← Book details Mundo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 187

Sashe 82

Mundo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana bu
e kular abincin kamshin girki ya daki hancin sa shi har yau mamaki yake Mun
o ce ta iya girki haka, abincin ya zuba a plate biyu ya saka spoon a kowanne ya tura gabanta, Yace "Ki cinye tas, umarni ne."
Sannan ya soma cin nasa, Mun
o sam bata jin cin abincin amma haka ta
auki spoon tayi loma
aya, tana ta taunawa a baki bata hadiye ba, Araab yana lura da ita har ya kusa cinye nasa ko rabi bata yi ba
Kallonta yayi yace "Zaki bu
e baki kici sosai ko sai na miki dure?"
ago kai tayi ta kalle sa da mamakin yace dure, gira ya
aga mata alamar fuskar sa ba wasa alamar da gaske yake, haka ta soma cusawa ba dan tana jin dadi ba, Araab ya cinye nasa har lokacin batayi rabi ba, ta kai hannu zata dibi abincin taji hannun sa shima ya kai kan cokalin, hannunsu ya gogi juna, suka kalli juna a tare kowane ya basar ta hanyar kawar da kai, Mun
o ta janye hannunta cikin sanyin murya tace "Zan cinye."
Banza yayi tamkar bai ji ta ba, ya debo abincin yana nufo bakin ta, tasan me yake nufi ba sai ya fa
a ba, kasa tai da kanta yasa hannj ya
aho ha
arta fuskarnan a murtuke, a hankali ta bu
e, bakinta idonta na kallon kasa Araab ya kai abincin bakin ta, tsintar kanta tayi ta hadiyewa ba jan lokaci, Araab ya cigaba da feeding
inta har ta cinye tas, kular ya bu
e zai sake zubawa ta kallesa a marairaice tace "Na koshi Allah Ya Araab." Ta karasa maganar a shagwabe wanda ita kanta batasan tayi ba, kallonta yake ganin yadda tai da fuska haka sound na maganar tata ta shagwaba yaji maganar ta har cikin ransa, kular ya mayar ya rufe, yace "Good haka akeso in anu bai miki ba ko ya isheki kiyi magana." Ya tashi ya nufi
aki jin yanayinsa wani iri, sai da ya bu
e karamin fridge dinsa na dau lime yasha, kana ya soma duba wasu takardu da yazo dasu daga office.
o kwanukan ta kwashe ta kai kitchen, tana wankewa tana tunanin Araab, da yadda ya zauna yau ya bata abinci a baki kamar wata baby, "Da alama labarina ya bashi tausayi amma da bazai bani abinci a baki ba nasani." Tacewa kanta, tana ajiye plate da ta dauraye a kwando.
************************
Laces manya-manya masu tsada guda uku Alhaji Hussain ke fito dasu daga cikin leda, Mumy dake gefen sa baki ta saki ba alamun wani murna kan fuskarta, Alhaji Hussain ya kalleta yace "Na siyo miki kaya masu tsada amma naga sam bakya murna ko basu miki kyau bane?"
Mumy nunfashi taja tana ganin ya kamata da dakatar da Alhaji Hussain ya rage kashe ku
i, Tace "Ba hakane bane sunyi kyau sosai, sai dai ina ganin kamar ka
an rage kashi kudi."
Dariya yayi yace "Haba kamar baki san ba da jimawa ba zan mayar da ninkin su ana yin auren Meenal da Araab ai nasha kwana, hidima ko ta nawa ce bazata gagare ni ba."
Mumy tace "Hakane." Tana gudun ya gano wani abu kan Meenal, ya numfasa yace "Wai ya jarabawarta ni fah har yau bata turo mun sakamakonta ba."
"Nima dai bani da masaniya akai, bari na duba girki na barsa akan wuta." Ta fa
a tana tashi bata so maganar tayi tsawo, Alhaji Hussain gyara zama yayi kan doguwar kujerar falonsa yana yin murmushi ganin burin sa ya kusa cika.
************************
Meenal sam bata da sukuni burinta kawai ta dawo Nigeria kusan kullum sai tayi mafarkin Araab sabuwar soyayyar sa na kamata, tunanin ta ya koma kan yadda zata samu mai biya mata ta dawo Nigeria, zuciyarta ta tsaya mata kan Farouq tana ganin shi ka
ai zata samu ya biya mata, kan gadonta ta gyara kwanciya dan yau ko lectures bata fita ba, ta marairaice tamkar a fili zata masa magana, ta dan daura pillow kan wuyanta ta yadda zai shaketa kadan, ta dauki wayarta ta kira Farouq, yana zaune a wurin wani shakatawa yana hutawa yana shan milkshake, yaga kiran "Sarkin naci yau kuma da me tazo?" Ya fa
a yana daukar waya.

