← Book details Mundo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 187

Sashe 27

Mundo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaskiya dole muyi ha
in gida."
Dariya yasa tare da sakinta yace "Umma kalli."
Itadai Mun
o tana ganin ya saketa ta wuce
akin Raheena da gudu, tana rufe kofa Raheena tace "
an gidanku
akin ki ne da zaki shigomin da gudu?"
"Rahane kiyi hakuri fitsari zanyi."
A fusace tace "Rahanen gidanku?

Ke wai dakikiyar ina ce?

Banace karki sake
irana da haka ba?"
aki ta nufa dan itakam batasan me take so ta kirata ba, taya sunanta Rahane amma tace ba haka ba?

Tana fitowa taji muryar Jauro yana cewa "Yanzu Salame sai da kika ba yaran nan ku
in nan ya canzo waya?

Shi yanzu bai kai ya nemi ku
insa da kansa ba?"
Da sauri ta karaso tace "Kawu ashe ka dawo?"
Salame ta dafata tace "Ba nace a daina cemai Kawu ba?"
Dariya tai tare da
an dungurin gefen kanta, hakan yasashi dariya tare da girgizawa Salame kai yace "Mun
o yaushe kika dawo?"
Binshi tai da sauri tana bashi labarin abinda ya faru a gidan da kayan da aka canza mata, murmushi kawai yake cikin jin dadi.

Salame kuwa baki ta ta
e ta kalli Bilal tace "Karka wani damu ba abinda zai iyayi, kai dai ka maida hankali ka daina hantarar ta."
Ta ja tsaki ta koma
akin Raheena tana nan a kwance ita daga
aki sai fita in har ka ganta a kitchen yunwa ce ta kamata.

"Zo ki dubamin takalman nan da aka turo ta waya mu gani ko sunyi sai mu siya, banasan abinda zai
atamin gayuna da bikin n
an."
Raheena ta mike zaune tana cewa "Kardai kusa mai tsini ku ba yara ba tsaf xaku fa
i garin gayu."
"Mu ba yara bane amma ba tsofafi bane, naga alama bakar magana kike san fa
amin."
Tare suka duba Salame ta dage ita mai tudu take so a haka suka tura kudi akan za'a turo musu daga Gombe.

"Raheena wallahi in takalmana basu zo ba sai kin biya ni ku
ina haka kawai ga takalma nan a kasuwa kikace in bari inzo akwai masu kyau agun wata bayan baki santa ba."
Komawa tai ta kwanta tace "In sun cinye zan biyaki shikenan?"
Fitowa tai tana cewa "Dolenki kuma wannan."
Waje ta fita inda ta hango Jauro da Mun
o suna magana, kwafa tai ta koma ciki wallahi ko batai rantsuwa ba tasan Jauro akwai munafircin da yake ha
a mata.
******
Yau da safe ya shirya cikin wando na suit da shirt fara yasa necktie ash da ratsin maroon, baisa suit din ba ya rike a hannu ya
auko jakarsa ya fito,
akin Ummy ya fara shiga tana zaune tana hailala kamar yanda ta saba, gefenta tea ne da alama tasha.

Zama yai ya kara gaisheta dan bayan sallar asuba sai ya gaisheta kafin ya wuce sashinsa.

Murmushi tai tace "An fito?"
Yace "Eh zan fara lekawa makarantar ne mu gama magana kafin na wuce, tunda makarantar baban Na'im ne banaji zamusha wahala gun sata."
Kai ta jinjina tace "Yanzu ka fahimci
aya daga cikin dalilin dayasa nace mu sata da kanmu?"
Bayan kansa ya shafa ya mi
e tare da
aukan tire
in data sha tea itama ta mi
e tana binshi da kallo shidai in har abinda ya shafeta ne sam baya gajiya ba kuma ya girman kai.

