← Book details Mundo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 187

Sashe 3

Mundo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zee Yabour
Da Ayusher Muhd
(MAI HAKURI)
Na Zee Yabour
Ayusher Muhd
*TEAM
AN TAGWAYE NOVEL*
GA MASU BUKATAR
AN TAGWAYE DUKA GUDA BIYAR 1500
GUDA HUDU 1300
GUDA UKU 1000
GUDA BIYU 700
GUDA
AYA 400
_*RAFEEQ*_ (Hajja Ce & Asmy B Aliyu)
_*MUN
O*_ (Ayusher Muh'd & Zee yabour)
_*FATHIYYA*_ (Billy s fari & Umm Asghar)
_*.ZAMANINMU A YAU*_ (Nana
iso & Jiddah Aliyu)
_*IYALINA (A'ilaty)*_ (Zainab Bawa & Sadiya Nasir Dan)
ACCOUNT NUMBER
2083371244
Zenith Bank
Aisha m salis
KATIN WAYA
+234 706 528 3730
Dandano page 3.......

Mikewa tai zata tattare kwanukan da suka ci abinci, kiran sunanta da taji anyi ne yasa ta yarda kwanan ta da ke hannunta, nan da nan gabanta yahau fad'uwa ta kalleshi idanunta sun tara kwalla.

Mikewa yai zuciyarsa na sake tafasa, ta sulale a kasa tana kallan kofar.

Kofar aka sake bugawa muryar macece tace "Mun
o wallahi in baki bud'e kofar nan ba duk abinda ya sameki ke kika jiyo.

In shi Laddo ya kasa d'aukan mataki ni aradun Allah bazan d'au ciki wata tara ki lamushemin yarinya bugu d'aya ba shegiya aljannar mayu."
Maccido ko bai bude ba yasan wacece a wajen, yana nan a tsaye ya tunanin abinyi, da alama mutane ne suka biyota dan yanaji ana cewa "Sahi wai bazaki bari ba?

Ko bakiji me Ardo yace bane?"
Zaman dirshan tai a wajen ta sa hannu aka tana ihu tace "Wallahi ko menene bazan yarda ba, mutane nawa yarinyarnan tana ci an kasa kasheta, dabobin mu nawa ta lamushe?

Amma ko yaushe tai sai dai a bada hakuri, itan uban wacece da bazamu kashe tsinaniya mu huta ba?

Ko tsoro kuke zata turo muku mayu?

To wallahi nidai ko menene sai dai ayi amma yau ko ni ko ita dole wani yabar duniyar nan."
"Sahi koma menene ki tashi mu koma in Ardo yazo bazamuji dadi ba."
Yawon bakinta ta tsirtar ta sake rusa mata kira tace "Mun
o aradun Allah ki fito kafin na sawa d'akin nan wuta, in su kin rike kuruwarsu to ni tawa tafi karfinki, banda munafirci akan me za'a b'oye abinda suke tsoro a fito dashi kowa yaji, bana tsoron komai tunda na rasa jaririyata."
Itakam kuka kawai takeyi a jikin gado, wai menene shaidarsu na cewar ita mayya ce?

Tunda ta taso takeji ana kiranta da haka har yau ta rasa menene hujjar su,
Buga kofar da aka sake yi itace tasa Maccido sake fusata kawai ya wuce jikin bango ya d'auko sandar sa.
o na ganinshi ta mike da gudu dan mahaifinta nada tsananin hakuri amma akwai zuciya, tun d'azu ta kula yau hakurinsa yakai karshe, cikin hanzari ta
ta riko kafafunsa tana girgiza kai, kallanta yai cike da taysayi yace "Sakeni."
Kai ta sake girgizawa tace "Baffa ka taimakeni kai hakuri, ya kakeso nai rayuwa in wani abin ya sameka?

Dan Allah kayi hakuri ka kyalesu, in dai har ina ganin ka koma mene zan iya jurewa nidai burina ka kasance cikin koshin lafiya."
Tsananin tausayinta ya sake kamashi, tabbas yanzu ya gama yanke hukunci dole ya d'auke 'yarsa subar kauyen nan.

