← Book details Mundo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 187

Sashe 32

Mundo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mundo ta kasa cin abinci kwata kwata, Sai maganin da Ikram ta kawo mata tasha, Salame bata dawo ta sake duba mata tunda ta gane Bilal bai farmata ba, hidimar gabanta ta cigaba.
*******************
Akwatuna ne set set jere gaban Ummy ta kalli Farouq tace "Duba ka gani me kuma muke bukata?"
Saman goshinsa ya shafa yace "Ummy ke ka
ai dai kike hidimar bikin nan dukanmu babu wanda yake so, anya kina ganin hakan ne ya dace?"
"Farouq meyasa bakwa fahimtata?

In ajali yazo min ya zakuyi?

Haka zaku zauna ba dangin mahaifinku?"
"Ummy kin damu da dangin mahaifi bayan su basu damu da mu ba."
Sallamarsu Ikram ce yasa shi yin shiru, sai da suka gaida Ummy da gida sannan suka gaida Ya Farouq "Yau kuma ina kawar taku?"
"Batada lafiya zazzabi takeyi." Ikram ta fa
a ai bata jira sunyi magana ba tace "Ummy mutanen gidansu basuda kirki wallahi, kinga
akin da take?

Allah kamar
akin mage."
"Wannan fa Allah store ne na tabbatar baki ganshi kusa da kitchen fah?"
Ummy jikinta ne yai sanyi tare da sake tausayin yarinyar sai dai a fili tace "Ku kuma iyayen sa ido ba?

Tasha magani?"
"Eh munsai mata."
Tana murmushi tace "Allah ya bata lafiya ku kuma ya baku lada."
"Ameen Ummyn mu."
Tashi sukai suka fito ta kalli Farouq tace "Yanzu ka sa kayan a bayan mota ka kai, kadaiji yaje bayasan mu jamai abin kunya da cewa zamu kai lefe."
Fuska ya ha
e yace "In haka ne sai suzo su amsa da kansu."
"In sake magana kenan?" Haka ya mike zuciyarshi duk ba dadi ya sa akwatinan a bayan mota wayar Araab ya kira ya sanar dashi.

Zuciyarsa ta sake tafasa akan iskancin nan, sai dai ya xaiyi baya iya take umarnin Ummy.

Ko minti biyu da isar Farouq sai ga wayar Abba, tana
auka yace "Menene bazaki bari sai dare ki aikoshi ba?

Yanzu me abin nan ya dada bayan mutane sunga sanda ake shigo da akwatin?

Kedai sai kin kaskantamu hankalinki xai kwanta ko?"
Ummy jiki a sanyaye tace "Kayi hakuri Yaya ba dalilina ke....." kashe wayar yai ya kalli Farouq wanda yake tsaye yana sake cika yana batsewa.

"Wai ku gaba
aya haka kuke ba tarbiyya?

Dan iskanci daka dawo kazo ka gaisheni?"
Yawun bakinsa ya ha
iya yana sake dannar zuciyarsa kawai sai gani sukai ya fara jan akwatina.

Mumy ta mike tace "Farouq me kakeyi?"
"Maida su gida zan tunda ba kwa bukata, sannan tunda Meenal ke san auran ai bata bukatar lefe."
Mumy ta sake rikewa tace "Ya isa me yasa ku bakwa jin magana ne?"
Fita yai daga gidan yana cewa "Ummy wallahi na rasa me yasa ta damu da wa
annan mutane da basa daraja ta.
****
Danejo sai da ta tabbatar dare ya ratsa ta kwashe kaf gwalagwalan mundo, ta fito ta nufi
angaren bukkar Mun
o ta haka ramen da Maccido ya fa
a mata farar takardace a manne ta zaro, bata damu ta bu
e ba saboda burinta ta gudu ba tare da sun sani ba.

"Waye nan?" Ta juyi muryar Ardo, da sauri ta fita ta baya ta fara gudu-gudu, sauri-sauri.

Ardo sintiri yake yana kallon
akin Danejo wai da gaske batazo ta bashi hakuri ba?

