar' kimanin shekaru 13 a duniya tana kwance, tayi firgigit ta tashi daga nauyayyen baccin da take wanda ya
auketa ba tare da ta shirya ba, tsabar gajiya, daga can cikin bacci taji kiran da farko ta d'auka mafarki ne sai dai yanda taji ana kiran ya sa ta zabura.

"MUN
O!" Suka k'ara kira cikin d'aga sauti da murya.

A rikice ta diro daga saman gadon k'arfen dake d'akin ta shige k'ark'ashi gadan jikinta na kyarma da tsuma.

Sanyin kasa na sake ratsa jikinta kasancewar yanayi ne na hunturu, k'aramar
riga mai kama da vest dake jikinta ya k'ara sa sanyi shiga jikin ta, duk da ba kasafai fulani suka fiya jin sanyi ba, amma yau har cikin jikinta takejin sanyin.

Wuri d'aya ta k'udundune, tasa hannu biyu ta toshe kunnuwanta tare da runtse idanunta.

Ba yau ce rana ta farko ba da take gamowa da irin haka ba, sai dai na yau ya sha bambam da sauran ranaku, Bata tab'a jin hayaniya irin wannan ba.

Sunan ta da suka k'ara kira cikin karaji, shine yasa hawaye soma zirya kan kumatun ta "Baffa kazo na maka gani na k'arshe na tabbata yau ba zasu barni ba." Abinda take fad'a cikin kuka kenan, har lokacin idonta a runtse, tana cikin tsoro da firgici.

"Aradun Allah Mun
o in kika bari na shigo baki bude ba sara
aya zan miki na aika ki lahira, tsinanniya, haihuwar Allah wadarai, gara mu kashe ki kowa ya huta." Wani daga cikin su ya fad'a.

Can k'arshe gadon ta sake shigewa ta manne da bango jikinta na kyarma kai kace cikin kankara aka sakata.

Wata dattijuwa ce ta taho a guje ta karaso tana hade hannayenta "Laddo na rok'e ka
da girman Allah kuyi hakuri, ku tsaya ai magana, yarinyar nan wallahi ba yadda kuke tunani take ba."
Tai maganar tana zubewa gaban wanda ta kira da Laddo.

A fusace yayo kanta rike da fatanyarsa kamar zai sareta yace "Wallahi Danejo in kika sake magana zan mik'a ki barzaho daga ke har jikar taki, abu
aya zan muku shine ki ce bak'ar kadarar can tazo ta tsallaka yarinyata da aka haifa, dan wallahi in har ta mutu kuma kunyi bankwana da duniya."
Danejo tamkar zata mishi sujada tace "Laddo yarinyar nan wallahi bata je bukar ku ba yau kwana arba'in kenan da kuka hana ta fita tunda matarka ta haihu....."
Wani daga cikinsu yayo kanta d'auke da adda tuni ta zame ta fad'i k'asa tare da runtse ido ya kalleta yace "Rufe muna baki munafukar Allah, Kowa yasan jikar ki mayya ce, mutane nawa tana lashewa a rugar nan, maitar ta
ai ba sai taje guri ba take kama mutum ko kin manta wata uku kenan da ta kama yarona, wallahi yau sai mun zubar da jininta."
Suna kaiwa nan suka hankade Danejo suka sake nufar bukar suka fara sara fatanya.

Ai tana ganin haka ta sake kudundunewa tana sake sa kuka tare da kiran sunan Baffa...

A fusace Laddo yace "Aradun Allah kika bari na fasa ginin nan baki fito ba sara d'aya zan miki na mikaki barzaho." Samari da yaran dake gun sai dadi sukeji ai gwara a zubda jinin ta ma kowa ya huta.

Sake shigewa kasan gadan tai ta cusa kanta cikin cinyoyinta ta sake toshe kunnanta tana hawaye.

Da gudu wani magidanci wanda bai gaza shekara arba'in ba ya shigo yana haki ya had'a gumi tamkar ba lokacin sanyi ba, d'akin ya nufa kai tsaye wasu daga cikin mazan suka finciko shi da k'arfi sukai baya dashi, idanunshi yayi ja yana girgiza kai da alama ba k'aramin gudu yayi ba, cikin tashin hankali yace "Dan girman Allah Laddo kuyi hak'uri, wannan ba shine mafita ba asibiti ya kamata muje ."
"Yi mun shiru makiri ai duk kaine sila, bakin ku d'aya, kai ka kawo mana fitina cikin ruga, ka fito da tsinanniyar
arka muje ta tsallake min yarinyata, dan wallahi in y'ata ta mutu kaima sai ka rasa taka."
Maccido gwiyoyinsa ya kai k'asa ya kama k'afafun Laddo yana rokar shi sai dai fir yaki yace a fito da Mun
o, dole Macci
ya nufi
akin cikin tsananin tashin hankali.