Sakin addar yai a kasa ya nufi kofa, ta d'auka bud'ewa zaiyi hakan yasa ta takure a gefe sai dai bai bud'e ba daga ciki yace "Sahi tun kafin raina ya b'aci ki ja kafafunki ki bar nan, wallahi karki bari raina ya b'aci na fito daga ciki, dan daga yanzu na daina shiru akan lamarin Mun
o banda wulakanci
yaushe kikaga ta lamushe miki 'ya?"
D'ankwalinta ta cire tai damara dashi tace "Na nawa kuma?

Yau aka santa da maita ko jiya?"
Kwafa yai yace "Karki tafi ki bari na fito kiga yanda Maccido zai d'au mataki, yayarta dake kusa da ita ta kamo hannunta tana turjewa, tace "Sahi kinga ki wuce mu koma, da safe kya dawo ina tsoron kar Ardo yace bakiji maganarsa ba."
Kasan leb'enta ta ciza tace "Takaici na meyasa bazasu iya illata yarinyar nan ba?

Kaf rugar nan ita kad'ai ce mayyar da aka kasa d'aukar mataki kanta, mayu nawa ana ganin bayan su sai ita duk abinda take ace sun kasa kona ta?"
Sa ke janta tayi tace "Koma menene ke dai ki wuce, in tayi zuciya ta tab'a kuruwarki kuma fa?"
Haka suka tafi tana zage-zage dashan alwashin dawowa.
******
Shiru ratsa d'akin bayan tafiyar su, Mund'o bata yi arba ba bacci ya fara d'aukan ta, Maccido tunani ya mai yawa a k'wak'walwa, ya tasheta ta koma kan gado ya fito ya wuce b'angarensa, ko kallan inda matarsa take baiyi ba, ya kwanta akan gadansa, itama gama shigo da kaya tayi ta kwanta a kusa dashi, juya mata baya yayi ya fara baccin sa, ko a jikinta baki ta tab'e a ranta tace "Sai dai kayi babu dalilin da zaisa ai tamin fada akan tsinnanniyar yarinyar can.

Abin haushi kaf kauyen babu mai shekarunta da baiyi aure ba, yo wazai auri mayya da hankalinsa?" Baki ta sake tab'ewa daga tare da gyara kwanciyar ta, cikin mintuna k'alilan bacci ya d'auketa.

Karfe hud'u na asuba ya tashi daga bacci , gefen sa ya waiga ya d'au fatanyarsa ya fito daga d'akin (sallah bawai ta damesu bane sunayji amma sai sanda suka bushi iska, kasancewar babu wadattacen ilimin addini a rugar, babu ma masu ilimin da zasu koyar dasu, Maccido ma yana kokarin sallah akan sauran.) kasan cewar hunturu ne dakyar yayi alwala ya fita gidan.

Tafkeken turken shanu ya nufa wanda yawan shanayen wurin kad'ai abun kallo ne, gefe yaja yayi sallah sannan ya fara kokarin duba su yaga ko akwai wanda bashi da lafiya, Madara mai kyau ya sha,
Sa'annin sa wanda duk 'yan uwansa ne suka karaso aka gaisa fuska dai babu fara'a saboda abinda ya faru jiya, Maccido ya warewa kowa wanda zai yi kiwo shima ya kwashi wasu ya nufi cikin dajin.
******+
Sanyin dake ratsa jikinta yana shigarta ne ya sa ta bud'e idanunta daga nannauyen baccin da take wanda ke cike da mafarki mai dadi wai gata da Baffanta a daji suna rayuwarsu babu mutanen rugar,
Zabura tayi garin kokarin zama sai jinta tayi a kasa, cikin rawar murya tace "Dadda awali jam....."
"Kina karasa magana ina wanka miki mari, banda abinda kika aikata jiya shine me makon ki yanki dare ki tatsi nono ki gyara gida kiyi wanke-wanke ki debo ruwa shine har kinada idanun bacci a rigar nan?"
Gwiwowinta tasa a kasa tace "Dadda kiyi hakuri bansan gari ya waye ba sannan wallahi ni ban....."
"Ina fad'a kina fad'i ko?