Su Ikram sun gama jera abinci a dinning zama yai bayan Ummy ta zauna, Farouq ne ya sauko shima a shirya, ya kalli Araab yace "Ummy karki damu binshi zanyi in tabbatar yayi abinda kika sashi."
Kallonsa tai tace "In banda abinka Araab ai in na sashi abu bana bukatar bincike."
Ikram da Ilham suka sa dariya sukace "Ya Farouq sorry sha ruwan sanyi."
"Na zafi zansha..."
Ya karasa yana zama akan kujera.

Araab ya gama ya
au lime juice
insa Ummy tace "Nikam ka tambayi likita karfa wannan shan tsamin yama illa wallahi."
"Bakomai Ummy ai kinga ma rage." Yai maganar tare da yi musu sallama ya fito.

Su Ilham suma suka fito dan tare zasu tafi tunda shima can zaije, ajiyesu yai sannam ya tafi gun Na'im wanda tare sukai makaranta badai abokinshi bane amma suna gaisawa, dan Araab sam bai yarda da aboki ba.

Basu sha wahala ba saboda harkar dai ta ku
ice suka gama komai akan ta fara zuwa gobe zasu bata uniform, irin makarantar da ke ha
e da boko da islamiyya ne.
*****
"Nace Araab
in nan kun mai mata ne?" Mum ta tambayi Layla kawarta wacce take kanwa ce ga mahaifin su Araab.

"Ba dai ce mishi kikai ni na sanar daku company dinshi bane?"
Mum tai murmushi tace "Haba dai kema kinsan bazan fa
aba tunda kince bayaso, maganar mata ni nake miki."
Tsaki tai tace "Ga ku
i ga kyau amma ko da wasa bazan baki shawarar yin ha
i dasu ba, mu kan mu a dole muka ha
a jini dasu kuma gashinan ha
in haryanzu bai mana rana ba sai bakin ciki da yake saka mu."
Mamaki ne ya kama Mum tace "Bangane ba."
Tsaki Layla taja tace
Kul na rabaki da kokarin hada zuri
a da DAN MACE, ina gargadin ki ku gaggauta cire wanann tunanin, banda babu kyau tonon asiri da kuma tamkar na dab
awa cikin wuk
a ne ai da na fyade miki biri har wutsiya
.

Sam Mum bata gane me ta ke nufi ba balle ta san amsar da zata bata.

Ayusher Ce
Da Zee Yabour
GA MASU BUKATAR
AN TAGWAYE DUKA GUDA BIYAR 1500
GUDA HUDU 1300
GUDA UKU 1000
GUDA BIYU 700
GUDA
AYA 400
_*RAFEEQ*_ (Hajja Ce & Asmy B Aliyu)
_*MUN
O*_ (Ayusher Muh'd & Zee yabour)
_*FATHIYYA*_ (Billy s fari & Umm Asghar)
_*.ZAMANINMU A YAU*_ (Nana
iso & Jiddah Aliyu)
_*IYALINA (A'ilaty)*_ (Zainab Bawa & Sadiya Nasir Dan)
ACCOUNT NUMBER
2083371244
Zenith Bank
Aisha m salis
KATIN WAYA
+234 706 528 3730
(MAI HAKURI....)
Zee Yabour
Ayusher Muhd
Hajiya Layla wacce
anwa ce ga Mahaifinsu Araab uwa
aya uba
aya, bata jima gidan
awarta Hajiya Laurat mahaifiyar su Yussy ta tafi, wanda ta barta cikin da zulumi da dogon nazari, Yussy ce ta shigo
akin ba sallama cikin za
uwa tace "Mum I hope ta bada goyon baya though nasan ma zata ji dad'in hakan."
Numfashi Hajiya Laurat taja tace "Akwai matsala Yussy am afraid."
Zabura tayi ka
an tace "Matsala Mum, wacce irin matsala?"
"Ta sanar dani
an mace ne kan mu janye zancen da alama akwai wani mummunan abu game da tarihin rayuwar sa." Mom tai maganar tana jan numfashi
"Ni dai Mum wlh ko
an tsohuwa ne ko ma
an waye ina son shi, kuma ko meye a tarihin sa ban damu ba, wata
ila ma sharri take masa, ko ba sharri bama ni ba wannan bane a gabana."
Kallon ta sosai tayi tace "Gaskiya son shi ya kama ki sosai, sai dai ina tsoro."
"Mum calm down ba wata damuwa, I just need your support ni zanyi handling sauran."
Hajiya Laurat ta sauke ajiyar zuciya tace "It's ok, you know farin cikin ku shine nawa"
"Yes Mum" Ta rungumeta tana mata peck, Hajiya Laurat tayi murmushi.
***********************************
o yau baccin yau rabi da rabi tayi sa tsabar zumudin yau zata fara zuwa makaranta, Su Ilham har gida suka kawo mata uniform da school bag da shoes wanda Ummy tasa Farouq ya siyan mata masu kyau da tsada irin su Ikram, Salame dasu Rahane basa gidan suka zo, Jauro ka
ai ne wanda murna ta cika sa ya masa sak'on godiya wurin Ummy.

