← Book details Mundo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 187

Sashe 107

Mundo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai kawai ta girgiza taja bargo ta sake duk
unewa, gaba
aya jikinshi ne yai sanyi, kwanto kanshi yai ta bayanta a hankali ya yaye mata bargon data ja ta rufe fuskarta dashi, hannu yasa ya zagayo dashi ta cikinta yana magana cikin wata murya yace
Me kike nufi?

Kai ta sake girgizawa cikin wani yanayi, hannunsa ya sake kaiwa ya ri
ota sosai yace
Matar
i ce ko me?

Bata tanka mai ba wanda hakan yasashi juyo da ita sosai, kai ta maida
asa, ya
ago da fuskarta yasa idanunshi cikin nata, gaba
aya baisan yanayin da yake ciki ba, samun kanshi yai da sake dakushe murya yace
In kin san haka meyasa kike yarda?
ago kai tayi ta
an kalle sa tace
Nasan sha
awa ke damunka, kuma a matsayina na matarka hakk
ina na amince ko mala
iku su tsine min, wani sashe na zuciyata sai yai ta tambayata in matar da Ya Araab ke so ce me zai mata?

Tafiya zaiyi ya dinga barinta?

Ta cusa kanta kasa wanda hakan yasa kanta ya kai daf da kirjinsa, tace
Ni bansan meke damuna ba.

To shi me yakeji akan ta?

Yasan tabbas ba kiyayya bace, sannan ba so bane, shi dai kawai yana son ganinta cikin farin ciki sannan ita ka
ai yakejin sha
awar kusanta, saman goshinsa ya shafa, yasa hannu ya rungumo ta yace
Aure dole sai da so za
a samu kwanciyar hankali?

Ta girgiza kai tace
Ni na isa ince
wani abu?

Na sani sarai ni bankai matar da zaka so ba, shiyasa ban tsawalawa kaina ba, balle kanada wacce kake so take son ka, tunda har yanzu bata hakura dakai ba.

Tunowa yai da Meenal tazo hakan yasa ya gane ashe tun jiya da ita take, kai ya karkatar yana sake rike fuskarta, ita kuma idanunta na kallon saman k
irjinsa wanda gashi ke kwance, ido take son rufewa amma tasan bazai barta ba.

Kishi kike?

Da sauri ta kalleshi tace
Ni?

Akan me?

Kalmar ji yayi ta masa zafi sosai, ya
aure fuska sosai yace
Ni I just don
t believe in love, rayuwar aure anayi ne bani in baka, and ina kokarina na ganin na saki farin ciki, ke da kika yarda da son kina min shi ne?

Kallansa take kafin ta
auke idanunta ta maidasu
asa, alamar batada amsa, janye jikinsa yai wani abu na sake tasomai ya bar
akin, itama mikewa tayi tana mamakin fushin kuma na menene?

Bayan itace ya kamata tai fushi?
******
A bakin company
in Bilal ya tsaya yana gyara zaman hularsa yace
Ai dole ma nasan aiki zai bani sai dai ni gaskiya bana som aiki kawai a dunkulo ku
i a bani amma ni ina zan iya aiki tun safe har yamma?
.

Da wannan tunanin ya shiga yana sake bin company
in da kallo, tabbas wannan shine daidai dashi wai ina ma za
a bashi babban matsayi ya kwashi rabon shi ya mori banza?

Ya ciji le
e yana canza salon tafiya yana kwambo.

Mai gadin sai daya kai shi kusa da office
in sannan ya juya dan dare yayi an riga an tashi, shima saboda sirri da zasuyi da Bilal ne yasa ya dawo.

Shiga yayi bayan ya masa iso, yana zaune akan kujera ya ha
e hannayensa guri
aya gaba
aya ya kasa wani kwakkwaran tunani, ya zaiyi da Meenal shi kenan ta ja mai abun kunya.

