← Book details Mundo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 187

Sashe 15

Mundo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Salame ta
ago ta tare da jawota suka shiga cikin gidan, Mun
o kam binta kawai take zugum-zugum kamar wata igiya.

Suna sake shiga ta sake rungumeta tana sake kakalo kuka ta
ago ta kama fuskarta tace "Tsakani da Allah su Maccido suna ina aka barmana ke kika koma haka?

Ji yanda kika dafe kikai baki bayan ke fara ce sol."
Jauro dake tsaye a kofa ya zuba mata ido yana kallan rainin wayaun Salame, matar da ko Mun
o bata ta
a gani ba itace take magana haka?

Hannayenta ta kamo tace "Nan gidan ku ne, karki damu ki saki jikinki kiyi abinda kikeso kinji ko?"
Yanzu kam tunanin Mun
aya lalai wannan matar mamantace da ba wanda taji ya ta
a zancenta, to sun san tana nan meyasa ba wanda ya kawota sai yanzu?

Salame kam ganin tayi nasara dan tun daga yanda Mun
o ke kallanta tasan an dace hakan yasa tace "Jikinki ma da dumi kamar bakya jin da
i ko?" Kai ta girgiza alamar a'a, tace "Danejo ta baki wasu sako tace ki
oye ne?

Ko in kinzo nan ki bani ko karki bani?"
Kai ta sake girgizawa tace "A'a bata bani komai ba."
Shafa kanta tai tace "Dama dai tambaya ne nasan ba lalai ta baki ba, yanzu dai muje ciki kiyi wanka kici abinci mu zamu
an killace dabobin nan ne." Ganin Salame ta sake ri
e hannunta yasa tabi bayanta duk kuwa da tsoron dake cinta.

A cikin gida kuwa Bilal ne yasha riga da wando irin crazy
in nan, headphone yasa a kunnensa yana d'an jin disco yana d'an takawa, drawer ya jawo dubu
arin nan ya d'auko ya jujuyata a san samunshi yaje ya cilawa wannan yaran amma kuma maganar gaskiya yana da bukatarsu dan har yayi cinikin wani takalmi da zai siya.

Tsaki yai yace "Haba kai bawa kullum cikin talauci babu wani farin ciki?" D'akinsa ya kalla wanda yai kacha-kacha, ya sake jan tsaki yace "Dole yarinyar nan ta gyaramin d'aki tabi ta raina mutane tanajin kanta kamar wata babba."
Yana fitowa ya tadda Raheena a kitchen ta soya kwai ta dafa indomie "Nima zuba min dan dama banajin shan shayin nan wallahi."
Bata ko kalleshi ba ta
auki kwananta tana neman fita, a fusace ya jayo rigarta ta baya ta dawo inda yake yace "Ke dan abu ta kazar ubanki ni zan miki magana ki maidani wani shaho?

Bakiji me nace miki bane?"
Cike da tsiwa tace "To ku
inka ne ko nawa?

Naga nima da kudina na siyo na dafa ko?"
Nan da nan ya fusata ya nunata da yatsa yace "Ni kikewa magana a haka?" Harara ta zabga mai tace "An fa
amaka
in karya nai ko kai ka bani ku
in?"
Ai nan ya kara hawa yayo kanta iya karfinsa, da gudu ta bar gun, zaro wayar dake bayan socket yai ya fara binta yana cewa "Wallahi yau sai kinsan ni kikaiwa magana a haka, ni sa'anki ne?"
Muryar Salame sukaji tace "Bakuda hankali ne?

Ba na fa
a muku inada baki ba a gidan?" Daidai nan Mun
o ta leko ta bayanta, ai tana ganin Bilal da bulala yasa jikinta ya hau rawa tunowa tai da yanda take shan duka a rigarsu, neman kwace hannunta tai daga hannun Salame wacce tai sauri ta rungumeta cikin
acin rai ta musu alama da ido, Bilal ya kalleta bayan ya ajiye bulalar yawa Mun
o wani kallo sama da kasa nan danan ya sa hannu ya toshe hancinsa yace "Ke kuma kwashe-kwashe kika fara yi ne?

Wannan dai daga ganinta a bola kika samota."
Raheena ta kalleshi tace "Ko gidan mahaukata ba?

Kalli dai kafafunta kamar almajira."
Salame ta musu dakuwa da hannu, cikin magana mara sauti tace "Ku bari ko ranku duka ya
aci akan yarinyar nan."
Juyota tai ta dawo inda take tace "Wannan Raheena ce ta yayarki gatanan ta girmeki sosai ita shekarunta ashirin da biyar, shi kuma wannan yayanki ne sunanshi Bilal shekarunsa talatin da
aya.

Su biyu ne yarana."
o ta kallesu cikin rawar murya tace "Ina kwana?"
Takaici ne ya hana Bilal amsawa, ina Umma ta samo wannan kazamar yariinyar kuma?

Badai kwana zatai a gidansu ba ko?

Tsaki yaja kawai ya nufi
akinsa, itama Raheena
akinta tai cikin kunar rai.

Dariya Salame tai tace "Karki damu haka suke muje ki cire kaya kiyi wanka sai nazo na baki abinci kici ko?"
Ita dai kawai binta takeyi ta kasa ko magana, ganin sun shiga
akinta yasa Raheena tace "Umma me kike shirin yi haka ne?"
Salame ta harareta tace "Wanka zatai sannan ki duba kayanki ko duguwar riga ce ki bata ta saka kafin a mata
inkuna itama."
Zani ta
aukar mata tace shiga ban
aki gashinan ki watsa ruwa.
auka tai ita dai ta nufi inda Salame ta nuna mata ta rufe
ofar, kallan ban
akin tai baki a bu
e tana jin wani mugun tashin hankali, itadai bata gane komai ba dan bata ta
a ganin irin wannan ban
akin ba tunda take a duniyar nan, to ina ruwan wankan yake?