" Zuciyarsa yake ji kamar zata fashe shikam sai yaushe Mundo zata fita daga mummunan zargi na mutanen rugar nan, sai yaushe zata samu 'yanci tayi rayuwa kamar sauran mutane, tun tana jaririya ko dabba ce ta rasu sai ace itace, ko ciwon kai mutum yake sai ace itace, kome ya samu wani a rugar itace, saboda wani dalili nasu wanda yafi alak'anta hakan da son zuciya irin na d'an adam.

A hankali ya nufi kofar da suka kusa balleta takaici ya sake kamashi, ya tura kofar yana sake danne zuciyarsa.

Cikin sanyin jiki ya kutso kai k'aramar bukkar tasu, D'akin yabi da kallo bai ga alamar ta a ciki ba, Cikin raunannen murya yace "Mun
o kina ina?"
"Baffa" Ta fad'a da dasashhiyar murya mai kamar rad'a wacce ke nuna tasha kuka.

Cikin rawar jiki ta fito k'ark'ashin gadon ta k'ank'ame shi.

Bayanta ya shafa a hankali yana jin hawaye na tausayinta na taho mishi yayi k'ok'arin mayar dasu.
agota yayi a hankali yana kallon yadda har lokacin hawaye basu fasa zirya kan kumatun ta ba.

A hankali ya share mata hawayen, Ya kama hannun ta zuwa waje, yana rike da ita tana tana sake ra
ewa ta jikinsa.

Tana ganinsu ta fara ja da baya, tana k'ok'arin b'oyewa bayan Maccido.

Suna ganinsu suka hau zage-zage shidai kawai rike yake da ita baice komai ba.

Laddo yai kwafa ya nunata da yatsa yace "Shegiya bakar mujiya, wuce muje ki tsallaka mun 'ya ta"Cewar Laddo cikin d'aga murya, Mun
o jikinta kawai ke kyarma, haka suka taso su gaba, Haka suka cigaba da tafiya suna hargagi da zage-zage.

Laddo takaici ya kamashi yanda yaga tana tafiya sumi-sumi, yace "Munafuka kamar mutuniyar kirki, dole kiji tsoro dan wannan karon kin tab'o abunda zai yi ajalin ki
idan kina cin mutane ki kwana lafiya d'iyar Laddo ta wuce maitar ki, bakar kadara." Har suka iso bukkar Laddo yana faman mita da hargagi, Kuka da ihun da suka fara jiyowa yasa Laddo sakin fatanyar sa ya k'arasa ciki da gudu.

Kallon
mutanen yai a birkice yace "Kukan me kuke?"
"Ta cinye ta Laddo" Cewar d'aya daga cikin matan tana kururuwa, Wata kururuwa Laddo yayi yace "Ta me?"
Tsohuwar da ta sanar dashi ta fashe da kuka ta zube a kasa.

"Aradun Allah yau sai na kashe Mun
o." Ya zaburi fatanyarsa yai waje a guje.....

Macci
o ya fakaici idon mutane da hankalinsu yayi kan abinda ke faruwa yaja hannun Mun
o suka dinga gudu sai da sukaje can bayan gari, Suka tsaya k'ark'ashin wata bishiya har lokacin jikinta bai saki ba tana cikin tsoro da firgici sai ajiyar zuciya da take faman saukewa.

Hawaye yaji ya zubo ta matse-matsin idanunsa, wani irin bala'i ne wannan?

Yarinya an hanata tayi rayuwar data dace?

Tunda ta taso bata mu'amala da kowa, hatta k'awa bata da ita a rugar, babu mai barin
an shi yazo kusa da ita, yara idan sun ganta guduwa suke dan iyayen su sun musu hud'ubar mayya ce zata cinye su, tun tana k'arama sai dai tayi wasan ta ita ka
ai, yanzu har fita ma an hanata, kullum tana
aki.

Zancen saurayi kuwa babu shi duk da kyawun da Allah ya bata, ga uwa uba diri tun yanzu mazaunanta sun fara bayyana, ga k'irjinta da ya soma cika kamar ba
ar shekara sha uku ba, sai dai duk da haka ta zama tamkar mujiya a cikin rugar babu mai sha'awarta balle wani ya furta mata kalmar so, Ko a cikin bukkar su daga mahaifinta sai kakarta Danejo take jin sanyi wurin su.

Kallonta yayi cike da tausayawa yana bin jelar gashinta da kallo wacce ta sauka har saman kafad'a, wanda kitson ne a kanta manya da Danejo ta samu ta mata, shima ranar k'in cin girkinta akayi saboda ta tab'a kan Mun
o a cewarsu sunaci mutuwa zasuyi.

A hankali ta
ago idanunta cikin kuka tace "Baffa Dan Allah ka nisanta ni da rugar nan, ka kaini can wani garin na zauna ni ko ni kadaice aradun Allah zanyi zamana, na gaji da nan, ba mai sona anan, na zama abun gudu da k'i.

Har dabobin rugar nan sun fini daraja da nutsuwa.
Chapter 1 · 0% Book details