← Book details Mundo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 187

Sashe 36

Mundo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Araab ya fito a angon shi, hula yasa akan kwantaccen sumar gashin kansa, ya
aura designer agogon sa wanda ya dace da farar fatar hannun sa ya sake haska shi.

Duk yana wanann shirin ne saboda farin cikin Ummy, ya fesa turarunkan sa masu k
amshi da tsada.

Wayarsa ya kalla wanda kiran Meenal yafi a irga, fitowa yai ya nufi cikin gida gun Ummy ya nuna mata yayi abinda ta umarceshi dashi sannan ya wuce.

Yakai hannunsa zai bu
ofa yaji Farouq na cewa "Ummy Allah abinda mutanen nan suke ya ishemu haba dan Allah kinyi jere basu ko yi godiya ba sai ma ce miki sukai ai dama ke ya kamata kiyi dole sannan yanzu dan wulakanci kanwar mamanta ta kira waya tace wai zata turo list
in abubuwan da taga ba'a sa ba?

Sannan wai ma basuji kunyar cewa a canza
akin Ya Araab ya dawo na Meenal ba?

Shi ya koma can?

Wai Ummy auren nan dole ne?

Allah ni sai na fa
awa Ya Araab."
Hannunsa ya zare daga jikin kofar yasa a cikin aljihunsa, kawai ya juya yabar gun,
akinsa ya koma ya zauna bakin gado, ya
auki robar lime
insa dake bedside drawer ya kafa kai bai ajiye ba sai da ya shanye duka.
(Ko tsamin baya ji)
Pen din hannunsa ya shiga jujjuya da yatsinsa biyu, zuciyar sa ta harzuka sosai wanda yake jin tamkar ya same su yace ya fasa auren, ba zai iya jure a wulak
anta masa mahaifiyarsa ko a nuna mata iyakar ta ba, zai iya d
aukar mataki akan ko waye.

Ummy ta kalli Farouq tace "Ku zama masu hakuri da bin komai a hankali, daga anyi auren ba shikenan ba tunda ita tana son mijinta?"
Farouq takaici ya sake kamashi yace "Ummy Allah abin ya isa haka."
"Nikam ko zaka fara kai Ikram da Ilham sai ka dawo ka
au Mun
o lokacin ta shirya?

Dan kar a samu matsala irinta jiya da sukai ta cewa ansan securities
in daga nan ne amma ba wanda yazo da wuri sannan wai abubuwa dayawa babu kuma ba wanda ke kusa da zasu tambaya."
Takaici ne ya sake rufeshi yace "Sai su suyi ko ba
yar su ke auran ba?"
Kallon sa tai hakan yasashi yin shiru tare da mikewa yace "In an gama mata ta shirya dan ina dawowa zan kaita."
Kai ta
aga ba wannan bane ka
ai dalilin da yasa takeso su bar gidan bataso Jauro yazo susan abinda ake ciki.

Mun
o kam bata tarar da kowa a gidan ba, haka ta fito ta biyo hanya tana mamaki ko ina suka yaje?

Sai kace a riga da kowa yake fita sanda yaso? taga gidansu Ikram ba'a haka.

Tana shigowa shi kuma ya shiga mota kenan, kallon kayan Meenal yai dake gefen motarshi sam ya manta da d
azu ya shiga dasu, wanda ganin su ya tado masa b
acin rai, zuciyar sa na harzuk
a, tada motar yayi yaja ta da karfi.
o ganin mota ta taho da karfi yasa ta matsa da sauri gashi ba gurin
uya dan a farfajiyar gidan take tsakiya.

Sai dayazo kusa da ita ya tsaya, hakan yasa ta dubebice, nan ya bu
e glass
in mota ya cilla mata jakar kayan yace "Take it to Ummy." Ba tare da ya kalle ta ba, ya sake fisgar mota da k
arfi, tabi bayan motar da kallo har lokacin gabanta fa
uwa yake.