Karya aka miki?

In bake ba uban waye zai kama musu jaririya?

Dama na fad'a miki duk sanda kika sake kama wani a rugar nan ki shirya had'uwa dani."
Tana kai nan ta finciko hannunta iya karfinta, randar dake waje ta nufa hannunta rike dana Mun
o wace ke hawaye, hankad'e murfin randar tayi ta debo ruwa masu balain sanyi ta hau sheka mata, tamkar zubar k'ank'ara haka Mun
o taji jikin ta, take ta hau kyarma jikinta na k'ank'amewa tsabar sanyi,, sai da Dadda ta tabbatar ruwan randar nan ta juye mata shi tass sannan ta kwad'a mata ab'in d'eban ruwan, tace "Yar' banza tashi ki biyoni."
Hawaye ke ambaliya kan kuncin ta, kayan jikinta jik'e sharkaf da ruwa har sun kame a jikinta, tsuman dake shanye ta d'auka ta sa a saman kirjinta, kowa ya ganta sai dai ya tab'e baki, babu mai nuna alamar tausayawa gareta, ta rasa wane irin bakin jinin Allah ya bata.

Dada bata tsaya ba sai gaban turken dabbobi, tace "Shiga maza ki gyarashi, ai jiya dama kika samu dan bana nan, kuma aradun Allah kika wuce awa d'aya zaki gamu dani."
Tana kainan ta juya tabar gun, kowa sai sake gaisheta yake suna jin dad'in hukuncin data d'auka.

Danejo ce ta taho gunta cikin sauri zatai magana ta daga mata hannu tace "Danejo ahir dinki kinji na fad'a miki, aiki nasa ta ba wani abin ba, in kuma iyakata akesan a nunamin to ina jira."
Danejo tace "A'a ba haka bane zancen abinci nazo na miki, dan Allah ki sanar dasu su dinga zuba abinci da ita, harda wannan yasa Maccido ya fusata."
Sauke ajiyar zuciya tai tace "Zan musu magana amma in basuyi ba kar kiga laifina, ra'ayinsu ne."
Haka ta mike jiki sanyaye ta kalli Dadda cikin sanyi tace "Dadda na san......" Hannu Dada ta d'aga mata alamar dakatar da ita tace "Ko me aka miki a rugar nan ki gode Allah baki da bakin magana, a kalla an barta da ranta, yarinyar da sanadinta rugar nan ke cikin tashin hankali da bala'i kala-kala, yarinya sai bakin jini da bakar zuciya?

Duk ta salwantar mana da rayuwar jama'a, banda asara da bakar zuciya kaf kauyen nan akwai sa'anta?

Duk sunyi aure sun haihu, to uban waye zai auri maye?

Ya aurowa kansa bala'i?

Ko wannan kyan nata baisa wani yaji sha'awar zama da ita ba, to ahir dinku wallahi in ma zaki taka mata birki ki taka, wannan karan ya zama na karshe da zata ci mana mutum a rugar nan, abinci kuma kome ta samu ta amsa tayi godiya."
Ta kama kujera ta mike ta wuce ciki tana
ingishi saboda kafarta
aya dake ciwo.

Danejo shiru tayi dan kaf kauyen ba wanda ake shakka sama da Dada, ita kadai ce matar kakan su Maccido data rage, tanada zafi gashi bata wasa, in tace abu ko Ardo wato mahaifinsu Maccido bai isa ya canza ba.

Jiki a sanyeye ta bar gun d'akinta ta nufa ta d'auko abu sannan ta nufi turken dabobbi.

Mun
o nata aiki tana wake-waken fulani ta haka take d'ebe kewar halin da take shiga.
Chapter 3 · 0% Book details