Muryarta ta sake yin kasa da ita tana jan wani nunfashi tamkar mara lafiyar gaske tace "Ka taimakeni Farouq kada na mutu a kasar nan na rasa masu mun suruta su binne ni."
"Meya sameki Meenal?" Ya tambaya cike da kulawa dan yadda yaji muryata ya yarda, "Ni kaina bansan actual meke damuna ba, kawai Nigeria nake son komawa amun magani, ko fita bana iya yi Farouq, ina cikin mayunwacin hali gashi bani da kowa a nan." Ta karasa da wani irin tari tana jan numfashi, ta ke hankalin Farouq ya tashi yana jin shine sila dan in ta mutu a kasar laifinsa ne da baya bata wrong direction, "Ka... tai...ma...k...eniiii kaaaa biii....ya mun kudin jirgi na koma gida."
Tayi maganar da kyar kamar mai koyon magana, "Toh zan siyar miki ticket tunda sai ki koma."
Farouq ya fa
a dan ya soma tsorata da jin yanayin ta, "Nagode Farouq." Tace tana wani tari, Farouq ya shiga jera mata sannu, yana kashe wayar, Meenal ta dirko daga kan gado tana juyi tace "Woo ni ashe dai na iya plan, sai Nigeria, gun ango na." Tayi shu'umin murmushi tace "Mun
o mai guri na zuwa sai mai tabarma ya kwashe, Araab mallakin Meenal ne ita ka
ai dan wallahi ta kowacce hanya sai na mallake sa, kuma ba sharing ehe." Ta bawa kanta tabbaci tana kissima yadda zata soma gudanar da shirinta tana isa 9ja ba zata jira iyayenta ka
ai su mata fighting ba, wannan karon da kanta zatayi dan dawo da Araab rayuwarta ya zama miji kuma uban yaranta.
****************
Bilal yau ya tashi bashi da ko sisi yana so ya kora kayan mayen sa, wayar Meenal ya soma kira, yaji user busy dan tun ranar ta saka shi busy kar ya rika damunta, tsaki yayi yace "Ko dawa take waya, ni dai bazan iya jira ba har sai kin turo bashi zanci idan kin dawo ki biya.

Ya jefa wayar aljihun sa, ya fito daga
akin sa, a falo yaga dubu dayan Salame kan kujera ya
auka yayi gaba da ita.

Salame ta fito daga kitchen babu komai ciki na kayan abinci dan yau yunwa take ji, dubu dayar da ta rage mata tayi niyyar siyan nama ta saka a abinci taci ta koshi, tazo
auka a siyo mata balangu da bread
da lemon kwalba tunda ba kayan abinci taga wayam babu, dube dube ta soma har kasan carpet duka kujerun falon sai da ta cire pillown su babu ku
in, "Ba wanda zai mun wannan aikin sai Bilal wallahi, zai zo ya sameni yau din nan." Tayi kwafa cikin mugun takaici tana hammar yunwa, ta zauna falon tana cewa "Allah yayi wadaran auren talaka ace abincin da zaka saka cikin ka ma yana gagararka, ita kuma wancan makirar nasan ko naje baza'a barni na shiga ba, da naje na cika cikina." Tayi tsaki tana jin ba zata kyale Mun
o na shan dadi suna cikin wahala ba.
******************
o an sakata cikin list na masu zana jarabawar WAEC da NECO na wannan shekarar, Araab ya biya kudinta tare da nasu Ikram, yau ma extra lesson suka tsaya yi, Ilham tace "Al'amarin ubangiji bashi da shamaki wai tare zamu gama makaranta dake Mun
o." Murmushi tayi tace "Ni kaina mamaki nake sai nake ganin kamar almara." Ilham tace "Ikon Allah kenan shi ya kaddara faruwar hakan HE IS THE BEST PLANNER." Mun
o da Ikram a tare suka ce "Hakane." Shigowar malami ajin ya katse maganar tasu suka maida hankali kan sa.

Sai biyar da rabi suka tashi, suna fitowa direba yana waje ya
auke su zuwa gida, Mun
o sai da ta fara shiga wurin Ummy, tana zaune falo tana shan inibi, suka gaisheta a tare dasu Ilham, ta amsa tana kallon Mun
o tace "Yan' makaranta an kusa gamawa ko?" Tayi dariya tace "Eh Ummy, sai dai haryanzu ina tsoro."
"Allah ya muku jagora, ki cire wannan a ranki kiyi karatunki."
Tace "Amin."
"Ga abinci can kan dining table waina ce yau mukayi na ajiye muku."
"Toh Ummy mungode." Ta
au ko basket na abincin kan dining table kana ta wuce bangarensu bata jira Ummy tace mata ba, hakan ya ma Ummy dadi tana ganin Mun
o ta fara sanin abunda ya kamata na zamantakewar aure.

Gidan tun kafin ta tafi makaranta ta gyara sa
akin Araab kadai ya rage.

Wanka tayi sosai taji dadin jikinta, ta saka cream mai santsi da kamshi, tabi jikinta da humra masu dadi na wurin Najah, kana ta saka wata english gown ta samanta ta bude ana ganin tsakanin boobs dinta da suka taso saman rigar sosai, rigar har kasa ta saukar mata mai gajeran hannu, vintage scarf ta daura a kanta, ta shafa lipstick mara kala kan lebbenta pink da ya kara masa kyau, har ta
au ko mayafi zata rufa tace
Harma zan gama bai dawo ba.

Ta fito ta shiga
akin Araab, tana gyarawa, lokaci yaja bata ankara ba dan tsayawa da tayi gyara na sosai.Ta kammala tana yawo da kaskon turaren wuta a hannunta cikin dakin, tana turara labule, Araab ya shigo wanda tun kofarsa ta shigowa gidan yake jin kamshi, yana shigowa dakin yaji wani sihirtaccen kamshi da ya saka shi lumshe ido ya bude su kamshin na ratsa shi (mata baku san tasirin da turaren wuta ke yi wurin mazajenku ba ko hmm
o jin shigowarsa yasa tace "Sannu da zuwa." Sam ta manfa da rigarta da yands take.
Chapter 82 · 0% Book details