Kallon Bilal yai yana takaicin wannan kaskancin, ace daga Araab ta koma wannan?

Har Bilal ya karaso ciki yana tunani, ga mamakinshi ganin Bilal yai yaja kujera ya zauna ya
aura kafa
aya kan
aya, yace
Oga ina wuni?

Kallanshi yai cikin wani yanayi kafin yace
Kenan sirrin da kake nufi tsakaninka da Meenal kenan?

Shafar keyarsa yai yace
Tuba nake oga amma kar kaga laifina.

Cikin tsawa yace
Kaci gidanku, kawa yarinyata ciki kace kar naga laifinka?

Zumbur Bilal ya mi
e yana kallanshi, ciki?

A ina?

Yarinyar da ko daf da kafadar ta bai taba tsayawa ba?

Ohhhh ciki taje aka mata shine zata ce shine?

To ai shi in haka ne shar dashi, sai ya ku
ance cikin sau
i komawa yai ya zauna yace
Oga tsautsayi ne, sau
aya ne tal, kasan abinka da shaid
an ni kaina tun ranar nake dana sani, to ita ta dage Araab take so.

Hannu Alhaji Husaini ya
aga mai yace
Kamin shiru ko sai na sa an
aure mun kai?

Ido Bilal ya kwalalo ya tuno jibgar da aka mai kwanaki, nan danan ya zube a
asa yace
Oga wallahi na tuba nabi Allah, ni wallahi wa
Dallah rufemin baki, yanzu kai ka shirya auranta ne ko me?

Naam?

Ya tambaya cikin daurewar kai, yanda yaga Alhaji Husaini na kallon sji ne yasa yace
Indai kun shirya nima sai na shirya, matsalar dai banida ku
Ido ya runtse yanajin kansa na sake ciwo kirjinsa ma wani irin nauyi, zan maka transfer na ku
i sai dai ba dayawa zan baka ba, duk wani abu mu mun yafe, kaidai ka sanar da iyayenka, kuma ka samu muhallin zama da ku
in dan a duniya da wannan abin kunyar ya fito to fa gwara na bar duniyar nan.

Jin za
a bashi ku
i yasa wani da
i ya
ara rufeshi tabbas shifa komai yazo mai a b
agas, tab kudi zai ci yanzu wannan company
in ma ai ya kusa zama nashi, can ya tafi mafarkin zaune wai gashi a tangamemen gida yana shan barasa, ga Meenal a gefe tana mai tausa a kafafunsa, dariya ne ya kwace masa wanda yasa Alhaji Husaini cewa
Dariyar me kake?

Ko dai ka fara zarewa ne?

Bilal yai saurin sunkuyar da kai yace
Oga kayi hak
uri murna ce ta kamani, da na
auka bazan iya auranta ba sai gashi komai na tafiya, ina matukar kaunarta shiyasa nake jin abin har k
asan raina.

Tsaki yai yace
Ka ajiyemun account details
inka ka fitar min daga office, in ka sanar da iyayenka sunzo anyi magana zan turama ku
in da zaka kama gidan.

Cikin hanzari ya rubuta ya fito, tunawa yai ashe ko na motar komawa bashi dashi, tsaki yai yace
Dan tsiya ko na mota ai sai ka bani.

Sai kuma ya kwashe da dariya tab lallai akwai kwasar ganima tun yanzu ya fara jin kansa babba.

Adaidaita ya tara tun a hanya ya kira abokinshi yace ya bashi aron ku
i yace bazai bada ba dan yasan Bilal ba biya zai ba, nan ya hau masifa akan wallahi ya jira zai sha mamaki, ya kashe wayar yana jan wani dogon tsaki yai wata muguwar kwafa, suna isa gida ya fito zai shiga ciki, mai adaidaita ya ri
o rigarshi yace
Malam bani ku
i na.