Dan dama tun ranar daya dawo ya sata a
aki yace karta kuskura tawa kowa zancen makarantar nan, ya mata dabara yace in ta fa
a Maccido bazaizo da wuri ba, tunda taji haka tai gum da bakin ta, Salame da yake tanata hidimar biki sam bata bi ta kanta ba balle ma tasan akwai abinda ke faruwq.

Ah Mun
o!

Bini bini ta tashi ta
aga window taga ko safiya ta soma wayewa, kiran assalatun farko tace "Ai tunda an kira sallah gari ya waye"
A hankali ta tashi ta shiga ban
aki bata so ta tashi Raheena wacce ke bacci tamkar gawa ko dogon motsi bata yi, dan itakam sam bata sanin sanda take dawowa gida in ta fita.
an yi abun arziki yau ta dan ta goge jiki, har zata fito ta tuna jiya zagin da Raheena ta mata kan tana warin baki, Brush wanda Jauro ya siyo mata ta nuna mata yadda ake amfani dashi ta d'auko ta matsa maclean sai data cikashi taf sannan ta kai baki, "Kai za
i gare shi kamar sikari" Ta tsotse tas, Kana ta sake zuba wani shima ta shanye, hadda fiddo harshe ta darje yadda Raheena ta nuna mata.

Tayi alwala tana cewa "Kawu yace idan baka sallah wuta za'a saka."
Cikin hanzari ta shirya wanda uniform
in sukayi cas a jikinta tamkar an gwada ta, ta saka k'aramin hijabin su wanda ya wuce kafa
a da ka
an, kallon kanta tayi a madubi, Tace "Aradu kamar bani ba." Ta hau jujjuyawa tana kallan kanta tana dariya, Lipstick
auka tace "Man gogawa a le
e shine naga Rahane na shafawa yana mata kyau" Ta
auka ta safa a baki ta maka a kumatunta da saman girarta, Taga kwalin Raheena shima ta shafa, sannan tai dige-dige ta gefe.

Ita kanta ta kalli kanta ya kai sau biyar a madubi tana cewa "Gaskiya Mun
o kinyi kyau." Sai ta kwashe da dariya "Lalai Baffa zai ce bani bace."
Safa ta
auka sam ta kasa gane inda ake sata a hannunta ta zura tace "Ahaf ashema safar hannu ce." kanan tayi sallah wacce duka dungure ce ba wani iyawa tayi ba, wurin saka takalmi ne ta soma kacaniya dan bata iya irin su ba, Hakanan ta zura basu sako ba ko igiya su bata
aure ba, dan rufaffun ne masu igiya a sama, Jakar ma ta gabanta ta goya ta fito falo, Ta zauna Su Ikram sunce zasu biyo su
auketa ta da wuri.
Chapter 27 · 0% Book details