Sashe 4
Mundo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jikinta yayi kacha-kacha saboda dattin wurin daya kama kayanta, a karo na biyu kenan data sake yin mika saboda bayanta daya sake amsawa tana jin k'asusun bayan suna wani k'ara,
Bubuga bayan nata tai tace "Mun
o kafin Dada ta zagayu ki ware kiyi aiki."
Zata tsuguna taji ance "Aiki ba komai a ciki ai bazai yiwu ba."
Cikin sauri ta juyo tace "Danejo!"
Ta karasa gunta da sauri sannan ta tsuguna ta gaisheta, Danejo tana murmushi ta mika mata kwaryar hannunta tace "Sha madara sai ki cigaba."
Amsa tai da sauri ta kafa kai tana sha, bata ajiye ba sai da ta shanye tas.
D'agowa tai ta kalli Danejo tana goge baki tace "Har na rayu."
Dariya tai tace "Da mutuwa kikai?"
D'aga kai tai tana dariya tace "Danejo kinsan d'azu da Dada ta zuba min ruwa na d'auka mala'ikon da ake cewa ne suka jani zuwa teku."
Danejo batasan sanda tasa dariya sosai ba tace "Lalai Mun
o ashe wahalar takai haka?
To yanzu fa?
Kin dawo duniya?"
Ta sake d'aga kai tace "Nadawo gashi ina gani biyu."
Amsar kwaryar tai tace "Ungo rigar dana dinka miki inkin gama aikin sai kiyi wanka kisa."
Amsa tai sannan ta daga ta sama, mai dogon hannuce, nan ta hau murna tana tsalle tace "Danejo aradun Allah kin raya ni, dama in sanyi ya busa ni ji nake kamar zan yi sayi a tsaye."
Kai Danejo ta jijiga tace "Yanzu sai ki saka yanda bazakiyi sayin ba, ni bari na wuce."
Ta sake godiya har Danejo ta bar gun, dadi ne ya sake kamata, lalai Baffa yau zai sha mamaki shima.
Jin ta tai wasai kamar ba abinda ya b'ata mata rai dan yarinyace mai tsananin hakuri, duk abin nan bazaka tab'a jin ta tanka ba, ko sa'aninta ne sai dai su mata abinda zasuyi su tafi.
****
Ta gama kenan ta d'au rigarta zata bar turken sam bata kula ba sai ji tai an hankadata da karfi, ji kake tim ta fad'i a kasa rigarnan ta fad'i a kasa itama,
agowa tai idanunta na neman zubar da kwalla.
Ganin Sahi ne yasa ta sadda kanta kasa kawai, Sahi ta matso ta dagota ta wanke ta da wani wawan mari.
Kuncinta ta rik'e kawai ta maida kanta kasa, wuyan rigarta ta cakumo da karfi tace "In shekara bakwai ina neman haihuwa ban samu ba, sai yanzu amma in haifa ki cinye min 'ya?
Sannan ace nai shiru?"
o har yanzu kanta na kasa rigarta kawai take kallo wace gefenta ya dan b'aci.
Sahi ganin yanda bata tanka mata ba yasa ta ranta ya sake b'aci, a fusace ta fara neman abin duka ita dai haryanzu tana tsaye kamar gunki.
Nan Sahi ta dawo da manjagarar da Mun
o tai amfani dashi gun gyara turken, tana neman kwad'a mata.
"Kina saukeshi a kanta to lalai kema ki shirya barin duniya.
Dan aradun Allah sai dai a binne ku lokaci d'aya."
Kallan Maccido tai takaici ya kamata ta cilar da manjagarar ta fita tana huci da tsinewa Mun
A hankali ta kalli Baffanta ta sakar mai murmushi, haka kawai yaji hankalinsa ya kasa kwanciya yana kiwo, nan yasa wani a cikin au ya rikemai nashi dabobin yace "Zaije ya dawo."
Ajiyar zuciya yai yana mata kallan tausayi, karasowa tai fuskarta a sake kamar ba wace ke cikin wani yanayi ba, ta d'aga mai rigarta tace "Baffa kalli."