Kwafa yayi ya koma ya zauna akan tabarmarsa daga nan bacci ya
aukeshi, bai farka ba sai dayaji ance "Waye nan."
Fitila ya haska ya mike yana cewa "Tanimu menene?"
Yace "Motai naji amma inaji ko gafiya ce."
Da sauri Ardo ya mike ya sa takalmi yana haska fitila,
akin Danejo yai kai tsaye, ba ita ba labarinta, lallai matar nan hakan ya sake tabbatar mishi da saninta Mundo ta bar rugar nan.

A fusace yace "Tanimu dubomin matarnan, inaji guduwa tai."
Tanimu kani ne ga Ardo yana kallanshi yace "Yaya ba ka saketa ba?

Ka barta taje inda taga dama in ta zauna anan ma me zata mana?

Ranshi ne ya
aci to amma me zaice?

Haka kawai yanda ta nunamai halin ko in kula yasa ransa ke kara
aci.
*****
angaren Mun
o kuwa gaba
aya ta canza, daga makaranta sai
aki, ko zama gidansu Ilham ta daina sosai, magana ta daina yi sosai in ba da dalili ba, Jauro ya tambayeta harya gaji.

Bilal kuwa tundaga ranar bata sake bari sun ha
u ba tana jin motsinsa take shigewa
aki.

Ganin Jauro ya damu dasan jin abinda ke damunta yasa Salame tace "Ina ganin rashin babanta ne me zai hana mu sa lokacin auransu da Bilal sai ka kai musu babban labari?"
Jauro ya kalleta yace "Wai ni ta ina zamu iya ha
a yaran can da Mun
"Nikam gani nake ita ka
ai zata iya shiryar mana dashi kasan tasiri mace akan namiji, balle suna matsayin ma
aurata, kuma kaga yanayin sa dole yana bukatar mace mai hakuri."
Shiru yayi sai dai zuciyarsa ta fara gamsuwa da hakan.
******
Hmmm su Meenal fa ba dama, gyaran jiki aketasha ko waje ta daina fita har da ajiye karatu wai sai bayan aure zata cigaba dan so take taba mijinta lokacinta gaba
aya.

Bayan gyaran jiki har mayukan bleaching ta ha
a nan danan ta canza, kawayenta kuwa kowa sai da ta sanar dashi zancen bikinta da Araab.

Yau tun safe ta tashi ta shiga kitchen da kanta tai girki, dole taje ta taradda Araab dan tana missing dinshi kuma tanaso ta kaimai katin aure datasa aka bugo da ndinner.

Gayu sosai taci ta shigo motar Abba dan key dinsa ta
auka ma yana bacci, bataji zata
ari rana ta ta
a gyaran jikin nan.

Tab yau Araab in ya ganta hankalinsa zai tashi.
o tana tsaye inda Araab ya umarceta ta dinga tsayawa tana jiran 'yan biyu su fito, wasa kawai take da yatsun hannunta.

Kai ya girgiza bayan ya zauna akan dinning ya zaro wayarsa yana dubawa yana cin chips a natse.

Tunda yaji sallamar Meenal ya sake
aure fuska, Mun
o kam daga ta ha
a ido dashi sai ta sake makalewa jikin kujera, ganin Meenal ta shigo yasa ta kauda kai dan bata manta da marin da ta mata ba.

Ta karaso tana yanga ta ajiyemai jakar tare da neman matsar da abincin gabanshi, wani mugun kallo ya mata wanda yasata maidawa, ta sake mikamai jakar abincin da ke hannunta cikin maganar tausayi tace "Yaya dan Allah ka amsa, tun safe na tashi na maka girki har ciwo naji ina sauri karka fita ban taradda kai ba." Bai tanka mata ba har yanzu sako yake karantawa a cikin wayarsa.

