← Book details Mundo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 187

Sashe 39

Mundo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka suka shiga mota ta zabga uban tagumi tana tunani, bakin ciki da takaici duk sun hanata sukuni.
*****
Ganin su Ilham sunki dawowa ga dare ya yi, yasa ta fito daga
akin sanye da kayan data zo da shi da hijab
in ta, Ummy tun dawowarta tana
aki tana sak
a da warwara, zaman d
akin ya soma isar ta ta taso ta fito falo, ha
uwa sukai da Mun
o zata fita.

Suna kallan juna a hankali Ummy ta sakar mata murmushi, Mun
o kamar an ta
ota sai idanunta suka fara cikowa tana takowa, kusa da ita tazo ta tsuguna tace "Ummy kuyi hakuri aradun Allah ban gane me yace ba sai naji kamar yace ga kayana inji Ummy."
Hannu tasa ta
agota ta share mata hawaye tace "Ba laifinki bane sannan Allah yayi sai hakan ta faru, karki wani damu kinji?

Kuma kema meyasa baki fa
a musu kai tsaye shi ya baki kayan ba?

Dan daga yanda suke magana basu sani ba."
Kai ta girgiza ta kalleta tace "Ina tsoro kar su sake yin fushi suzo miki nan suyi ta fa
Araab da ya taho gun Ummy saboda wayar data mai akan yazo tana son ganin shi ne yaja ya tsaya.

Yana shigowa yaji kalamanta hakan yasa ya kalli yarinyar, a ranshi yace "Shiyasa duk abinda akai bata bari sun san dakanshi ya bata ba?

Ya
auka ta
in hankalin nata na dindindin ne ashe zuwa yake yana tafiya, kuma ashe itace ya gani a hoto dasu Ilham.

Lallai kwalliyar nan na canza mutum."
Ummy ce ta dafata tace "In kinje gida ki kwanta kar kiyi tunanin komai kinji?

Zan samu Kawunki muyi waccar maganar."
Kai ta
aga ta sake cewa "Kuyi hakuri dan Allah Ummy." Tana kaiwa nan ta
ago ta hangeshi a tsaye ya jingina da bango ya sa hannu
aya cikin aljihu yana kallon ta.

Da sauri tai hanyar waje tana ji Ummy na cewa kice driver ya saukeki.

To kawai tace tana zamba
a sauri, tana fitowa tai tuntu
e ta cigaba da sauri ko drivern bata wa magana ba tai waje duk a tsorace.
*****
Mumy kam tun a wurin event ta kira Alhaji Hussain ta fara zayyana masa, suna komawa gida ta sake zuzuta abun ta zayyane masa komai hadda k
ari, shiyasa ta taho kafin a watse.

Saboda tana ji idan bata kai karar ba zuciyarta ba zatayi sanyi ba, Alhaji Hussain nan take yaji zuciyar sa na wani irin k
ona
acin rai ya mamaye sa, ba shiri ya kira Alhaji Sunusi da Kabiru a waya yace suzo yanzun nan yana neman su.
***************
Fuska Ummy ta damke sosai tai tace "Bu
e babban falo Baban ka Husain yana zuwa yanzu."
"Bazasu iya hakura sai gobe ba?

In ma auran ne basa so su ce sun fasa menene zasuzo wa mutane gida yanzu?"
"Ba dai kasan laifinka ba kenan ko?"
Shiru yai dan ya kula ran Ummy a
ace yake matuka, wucewa yai ya bu
e tasa masu aiki su kawo ruwa da juices aka ajiye a falan, alamun shigowar mota taji ta
auka sune sai taga su Ilham, Araab ne ya kalleta akan me Ummynsa da bata rasa komai a rayuwa ba zata dinga tsoron wasu mutane? ransa ne ya sake
aci.

Fitowa yai ya kalli su Ilham da Ikram da suka shigo duk jiki a sanyaye, yace "Kunsan kawarku batada hankali akan me bazaku jadadda mata kayan da zata sa ba?"
"Yaushe aka ce ma batada hankali?

Bayan laifinka ne?

Akan me bazaka kai kayan inda kai niyya ba?

Ko kuma ka kawomin da kanka kafin ka fita?" Ummy tai maganar tana kallon shi.

Shiru yai kawai baice komai ba lalai Ummy yau a wuya take bayasan ya sake
ata mata rai.
aki su Ilham suka wuce suka zauna a bakin gado, kallan kayan Meenal wanda ta cire sukai Ikram tai tsaki tace "Bakin ciki yau kamar ya kasheni, wai muna me duk abin nan ya faru?"
"Duk ba ke kika nace muje muyi pictures ba Allah na tabbatar sun daketa tunda ya Farouq bai gun balle ya fa
a mana, da nasan abinda ya faru kenan ai ko zama baza muyi ba zamu dawo gida."
Kwafa Ikram tai tace "Shiyasa suka dinga mana gani-gani kana magana ana baka amsa kamar ba
a so ashe dalilinsu kenan."
****
Sake bu
e gate akayi Ummy ta kalli Farouq tace "Kaje ku zauna da su Ilham a falon sama karsu sauko har sai na sanar daku."
Kallon Araab yayi wanda ya mishi alama daya wuce, haka ya mike rai jagule, jibi dama zai koma tunda ranar ne
aurin aure, ya kamata ya koma tun lastweek amma ya
aga saboda biki gashi yazo da abubuwan b
acin rai.

Babban falo ya shiga ta waje, daga kallo
aya zaka san cikin rashin arziki sukazo, su uku ne,
aya kanin su Alhaji Husaini ne wanda yake gambon su sunanshi Alhaji Kabiru sai kuma mijin Hajiya Layla wato Alhaji Sunusi.
*****
Shigowa Ummy tai ta zauna akan kujera dake gefe, mai aiki ce ta shigo da fruits ta ajiye ta juya.