Yanayin yadda yayi maganar da sauri, da tsabar tsoron sa da take yasa sam bata ji me yace sosai ba, yaji kamar yace "Ummy kamar kuma take it Ummy itadai koma meye ta gane bata yai inji Ummy."
aukan kayan tayi tace "Kayan da Ummy ta
inkamin ne to meya kaishi hannunshi?" Kai ta girgiza tace "Kila ko Ilham ce."
Ciki ta shiga ta sanar da Ummy taje basa gidan sannan ta gode sosai da kayan data bata.

Ummy tace "Yi maza ki shirya Farouq yanzu zai dawo ya kaiki, Meemaglam tana ciki kije ta gyaraki kafin ya karaso."
Da sauri ta mike ta hau sama.

Ganinsu Ilham basa nan yasa ta nutsu kwalliya ta gama mata sannan ta kalli kan gado inda taga lace na anko wanda su Ikram suka ajiye mata.

Kallon Meeman tai tace "Oh kaya biyu gareni?" Tayi maganar tana ciro wanda Araab ya bata.

Meema cike da mamaki ta kalli ha
e tsadadden
inkin tace "Gaskiya kisa wannan yafi ha
uwa, wai zabgi, yasha tsada kam daga gani."
o ta zura riga sai dai bata kamata ba wanda hakan ya sake yi mata dadi, Meema tace "Kai!

Gaskiya kinyi kyau, sai kace kece amarya?"
Dariya tai ita kanta ta shiga jujjuya wa dan tabbas tasan tayi kyau sosai ba na wasa ba.

Ta fito falo wanda taci karo da Farouq baki ya saki yace "Mun
o wannan gayun fa?

Ai sai a kasa ganeki."
Dariya tayi tare da rufe fuska, "Ina kika samo kaya kamar amarya?"
Cike da jin dadi tace "Ummy ce tace a ban."
Kai ya jinjina a ranshi yace Ummy na son yarinyar nan kayanta haryafi nasu Ilham.

Sun leka zasuwa Ummy sallama sukaga tana sallah yace "Muje na ajiyeki zan dawo na shirya kinsan mu na kusa da ango shiin mu daban yake."
Ta fito suka shiga mota, sai murmushi take tana jin lallai yau daban take.

Hmmmmmm
*****
Meenal wannan kiran shine na kusan hamsin data mai, hawaye ne suka fara neman zubo mata, me Araab yake nufi?

Gashi har an taru babu kayanta ba labari, waya su Mumy suke ta mata akan ta zo saboda akwai baki da sukazo daga Abuja sunaso su wuce.

Haka ta sa aka
auko material data
inka wanda take planning zasuyi party bayan biki ta saka, tayi kyau sai dai bakin ciki da takaici yasa ko ganin kyan bata gani ba, dan wancan taci buri kuma yafi tsada da had
uwa, sai taji dama bata ce ya karb
o mata ba, tana ji kawayenta na gulmarta, ko magana ta daina yi duk yanda taso ta daure sai data kasa hawaye ne ya wanke fuskarta, sai da mai make-up ta gyara mata fuska tace "In kika cigaba gaskiya bazakiyi kyau ba, fuskar ki gaba d
aya lalacewa zatayi
Tanaji kawarta na cewa "Dama san maso wani ai k
oshin wahala."
Tunda ta shiga mota batace komai ba tsabar takaicin da take ciki wanda take jin tamkar ta d
aura a hannu a kai tayi ta zunduma ihu.
****
Kiran Ummy daya gani ne yasa ya
aga yana zaune a cikin office
inshi yana duba takardu.

"Araab kana ina?"
"Ummy ina gun aiki, bazan samu zuwa ba shiyasa na aiko miki da kayan Meenal."
"Kayan Meenal?

Ta tambaya cike da mamaki tana sake duba
akin.

"Wa ka ba?