Mun
o dake gefe tana jiran su Ikram su fito su wuce school, ta kauda fuskarta gefe a ranta tace "Wannan wannan da alama sune irin su Mugarbo yake ko musambo da muke kallo a film." Ido ta zaro ganin ya kalli inda take da sauri ta matsa kamar zata shige cikin bango.

Tana hangoshi ta kasa ya sa tissue ya amshi jakar "Ke Manda." Yawun bakinta ta ha
iya dan tsoro yake bata, dakyar ta mike yace "Kinci abinci?" Cike da tsoro tace "Sai na koma." Mika mata yai yace "Amsa kije kici." Ido ta zaro wani kallo daya mata ne yasa ta kasa musawa ta amsa tare da komawa inda yace ta dinga tsayawa in tazo gidan.

Meenal ta nufi inda Mun
o take tana huci, ido ta zaro cike da tsoro tace "Aradun Allah shiya bani....."
KU CIGABA DA BIYO ZEE YABOUR DA AYUSHER MUHD CIKIN TAFIYAR LITTAFIN NN
GA MASU BUKATAR
AN TAGWAYE DUKA GUDA BIYAR 1500
GUDA HUDU 1300
GUDA UKU 1000
GUDA BIYU 700
GUDA
AYA 400
_*RAFEEQ*_ (Hajja Ce & Asmy B Aliyu)
_*MUN
O*_ (Ayusher Muh'd & Zee yabour)
_*FATHIYYA*_ (Billy s fari & Umm Asghar)
_*.ZAMANINMU A YAU*_ (Nana
iso & Jiddah Aliyu)
_*IYALINA (A'ilaty)*_ (Zainab Bawa & Sadiya Nasir Dan)
ACCOUNT NUMBER
2083371244
Zenith Bank
Aisha m salis
KATIN WAYA
+234 706 528 3730
MUNDO
(MAI HAKURI
AYUSHER MUHD
DA ZEE YABOUR
Cikin zafin rai ta fisge basket na abincin tamkar zata had
a da hannun Mun
o wacce ta saki cikin sauri tana ja baya, tana gudun ta sake marinta kamar ranar.

Ta juya tana duban Araab wanda ke k
arin mi
ewa ya bar dining area
in.

"Haba Yaya Araab na dage na maka girki dan cin fuska shine zaka ba wannan kucakar ba ma su Ilham ba?" Kafa
a ya
aga irin ko oho yayi gaba abun sa, Meenal tamkar zata fashe da kuka tsabar haushi, Mun
o na ganin ya bar wurin itama ta nufi wurinsu Ikram dan dama tana san shiga shi take tsoro, sun gama shirin makaranta kenan suka sauka gaba
aya, Mun
o ganin babu Meenal a falon yasa a ranta tace
Dama kin ha
ura dashi, mutum ba fara'a?

Ba maganar kirki?

Hmm zaki sha wahala ne tabb nikam da na aure sa gara na mutu banyi aure ba." Tayi saurin kama bakinta da cewa kanta
Wa ma zai aura miki shi kema kinsan yafi k
arfin ki." Baki ta
an ta
e.

Ikram ce ta katse mata tunani da cewa
Shiga mota mu tafi Mun
o kar muyi latti." Ta bu
e murfin mota ta shiga, direba yaja su.
**************************
Danejo tun barinta rugar
aramin k
auyen unguwar su ta nufa wanda anan ake samun motar kano, taci sa
a ta tarar ana lodi tana zuwa itace mutum ta k
arshe ta kwance ha
ar zani ta biya, Ta shiga motar ri
e da kullin kayanta, ta
aga zuwa birnin dabo.

Bayan direba ya ajiyesu tasha, hankalinta ya tashi ganin mutane nata gilmawa, tofa nan ta rasa ina zata nufa.

Haka ta fito tashar ta tsaya bakin titi tana tambayar Dan Allah ko akwai wanda yasan Jauro da yawa basa kulata ganin wautar ta, wasu ma kallan mahaukaciya suka fara mata, babban birni kamar kano taya take tsammani a san shi?

Tun tana jin
arfi har ta soma galabaita.
Chapter 32 · 0% Book details