Ganin yanda ta daure yasa shima ya saki fuska yace "Inyeee wani d'an aljannan ne yaba wannan yar filon riga?"
Tana dariya tace "Danejo, da naso sai na sa ka gani."
Dariya yai shima yace "Asha ashe na yi gaggawar gani."
Ta sauke rigar tace "Baffa me kake anan dabobbin fa?"
"Sun tafi yawo zasuje su dawo."
Ido ta zaro tace "Baffa?
Ka barsu?"
Ya furzar da iska yace "To ya zanyi?
Nayi-nayi su dawo sun ki wai su dole sai sunje yawo zasu dawo."
"Hande in boni!
Shikenan yau Ardo sare mu zaisa ai, dama jiya an kusa sareni ya hana yanzu ka ja za'ai gaba damu."
Ya zaro ido yace "Yanzu ya zamuyi?
Tunda muna san barin rugar ko mu gudu?"
Ta kalleshi tace "Yanzu?"
Dariya yasa dan shiriritar Mun
o tayi yawa, duk da yana alakanta hakan da rashin aboki.
Zee Yabour
Da Ayusher Muhd
(MAI HAKURI)
Na Zee Yabour
Ayusher Muhd
*TEAM
AN TAGWAYE NOVEL*
GA MASU BUKATAR
AN TAGWAYE DUKA GUDA BIYAR 1500
GUDA HUDU 1300
GUDA UKU 1000
GUDA BIYU 700
GUDA
AYA 400
_*RAFEEQ*_ (Hajja Ce & Asmy B Aliyu)
_*MUN
O*_ (Ayusher Muh'd & Zee yabour)
_*FATHIYYA*_ (Billy s fari & Umm Asghar)
_*.ZAMANINMU A YAU*_ (Nana
iso & Jiddah Aliyu)
_*IYALINA (A'ilaty)*_ (Zainab Bawa & Sadiya Nasir Dan)
ACCOUNT NUMBER
2083371244
Zenith Bank
Aisha m salis
KATIN WAYA
+234 706 528 3730
Dandano page 4.......
Maccid'o ya kalleta yace "Jeki canza kaya kizo muje wani guri, karki bari kowa ya ganki, kinji?"
Kai ta d'aga da sauri dadi duk ya hanata sukuni, da sauri ta nufi d'akinta,?
Tunanin ta yadda zatayi wanka, sanyi take ji sosai, wanda ke ratsa k'asusuwan jikin ta, gidan babu mai bata ruwan d'umin da zata yi wanka,
haka nan ta d'au bokiti ta d'ebo ruwa ta shiga wankan wanda ya d'auketa mintuna saboda sanyin ruwa, sai da dan' tsaya ta damtse ido kana take kwarawa jikinta ruwan, shiyasa sai tayi kwana biyu bata yi wanka saboda tsoron saka ruwan sanyin a jikinta da yadda baya shafa mata lafiya, yanzu sai mura ta mata mugun kamu kuma irin murar nan mai azaba da ke saukar mata ciwon kai.
Kayan da Danejo ta d'inka mata ta saka, ba kwalliya tayi ba dan ko mai bata shafa ba saboda batada shi, sai dai ta yi kyau dama (sabon kaya ko ba kwalliya akace....) tana fitowa taji ance "Dan iskanci sai nace kizo ki d'ebo ruwa b'angarena?" maganar Altine wato matar Baffa ce ta doki kunnuwan ta, da sauri ta russuna ta gaisheta tare da cewa "Kiyi hakuri wallahi ina tashi Dada ce ta sani gyaran turke."
"Wannan ba matsala ta bace, ki wuce ki d'ebo mana ruwa, banda rainin wayo ai ita Dadan baki manta da aikin da ta sakaki ba amma ni nawa da ya zama aikin ki kullum sai kinga dama kike yi." Ta jefa mata muguwara
harara tare da cigaba "Uban me kike a tsaye kuma?"
Da sauri ta nufi b'angaren Abba ta d'auko bokiti zata fito taji kukan Gid'ad'o, sam ta manta an mata iyaka da shiga ciki, da sauri ta shiga ta tarar dashi a kasa da alama abu yaje d'aukowa ya fadi, da gudu ta karasa ta d'aga shi, Ta fara jijigashi tana cewa "Yi shiru an gidadon Baffa ina kaji ciwo?".