Fincike rigarshi yai yace
Dalla ina zuwa, a tsinaniyar
ari biyun ka zaka wani kamoni, ko ce maka akai ni sa
anka ne?

Mai adaidaita yace
Zan jiraka wallahi ka fitomin da ku
i na ehe.

Shiga yai yana kumbura yana cewa
Zancen banza da wofi kenan, duk sai naci abu ta kazar ubanku ku jirani.

Salame ya gani tana dafa magani a waje a murhu, hanci ya toshe yace
Momcy kefa wallahi yanzu kin fara komawa mutuniyar riga what
s this fisabillilahi?

Ludayin ta nunashi dashi tace
Kamin shiru ko sai na buga ma?

Ka barni da abin da ke kaina bana san shirme kaji na fa
a ma.

Baya yaja yana dariya yace
an bani 200 mana zan biya adaidaita.

A wani dalilin?

Ko ajiya ka bani?
an Allah bani bana son mai adaidaitan nan yamin hauka.

A kufule ta zaro a ma
aurin zaninta ta bashi tace
Kuma wallahi zaka biyani.

Karma ki damu in na tashi ma ninkata sau dari zanyi kedai ki jira.

Kai kawai ta girgiza cikin takaici.
*******
Salau ne ya kalli Jauro wanda ya mi
a masa dubu biyar yace
Gashi ka ri
e ka koma gun iyalinka, haka zakai ta zama anan?

Amsa yayi yasa a aljihu sannan yace
Kaga Jauro wallahi ni da komawa sai dai akai gawata amma badai da numfashi na ba, mutanen da kana kallo sai da sukai ajalin Maccido hankalinsu ya kwanta sune zan koma gunsu?

Na kai kaina kenan su kashe?

Jauro yai shiru shidai yanzu tsoron rayuwa yake tunda shi gashinan yana ganin ishara?

Shi sai yake ganin bai kamata Salau yabar yaranshi da suke alhakinshi.

Zaiyi magana Salau yace
Ba dai a gunka nake ba dan haka ka kyaleni dan Allah, inji da kaina nima in kuma tsira da rayuwata.

Hakan yasa shi yai shiru, yana kallo Salau ya koma ciki shi kuma ya juyo, zuciyarshi cike da tunani kala-kala.
******
Meenal a zabure ta kalli Dad
inta jikinta har rawa yake tace
Dady me kake nufi da auren yaran can?

A wani dalili zan aureshi?

Wani mugun kallo ya mata yace
Wato ke dai burinki ki tozartamu ko?

To wallahi baki isa ba doka ce na baki ba shawara ba, sannan auran nan duk inda sati biyu yake ki shirya tsintar kanki a gidanshi, bazaki maidamu mahaukata ba, kija mana abin kunya, ki samu asarar kudi, ke kuma ba karatu ba sannan auran ma kice a
Gaba
aya bata gane me yake nufi ba kuka ta fashe dashi tace
Dady da na auri shi gwara na dawamma ba aure.

Kina sake magana zan fasa bakinki, shashasha to ni na kirashi na kumaji komai na kuma yanke hukunci.

Tsawar daya sake daka mata ne yasa ta mi
e da sauri tana hawaye ta shiga daki ta fashe da kuka kamar ranta zai fita.
******
Araab bayan yayi sallar isha
i ya dawo gida, gaba
aya tun dazu ransa yake a
ace ya samu natsuwa ta kwanciya amma zuciyarshi ta kasa natsuwa na kalamanta, wato bata son shi jikinta take bashi?

Tunda mala
iku zasu tsine mata kenan gashinan yayi abinda yakeso ya kyaleta?

Ido ya runtse hakan ba k
aramin k
ona mai rai yayi ba.
************
o bayan tayi sallah flask ta bu
e, ga mamakinta Araab bai ci abincin ba, ita kuma da taga ta ajiyemai a dining sai tai tunanin yaci tunda haka ya saba.
Chapter 107 · 0% Book details