Kafa ya
aura kan
aya kafar ya kalleta yana jin tana gaisheshi, Araab ma ya gaisheshi sai dai bai amsa ba sai cewa yai "Banyi niyyar zuwa ba saboda daga ke har wannan
an naki ba wanda nake son gani, ba kuma ba wanda nake san magana dashi."
Nuna Araab yai yace "Kai banda bakada kunya bakasan karamcin da muka maka ba mu zaka tozarta a cikin mutane?

Wace
ar iska ka kawo kuka wulakanta mun iyali na yau?"
Araab zuciyarsa ke tsananin k
ona yayi shiru sanin duk maganar da zata fito bakinsa a hali yanzu ba mai dadi bace, Alhaji Hussain ya sake kallon Araab yace "Dan gidanku ba magana nake maka ba ko sai na tashi na tsinkeka da mari?

Kana ganin wannan ku
in dakai shine zaisa mu kasa hukunta ka ko me?"
Alhaji Sunusi ne ya kalli Alhaji Husaini yace "Yaya ka zauna ayi magana a hankali muji dalili mu kuma san meke faruwa."
"A haka zan zauna yaro karami ina mai magana ya manna min hauka?"
"Araab ba magana yake maka ba?" Muryar Alhaji Kabiru ce ta shigo.

Kallon sa yayi yace "Kawu baka ji yace baisan jin magana daga garemu ba?

Me kuma zamu ce."
"Uwaka zakace dan banza mara kunya, fa
amin yarinyar da kaba kayan ya
ta karuwarka ce ko me?"
"A'uzubillahi Minashaidanir rajeem." Yaya taya zaka jefo Araab da wannan mummunar kalmar?

Naji yayi laifi dan da kace zakazo jira nake kazo na baka hakuri shima ya ba ka hakuri sai dai bansan ta yanda zan
auki kalmar nan ba, zan jure komai amma banda irin wannan."
Araab ne ya kalleta, ya sani sarai Ummy sune rayuwarta akansu ba wahala da tsangwamar da bata sha ba.

"Ni kike fa
awa haka?"
Da fashi Alhaji Kabiru yai yace "Yaya kai da
i na dakai rashin hakuri komai na duniya hakuri ake dashi, ka tsaya mubi komai a sannu."
Zama yayi yana sake cewa "Amma kun dai ji abinda take cemin."
Araab zai yi magana Ummy ta kalleshi wanda yasashi yin shiru ya dunkule hannunsa a saman cinyarsa.

Alhaji Kabiru ne yace "Araab fa
a mana dalilinka na wulakanta Meenal kabawa wata da ba
a sani ba kayanta."
"Ya fara fa
amana wacce
ar iska dai yakai dan ya wulakanta min yarinya." Maganar Alhaji Husaini ce ta sake shigowa ciki.

Ummy kalmar nan ta fara kaita bango yanda ta kalleshi ne yasashi cewa "Banda ma mu uban waye zai auri
an naki?

Ko dan kinga na bashi Meenal kina tunani kowa ma zai yarda ya auri
anki?"
"Menene dashi da har baza'a aureshi ba?"
Alhaji Husaini ya sake hasala lallai yau Ummy neman magana take yana magana tana magana?

Sake gyara zama yayi yace "Kina tunanin har yanzu mutane kyau da ku
i suke dubawa a aure?

To dangi shine abu na farko, kalli gidanki a haka ne ake bikin
anki na farko?

Ba kowa daga ku sai ku?"
Araab ne ya fara shirin magana da sauri tasa hannu saman kafa
arsa wanda hakan ya sashi ji kamar yai ihu dan bakin ciki.

Ummy tai murmushi tare da ha
e hannaye tace "Koma menene kafi kowa sani yanda akai na zama zuri'arku, sannan gori Yaya ai kai zamuwa da kuka zame baku bar
an uwan mahaifinshi sunzo nan ba."
Tsaki yaja yace "Zancen banza da wofi kike, uban waye zaizo gida ba tarbiya?

Daga ke har
anki, shiyasa har yau muku zargin
an biyun nan ba jinin mu ba......."
Hannu ta
aga mai tace "Dakata dan Allah Yaya, wai ku zaman lafiya ne bakwaso ko kawai dan kunga ina shiru shi kenan sai na zama
ar iska?

Wallahi kul ka sake shegantamin yara, sannan kunsan da haka kuka bamu auran
ar taku?

Ko mu kukaga muna binku akan auran?"
Baki dukkansu suka saki Alhaji Kabiru yace "Mu kike fa
awa haka?

Naji Ya Husaini yayi laifi amma taya zaki mana magana haka?"
"Wai me muka tsare muku?

Ku kawai zaman lafiya ne bakwa so muyi daku?"
"Ehhh lallai yau kin tabbatar mana da tsintacciyar mage bata mage na tabbatar da ha
in bakinki aka tura karuwarsa gun bikin ya
ta dan a tozarta mu to kanku kuka tozarta na kai karuwa."
Ummy ta shafi fuskarta da tafin hannayenta tace "Allah na gode maka da ka nunamin abinda na kasa gani, ban ta
a zatan tsanar da kuke mana har takai haka ba."
Alhaji Sunusi yace "Ku tsaya karfa garin gyara....."
Katse shi Alhaji Husaini yai yace "Haka kika ce?

To ni kuma zanga uban da zai baki
arsa, na baki nan da wasu 'yan awani ki zo dake da
anki ku nemi yafiyar duka kalaman da kuma fa
a mana in ba haka ba mun janye auren nan."
Mamaki ne ya kama Ummy, tace "Kana nufin auran jibi sai ku fasa?
Chapter 39 · 0% Book details