Saukar dundun da taji baya mai azabar zafi yasa
tayi saurin kai k'asa, Altine ta fincike d'anta ta k'ara kai mata wani, wanda ya saka ta durk'ushewa gaba d'aya, tana jin tamkar an karya mata k'ashin baya, ta runtse idonta tsabar azaba, K'afa tasa ta hankad'eta tace "Shegiya muguwa, wato kinci yarinyar Laddo baki k'oshi ba shine zaki kama kaninki?
Dama gaskiyar mutane da sukace in kika gama kama na waje cikin gida zaki dawo, to wallahi ko ciwon kai Gidado yayi sai kinga abinda zan miki a kauyen nan."
Da kyar Mun
o taja kafafunta zuwa waje,
bokiti kawai ta d'auka ta fita tana share kwallar dake zubo mata.
"Ke da nake jiranki me kuma kike da bokiti?"
Da sauri ta goge idanunta tayi murmushi tace "Baffa kayi hakuri na manta ban zuba ruwa bangaren Altine ba"
Idanunta da yanayinta ya tabbatar kawai abunda take b'oyewa, bai tambayeta ba sanin ko meye ba mai dad'i ba baya son jin abunda zai hargitsa masa tunani yanzu ya b'ata ransa, bashi da wata damuwa yanzu a duniya irin Mundo, yana fatan ranar da zata samu yanci ta fita daga zargin mutanen rugar tayi rayuwa kamar sauran mutanen, babban burinsa yanzu ya sama mata sauyi a rayuwarta, itama ta zama mutum kamar kowa tayi rayuwa mai cike da yanci kai,
Kawar da tunanin yayi ya numfasa yace "Toh
kiyi maza ki gama kizo muje, dan banasan rana ta fad'i bamuje mun dawo ba."
Da sauri ta d'aga kai alamar to sannan ta tafi.
Maccido yana tafe yana tunani tabbas abinda ya tsara shi zai aikata dole ya d'auke 'yarsa daga kauyen nan subar garin, ta haka zata samu yanci tayi rayuwa kamar kowane mutum, ta shaida itama tana da daraja da martaba dan' adam .
*******
KANO TA DABO.....
Had'adden gini ne na zamani, wanda sai wanda yaci ya tada kai da naira zai iya zama mallakin gidan, Tsaruwar wajen gidan kad'ai abun kallo ce, kama daga furanni da itatuwa da akayi wa bakin gidan ado dasu, kai hatta fitilun k'ofar gidan abun kallo ne, duk da unguwa ce ta masu hannu da shuni wato nasarawa gra, Gidan yana cikin gidajen da suka amsa suna a layin da unguwar ma baki d'aya, Tsadaddan mota ce kirar BMW X5 a bakin gate, sake horn yayi a karo na biyu, Fuskar sa na nuna alamar k'osawa da tsayuwar sa bakin gate d'in,
Matashi ne wanda bai fii shekara talatin a duniya ba, ba fari bane sannan bai yi duhu can ba, hancinsa a tsaye yake, saje kad'an da ya kewayar fuska ya k'ara masa, labb'an sa kalar pink wanda suka k'ara k'awata fuskar tasa, Sanye yake da yadi fari mai shara-shara wanda kana hango singlet d'in jikinsa.
A fusace ya zare belt dake zagaye k'ugun sa ya nufi kofar ya sa key
ya bud'e yana k'ok'arin bud'e gate, Sautin kid'an dake tashi ya sa shi waigowa Mota ce k'irar Toyota ta wuce da gudun bala'i tamkar zata tashi sama, Kallo
aya yayi wa motar ya gane mallakin ta, Siririn tsaki yayi ya maida kansa kan gate ya sake kokarin bu
ewa.
Daga ciki aka bu
e wani dattijo ne yace "Tuba nake yallabai Arab Hassan wallahi na shiga ciki ne sam banji karar horn dinka ba." Yayi maganar muryarsa na d'an rawa wanda ke nuni ba k'aramin shakkar sa yake ba haka yana gudun yi masa laifi.