Sannan yanzu Araab kayan da zatasa haryanzu ba'a kai mata ba?"
"Man
o take ko Manda, ita dai naba ta baki."
Mikewa tai ta fito ko ina ta duba babu, tana hawa sama taga kayan Mun
o nan danan hankalinta ya tashi tace "Araab inaji fa yarinyar ta
auka bata kai ba tasa, tunda ga kayanta anan, ka tabbatar ka mata bayani?"
Eh Ummy
Ya fa
a yana raya wa ransa tabbas yarinyar bata da kai, ita hankalinta ba zai bata kayan basu dace da ita ba
"Yi sauri ka fito kaje wurin bikin, kasan dai yau ana buk
atar zuwan ka, bari na kira Farouq kar ya
karasa da ita in bai isa ba......."
Eheem
*******
Salame ta gaji ji take duk jikinta ciwo yake saboda tsanannin tafiya sai dai in ta tuno arziki sai ta ware, yau sai biyayya take wa Jauro,
Motar a kauye ta sauka ta kalleshi tace "Musai bread ko kasan mutanen mu."
Kallanta yai yace "Salame kina tunanin komai zai tafi lafiya?

Rabona dasu harna manta."
Dariya tai tace "Ko ma menene ai arziki ne ya kawomu sannan mu gun Danejo da Maccido mukazo koma menene suyi su gaji ko sunk
i ko sun so kai jininsu ne
Dubu uku ta ciro aka siya bread guda shida, suka biyo hanyar zuwa ruga, suna ta keta gonaki da ciyayi, Salame har da k
aya ta suke ta, taji azaba sosai amma ta daure saboda zumudin samun dukiya, sun sha tafiya kafafunsu sukayi butu-butu,
Yau ta kud
urta zasu koma ba zata iya kwanan rugar ba, tana samun ta amshi dukiyar ba abinda zata zauna yi, tasan kila suce bazasu bayar ba sai sunzo
aurin aure, ko zata ce a d
aura auren ma yau ta dage da zancen auren ayi a mik
a mata dukiyar, yadda tanaa zuwa kano ba sai ta tare ba zata sa Bilal ya saketa tasan tana nuna masa kud
i zai amince,
Dariya ce ta kwace a ranta dan tabbas komai yaki ba shakka plan dinta babu tuntu
e bare ta gar
a.......
(Bakin mu da goro
KU CIGABA DA BIYO ZEE YABOUR DA AYUSHER MUHD CIKIN TAFIYAR LITTAFIN NN
GA MASU BUKATAR
AN TAGWAYE DUKA GUDA BIYAR 1500
GUDA HUDU 1300
GUDA UKU 1000
GUDA BIYU 700
GUDA
AYA 400
_*RAFEEQ*_ (Hajja Ce & Asmy B Aliyu)
_*MUN
O*_ (Ayusher Muh'd & Zee yabour)
_*FATHIYYA*_ (Billy s fari & Umm Asghar)
_*.ZAMANINMU A YAU*_ (Nana
iso & Jiddah Aliyu)
_*IYALINA (A'ilaty)*_ (Zainab Bawa & Sadiya Nasir Dan)
ACCOUNT NUMBER
2083371244
Zenith Bank
Aisha m salis
KATIN WAYA
+234 706 528 3730
(MAI HAKURI.....)
ZEE YABOUR
AYUSHER MUHD
Zuciyarta fal farin ciki tana jin wani annashuwa na ganin tayi kyau, da yadda yanzu take samun kulawa itama ana d
aukar ta tamkar kowane dan
adam,
Motoci ne fake a wurin wanda kana gani kasan biki ne na masu hannu da shuni, Mundo ta ware ido tana kallon had
uwar su, A ranta tana jinjinawa,
Tare suka fito da Farouq ya nuna gate pass d
inta aka barta ta shiga, Shi kuma ya juya ba tare da ya shiga ba, yana sauri yaje ya shirya, hasken fitilun gun da yanda akai decoration
in gun ne ya haskata, Cikin natsuwa take tafiya, tana waige waige ko zata ga su Ilham.
Chapter 36 · 0% Book details