Su ko fanfo basu dashi a rigar su banda bohol na tuka-tuka da ta ta
a ganin a kauye to gashi nan babu shi a cikin
akin nan.

Kallan
an farin randar tai nan da nan tace "Oh su tasu randar fara ce ashe.

Tsugunawa tai ta
ebo ruwan dake cikin toilet seat da hannunta ta wanke fuskarta kasa wanke jikinta tai saboda ruwan sam baya debuwa da kyau, ajiyar zuciya tai tace "Hala waccen mai fad'an ce ta karar da ruwan gidan? ita kuma matar bata san an karar ba tace na shigo?"
Idanunta ne suka kai wajan madubi wanda duk ya farfashe kawai ta hango fuskarta a cikinsa, hangota tayi kamar wata aljana tayi saurin rintsa ido tana matsewa jikin bango saboda madubin ya lalata kamaninta, ajiyar zuciya tai ta sauke idanunta akan wata roba mai murfi fara, nan taje ta bude murfin da karfi, nan danan dadi yazo mata tace "Baffa aradun Allah akwai ruwa." Nan ta d'ebi ruwan ta watsa."
*****
aki kuwa Salame ce tasa cokali taci indomie
in nan spoon biyu sannan tace "Ba jiya na fa
a miki mu
n kusa yin arziki ba ko kin manta ne Raheena?" Raheena cikin rashin kunya tace "Amma wannan mai kama da mahaukaciyar itace mai arzikin ko me?

Sam na kasa ganewa."
"Kici abinci kije waje kiga dabobbin data taho dashi, ke dai yanzu kiyi lissafin abubuwan da kikeso na gyaran
aki dan bene zamuyi a gidan nan,
akinki zai koma sama wannan kuma sai ki bar mata." Ido Raheena ta zaro tace "Wai Umma da gaske?"
"Kina tunanin ina aikin banza ne?

Matsala
aya ubanta yasan gidan nan kar mu cinye kudi yazo ya tada mana hauka dan Allah ba hakuri garesu ba, wallahi zai sa mana adda a wuya."
Raheena ta cigaba da cin indomie
inta tace "Umma kisamo hanyar da bazai samu yazo ba shikenan dan ni wallahi inada abubuwan da nakeso sosai."
"Kibar komai a gurina kedai ki samo mata riga ta saka sannan ki
an dafa mata indomie
in mana in kinada ragowa."
Kai ta girgiza da sauri sannan tace "Allah a'a tasha shayi su dama ai basu san komai ba sai shayi da bread.

Nifa Allah ko yanzu bazan iya kwana da ita ba, kalli jikinta fa Umma?
akin nan tunda ta shigo yake warin dabobbi."
"To kuwa sai dai kisan yanda zakiyi amma dole anan zata kwana."
Baki ta taro tace "Ni dama akwai bikin da zamuyi yau sai jibi za'a gama kafin na dawo tabarmin
akina gaskiya dan bazan iya zama da ita ba."
Salame idanta nakan Raheena tace "Kinsan dai na fa
a miki ba inda zakije sai kin dire ragowar ku
in nan ko? ehe sai kin diresu karma kiyi tunanin zan saurara miki." Abinda tace kenan ta fito daga
akin dan ita yanzu burinta suje a saida dabobbin nan dan da itama za'a bazata iya barin Jauro yaje shi ka
ai ba.

Sam ta manta da Mun
o a ban
aki kawai ta fito tasa Jauro a gaba suka shiga motar Kabir Dogo suka nufi kasuwa tana tafe tana tunanin abubuwan da zata siya da kuma yanda zata hana Maccid'o zuwa birni.

A can gida kuwa Raheena tana gama cin indomie ta fito falo ta zauna, wai warin jikin Mun
o ya isheta, ita kuwa bayan ta ga dai tabbas ruwan farar randar nan da ta gani ya kare ko wankan ba tayi ba kayan data cire ta
auka ta sake maidawa dan haka suka saba yi dama tun a can rugar, tazo bu
e kofa ta kasa, dan
azu da zata shiga kofar a
an bu
e take sam batasan wai hannun kofar za'a mur
a ba itadai tayi ta turawa iya karfinta ta kasa nan da nan yanda ake rufeta a
aki a kauye ya dawo mata cikin kanta, tsugunawa tai kawai tasa kanta a cikin cinyoyinta tana kiran sunan Baffanta.

Bilal ne ya cilowa Raheena leda ba
a kan cinyarta, ta kalleshi tace "Na menene?"
"Tashi ki dafamin kafin na gama shirin fita sannan Allah karki cika maggi a suyar kwan."
Kamar zatai magana sai taga kamar idanunsa sun
an yi ja da alama
an fitar da yai sai daya sha wani abin kafin ya dawo, saboda tafi kowa kuma sanin abinda yake in har hankalinshi baya jikinsa yasa bata yi masa musu ba.

Yaje wucewa yaji alamun kuka ta
akin Raheena, takaici ne ya kamashi yai kwafa yace "Ai ko menene dole Umma tazo ta sallami wannan masu zubin ragunan dan tabbas bazan barta a gidan nan ba."
Kamar zai wuce kawai yaji dole ya leka dan yarinyar nan yana san sanin daga ina take sannan kudin da akace tazo dashi ya amshi rabanshi kafin nan.

Kofar ya tura jin kukan daga band'aki yasa ya karasa yace "Ke dalla uban ke kikewa mutane?"
Jin mutum yasa ta mike tace "Dan Allah a bud'e min kofa." Cikin hausarta ta rabi filo.
Chapter 15 · 0% Book details